Rumbun Qaya page 55

Rumbun Qaya page 55

Rumbun Qaya page 55

RQ

   55

*******Hannun sa daya na kan sitiyari dayan na rike da wayar sa yana neman number Hydar, kiran sa yayi ya dora wayar a gefen sa ya gyara zaman AirPod din dake makale a kunnen sa. Line busy yaji alamun waya yake har zai katse sai kuma yaji ya dauka


“Yallabai barka da rana.” Hydar yace cikin rashin sanin dalilin kiran aryan din 


“Barka dai, ya gida ya family?”


“Alhamdulillah. Komai lafiya.”


“Masha Allah, please wata yar tambaya nake da ita idan ba damuwa.”


“Ba damuwa, go ahead.”


“Akan maganar ammy ne…”


“Ok… ina jin ka.”


“Yaushe ne ganin ku na karshe da ita, sannan me ya faru a lokacin?”


“Umm, bari na dan fito daga office zan kiraka minti biyu.”


“Ok ba damuwa.” Yace yana tsaida kansa akan titin daidai lokacin da ya shigo cikin layin nasu. Parking yayi a gaban gate din me gadi ya fito zai bude masa gate din yace ya barshi ya dan yi baya da kujerar da yake kai ya zura hannu ya dauko system dinsa a bayan motar ya kunna ta, a daidai lokacin kiran Hydar ya shigo, ya daga yana bada dukkan attention dinsa gareshi, domin akwai wani abu da yake son karasa tattarawa wanda zai tabbatar masa da abinda ya gano.


“Kana jina?” 


“Eh ina jinka.” Yace masa


“Ok…”


*TUNA BAYA*


****Tafiya sukayi da nisa sosai kafin ya isa gidan da zai kai ta, bisa umarnin Hajiya zeenat din, a lokacin ammy bata cikin hayyacin ta bacci take sosai me nauyin gaske don sai da suka sauya mata abun hawa daga napep din suka saka ta a mota duk bata sani ba. Kwana uku tsakani ta farfado cikin wani irin yanayi ga wani azababben ciwo da kanta yake yi mata dan da farko kasa gane in da take tayi da abinda yake faruwa, sai daga baya abinda ya faru ya shiga dawo mata, a zabure ta mike da nufin guduwa amma sai taji ta a daddaure, motsi taji a kofar dakin da yake ta karancin haske kasancewar magriba ce, hasken touchlight ne ya dalle mata ido tayi saurin kawar da kanta, kautar ta hasken yayi zuwa wani shashen sannan ta samu damar ganin shi duk da ba tar ba saboda haske tan da yayi.


“Kin farfado kenan, lallai maganin nan akwai mugun karfi na gaske.”


“Ina ne nan?” Tace muryar ta na rawa saboda gano abinda yake faruwa da tayi


“Nan? Baki san ina ne ba ko? Gidan yankan kai ne.”


“Innalillahi wa inna ilahi, Raihana yarana.”


“Tab ai ke da ganin su, sai dai a lahira idan kuna da rabon ganawa.”


“Dan Allah dan girman Allah Kiyi min rai, wallahi yarana basu da kowa sai ni, mahaifin su yana kurkuku dan Allah ku kyale ni na tafi.”


“Tabb, ai kin shigo kenan wallahi. Idan kin ga kin fita daga gidan nan sai dai idan gawar ki ce.”


Sai ya juya zai yayi hanyar fita, magiya take masa tana kuka amma yayi biris kamar be ji ba, ya kai kofar kenan tace


“Toh dan Allah zanyi sallah.”


“Ba dai anan ba.”  Yace sannan yayi ficewar sa.


