Rumbun Qaya Page 46

Rumbun Qaya Page 46

 

Rumbun Qaya Page 46

RQ

      Page 46

***

"Kina da alwala?" Yace yana rike hannun ta cikin nasa. Da kai ta amsa masa yace ta tashi suyi raka'a biyu su godewa Allah. A take wani novel da ta karanta ya fado mata da irin hakan ta faru abinda ya biyo baya. Kasa boye tsoron ta tayi har sai da ya dakata da kokarin shinfida sallar da yake ya zuba mata ido.


"Raihana?" Ya kira sunan ta yana dawowa wajen da take tsaye. 


"Menene? Me yasa duk kike a tsorace?" 


"Ba..ba komai." Tace ba wai dan babu koman ba. 


"Please ki kwantar da hankalin ki, ki saki jikinki dan Allah."


"Tohm." Tace da sauri


"Me kike tunani?" 


"Ni ba komai."


"Tom, koma menene kike tunani ki daina, ki nutsu sallah kawai zamuyi mu godewa Allah, sai ki bani labarin abinda ya faru bayan na dawo, shikenan sai muyi bacci."


"Tom."


Ta sake cewa tana jin tsoron na raguwa zuwa kaso tamanin duk kuwa da tasan zai iya fada mata kawai dan ta nutsu amma kuma sai taji ta dan samu nutsuwa ko da babu yawa, saboda muryar sa da yayi maganar bata nuna da wasa yake ba. Daga gefen damar sa ta tsaya sukayi raka'a biyu sannan yayi musu addu'a sosai har sai da ya fara bata mamakin yadda yake zubo addu'oi babu kakkautawa wanda ya haifar mata da wata irin nutsuwa a tattare da ita. 

   Bayan sun gama ta ninke abun sallar ta ajiye su a wajen da taga yana ajiye su sannan ta tsaya daga tsaye ba tare da ta cire Hijab din ba bata kuma zauna ba. Be lura da ita ba dan yana idar wa toilet ya nufa yaje ya wanko bakin sa da mouth freshner me kamshin mint bayan yayi brush sannan ya watsa ma jikin sa ruwa dan ba karamin jin zafi ne dashi ba shiyasa idan zafi yazo baya gajiya da watsa ruwa, ba kuma ya taba kwanciya da riga a jikin sa haka zai kure AC ya baje haka ka'idar sa take tun da ma. Yanzun ma hakan ce ta faru bayan ya watsa ruwan ya fito daure da towel din ta yi saurin janye idon ta daga kallon sa dan ta lura ko kifi ba zai nuna masa son ruwa ba. Taune leben sa na sama yayi ya nufo ta gadan gadan kamar wanda zai cike jikin ta, sai kuma ya tsaya a daidai gabanta ya yarfa mata ruwan hannun sa a fuska.


"Matsoraciya, jeki yi wanka kizo mu kwanta."


"Nayi dazu ai."


"Yen yen,dirty girl, na dazu ai ya yi expire."


"Allah be ba, ni bana son nayi yanzu."


"Kina so nayi miki?" Ya kakantar da muryar sa ya fada kamar rada.


"A ah, zanyi da kaina." Tace da sauri tana kokarin barin wajen


"No bari dai nayi miki,karki sha wahala."


Yace yana riko da jikinsa, rikon da yasa ta jin wannan abun da take ji a duk sanda suka samu body contact. 


"Wallahi tallahi zanyi da kaina,."


"Muje toh kiyi na gani, na tabbatar kin iya din." 


"Na shiga uku, dan Allah kayi hakuri."


"Ba zan hakura ba, komai sai ace na hakura ni yanzu dai bazan hakura ba, muje kawai."


Ya rike ta gam ya nufi hanyar toilet din da ita, kwalla ce ta fara sakko mata daga idon ta, ga wani tsoro da ya mamaye ta, ya bud'e toilet din ya shigar da ita, ya tura kofar da kafarsa. Rufe idon ta kawai tayi kam ya juyo da ita tana facing dinsa sosai, ya kama zip din rigar tata ya shiga ja a hankali yana kallon fuskar ta da ta soma hawaye. Sai da ya kawo zip din kusan kasan kirjin ta sannan ya tsaya chak yana kallon halittar Allah,a cike suke taf gasu farare ta saka musu white bra me adon lace a jikin saman. 


"Beautiful." 


