Rumbun Qaya page 54

Rumbun Qaya page 54

Rumbun Qaya page 54

 RQ

    54

****Bata zauna ba ko da suka shiga dan hankalin ta be gama kwanciya da yanayin da Zeenatun ta nuna ba. 

“Ki zauna mana kawata, kamar wata baku wa.”

“Ba zama nazo yi ba, abu nazo dauka a gidan mu da kuka kwace saboda tsantsar zalunci.”

“Da yaushe ya zama gidan ku Aisha?”

Daddy yace yana dariya

“Kafi kowa sani ai, saboda tsabar zalunci da rashin tsoron Allah kuka kwace.”

“Be sanar dake daidai ba, babu biyar dinsa a gidan nan saboda haka ba mallakin sa bane ba, sai dai ba zan hana ki daukar ahinda zaki dauka ba, kuje tare madam ta dauki abinda zata dauka kizo mu tafi kar mu makara.”


Yace yana kallon Hajiya Zeenat da tayi kamar bata falon tunda suka fara magana, tana kuma sane tana so ammyn ta gane babu wani abu da yayi saura tsakanin su da Daddyn idan ba tazo da niyyar rokon sa ne. Dama kuma abinda tazo da niyyar kenan sai dai furucin Daddy ya wargaza duk shirin ta na neman wa mai gidan nata sassauci a wajen sa. Aryan ne ya sakko daga sama, ganin ammyn yasa shi yin saurin tahowa wajenta, itama shi take kallo sai taga ya rame ya lalace yaron gaba daya, da sauri ta bude masa hannun ta ya shige jikin ta sai ya fashe da kuka. Tsananin tausayin sa ya kamata fiye da tausayin nata yaran da aka raba da mahaifin su, su a kalla suna da ita amma shi kuwa fa? Babu tabaccin Zeenat zata barshi ya samu kusanci da mahaifin nasa sannan kuma ga rashin uwa wadda ta kasance jigo a rayuwar yayanta. Ran Hajiya zeenat ne ya baci, ta kalli fuskar Daddy taga kamar ta sauya mata, sai tayi saurin matsawa ta kama hannun Aryan din tana fadada murmushin fuskar ta


“Menene my boy? Me kake so eh?”


Kwace hannun sa yayi da karfi yana matsawa sosai daga jikin ta


“Karki sakè taba ni, bana son ki ni mom dina nake so, ammy dan Allah ki tafi dani.”


“Baka da hankali ne Aryan?” Daddy yace 


“Calm down alhaji na, he’s just a kid, kuma kasan sai a hankali aisha ce kawai take son wasa da hankalin sa, idan ba haka ba ai Ya hakura ko?”


“Kiji tsoron Allah Zeenatu, ki sani zaki mutu sannan zaki koma ga Allah a lokacin zaki girbi duk abinda kika shuka.”


“Da nayi me?”


“Ya isa haka please, kuje please ta dauki abinda zata dauka ta wuce, Aryan wuce sama kafin na saba maka.”


“Zakayi nadama sosai IBRAHIM, nadamar da bata da amfani kuma.”


Shiru yayi be ce komai ba, ta juya tayi hanyar fita daga falon kwalla na sake taruwa a idanun ta. Tana jin ihun kukan Aryan din Amma babu yadda zata iya. A compound din ta tsaya zeenat din ta fito, bata kalle ta ba, kawai tabi bayanta suka fita daga gidan zuwa tsohon gidan nasu, ta bude kofar ta matsa mata hanya ta shiga, yadda suka fita suka bar gidan haka suka tarar dashi sai uwar kurar da yayi, bedroom din Abby ta nufa kai tsaye tana danne abinda yake taso mata na rauni sosai. Wajen da tasan ya ajiye jakar ta bude ta dauko ta bude ta, ta tabbatar da komai yana ciki sannan ta dauki duk abinda take tunanin zasuyi amfani dashi sai ta koma bedroom dinta nan ma ta dauki abinda zata dauka din ta gama ta fito ta nufi hanyar barin gidan.


“Baki ji ba, sai na fara bincika me kika dauka sannan zaki tafi.”