Kukan ta ne ya karu, tabbas akwai matsala gagaruma idan har ta cigaba da zama a wajen, ya rayuwar yaran ta zata kasance? Dole tayi wani yinkurin ganin ta bar wajen. Duhu ya mamaye dakin sosai alamun dare ya fara turawa, babu motsin kowa da komai kamar ma ita kadai ce take zaune a wajen, motsa hannun ta, tayi kokarin yi ko zata iya kwance daurin dake jikin nata amma ta gaza, bata hakura ba ta cigaba da gwadawa duk da bata da yakinin zata iya din. Motsi tajiyo daga nesa kamar suna musu, maganar na tunkaro ta har suka iso kofar dakin sannan suka shigo a kusan tare. Matashin nan ne na dazu tare da wani babba dan zai yi kusan saan su Abby ko ya dara su, bata san musun me sukeyi ba kafin su shigo ta dai ji yana cewa


_”Dole a barta tayi sallah, idan hajiyan tazo kace nine nace.”_


Anan ta fuskanci akan dalilin musun nasu, shi matashin yace ba zatayi ba shine shi kuma yace a ah, da kansa ya karaso ya kwance ta sannan yace ta taso, ta mike da kyar kamar zata fadi dan yadda jikinta yake a sakè kamar zata fadi saboda emptiness din da take ji a tattare da ita hade da wata irin yunwa wadda damuwar da take ciki ta hana ta tasiri a gareta.

Waje suka fito ya samu wata babbar tasa ya zubo mata ruwa ya bata, sai da ta kafa kai ta fara sha sosai har ta kusan shayewa ma saboda tsabar ishirwar da take ji, karo mata yayi tayi alwala bayan ta dan kama ruwa sannan ta koma cikin dakin dan a yanayin wajen da yadda bata jin motsin komai sai kukan tsintsaye ko hanya suka bude mata suka ce ta tafi ba zata iya ba, wani irin waje ne me matukar abun tsoro, tayi mamaki kwarai yadda suka iya zama a wajen sai dai duba da yadda  baban yake furta kalmomin sa ya tabbatar mata da bafulatani ne irin na rugar nan wanda suka iya rayuwa a jeji daga su sai dabbobin su. Dankwalin ta, ta cire ta zauna a zaune ta kabbara sallar dan bata jin zata iya yi a tsaye saboda yadda take jin jiri na dibar ta. Ta dade tana jero sallolin kafin ta idar ta kalli kwanon da ya ajiye mata a gefen ta, tana sallar. Jawo shi tayi ta bude sai taga shinkafa ce da mai da yaji, cikin sauri sauri ta hau ci saboda tsabar galabaita batayi tunanin komai ba dan ta riga ta lissafa ba zata yarda ta zauna a gidan nan ba dan haka dole tana bukatar kuzari sosai yadda zata iya tsere musu idan ta samu damar tserewar. Tas ta cinye bata rage komai ba, ta yi hamdala ta gyara dankwalin nata sosai ta kwanta lamo a kasan wajen tana ji aka rufo ta, ta waje tayi shiru tunanin halin da yaran suke ciki musamman raihana da ta kasance karama, bata da alamun yin bacci har dare ya tsala sosai sai kukan sauro da yake tashi kamar ana kada ganga, tashi tayi tunda da alwalar ta, ta cigaba da sallolin ta a tsaye dan dama dazu da rashin kuzari ya hanata yi a tsayen. Har gari yayi sha bata runtsa ba, bata kuma ji motsin kowa ba sai chan zuwa lokacin da rana ta daga sosai sannan taji ana bude kofar. Matashin nan ne ya shigo dauke da kwanon abinci ya dire mata fuskar sa a rufe da bakin abu dama kuma ba gane shi tayi jiya ba saboda babu isahshen hasken da zata iya tantance shi. Fita yayi tayi shiru bata da niyyar daukar abincin bare taci. Sakè rufe ta, taji yayi ya bar wajen chan bayan kusan awa guda taji an sakè bude ta, Yanzu bata d’ago ba tana a zaune a yadda take sai da taji muryar sa ta d’ago suka hada ido.


