Rumbun Qaya Page 47

Rumbun Qaya Page 47

Rumbun Qaya Page 47

RQ

         Page 47

***System din tasa ya kunna yana daga tsayen ya hau duba abinda yake son dubawar. Tana zaune a kujerar sa tana satar kallon sa, yadda yaci serious sosai yana aikin be san tana kallon nasa ba. Dagowa yayi bayan yaga duk bayanin da yake son gani din karaf ya kamata tana kallon sa, wata irin kunya ce ta lullube ta, tayi saurin sunkuyar da kanta yayi murmushi yana takowa wajenta.


"Kina bukatar wani abun ne?" Yace yana dafa saman kujerar da take zaune. Girgiza masa kai tayi alamar a ah


"Kallon mijinki kawai kike yi? Kinga handsome guy ko?"


"Ni a'ah, aikin fa nake son ganin."


"Ba wani, kina satar kallona fa tun dazu na ganki."


"Ni ba haka bane ba." Tace tana yunkurin mikewa. Hannu yasa ya maida ita baya ta zauna a kujerar yayi mata rumfa yana kallon cikin idon ta


"Ina zaki?" 


"Office dinmu zanje, abu zan duba."


"Baki da wani office da ya wuce nan ai,." Ya nuna kujerar da take kai yana sake matsota. Dauke kanta tayi ganin yadda ya zo daf da ita kamshin oil turaren ta na touch yana shigar masa hanci. Saman hancin nata ya ciza kad'an yace 


"Battery na ne yayi low, shine nake son nayi charge saboda yadda aikin zai tafi sosai."


"Na'am?" Tace cikin rashin gane abinda yake nufi da b3.


"Bari kiga." 


Yace yana mikar da ita tsaye, ya jawota jikinsa sosai tayi saurin kulle idon ta,saman lips dinta yayi kissing a hankali yana cigaba da kallon kyakkyawar fuskar ta zuwa lips din nata da shine abu na biyu da ke jan hankalin sa a jikinta. Bakin nasa ya kai kan nata ya soma kissing dinta gently, da sauri ta rik'e wuyan rigar sa jin yadda abun ya shiga kanta har zuwa kwakwalwarta ya chakude da wani irin mixed feeling. Rik'e shin da tayi ya bashi damar yin yadda yake so da ita domin ya samu full support din da yake so ya cigaba da kissing din nata yana wasa da harshen sa a cikin bakin ta cikin wani irin salo da shi kansa be san ya iya shi ba. Knocking akayi a kofar yana ji amma be fasa abinda yake yi din ba, sai da aka kuma kwankwasawa sannan ya cikata yana jan tsaki da dan karfi. Yasan Kamal ne kadai zai iya zuwa bayan ya bada sakon kar wanda yazo masa office. Kallon gaban rigar sa yayi ya kalle ta sai yayi murmushi kawai ya kama hannun ta ya bud'e kofar da take cikin office din, dan karamin daki ne dauke da couch da fridge sai toilet a ciki. Ya sha kwana a ciki idan yana son karasa wani aikin. Suits dinsa ne guda biyar ya rataye jikin wata hanger. Zaunar da ita yayi a gefen couch din, ya zare rigar jikin sa ya ajiye a gefen ta ya dauki silk long sleeve black ya dora akan wandon yadin sannan ya fito ya karasa gaban kofar ya bud'e yana matsa masa hanyar.


"Shiru inaa ta knocking, wannan dressing din fa?" 


"Wanne zan amsa?"


"Dukka." Yace yana shigowa ciki


"Kai da aka kawo maka amarya menene na fitowa aiki haka?"


"Akwai abinda dole sai nazo, maganar kayan da zasu karaso gobe ban saka hannu ba bare a fitar da kudin, sannan akan case din nan, zamu hadu da Barr. Awais shima."


"Ok, nima kuma tafiya zan."


"Please ka ajiye aikin nan, kazo mu zauna anan kawai."


"Toh haka ake ajiye aiki kai tsaye? Aiki ma irin namu me sarkakiyar tsiya, ko zan bar aiki sai an bi matakai masu yawa."


"Haka ne, yanzu yaushe zaka wuce?"


"Next week zan tafi in sha Allah."


"Ok, Allah ya kaimu."


"Ya kanwar tawa? Hope dai babu wata matsala."


"Eh babu."


"Man, karka je ka wahalar da yarinyar mutane ba, yawwa."


"Ni me zanyi?"


"Na sanka ne, yanzu sai kayi abu kai tsaye, dan yanayin ka na jiyan nan ni kadai ina zaune na dinga tunowa."


