Rumbun Qaya Page 52

Rumbun Qaya Page 52

Rumbun Qaya  Page 52

Rumbun Qaya

     Page 52

****Tun da Adam ya tafi Ya Nabeela take tsaye tana kaiwa da komowa, tana jiran jin yadda Kamal sukayi da Aryan akan maganar domin tasan halin Aryan idan har suka yi kokarin danne shari'ar nan toh fa zai dauki doka a hannun sa ne wanda ba zata taba so ya shiga matsalaa ba. Kiran Kamal ne ya shigo tayi wajen wayar da sauri ta daga


"Ya akayi Kamal? Ka same shi?"


"Eh na same shi, munyi magana amma kinsan taurin kan Aryan, be bani damar ma da zamuyi magana sosai ba, dan haka yanzu ma ina hanyar office zan kiraki da na samu kan labarin in sha Allah, karki damu babu abinda zai faru shima yace yana hanyar zuwa gidan."


"Nan zai zo? Gwara yazo ai ni zan masa maganar, ni ko visa za'a yiwa Aryan ne ya dauki matar sa su tafi? Wallahi bana son tashin hankali kwata-kwata."


"Babu abinda zai faru fa, karki damu gaskiya ce zatayi halin ta, nasan waye Aryan nasan kuma ba zai yi abinda yasan zai bata shi ba"


"Toh shikenan, bari ya karaso naji ko ni zai fada min abinda yake faruwa."


"Ok, yadda kukayi let me know."


"I will! kaima sai ka sanar dani."


"In sha Allah."


Ajiye wayar tayi Dr Farouk ya kalle ta sai ya mika mata hannun sa yace tazo ta zauna, zama tayi a gefen sa jikin ta duk a sanyaye kalou.


"Calm down Maman Aryan, kinsan fa halin yaron naki, da kin bashi matar sa ma da duk hakan bata faru ba, ko da rike shin nan honeymoon kawai kika tura shi shikenan fa."


"Ai wallahi ban san za'a yi haka ba, da ban fara ba ma wallahi, wai ni dai muyi biki a kai lefe da komai nake so ayi, ashe yace bari ya samu wani aikin yayi."


"Toh wai kin yarda da maganar Adam ne? Kila ma Hajiyan wani wajen ta tafi ta huta "


"Hmm, nasan waye Aryan, tsaf zai aikata wani abu wallahi. Dama Daddy ke hanashi dani wasu abubuwan, sai Kamal kuma. Toh babu ni babu daddy Kamal din ma ya tafi, kana ganin zai bari abinda ya dade yana tanadi ya salwanta a kankanin lokaci?"


"Gashi nan naji an shigo da mota."


Mikewa tayi da sauri tayi compound din dan ba zata bari ma ya shigo ciki ba saboda yadda ta matsu. Parking yayi ya hangi fitowar ta tana kallon side din da yake. Murmushi yayi kad'an yasan halin rikicewar ta, ya sake tattaro calmness dinsa ya balle murfin motar ya fito ya nufe ta hannun sa zube a cikin aljihun wandon sa. Fuskar sa ta ke kallo tana son gano wani abun amma sam ya hana mata duk wani clue da zata iya gani a tattare dashi. He looks so calm da ya hana mata gano ainahin abinda yake sussukar zuciyar shi. Tafiyar sa ta maida hankali har ya karaso ya tsaya a gabanta cikin sigar zolaya yace


"Ya Nabeela yau tara ta kika fito yi haka?"


"Me yake faruwa? Fada min maza maza."


"Aina fa?"


"Gama da case din Hajiya, abinda Adam yazo yana magana akai gaskiya ne?"


"Ohh, Kamal ya fada min dazu, kawai shirmen sa ne dan Allah karki biye masa, matar da ta iya tserewa hukunci daga hukuma ni ne zan iya dauke ta? Na kaita ina ma toh?"


"Are you telling me the truth?" Ta kalle kwayar idon sa. 


"Ku shigo ciki Maman Aryan, wannan tsarewa tun a waje." 


Dr Farouk yace yana tsaye jikin kofar shiga ciki. Juyawa tayi ta shiga ciki Aryan din ya bi bayanta. Ko zama bata yi ba ta sake watso masa tambayar, ya gid'a mata kai yace


"Bansan komai akai ba."


Wata katotuwar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zauna.


"Barka da gida Dr?"


"Barka dai kanina, ya angonci?"


Murmushi Aryan yayi tunowar da yayi ya ganshi ranar ya kuma san da biyu ya tambaye shi angoncin dan a karshen muryar sa ta nuna sigar tsokana.


"Ango kasha kamshi, gashi dai wannan yayar taka ta hanaka matar ka, bansan me take nufi damu ba, idan kuma sai mun kai kara wajen Daddy ne toh."