“Yi maza ki taso, karki bata lokaci har tazo ta same ki anan, zan bude miki hanya kiyi gabas zaki ga wata doguwar hanyar yar siririya kiyi ta binta zata fitar dake har titi, karki tsaya dan daf suke da isowa nan.”


A gigice ta mike tayi hanyar fita suka fita a tare ya fito da ita har waje ta bayan gidan sannan ya nuna mata hanyar da zata bi, zata tsaya yi masa godiya yace tayi sauri. Gudu ta shiga yi na fitar hankali baji ba gani tana gudu tana addua da karfi, ta sha wahala sosai dan sai da taji kamar kafafun ta ba ajikinta suke ba, amma ta daure ta cigaba da gudun har fara hango titin me dauke da motoci yan tsirari, murna ta hau yi ta kara daga kafarta sosai tana jin a ranta ta kubuta har ta karaso titin kanta tsaye ta fada kan kwaltar ba tare da ta duba ko taji karar motar da take shararo gudu na musamman. Shi kansa be lura da ita ba, dan ba hanya ce ta wuce war mutane a kafa ba, dan baya tunanin akwai wani kauye a kusa da wajen saboda hatsarin sa, highway ce dan haka a full speed yake tafiya abinda ya hanashi samun damar taka birki har yayi wani irin tafiyar yaji da ita, ta kwalla kara karar da ta ankarar dashi abinda ya faru.


****Nannauyar ajiyar zuciya Hydar ya sauke kafin yace


“Labarin mutuwar ammmy shine abinda ya taba faruwa damu wanda ya samu a cikin matsanancin tashin hankali, mun sha wahala matuka kafin rayuwar mu ta dawo daidai, munyi kuka tamkar idanun mu zasu rufe saboda azaba, amma Ya zamuyi? Haka Allah ya tsara, abin tashin hankalin shine rashin ganin gawar ta, yafi komai daga mana hankali.”


“Allah ya gafarta mata zububanta, Allah yasa muyi kyakkyawan karshe.” Aryan yace muryar sa a ciki


“Amin.”


“Gobe Friday, zaka iya shigowa kano? Nayi maka booking flight din yamma, idan ka bar Office ka shigo akwai abinda nake son nuna maka.”


“Ok, ba damuwa zan yi kokari nazo.”


“Nagode sosai, Nagode da bani lokacin ka.”


“Babu bukatar godiya,kai dai ka kula min da kanwata, shine kawai.”


“Ko? Zan duba yiwuwar hakan toh.”


“Karka manta dai, kanwar maza ce.”


“Haka kace dai.” 


“Haka ne ma, bari na koma Office na bar ayyuka.”


“Ok, sai ka shigo.”


Suka ajiya wayar.

  

   Hoton dake kan system din ya sake budewa sosai, ya kara kallon sa sannan ya fita ya bude dayan, ya tabbatar da dukkan information din daya ne kafin ya kashe system din ya maida ita back seat din ya d’ago kujerar daidai sannan ya kashe AC motar ya kashe motar ya fito rike da wayar sa ta office a hannu dan da suna magana da hydar kiran zainab ya shigo sai dai be daga ba. Kofar jikin gate din ya tura ya shiga gidan ya hangi motar Adam a parking area ya wuce ciki ya shiga falon. Babu kowa kamar ko da yaushe sai tv dake a kunne tana ta fama ita kadai, kashe ta yayi ya kunna hasken falon wanda yake da a kashe sannan ya haura saman zuwa bedroom dinsa. A falon saman ya tarar da Adam yana waya yana daga muryar cikin tashin hankali dan da gaske karamar magana tana neman zama babba babu labarin Hajiya zeenat babu dalilin ta wanda babu wanda yake zargi illa Aryan gashi ya rasa yadda zai masa ya gano wani. Wuce shi Aryan yayi kamar be ganshi ba yayi saurin shan gabansa yana katse wayar. Wani kallo Aryan din ya watsa masa kafin ya giciye shi ya saka key zai bude dakin kasa Adam din ya rike kofar yana tare shi


“Ina ka kai min uwata?”