"Hmm. Ni yanzu bayan an min auren har zaman auren za'a koya min?"


"Emana, karka wahalar ma mutane da yar su."


"Ina Haydar?"


"Be kirani ba, kila ba da wuri zai wuce ba, ko kuma ya fasa, kaima naji Ya Nabeela ta kira sweetheart tace ta shirya zata zo ta dauke ta su tafi gidan naku."


"Tana nan ai."


"Wa din?"


"Wadda zasu je wajen nata."


Dariya Kamal ya kwashe da ita, ya nuna Aryan da hannu yana sake kyalkyalawa.


"Abinda ya faru da rigar ka kenan?"


"Ban sani ba, kaga ni yanzu aiki na ya tsaya gashi da wuri nake son mu tafi."


"No wonder naga mutuniyar ka hankalin ta a tashe, kamar ma kuka tayi,."


"Wa?"


"Z..." Da sauri Aryan ya tare shi


"Forget it, yanzu zan cigaba da aiki, sai anjima?"


"Wanne aikin a ciki? Na office ko na..."


"Na abinda yazo kanka." 


Dariya kawai Kamal yake sosai, har ya fita cike da mamakin Aryan din. Murmushi ya samu kansa da yi ya koma wajen wayarsa ya dauka ya kira Ya Nabeela yace mata kar suje gidan zasu zo tare anjima kad'an. Bar ta yayi a ciki ya karasa aikin da yazo yi dan ya lura idan ya biye mata ba zai aikin ba. Cikin minti talatin ya kammala ya rufe komai ya kashe computer ya bita ciki. Ya sameta a zaune tana danna wayarta tana ganin shi ta mike tsaye. Kofar ya rufe ya shigo ciki ya wuce wajen kayan nasa ya dauki wandon suit ya hau zare na jikin sa zai cire. Saurin dauke kanta tayi daga bangaren sa, yana sane yayi mata haka dan yaga yadda zatayi, ta kuwa bashi dariya ganin yadda ta kauda kai da sauri. Cirewa yayi ya saka na suit din ya ninke wanda ya cire din kamar yadda yaga ta ninke masa rigar ya hada su waje daya.

  Tare suka sake fitowa wannan karon ma sai da ya rike hannun ta duk da zillewar da ta dinga yi dan har ga Allah kunya take ji sosai. Office din Kamal ya nufa da ita ya tura bayan ya kwankwasa suka shiga. Waya Kamal din yake amsawa yana jikin window yana kallon harabar wajen. Shigowar su ta sashi juyowa yayi sallama da wayar. Gaishe shi Raihana tayi ya amsa fuskar sa dauke da murmushin farin ciki sannan ya dora da


"Ya bakunta? Hope babu wata matsala."


"Babu." Tace a kunyace.


"Zamu wuce, na kira ya Nabeela nace zamu zo gidan nata, ka kira Madam sai mu biya mu dauke ta mu wuce tare ko?"


"Wa zai shiga motar newly weds? A barmun baby na zan kawo ta anjima tunda dai nasan kuna chan har dare."


"Kana da matsala wallahi."


"Naji, kanwata sai mun karaso."


"Ok tam."


Tace ta zame hannun ta a hankali daga cikin na Aryan din. Be ce komai ba, ya juya ta bishi a baya suka fito daga office din zuwa reception. Kara bin su yan office din sukayi da kallo Aryan din na lura dasu, bashi da lokacin tsayawa ya bata da ya basu amsar kus kus kus din da yaji suna yi. Zee rufe fuskar ta tayi da mayafin ta, ta dunkufar da kanta akan desk kuka na sake taso mata dan ta tabbatar da abinda take tunani ne ya faru. Suna fita ta dauki wayarta ta shiga toilet ta danna number Adam, ya dade yana neman hadin kanta akam office din nasu amma saboda Aryan taki bashi irin bayanan da yake nema amma yanzu a shirye take da tayi komai. 

  Yana zaune a falon Alhaji Nasara wanda gama wayar su kenan da SAN Mandawari wanda ya bashi wani tabbaci akan case din Hajiya Zeenat din zuwa ranar da za'a sake zama wanda ya rige saura kwanaki kad'an. Mikewa Adam din yayi ya dan yi excusing kansa zuwa waje sannan ya d'aga wayar Zainab din da mamakin dalilin kiran shi da tayi. Da wani ne ya kirashi a lokacin bazai daga ba amma ganin itace ya kuma tabbatar maganar da ta shafi Aryan din ce yasa ya fito ya daga dan kar koma menene ta chanja shawara idan be daga ba.