"Ko zaku kai sai na gama shirya kanwata, shima Daddyn ba zai ce komai ba."


"A ah, zai fada fa, ai ba haka ake ba, ke haka aka miki da aka aura miki ni?"


"Aka aura maka ni dai." Tace tana dariya


"A ah dai, kin ga handsome guy kika nace kika ce idan bani ba sai rijiya."


"Ahaap, ai kullum aka tashi maganar haka kake cewa, bayan kowa yasan ba haka bane ba."


"Haka ne ai ko Aryan?"


"Haka ne."


 Yace yana murmushin jin dadin yanayin rayuwar su. Dr simple mutum ne me raha da iya tafi da iyali ba tare da cin mutunci ba. Zaman su lafiya lou babu wata matsala. Hakan yana bashi sha'awa wani lokacin shi kadai sai yayi ta hasashen dama hakan ce ta kasance tsakanin su daddy. 


"Aryan?" Ya Nabeela ta kira sunan sa jin ana magana be ce komai ba. Ya tafi duniyar tunanin har be ji tambayar da Dr Farouk din ya sake jeho masa ba.


"Dr ne yake maka magana,."


"Sorry sir, banji bane ba wallahi, na tafi wani tunani."


"Cewa nayi yanzu shikenan haka zaka zuba ido a hanaka matar ka, ko dan kewayowa ai yakamata ka dinga yi."


Shiru yayi yana dariya kasa k'asa, be san yaa Nabeela ta riga tasan da zuwam da yayi ba, wanda ta zata shine kawai.


"Duk yadda akayi Dr ni bani da matsala."


"Auw haka kace?"


"Wai me ya faru ne? Ko dai Aryan kana dan lekowa ne?"


"Ba ya lekowa, kanina ba haka yake ba." 


"Anya?"


"Toh yaushe yazo? Kin hana shi kince kar yazo."


"Toh shikenan."


"Shiga ku gaisa Aryan, karka biye ta yayar nan taka kaje ka sake kafa gwamnatin ka."


"Kai kake zuga shi ko?"


"Laifi nayi?"


"Emana, nace fa sai ne neme shi."


"Sai kisa a toshe kofar baya." Dr yace yana mikewa


"Na'am?"


"No bance wani Abu ba, muje ki tayani shiryawa na wuce office kar na makara."


"Ok, Aryan ga hanya ne, sai anjima." Tace tana mikewa tabi bayan Dr da yake dariya.


Dan jim yayi a zaune kafin ya mike ya nufi dakin da take. Kansa tsaye ba tare da neman excuse ko knocking ba, ya murd'a kofar ya tura kansa ciki.


   Wanka tayi ta fito tana zaune tana shafa lotion din jergens a fatar jikin ta da tayi wani irin sulbi da kyau. Big size pink tpwel ne daure a jikin ta wanda ya sakko sosai ya rufe bayanta zuwa saman sangalalin kafarta. Bata kawo shigowar kowa a lokacin ba dan manta bata murza key din bayan fitar Ya Nabeelan ba. Dakin a share yake tas tas sai kamshin turarukan da Ya Nabeela ta hado mata ke tashi a dakin hade da kamshin room freshener din da moping mist sai ya bada wani irin kamshi me sanyin dadi. 

   Farko da taji an murd'a kofar ta dauka Ya nabeela ce duk da bata shigowa kai tsaye kuma ba zata so ya ganta haka ba da kunya amma bata yi yunkurin tashi ba saboda ta riga tasan kafin tace ta tashi ta riga ta shigo dan haka gwara ta zauna a haka da ta tashi kuma ta shigo sai kunyar tafi haka. Kamshin turaren sa ne ya fara iso mata kafin shi din da kansa ya bayyana a tsakiyar dakin kasancewar dakin bashi da wani girma. Matsananciyar kunya ce ta rufe ta, ta sunkuyar da kanta ta gagara ko da kwakkwaran motsi ne. Be tanka ba, be kuma matsa daga in da yake a tsaye ba yana kallon ta yana nakaltar yanayin da ta shiga. Tun daga saman kanta zuwa yan yatsun kafafuwanta ya bi da kallo kafin ya ajiye idon sa akan gashin kanta da yake a bud'e kuma a sake ba tare da ta saka ribbon ta kama shi ba. Kusan mintuna uku ya dauka yana tsaye a wajen da yake kafin ya tattaro kansa yace


"Tashi kisa kayan ki."


Kasa tashin tayi dan tasan idan ta tashi toh kunyar sai tafi ma ta yanzu.


