RQ
Page 56
****Katse wayar yayi ya fito zuwa dining ya zauna gami da jawo warmers din ya bud'e ya zuba abincin dan madaidaci ya yi bismillah ya shiga ci a hankali yana danna wayarsa da yake kokarin tura mata sako. Yaci ba laifi dan ba wani breakfast yayi sosai ba ya ture plate din yana mikewa, ya koma tsakiyar falon ya zauna a cikin kujerun falon da ya dade be yi irin zaman ba.
***A firgice ta farka daga baccin da take, ta kwala sunan Aryan dan dama da sunan nasa baccin yaci karfin ta. Ladi ce ta shigo da saurin, ta zura mata ido tana kallon ta kafin ta kurma uban ihu bayan ta lura da in da take. Tashi tayi tana yunkurin kakkabe jikinta saboda wani irin mugun kyankyamin wajen da take da yadda dakin yayi mugun datti.
"Ahe kin farka." Ladi tace tana matsowa kusa da ita, da sauri Hajiya Zeenat ta daka mata tsawa tana kallon ta cikin yanayin kyankyamin tace
"Karki kuskura ki matso kusa dani."
"Aradun Allah sai na matso ki, mune yanzu dangin ki tare damu zakiyi rayuwa."
"Inji uban wa, na rantse da Allah kika sake matso ni sai nasa anyi maganin ki."
"Tab lallai, baki san ma wacece ni ba."
Kallon banza Hajiya Zeenat tayi mata, ta yi hanyar fita daga dakin a fusace, dariya ladi tasa tana gyara daurin zanin ta, ta bita da kallo dan tasan ko kusa bata isa ta zura kafarta waje daga dakin ba. A tsorace ta juyo dakin gami banko kyauren da ya kusa karyewa jikinta na rawa tace
"Menene a waje?"
"Jeki ki gani mana, aradun Allah sai ta cinye ki tas har kashin ki."
"Dan Allah menene? Kamar kura na gani."
"Ba kamar ba, itace wallahi. Kuma an riga na sanar da ita da kin fito tayi kalaci dake."
"Na shiga uku, abinda yaron nan zai min Kenan?"
"Ke kika san shi, kinga tafiya ta gashi nan garin buga kyauren kin kusan balla shi, idan ya karasa ballewa aradun Allah har cikin dakin nan sai ta shigo ta shinshina ki kuma."
Da sauri Hajiya Zeenat ta damke ta ganin zata fita ta barta ita kadai, wani kallo Ladi tayi mata me cike da izgili tace
"Ke da kika ce kar na matso ki, uban mi yasa zaki rike ni?"
"Kiyi min rai, wallahi zan baki kudi, idan har kika taimake ni duk wata matsalar ki ta kau, sai kin zama abun kwatance a garin nan amma dan Allah ki barni na tafi, ba zan iya rayuwa anan ba."
"Mu da muke rayuwa a wajen uban mi ya cinye mu?"
"Dan Allah ni dai, kinji kanwata dan Allah."
"Alkuran ko me zaki bani ba zan taimaka miki ba. Kuma kika sake rike ni idan zan fita sai na kira kurar nan ta shigo, zan bawa lantis tuwon dawa ta kawo miki da ruwan randa me sonyi, idan kin ci, cikinki, idan baki ci ba ma dai cikin ki."
Sai ta juya ta fita gami da barin kofar a bud'e. Da sauri Hajiya Zeenat ta mayar da kyauren ta rufe cikin tsananin tashin hankali, lallai Aryan ya shirya tozarta ta, dama tasan halin yaron shegen taurin kai da kafiya, amma bata taba tunanin zai mata wannan azabar ba. In da ta tashi ta koma ta zauna cikin tsananin tsoro hankalin ta na kan kofar tana jin gunjin kurar da take a sake tana shawagin ta kamar yadda akuya ke yawo a tsakar gida. Taba kyauren akayi ta tsorata sai ga ladidi ta shigo da wata mummunar langa da ruwa a Kofin silba ta dire mata a gabanta tana kallon ta.
