Rumbun Qaya Page 45
Health College

Rumbun Qaya Page 45

Rumbun Qaya Page 45

 RQ

      PAGE 45

***Babban dan yatsan sa ya saka a hankali ya shafa lips din nata a hankali in a stylish way, bud'e idon tayi da sauri tana kokarin tashi. Girgiza mata kai yayi ya matse ta sosai yana hadiye wayun bakin sa a hankali. Maida idonta tayi ta rufe hakan ya bashi damar yi mata light kiss akan lips din nata. Yana jin sanda ta matso da dan karfi yayi murmushi kawai yana jin zuciyar sa wasai. Bacci ne ya dauke shi da karfin gaske, domin hatta bugun zuciyar ya daidaita a lokacin, dama akwai alluran da Dr Mahfouz yayi masa masu saka bacci shiyasa yana kwanciya baccin ya dauke shi. Bud'e idon tayi ta lallaba a hankali da k'yar ta zare jikinta, bata jin bacci bata ma ga dalilin da zatayi bacci a irin wannan lokacin ba da bata gama tantance me yake faruwa da ita ba. Sadaf sadaf ta bud'e dakin ta fice zuwa falon ta samu kujera ta zauna akai ta shiga kundin tunanin abubuwan da suke faruwa da kuma yadda akayi suka faru haka cikin kankanin lokaci. Wayar ta da take ajiye tun dazun akan kujerar ta dauka ta fara da kiran Hamma Hydar tunda dai shine ya kawo ta domin ta tabbatar daga bakin sa. Lokacin yana gidan Adda Maimuna tare da Muhd da ya shiga tashin hankali sosai saboda abinda ya faru dan Alhaji Kabir be sanar dashi komai ba sai jiya bayan an daura auren saboda yadda zai fi karbar KADDARAR sa a yadda tazo masa ba tare da yace zai tada hankali ba. Duk da hakan kuwa sai da hankalin sa ya tashi domin har ya dauki hutu a wajen aikin sa sannan yana ta kiran abokan sa na nesa yana sanar dasu bayan invitation card din da ya buga saboda na kusa duk kuwa da a kurarren lokaci komai ya faru. Shiri yake sosai cike da doki da farin ciki amma sai ya samu labarin yadda abun ya kasance. Ya masifar shiga shock da damuwa me tsanani domin yaga samu yaga rashi gashi ya kwallafa rai akan ta har kwanciya ciwo yayi daga jiyan zuwa yau duk ya zama wani iri abun tausayi. Sosai iyayen sa suka tausaya masa dan basu dauka abun zai taba shi hakan ba. Shine da Hydar yazo ya same shi ya kara bashi hakuri ya kuma nuna masa komai mukaddari ne daga Allah. Toh suna cikin maganar ne Raihanan ta kirashi sai yaki dagawa saboda baya so ya kara sosa ran Muhd din. Ganin be daga ba yasa ta juya akalar kiran zuwa Lamido. Shi ya d'aga ya kuma sanar da ita komai har abinda Aryan din be gaya mata ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta share yar kwallar da ta zubo mata. Yadda komai ya kasance ne yake bata mamaki gashi dai ta zama matar aure a wani irin yanayi da ba zata iya tantance shi ba. Tabbas tana son Aryan dan bata san tana son shi har hakan ba sai da maganar ta da Muhd ta taso. Amma duk da hakan bata so irin wannan auren ba, babu lefe babu kayan daki babu komai ko lalle babu a hannun ta haka nan take kamar ba amarya ba. Ajiye wayar tayi ta sauko daga kan kujerar ta kwantar da kanta a jikin ta shiga tunanin yadda rayuwar zata kasance mata, ya zaman su zai kasance da Aryan din duk da taga sabon Aryan akan wanda ta sani a office a yau, amma kuma zama ne na dindindin, magana ake ta har abadah. Tana cikin tunanin bacci ya dauke ta itama. 