"Tashi kisa kayan ki ko nazo na saka miki da kai na." Ya sake fada mata cikin muryar sa da take nuna gaskiyar abinda zai iya aikatawa din. Kamar ta rushe da kuka haka ta tashi tana kara jan towel din duk da ya ma.sauka sosai ta cigaba da jan jikinta tana matse shi har ta karasa wajen da kayan nata suke, ta bud'e wardrobe din hakan ya bashi damar ganin bayan nata sosai. Taune k'asan lips dinsa yayi ya kad'a kai ya karasa wajen da ta tashi ya zauna yana daukar lotion din nata ya hau duba jikin container din. Ganin kamar hankalin sa baya kanta tayi saurin daukar kayan zata shiga toilet, ya dakatar da ita ba tare da ya kalle ta ba, ya cigaba da duba abinda yake dubawar. Fasa shiga toilet din tayi duk da ba haka taso ba, ta dauki doguwar rigar da ita kadai take jin zata iya sakawa ba tare da ta kara kunyata ba, ta doro ta a saman towel din, tana kokarin zura kan rigar taji an rik'e rigar kam. Kicin-kicin sakawa ta hau yi ya hanata duk wani yunkurin ta, ya saka hannu ya fincike rigar daga kanta ya ya rungume ta a jikinsa. Saura kiris ta saki towel din saboda yadda ta shiga shock, sai taji ya tayata rike shi saboda kar ya saukan abinda ya bata mamaki ta kalli fuskar sa ya dan harare ta kad'an sannan yace


"Idan na sake towel din nan ya fadi ai na kad'e har ganye na, dan haka ki kara rike shi gam, so kawai nake naji wani abu." 

   Yace yana kashe mata gira. Barin kallon sa tayi dan ta gane abinda yake nufi tayi gajeran murmushi ba tare da ta bari ya gani ba. Sai da yayi kamar minti biyu sannan ya saketa yana matsawa baya


"Kiyi sauri kisa rigar." 


Da sauri ta rarumi rigar ta sake dorata akan towel din sannan ta zare shi ta kasa. 


"Zonan." 


Wajen da yake zaune ta je, ya nuna masa gefen sa da hannu yace ta zauna, ta zauna tana sadda kanta k'asa. Gashin ta da yake har lokacin a yadda yaken ya kai hannu ya gyara mata shi yayi baya sosai, sannan ya tallafo fuskar ta da hannun sa suka kalli juna.


"Magana nazo muyi Raihana." Yace yana kara saka idon sa cikin nata ya kuma hanata dauke natan saboda ya kara samun tasiri akan ta da abinda zai fada matan,da kuma labarin da yake so ta bashi.


"Labari nake so ki bani."


"Labarin Ammy." 


Yanayin ta ne ya sauya a lokaci daya, ya hangi wani irin abu me girma a cikin kwayar idon ta, wanda ya karasa kashe sauran kuzarin da yake dashi da karsashin sa, hade da wani irin matsananciyar soyayyar ta me zafin gaske dake shigaar sa tana huda shi. Lips dinta da suka yi fresh ya kalla, ya sunkuyar da kansa yayi kissing dinsu kad'an sannan ya gid'a masa kanta yana damke hannun ta a cikin nasa dukka biyun yana son tabbatar da ta ta samu nutsuwar da yake bukata daga gareta. Motsa bakin ta, tayi tana son fara magana tana kuma tunanin ta yadda zata fara. 


"Come here." 


Yace yana bud'e mata hannun sa, bata ki ba, ta shigo jikin nasa lamo kirjinsa ya hadu da nata ya haifar masa da wani yar. Da sauri ya dago ta ya zuba wa wajen kallo ya tabbatar da abinda yake son tabbatarwar. Murmushi ya yi me taushi ya sake rungumota yana son jin su sosai a jikin shi duk da hakan zai iya sanya shi wuce gona da iri amma zai yi takatsantsan har ya samu abinda yake son samun. 


***TUNA BAYA






****Alhamdulillah.. Jamaaa sai bayan azumi ko?👏😊😁 Allah ya kawo mu wata me alfarma, Allah ya sa muyi azumi lafiya mu gama lafiya, ya sa muna cikin bayin da za'a yanta idan Allah ya kaimu. Ina barar adduoin ku dan Allah musamman akan ido, ina fatan zaku sakani cikin addu'ar ku a wannan azumin dan yana cikin abinda ya ke kawo mana tsaiko a kowanne lokaci. Ayi hakuri naso gama book din a Yan kwanakin nan amma hakan yaci tura sakamakon ido da ya matsa min sosai kuma bana so na gajarce labarin.Wanda na batawa ko zafafa suka batawa dan Allah a yafi juna, Allah ya kaimu da rai da lafiya kamar yau ne idan muna da rai da lafiya

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post