"Taimako na zakiyi dan Allah, zan baki kudi da duk wani jin dadin duniya, waya kawai zaki samo min dan Allah."
"Bamu da netiwok a garin nan ai, sai an je chan hayi ake samu ayi waya, su waye ma masu wayar a kaf garin nan? Basu fi mutum hudu ba."
"Na shiga uku, Aryan!!!"
"Inna Ladi tace idan kin cinye ki taba kyauren nan zan zo na dauki langar."
"Ki zauna anan toh dan Allah karki tafi."
"Chab, so kike taci ubana Kenan."
"Toh ya sunan kauyan nan?"
"Oho nima ban sani ba."
"Shegu marasa iya magana." Hajiya Zeenat tace k'asa k'asa cikin bacin rai, juyawa Landis tayi ta fice tana kada kugu. Zame dankwalin kanta Hajiya Zeenat tayi dan wani irin tururin zafi ne ke fitowa daga cikin jikin ta. Da dan kwalin ta dinga kokarin firfita ta dan ja kwanon kad'an ta bud'e tuwon da sauri ta rufe ganin wata irin miya tsululu kamar an wanke kai, kwalla ce ta taru a idonta, lallai Aryan ya gama cutar ta, cuta me tsananin gaske, ba kuma zata kyale shi ba wallahi sai ta nuna masa ita uwar dakin sa ce a rashin mutunci. Tun da magribar fari sauro ya fara gud'a acikin kunnuwan Hajiya Zeenat, ta shiga aikin kore su amma ko gezau kamar ma kara turosu ake yi ga wani irin shegen kuka da suke kamar zasu ci babu sannan ga kukan da cikin ta yake yi dan daga prison take dole tana tare da yunwa. Bata yi tunanin yin sallah ba ko kad'an dan bata bukatar abinda zai fitar da ita waje. Ladi ce ta dawo dakin dauke da yar karamar touchlight ta haska.
"Kiritta ce ko musulma?"
"Ban..." Da ban sani ba zata ce, sai kuma ta tuna, ta ja tsaki cikin kunar Tai tace
"Ina zanyi alwalar?"
"Taso muje, ni shaf na manta ma ashe kina sallah, da naji baki magana ba na dauka kiritta ce."
"Amma ai kinsan ni mace ce ko?"
"Taso kafin K'adari ya dawo da kurar nan, sun dan fita shawagi sai kiyi da jiki."
Da sauri Hajiya Zeenat ta mike tabi bayanta dan dama fitsari take ji, sai data fara tabbatar da babu kurar sannan ta yarda ta fito ta rakata kofar bayin da babu ko rufi sai dan zagaye shi da wanda idan kana tsaye tsaf za'a hango ka. Gefe ta samu tayi fitsarin dan babu yadda zatayi, ta fito tayi alwalar sannan ta koma ciki. Wata tsohuwar darduma ladi ta kawo mata tace ta barshi zata shinfida dankwalin ta, juyawa tayi da kayarta ta bar mata touchlight din ta yi sallar sharp sharp ta idar ta zauna jigum sai taji motsi alamun wanda aka ce ya fita da kurar ya dawo, kara nutsuwa tayi ta dauki ruwan a ba yadda zatayi tasha kad'an ta ajiye.
Kayan abincin da Aryan yasa a siyo mata Buba ya kawo dama abinda ya fitar dashi tun rana kenan, maimakon akai dakin da take sai Ladi tace akai mata dakin ta dan so take sai ta koya mata hankali sannan zata kyale ta, katifar dai da maganin sauro ta bawa ladidi ta kai mata ta shinfida mata da sabon bedsheet dan karami sai pure water leda biyar. Ta dan ji dama dama da aka kawo karamar katifar da ruwa da maganin sauro, sai dai kuma taji babu dadi dan alamu sun nuna bata da shirin tafiya yanzu kenan.