Ya furta cikin muryar sa da ta soma shigewa ciki sosai saboda wani yanayi da ya shiga lokaci daya. Hannu ta saka zata ja rigar sama yayi saurin rike hannun nata abunda ya ja rigar ta subce daga hannun sa tayi k'asa gaba daya. Kicin-kicin kwatar hannun ta, ya hanata ta hanyar rike hannayen nata duk biyun sannan yace.


"Idan baki nutsu ba zaki jawo na karya alkawarin da nayi,."


"Dan Allah kayi h..." Bata karasa ba yayi mata wata irin runguma da karfin gaske, jikinsu ya hadu waje daya a tare suka ji wani irin abu kamar electric shocking, bakin ta ya laluba ya hade shi da nasa waje daya ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. Kusan minti biyar ya dauka a haka yana jin tamkar notikan kansa na kukkuncewa, ya damtse idon sa sanann ya hau girgiza kansa. A hankali ya saketa tayi saurin daukar rigar ta hau kare jikin ta da yake rawa kamar mazari. Wajen shower din ya nufa ya kunna ruwan sanyi ya sakar wa kansa hade da sauke ajiyar zuciya da karfi. Fita tayi da dan gudun ta, ta yi saurin zura rigar ta koma jikin gadon ta tsaya kafarta sai wani irin rawa take kamar mazari. Fitowa yayi daure da wani sabon towel din idanun sa da suka dan yi ja ya zuba mata jikinsa yayi masifar weak a hankali ya motsa bakin sa yace


"Je kiyi wankan."

 

 Wuce shi tayi ta shiga toilet din, shi kuma ya fice daga dakin ya sauka k'asa gaba daya. Da sanda ta fito da ta ga baya nan tayi saurin daukar rigar da ta cire ta mayar ta haye gadon ta dukunkune waje daya ta rufe idon ta. Ya Dade a kasan be dawo ba ya zauna zaman duba wani abu a system dinsa yana yi yana shan black tea ga wani irin dum da kansa yayi masa, abinda ya hanashi shigowa dakin kenan har sai da ta gaji da kallon hanya ta hakura tayi bacci a sake da tunanin ba zai dawo ba watakila. Ta dade da baccin ma sannan ya hauro saman ya shigo dakin ya hange  ta kwance ta rungume pillown sa a jikinta rigar ta tattare har wajen cinyar ta a waje tana bacci cikin kwanciyar hankali wanda ma baki daya ta manta a in da take. Kashe hasken dakin yayi ya dan haska da flashlight din wayar sa ya karaso ya hawo gadon ya kwanta a gefen ta yana kallon fuskarta. Ta rame sosai ba kamar sanda tana zuwa aiki ba, sai dai ta kara haske sosai sannan tana dauke da wannan innocent look din da ya fara gani a tattare da ita ranar da ta kawo request letter dinta, da yanayin yadda tayi a lokacin da yace Kamal yayi rejecting dinta kawai. Murmushi yayi ya kai hannu ya gyara mata gashin ta da ya dan tattashi ya sakko saman goshin ta sai ya ji kamar zufa take yi, karo karfin AC yayi dan dama itace ta rage ya kwanta rigingine yana kallon saman dakin domin sam babu bacci a idon sa har lokacin. Ya dade sosai a kwance ganin yadda ta ke ta juye-juye yayi tunanin ko sanyin dakin ne yayi mata yawa kuma, sai ya mike ya jawo standing fan ya jona a jikin socket ya kunna ta daga dan nesa da gadon ya rage AC zuwa low sannan ya kwanta yana jawo ta jikinsa gaba daya ya rungume ta tsam tsam.

   Ita ta fara tashi da asubah ta ganta kwance jikinsa rigar jikin ta a bud'e zip din har k'asa. Da sauri ta jawo ta ta gyara ta tashi ta zauna a daidai lokacin ya bud'e idonsa ya ganta zaune a gefen sa, ya mata murmushi bayan yayi salati ta mayar masa tana sunkuyar da kanta a kunyace. Tashi yayi ya zauna ya jingina da pillow kusa da ita.


"An kira sallah?" Yace mata ta daga kai sai ya hau sakkowa a hankali daga gadon sannan ya fita daga dakin bayan ya kunna mata hasken dakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta mike zuwa toilet ta yo alwala hade da brush sannan tazo ta shinfida sallaya ya shigo yana gyara hannun jallabiyar sa fara kansa sanye da tashi kafiya naci yayi shirin zuwa masjid sai kamshi yake, ka'idar sa ce in dai zai je masallaci sai ya fesa turare ko da kuwa ba wanka yayi ba, shiyasa kullum cikin kamshi yake hakan kuma da yake sunna ce me kyau domin ba zai je masallaci ya cutar da wani ba.