“A wanne dalili kenan?” Ta ja ta tsaya cike da mamakin ta


“Wai kina nufin har yanzu bakiyi laushi ba aisha? Na fa ciku wasa ya kamata ace kin saduda , kin gane ni din ba ta wasa bace ba, idan kuma kina so kibi khadija in da ta tafi sai ki sanar dani, abu me mafi sauki a gareni na sa a kaddamar miki, duk wani abu da zai bani matsala kawar dashi nake ya kamata ki sani, dan haka idan kina son kanki da arziki kar na sakè ganin kafarki anan, ki koma chan kiyi rayuwar ki da yaranki.”


“Idan raina a hannun ki yake Zeenat karki barni na bar nan wajen ba tare da kin kashe ni ba, har wani tinkaho kike da abinda kika aikata kenan.”


“Hmm, kar dai ki cika baki wallahi, shawara na baki saboda har yanzu ke din kawata ce, amma idan kika ce zaki shiga gonata, toh tabbas zakiyi dana sani mara amfani.”


“Idan kuma na samu hujjar da zan rusa miki duk shirin ki, ina fatan zaki iya wanke kanki tamkar yadda kikayi a Yanzu.”


Wani irin murmushi tayi, ta kada kanta kadan sannan tace


“Mu zuba dan halak ka fasa, sai dai ina me baki shawarar karki kuskura ki bari na wai wayo ki,ki tsaya a in da na ajiye ki karki tsallake limit dinki.”


“Bana bukatar shawarar ki.” 


Sai ta juya ta fice daga gidan. Shiru zeenat tayi bayan fitar ta, ta tabbatar akwai dalilin furucin ammyn, dan haka ba zatayi kasa a guiwa ba, sai ta binciko abinda ta taka. Wayarta ta daga cikin yanayin bacin rai ta danna kira, ta tsaya tana jijjiga kafa da dan sauri sauri tana jiran a daga wayar. Yana dagawa tace


“Follow her.” Sai ta katse kiran ta maida wayar handbag dinta ta fito tana daidaita kanta ta koma cikin gidan ta samu Daddy a tsaye jikin motar suna magana da Moses, bude mata kofar Driver yayi ta zauna sannan daddy ya shiga shima yana tambayar ta ina ammyn.


“Ta tafi.” Kawai tace masa bata sakè cewa komai ba, be kuma tambaya ba shima suka fita daga gidan.


*****Zuciyar ammyn a chunkushe ta tari abun hawa, gidan da ta sauka ta nufa tace me napep din ya jirata, kayanta kawai ta dauka amma sai tayi mantuwa ta bar jakar da ta dauko a dakin Abbyn suka dauki hanyar tasha dan bata jin zata sake kwana a kano. Tayi nisa sosai a tunani har me napep din ya dauke hanyar da suke kai bata lura ba, sai da yayi tafiya sosai da ita sannan ta Ankara, tayi saurin tambayar sa in da zai kaita, juyowa yayi da nufin bata amsa ya fesa mata wani abu a fuska wanda yayi sanadiyyar gushewar hankalin ta.****A hankali Aryan yake murza hannun ta kadan kadan yana kallon dan bakin ta karami da yake magana, shirun da tayi ya saka shi jawota jikin sa ya rungume ta tsam tsam duk da nauyin da yake ji a zuciyar sa amma dole ya dake domin yana da bukatar nutsuwarsa. Ta dade lafe a jikin sa tana sauke ajiyar zuciya a jere har ta samu bugun zuciyar ta ya daidaita ta samu nutsuwa sosai. D’ago kanta yayi daga jikin nasa ya tallafi fuskar tata da hannun sa biyu, a hankali ya motsa bakin sa cikin muryar sa da ta shige ciki sosai yace


“Zan dawo da daddare kinji? Sai mu karasa maganar for now ki huta sosai, karki stressing kanki kwata-kwata.” Gida masa kai tayi a hankali ya yi mata perk a gefen kumatunta Sannan ya dan ja mata hanci kadan sukayi murmushi a tare


“Me Ya Nabee take bawa kumatun nan naki? Kamar bread irin bugun katon nan saboda laushi.”