***Kamar yadda Aryan suka tsara da Hydar haka akayi daga office ya wuce airport kai tsaye yana zuwa suka taso zuwa Kano. Yana sauka ya wuce gidan Adda Maimuna bayan ya kira Muhammad ya sanar dashi zuwan sa. Sai da ya isa gidan ya huta sannan ya kira Aryan yace masa ya sauka. Gashi nan zai zo ya dauke shi yace masa sannan suka ajiye wayar. Muhammad da suke zaune tare ya kalle shi cikin son Karin bayani yace
"Kamar dan rainin hankalin nan ko?"
"Wai Aryan?"
"Eh shi, guy din nan ko? Hmm amma ba komai haka Allah ya kaddara."
"Toh ya za'a yi da abinda Allah ya kaddara?"
"Haka ne, amma ni sam be yi mun ba, bai kuma dace da Raihana ba, sai uban girman kai da nuna shi ya isa."
"Calm down bro, komai ya wuce please a daina tuna baya, Allah zai musanya maka da mafi alkhairi ."
"It's hard ai, kawai kai dai ayi sha'ani."
"Na sani, ayi hakuri dai."
"Wai ko tsoron sa kake ne?"
"Tsoro? Me yasa zanji tsoron sa?" Yace a dan hasale dan dama akwai shi da saurin tunzura kamar Aryan din
"Naga kana goyon bayan sa ne."
"Yanzu shi yake auren kanwata, ko ina so ko bana so I have to respect the fact that mijin tane."
"Ok ok, naji shikenan?"
Mikewa Hydar yayi dan har ga Allah Muhammad din ya bashi haushi sosai.
"Na fita ba lallai na dawo yau ba, zan samu hotel na zauna kawai."
"Saboda nayi magana?"
"Yes, bana so a zarge ni da abinda bashi bane ba."
Sai ya fita, ya bar Muhammad din a tsaye. Biyo shi yayi ya tarar dashi a waje yana jiran Aryan din ya tsaya gefensa yana kallon yanayin fuskar sa, zai yi magana Aryan din ya shigo layin. Fasa maganar yayi yaji duk ransa ya baci ganin Aryan din sai kawai ya juya ya koma ciki. Aryan na ankare dashi dan yana shigowa layin dashi ya fara ankarewa. Parking yayi a gaban Hydar din ya sauke glass din. Bud'e kofar side din me zaman banza Hydar yayi ya shiga ya mika masa hannu suka gaisa sannan Aryan din ya ja suka bar wajen.
Gidan ya Nabeela ya wuce dasu kai tsaye don yana so yaga Raihana dan ko da yace zai koma jiyan be koma ba sun dai yi waya da daddaren dan har sai da yaga ta fara hamma sannan yace ta kwanta suka ajiye wayar ya shiga wani aikin.
Tana falon ya Nabeelan suna hira tana tsefewa Amal kanta suka shigo da sallamar su, wani yar taji tun daga kanta zuwa kafafunta amma sai ta kasa dagowa ta kalli kofar duk da tana jin idanun sa akanta yana takowa cikin falon Hydar na biye dashi a baya. Riga ce me gajeren hannun a jikinta da dogon skirt sai Chantilly Cap da ta rufe gashin kanta. Maganar Hydar yasa ta dago da sauri dan bata yi zato ko tsammanin ganin sa ba. Fuskarta ce ta fadada da fara'ah
"Hamma na?"
"Umm kanwata, sai gani."
"Sannu da zuwa." Ya Nabeela tace tana murmushi
"Yawwa sister, sannu da gida."
"Yawwa, ya hanya anzo lafiya?"
"Lafiya lou, mun same ku lafiya?"
"Alhamdulillah wallahi."
"Hamma ina wuni?" Tace a kunyace tana satar kallon Aryan da yake kokarin zama kan kujerar da take.
"Lafiya lou."
"Ya Nabeela... Ya gida?"
"Lafiya lou, Aryan."
"How are you?"