"Ok na zata komawa kikayi, naje masjid toh."


"Ok." Tace a hankali ya juya ya fita ita kuma ta kabbara sallarta. Ko da ya dawo sai ya tsaya wajen Baba maigadi yayi masa maganar gyaran gidan da yake so ayi, so samu a gama magana da masu aiki su fara aikin ko zuwa jibi ne. Maganar ta zaunar dashi sosai dan har ta gyara dakin ta fesa air freshener da ta gani a kayan toilet din. Toilet din ta shiga ta fara wankewa ya shigo, tsayawa yayi cike da mamakin ta, haka ake dama? Kamar wadda aka turo aiki daga zuwa sai ta fara aiki. Toilet din ya bita ya sameta tana wankewa ya dago ta, ta hanyar riko waist dinta ya mikar da ita tsaye yana hararar ta.


"Waya saki?" 


"Ba kowa."


"So kike Hydar yace na bawa kanwar sa aiki ko?"


"Wanke toilet din?"


"Ehen, matsa kiga na wanke." 


Ya matsar da ita gefe ya dauki abun wankewar ya shiga wankewa. Kana gani kasan be iya ba, be saba ba da ma dai shara ce yanayin ta sosai dan baya ma jira ayi masa, toilet ne dai yake sawa a wanke masa. Tana tsaye ya yi abinda zai yi yace ya gama ya jawo ta suka fito ya rufe toilet din lokacin kusan bakwai da rabi. Kwanciya yayi yace tazo su kwanta taki ta fice ta barshi a dakin, alarm yasa zuwa karfe tara saboda yana so ya je office yaga wani aiki, sannan zasu hadu da Barrister Awais ma akan maganar case din nan. 

  Kitchen ta wuce kai tsaye bayan ta sakko ta tarar da Baba Hajara matar Baba me gadi a kitchen din tana goge goge kofar bayan kuma a bud'e da alama ta nan din ta shigo. Gaisawa sukayi a sake don ta gane ta, ta amsa tana mata sannu da aiki. Tayata zatayi ta hanata tace ta barshi, maimakon ta tafi sai ta tsaya a kitchen din suna yar hira kad'an kad'an har ta gama ta shigo falon zata gyara ita kuma Raihanan ta wuce dakin k'asan da suka fara zama ta saka key a kofar ta fada wanka, ta gama ta fito ta shirya cikin wata riga da skirt din atamfar ta sea green da orange dinkin fitted sannan ta warware gashin kanta ta taje shi ta saka masa mai ya kwanta, ta daura dankwalin normal dauri sannan ta ciro orange veil ta dora akai ta fito kafarta ta sanye da flat shoe. Baba Hajara ta gama aikin har ta fita sai ta zauna a falon rike da wayar ta, data kunna ta tana son kiran Daadah. Bayan sun gama wayar harda yar kwallar ta sai taji ana knocking. Ta tashi tana gyara mayafin jikinta sannan ta karasa ta bud'e. Baba me gadi ne ta gaishe shi a mutunci sannan ta karbi basket din hannun sa ta shigo dashi ciki. Breakfast ne daga gidan ya Nabeela sai ta kai kitchen ta dauko basket din jiya da aka wanke kayan ciki ta mika masa ya bawa driver da ya kawo ita kuma ta dawo ta samu plate ta zuba pepper soup din da chips ta hada da tea ta zauna a kitchen din taci sannan ta dawo falon. A shirye ya fito cikin shigar navy blue yadin filtex. Kansa sanye da hula dark and navy blue sai takalmin kafarsa sau ciki shima navy blue. Shigar tayi masifar karbar sa sai walwali yake fuskar sa a sake ya karaso falon idon sa akanta. A kusa da ita daf ya zauna har kafadar shi na gogar tata, kamshin turaren sa na Hugo Boss ya hadu da nata turaren black oud ya bada wani kamshi me sanyin dadi.


"Good morning my wife."