  Shi ya fara tashi ana kiran sallar la'asar lokacin, yayi salati bayan ya bud'e idon sa, mikewa yayi da sauri ganin bata dakin, sai yaji kamar dama chan mafarki yake yi. Fitowa yayi falon ya hange ta daga chan ta dora kanta a jikin kujerar. Ajiyar zuciya ya sauke ya karasa ya zagaye daidai saitin in da fuskar ta take, ya durkusa a gabanta yana kallon innocent face dinta, bacci take tsakanin ta da Allah amma kuma kana gani kasan bata ji dadin baccin ba kwata-kwata domin akan hannun ta ta dora kan nata wanda ya tabbatar zuwa lokacin hannun ya gama yin tsami. Kallon falon yayi, sai ya tashi ya dauko t-pillow ya ajiye daga saitin bayan ta, ya kai hannun sa a hankali ya zare kan nata daga kan hannun ya gyara mata kwanciyar yana fatan kar ta tashi. Bata tashin ba sai motsawa da tayi kad'an ta jan numfashi ta cigaba da baccin. Komawa ciki yayi ya fada toilet da sauri jin ana kokarin tada sallar. Wanka yayi a gurguje ya dauro alwala ya fito, be tsaya komai ba ya zura jallabiyar sa ta dazu ya fesa turare ya fita zuwa masallacin. Bayan sun idar da sallar ya dawo ciki ya zauna a gabanta ya tankwashe kafarsa yana kallon ta. Kamar mafarki haka yake ji, amma kuma gaske ne komai ya faru ya wuce bayan da ya gama cire rai da komai ma ya barwa Allah zabin sa. Sai gashi Ya yi masa abinda be taba tunani ba. Sunkoyowa yayi daidai fuskar ta yayi mata peck a kumatu anan idanun sa suka gane masa cleavage dinta,tsayawa yayi chak yaja numfashi da dan karfi ganin fararen boobs dinta da suka cika sosai. Damke hannuwansa yayi ya hade su waje daya kwakwalwar sa ta shiga chaji zuciyar sa kuma na masa bitar da yake ji kamar ya kai hannun sa. Daurewa yayi ya cije saboda baya son ya zake har ta samu damar yin tunanin ko jikinta yake so, sai dai ya kasa dauke idon sa daga kai har sake durkosowa yayi sosai yana more kallon su abinda be taba gani ba, hasaso yadda zasu zama a fili idan babu wani shamaki da ya tare shi. Motsi tayi alamun zata farka yayi saurin gyara zaman sa. A hankali ta bud'e idonta sai ta ga mutum a gabanta a zaune dirshen kamar me gadin ta, da sauri brain dinta tayi mata rewinding abinda ya faru, kunya ce ta kamata ta kasa motsawa bare ta yinkurin tashi zaune ganin yadda yake zaune a gabanta kamar me daukar karatu gashi kuma saman rigar ta ya bud'e sosai har ana kirjinta. Murmushi ya sakar mata ya mika mata hannun sa ta kama ya taimaka mata ta tashi zaune tana kin kallon sa. 

"Kin tashi?"

"Umm."

"Toh ya baccin?"

"Lafiya lou." Tace muryar ta kalar tausayi

"Shine kika gudo kika barni ko?"

"Wayata nazo dauka."

"Ok, tashi toh kiyi sallah, la'asar ta wuce sosai." 

"Tom." 

Tace ta mike a hankali, tashi yayi shima suka jera zuwa bedroom din kamar tace ba sai yaje ba amma ta kasa magana. Toilet din ta shige shi kuma ya jawo akwatin kayan ta, ya bud'e mata, ya daddaga ya dauko mata wata doguwar riga me zip ta gaba da yake ganin zata fi dadi da yanayin weather din hade da Hijab ya ajiye mata a gefen gado, ya rufe ya fita domin ya dan mata warming abincin dazun dan ba wani ci tayi ba kuma baya so ta zauna da yunwa. Ganin kayan a saman gadon yasa ta dauka ta koma toilet din ta chanja dan dama sun takure ta kayan. Sallah ta tayar tana sallar ya dawo dauke da abincin a plate da exoctic me sanyi da cup ya ajiye mata ya ja mata kofar dan ya lura nauyin sa take ji.  Falon ya koma ya dauki wayarta ya kwanta ya bud'e gallery ya shiga kallon pictures dinta da na yan gidan su ita kuma ganin be dawo ba, yasa ta sauki abinci taci fiye da rabi dan dama yunwa take ji tasha juice din shima. Ji tayi ta samu nutsuwa sosai dama da yunwa a jikinta. Tunanin kwashe kayan tayi ta dauki tray din ta bude kofar a hankali ta fito. Lokacin ya haye sama dauko notepad dinsa shiyasa bata ganshi ba. Kitchen din ta shiga ta ajiye tray din sannan ta cire janye hannun Hijab din nata ta tattare dattin dake kan plate din abincin guda biyu ta kwashe ta zuba a ledar dustbin sannan ta saka su a sink ta wanke su ta ajiye a gefe, sauran warmers din dake da abinci a ciki ta dora su kan dinning din sannan ta dauki hadin salad din ta sakashi fridge. Ya dan dade a tsaye yana kallon bayanta, dan tana shigowa ya sakko kasan yaji motsin ta a kitchen din sai ya taho ya ganta yana gyara kayan. Takowa ya shiga yi a hankali sai da yazo daf da ita sannan ta ankare da farko ma tsorata tayi ganin shine yasa ta maze.