"Ya akayi?" Yace kai tsaye babu ko sallama bayan ya daga wayar


"Magana nake so muyi."


"Ina sauraron ki."


"Oga Aryan yayi aure ne?" 


"Aure?" Yace da sauri


"Eh, kamar hakan ne. Kwana biyu baya zuwa office sai yau suka zo tare da yarinyar nan Raihana, hannun sa cikin nata suka kuma shiga office dinsa."


"Come again please, ban gane ba."


"Abinda nake tunani kenan, na tabbatar idan babu wani dalili babu abinda zai saka shi rike hannun ta a cikin mutane haka."


"Toh ke haka ake daura aure babu wanda yaji."


"Please ka dai bincika, ka taimaka min wallahi son da nake masa zan iya mutuwa idan ban same shi ba, wallahi duk zaman nan da nake zaman jiran sa nake wallahi."


Wani shu'umin murmushi Adam yayi, ta zo gidan sauki domin dama hanya yake nema da zai rusa Aryan din, idan har zai samu taimakon yarinyar komai zai zo masa da sauki


"Yanzu ina wani abu, zan neme ki anjima mu hadu face to face muyi magana, before then zan kokari na bincika naji gaskiyar batun."


"Ok nagode."


Ta katse wayar ta dauraye fuskarta ta fito tana jin zuciyar ta na kekakashewa, cike da tsanar Raihanan.


***Da hannu daya yake driving dayan kuma yana rike da nata a saman cinyarsa yana murzawa a hankali. Tunda suka shigo motar be yi magana ba, har suka karaso gidan Ya Nabeela ya kashe motar sannan ya juyo ya kalle ta bayan ya sakar mata hannu


"Nan gidan sister na ne, my only sister da take tamkar uwa a gareni, ki saki jikinki kinji? Zanje na dawo sai mu tafi."


"Ok."


Tace sannan ya bud'e motar ta fita shima ya fito suka nufi cikin gidan. Su Amna ne suka fito da gudu suka d'ane shi cike da murnar ganin sa dan kwana biyi be shigo gidan nasu ba. Daga su yayi daidai yana dariya kafin ya kama hannun su, su karasa shiga cikin falon da Ya Nabeelan take zaune tana rubuta list na kayan Raihanan da zasu siya. Ajiye pen din tayi ta rungume Raihanan a jikin tana mata sannu da zuwa. A kunyace ta amsa ta gaishe ta tana dan russunawa ta amsa a sake tana kallon nutsuwa da kyawun Raihanan wanda bata da maraba da Ammy a wanchan lokacin dan hatta murmushin ta irin nata ne. Dole kanin ta ya shiga yanayi sanda yayi tunanin ta rasa ta dan ma dai Aryan din da taurin zuciya yake idan wani ne sai abun yafi hakan. Zama tayi a k'asan carpet da sauri Ya Nabeelan ta daga ta, ta zaunar da ita a saman kujerar sannan ta kalli Aryan da ya nuna kamar ta share shi tayi dariya.


"Yau ni ake sharewa?" 


"Ba dole ba, kanwata tazo ai sai abinda ka gani."


"Ai shikenan, tafiya ma zan, sai anjima zan dawo."


"Ok, amma ita anan zaka barta gaba daya sai bayan kwana biyu." 


Da sauri ya kalli Ya Nabeelan, ta gid'a masa kai alamar abinda yaji hakan take nufi. Sauke kansa k'asa yayi kawai ba tare da yace komai ba 


"Idan ka gama ka wuce gida kawai ma, zan neme ka idan mun gama muma. Ba gobe ba ba jibi ba, sai kaji mu kawai."


"Ok." Yace ya mike kasan zuciyar sa na fada masa yace a ah, amma kuma yasan ko giyar wake yasha ba zai taba iya cewa Ya Nabeela a ah ba, duk abinda ta tsara hakan za'a yi dole. Har ya kai kofa tace


"Ka bawa Malam Bala kayan ta ya kawo nan please, anjima zamu fita tare kuma."


"Ok." Yace a sanyaye ya bud'e kofar ya fice. Yanayin sa ya nuna mata sam ba haka yaso ba, kawai ba zai mata musu bane ba, tausayin sa taji amma kuma ba zata bari tausayin yayi tasiri ba, zata yi abinda ya dace domin shi namiji ne, tasan duk sumi sumi din namiji a wannan bangaren bashi da kunya. Ita kuma Raihana tamkar kanwarta ciki daya daya haka take jin ta, dan haka dole tayi mata abinda take ganin zata kara kima da daraja a idon Aryan din duk da tasan bashi da matsala amma kuma dai hakan shine daidai.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post