Dariya ta kyalkyale da ita, ya tsaya yana kallon ta cike da zallar kaunar ta me chakude da tausayin ta sosai.


“Dariya tana miki kyau sosai, ni Kinga ban iya ba.”


“Tafi maka kyau ai, tunda dama baka yi so idan kayi sai kayi kyau.” 


“Really?”


“Umm.”


“Tam zan dinga yi miki, ke kadai kawai kinji?”


“Banda Zainab?”


“Zainab?” Yace 


“Umm ta Office.”


“Ohh..” sai yayi dariya kadan


“Ke da ita toh,sai a raba 50/50.”


Turo baki tayi ta juyar da kanta da jikin ta gaba daya daga kallon side din da yake, murmushi yayi yana jin wani dadi a ransa,ya juyo da ita gaba daya zuwa jikinsa ya matse ta a hankali ya dora habar sa a saman gashin ta dake fitar da wani irin kamshi me ratsa zuciya. Ya dade a haka tana manne dashi tana jin heartbeat dinsa kafin ya dan saketa kadan jin wayar sa na kara alamun kira, ciro wayar yayi ta dan yunkura zata tashi ya hanata ya daga wayar yana makala a kunne.


“Daddy barka da rana.” Yace a nutse 


“Alhamdulillah.” Ya furta sai ya dora


“Ya jikin?” 


“Allah ya kara sauki, eh in sha Allah ina kan kokarin, duk yadda ake ciki zan sanar in sha Allah, komai lafiya lou. Ok a huta lafiya.”


Sai ya katse wayar ya tura ta aljihun gaban rigar sa


“Yaushe Ya nabeela zata gama shirya min ke?” Ya watso mata tambayar ba tare da ta shirya ba, bata amsa ba sai dan murmushi da tayi.


“Zan fada mata tayi sauri, dan tafiya zamuyi zamu bi su Daddy Ina bukatar na huta sosai, nauyin dake kaina da zuciya ta yayi sauki, ina so na bar komai behind me for sometime, wanda nake fatan komai ya daidaita kafin dawowar mu, just pray for me kinji? Akwai abinda nake son achieving idan Allah ya tabbatar ba ni kadai ba, mutane da yawa zasu samu farin ciki wanda nake da yakinin samun wanzuwar wani shashe na daga farin cikin da muka rasa a baya.”


“Allah ya bada sa’ah ya tabbatar da alkhaiiri.”


“Amin My wife.” 


Daga shi tayi ya mike hannayen sa zube cikin aljihun sa, ya dan sake kallon ta sannan ya nufi hanyar da ya saba shigowa don baya son komawa ta falon su hadu da Ya nabeela tayi masa tsiya.

   Yana fita ta yi baya ta kwanta a saman gadon wani irin mixed feeling na bijiro mata, koman sa burgeta yake, nutsuwar sa da yadda yake a kame ga wani irin charisma shi yafi komai birgeta a tattare dashi. Yadda yake treating dinta yafi komai tafiya da ita. Wayar ta , ta dauka ta kira Dadah suka yi hira sosai, sannan ta kira Abbyn ta da su Hamma hydar, dukkan su tambayar ta suke ko akwai wata matsala amma sai tace a ah, suna gama wayar duk suka turo mata kudi a tare kamar hadin baki, wai ko zata bukaci wani abun, murmushi tayi cikin farin ciki da yadda yan uwanta suke kokarin ganin sun faranta mata, da kokarin ganin bata yi lacking komai ba tun kuwa da ta taso.


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_**ZAFAFA BIYAR BACTH A*1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*_Duk biyar 1500_


*______________________________**_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥

_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_

_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_


_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_

_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_


1  _*IDON NERA*_

    Mamuhgee


2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata 

    Billyn Abdul


3  _*RUMBUN QAYA*_

     Hafsat Rano


4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata

    Hafsat Miss Xoxo


5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata

    Safiya Huguma_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_


Guda 5 1200

Guda 4 1000

Guda 3 800

Guda 2 600

Guda 1 400


_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_


_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_


Saiku tura shedar ta👇


_*09033181070*_

Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇

09166221261

TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥

MUNGODE🙏🙏❤️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post