Yace muryar sa k'asa-kasa yadda ita kadai zataji. Sunna kanta kasa tayi ba tare ta amsa ba. Murmushi yayi kawai dan dama yasan ba zata amsa ba. Mai aikin Ya Nabeela ce ta kawo musu juice da ruwa Hydar na lura da yadda Raihana duk ta takura. Mikewa tayi zata bar falon ya tsaida ita.
"Raihana, banga kin gaida Aryan ba."
Diriricewa tayi, shi kuwa gogan ya coge yana kallon yadda zatayi.
"Um um... Dama."
"Ta gaishe ni, kasan gaisuwar couples sai ka kura kunne sosai zaka iya ji." Aryan ya fada yana yin baya akan kujerar. Kallon sa tayi da sauri ya kashe mata ido daya tayi saurin dauke kanta tana murmushi
"Umm lallai, abun na masoya na Kenan". Ya Nabeela tace tana dariya.
"Yunwa nake jiiii." Yace yana kallon Raihanan kamar itace me gidan.
"Kanwata kawo wa mijinki da yayanki abinci."
"Yanzu naga cin abinci a gidan Adda Maimuna wallahi."
"Ka ci dai ko babu yawa ai."
"Toh ya Nabeela." Yace yana murmushi
Kitchen din Raihana ta wuce ta hado musu abincin akan tray ta dawo falon, ta tarar Ya Nabeela ta tashi Hamma Hydar yana tsaye a jikin console yana waya sai Aryan din a zaune. A kasan rug din ta ajiye daidai saitin gaban sa. Ta yunkura zata tashi ya kamo hannun ta yana kokarin saka idanun sa cikin nata. Kin kallon sa tayi ya shiga murza hannun a hankali a hankali yana kashe mata ido daya.
"Zuba min."
"Ok." Tace ta durkusa ta shiga zuba abincin a hankali, zamowa yayi ya zauna ya rike hannun ganin tana ta cika plate din dan ba wata yunwa da yake ji kawai so yake kar ta tafi. Dawowa Hydar yayi wajen ya zauna a k'asan ta dauki wani plate din zata zuba masa Aryan yace ta barshi suci tare dan shima ba wani ci zai ba. Tashi tayi ta basu wajen suka ci abincin sannan ya Nabeela ta dawo suka cigaba da hira har kusan magriba sannan suka tafi. Direct main house suka tafi tare dan so yake ya sanar dashi komai tun daga kan binciken sa da kuma abinda suke shirin yi a goben dan yaga karar Hydar din ma sosai da be tambaye shi ba.
Bayan sun yi sallah suka zauna a dakin Aryan din ya bud'e masa komai, ba karamin mamaki da kaduwa Hydar ya shiga ba, dan sai da ya zubar da hawaye, idan abinda suke tunani ya zama gaskiya wanne irin farin ciki Abby zai? Dadah, Raihana,Lamido da Sadeeq? Ji yayi gabaki daya ya kagu yaga goben tayi, dan baya jin ma zai iya runtsawa.
Da asubah bayan sun dawo daga masjid wani tunani ya zo wa Aryan, wayar sa ya dauka ya kira Ya Nabeela yace zasu je wani waje da Raihana da Hydar idan ba damuwa. Toh tace kawai bata kuma bi baasin ina za an ba tunda dai matar sa ce. Dakin Raihanan ta wuce ta same ta tace ta shirya Aryan zaizo da Hydar zasuje unguwa. Da murnar ta, ta hau shiryawa dan yace zuwa bakwai yake so su tafi. Tana shiryawa yayi mata text message yace ta dau spare kaya two set, mamakin in da zasu yasa ta kusan makara da shiryawa a gurguje ta karasa ta sha tea da biscuits saboda yayi wuri sosai ta iya cin abinci me nauyi. Zuwa sukayi ta fita lokacin ma Ya Nabeela ta koma bacci sunyi sallama. A shirye shima Adam suka fito suka rufa musu baya, office Aryan ya fara zuwa ya fito ya dawo kujerar baya kusa da Raihanan Malam Yahya driver ya shiga mazaunin sa yaja motar suka dau hanya.