 Yace yana dan ture kafadarta da tasa, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa dan bata jure kallon idon sa ta gaishe shi ya amsa sannan ya dora da korafin kin tayashi baccin kuma ta barshi har zai makara. Murmushi kawai ta sanar dashi an kawo breakfast yana kitchen sai ya kama hannun ta suka nufi kitchen din ya haye kan dinning din ya nuna mata alamar ta basu breakfast din. Zuba masa tayi daidai daidai Kar ma yace yayi yawa sannan ta dauko mug zata hada masa tea yace karta hada dashi ta ajiye yace tazo suci. Girgiza masa kai tayi tace taci yace be yarda ba sai da ta nuna masa plate da cup din dan dama saboda hakan taki wanke su sannan ya kyale ta, ta wanke su a sink ta ajiye yana kallon ta yana cin abincin sa hankali kwance sai da ya gama tas tana wajen sink din kamar me neman abu, ta bayan ta ya zagayo ya ajiye plate din sannan ya dora kansa a saman kafadarta ya shaki kamshin jikinta


"Ki rage kunyar nan dan tayi yawa."


"Kinga ba dan kin saka turare me kamshi ba, kin saka kuma wannan fitted rigar da kin rakani office."


"Zan chanja Allah." Tace da sauri dan har ta hasaso ya barta ita kadai a gidan nan duk da akwai mutane a bq amma ba ai ba zuwa wajen su zatayi ba.


"Yi sauri toh, ina jiranki a falo."


Ya saketa ta juya da sauri ya bi bayan ta da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a cikin kansa. He can't wait. Kad'a kansa yayi ya koma falon yana zaune suna waya da Kamal yana tsokanar sa ta fito tasa black abaya da medium veil, kallon sama da kasa yayi mata ya gamsu da shigar sannan ya dauke idonsa daga kanta ya karasa bawa Kamal din amsa sannan ya katse wayar yana mikewa.

  Hannun sa cikin nata suka fito compound din gidan in da motar sa take ya bud'e mata ta shiga sannan ya zagaya ya shiga shima ya kunna motar, da sauri Baba maigadi ya bud'e musu kofar yana daga musu hannu suka fita daga gidan. 

   Babu wanda yasan da labarin auren a office din dan haka ne ma ko da suka shigo hannun sa cikin nata ya saka kowa mamaki, musamman su Zainab da mutuwar zaune kawai sukayi ita da Cynthia. Be ko kalle su ba ya wuce kai tsaye office dinsa hannun sa har lokacin yana cikin nata, ita duk kunya ta cikata sanin cewa basu san me ya faru ba amma kuma shi ko a jikin sa ya shige office din yana shiga ya nuna mata kujerar sa yace ta zauna ya zare hular kansa ya ajiye ya dauki wayarsa ya kira reception din, Cynthia ce ta daga dan Zainab ta masifar rud'ewa tsoron abinda ta gani da abinda take tunani ya hanata komawa ma ta zauna a wajen zaman ta. Duk dadewar da tayi tana aiki a company saboda Aryan din ne, wani irin son sa take tun ganin farko da tayi masa a lokacin suna jamia da ya zo wajen wani lecturer dinsu tun daga lokacin take bibiyar sa har sai da ta samu nasarar fara aiki dasu kuma tayi kokari sosai ta shiga jikin sa dan kafin zuwa Raihana yana sakewa da ita ko da babu yawa hakan kuma ya fiye mata komai sai gashi cikin kankanin lokaci rayuwar ta na neman dagulewa akan karamar yarinyar da bata shige sa'ar kanwar kanwar ta ba. Umarni ya bayar akan kar wanda ya shigo masa office sannan ya katse Cynthia da ta daga wayar ta kama baki tana kallon Zainab din


"Oga yace kar wanda ya shigo masa office."


"Na shiga uku."


"Akwai matsala fa zee, yarinyar nan dai ta gama siye zuciyar sa wallahi, hannun su fa hade da juna suka shiigo babu ko kunyar idon mutane duk da babu wanda yasan alakar dake tsakanin su, ya bani kunya sosai wallahi."


Ita dai zee bata da bakin magana ita kadai tasan abinda take ji dan ta tabbatar babu yadda za'a yi Aryan ya riko hannun yarinyar haka babu wani dalili. Ita kanta ta sha gwada shi da shigar da bata dace ba amma be taba ganewa ba ma dan sai ta shiga office din su gama magana be ko daga kai ya kalle ta ba.


"Yarinyar nan Allah sa oga ba auren ta yayi ba." 


"Haba aure? Haka ake auren zee?"


"Nasan abinda yasa nace haka."


"Toh, zamuji ko ma menene." 


Tace tana komawa seat dinta dan ta lura kamar Zainab din bata cikin hayyacin ta.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post