"Wa ya fada miki amarya tana aiki?"

Ya lakace mata hanci yana murmushi. 

"Baba Hajara zata shigo ta wannan kofar idan zatayi gyaran wajen, yanzu ma nasan Baba mai gadi ne ya sanar da ita kina nan shiyasa bata shigo ba, kinsan gidan ango da amarya ba'a zuwa karka bata musu budget."

"Na'am?"

"Ehen, kinci abincin?"

"Um naci."

"Good girl, wannan Hijab din bakya jin zafi?"

Yace yana mata nuni da Hijab din jikinta. Gida masa kai tayi da sauri. 

"I don't like it." 

Ya kama zare mata shi, ya cire shi ya ajiye a saman dinning din ya sa hannu ya daga ta sama ya dora ta akan dinning din. Yadda ya daga tan batare da tayi aune ba yasa ta zaro ido a tsorace. Tsayawa yayi a gabanta yana kallon jelar gashin da take a daure. Sumar kan nata ya shafa me sulbi da laushi irin ta Fulani, bata taba saka mata relaxer ba tun da take, amma zaka rantse ta saka ne saboda yadda take a kwance ko tashi batayi. Kamar dan kauye haka yake kallon gashin nata cike da yabawa, komai yayi masa yadda yake so, yasan ba wayon sa bane ba, ba kuma chanchantar sa bace yasa Allah ya bashi domin sai yau ya kara tabbatar da Raihanan ta hadu ta ko ina, body structure, gashi farar fatar da kuma kyakkyawar fuskar ta me dauke da beautiful eyes irin na Ammyn ta.

"I love everything about you, everything."

Yace yana kama zip din gaban rigar ya rik'e, ya dan ja kad'an ya dauko zuwa daidai saman tudun abubuwan nata yadda zai iya hangen su ta hakan ma. Da farko ta zata dukka zai sauke amma sai taga ya barshi kad'an yana murmushi. 

****Gaba daya Raihana ta kasa gane kan Aryan, kamar zai maida ita cikin sa haka yake duk da be mata wani abu bayan runguma da dan peck ba amma kuma ko kallon idon sa bata iya yi saboda yadda suke ciki sosai suke haifar mata da wani irin yanayi. Tare sukayi sallar magriba da isha sannan yace mata tazo su koma saman saboda chan ne main bedroom dinsa, marairace masa tayi tace zata kwana ita anan din duk kuwa da tasan akwai tsoro sosai, be ko tsaya jin me take cewa ba ya kama hannun ta, suka fito ya haura saman da ita ya kaita har dakin nasa ya dawo ya dauki wayoyin su ya kashe hasken kasan ya haye saman. Tana zaune in da ya barta duk tsoro ya cikata, ya shigo ya ajiye komai akan bedside ya zauna a gefen ta ya kunna wayar sa dake a kashe saboda yana son kiran Kamal da Ya Nabeela. Kamal din ya fara kira be dauka ba lokacin ya tsaya masallaci suna magana da wani neighbor dinsa ya bar wayar ya gida. Sai ya kira Ya Nabeela wadda dama tun dazu take neman wayar sa a kashe ta daga sukayi maganar yana son kaya tace masa sai suje gobe yace toh sannan sukayi sallama.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post