“Uwarka? Wacece kuma haka?”


“Baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba tunda ba wai ka wani san dadin iyaye bane ko kuma kasan shakuwar dake tsakanin uwa da danta.”


Kamar an soke shi da mashi haka Aryan yaji maganar, tayi masifar taba shi amma sai ya dake ya fuske tamkar be ji me Adam din yace ba, ya sa hannu ya fincike hannun sa ya hankade shi baya ya shige dakin gami da banko kofar yana jin Adam din na dura duren ashar ya dafe kansa ya jingina da kofar kirjinsa na wani irin harbawa. Ya dan dade a tsaye a wajen kafin ya karasa gaban side drawers dinsa ya ciro maganin sa ya dauki ruwa yasha sannan ya rage rigar jikinsa ya kwanta a saman gadon ya jawo wayarsa ya kunno karatun alkurani me girma yana saurara a hankali nutsuwa na shigar sa tana ratsa shi har ya samu ya dawo daidai.

  Kusan awar shi daya a kwance ba bacci yake ba kawai yana sakawa da warware abinda yake shiri yi ne a cikin yan kwanakin nan, yana kuma fatan ya samu nasara. Yunwa ce ta soma nukurkusarsa, baya son sakè haduwa da Adam bare har ya biye masa su yi musayar magana Shiyasa ya dade a kwancen ma. A tunanin sa ya tafi dan haka ya dauki jallabiyar sa me gajeran hannu ya zura akan farar singlet dinsa ya sakko kasan zuwa dinning area, ya samu an jere abincin akan dinning din sai dai babu plate. Kitchen din ya nufa ya bude wajen da plates din suke ya dauko zai fito Kamal ya kirashi sai ya tsaya rike da plate din a jikin sink ya daga wayar.


“Ina ka shiga ne wai?”


Kamal yace yana fitowa daga meeting din da sukayi, a gajiya yake tikis dan ya matsu da kiran Aryan din ne ma Shiyasa amma da kashe wayar zai kawai ya koma ya kwanta dan kusan kwana uku kenan basa samun isashen bacci akan wani case da sukeyi 


“Na dan kwanta ne, Yanzu kuma na sakko zan yi lunch .”


“Ok, kunyi magana da Ya nabeela ?”


“Eh munyi, kasan ta. Komai ma abun damuwa me a wajen ta.”


“Dole ne ai, ni kaina na damu din, kawai dan ni namiji ne. Please Aryan Karki yi wani abu, akwai shirin da nake akan case din nan, amma for now don’t make any move.”


“Ok.” Yace a gajarce 


“Good.”


“Em akwai abinda nake so dama na fada maka.”


“Ok, ina ji.”


“I think na gano in da Ammy take.”


“Wait what!? Are you serious?”


“Yeah, ba kace I should take over ba, so na gano in da take, kuma na gama planning yadda zamu je mu ganta, ni da hydar.”


“Ku jira ni, zan shigo Sunday sai muje.”


“Saturday zamu je, zai shigo kano gobe sai muje Saturday.”


“Noo ku jira ni.”


“Why? Ba zan iya yi ni kadai ba? Dole sai kazo?”


“Zaka iya, but Inaso nazo nima.”


“Wannan karon dai just allow me please.”


“Aryan?”


“Pleaseee.”


“Ok,ok. Shikenan.”


“Yauwa, Atleast nayi wani abu, Inaso raihana ta kara sakin jiki dani, idan hakan ta faru zata kara yarda dani. Zata yarda ni ma I’m a good person, ba Halin mu daya da daddy ba.”


“Naji naji, don’t change the topic. Na gaji tikis zan je na huta, zamuyi magana anjima.”


“Ok.” Yace ya katse wayar. Da sauri Adam dake makale a jikin kofar kitchen din ya bar wajen yana wani irin murmushi.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post