Rumbun Qaya page 57

Rumbun Qaya page 57

Rumbun Qaya page 57

RQ

    57

***Dan satar kallon sa tayi ganin ya dawo bayan, gaba daya attention din sa yana kan wayar dake hannun sa. Kauda kanta tayi zuwa windown ta zurawa tagar ido cikin tunanin in da zasu haka kuma har da hamma hydar. Kamar ba shi ba ma dan tunda suka shigo motar be yi magana ba, bare kuma Aryan din da dama shi ba gwanin magana bane ba. Ya dau kusan mintuna sha biyar akan wayar tasa kafin ya kashe ta ya ajiye ta a gefe sannan yace


“Kunyi magana da Lamido ne?”


“Eh munyi, yace be samu flight din safe ba sai dai na 12pm.”


“Ok, Kamal ma yace yana hanya duk da nace masa noo, Ya dage sai yazo. tafiya ce me dan tsawo, inaga sai dai ma su same mu a gida kawai idan abinda muke so ya tabbata muna zuwa in sha Allah zamu juyo ai.”


“I hope so, amma dai inaga so dai suke ayi komai suna nan, ban zata Lamido zai samu time haka ba.”


“Dole ne ai, idan ka duba muhimmancin abinda za’a yi din.”


“Haka ne, Sadeeq dai ban sanar dashi ba, kasan Shima he’s always busy a hospital plus nasan yana da wani surgery da zai yi yau a private hospital dinsu bana so na raba masa hankali.”


“Yeah it’s good da ka kyale shi, mu ma mun isa ai.”


Sai ya juyo da kallon sa kan raihana da tayi tsam tana son fuskantar abinda suke cewa din amma ta gaza gane komai.


“My wife.” Yace yana dan jan jikin sa kadan zuwa bangaren ta sannan ya kwanto da kansa gefenta.


“Umm.” Tace a hankali ya sa hannu ya dauki wayarta dake saman cinyarta ya kunna, hoton ta ne akan wallpaper din sanye da khakhi na Nysc tayi murmushi me kyau da ya kara fito da ainahin kyawunta sosai. 


“Corper.” Yayi dariya da ya tuna sunan da yake fada mata. Murmushi tayi itama ya ajiye wayar a inda ya dauka Maimakon ya tashi zaune sosai sai ya dora kansa a saman cinyar tata ya kulle idon sa.


“Jiya banyi bacci sosai ba. Bacci nake ji sosai.”


“Me yasa?”


“Ina ta tunani, kaina kamar zai fashe na saka wannan na warware.”


“Ok, ayya.”


Shiru yayi idon sa a kullen amma ba bacci yake ba, kasa nutsuwa tayi har sai da ta furta


“Ina zamu?”


Bude idon yayi ya zuba mata su akan fuskar ta, tayi saurin janye idonta ganin yadda kallon nasa yayi tasiri akanta. 


“Siyar dake za muyi,Hydar nawa ma akayi cinikin kan ta?”


“Wa fa?” Hydar yace yana waigowa bayan dan ba jin hirar su yake ba. Da hannu Aryan ya nuna masa raihana sai hydar yasa dariya


“Kan kanwata ai me daraja ne, ba zai siyu ba.”


Tashi zaune Aryan yayi jin wayar sa tayi vibrating, dubawa yayi sannan yace


“Malam Yahya duba side mirror akwai masu bin mu ko?”


Kallon side mirror Malam Yahya yayi sannan ya kalli rear mirror ya gida kansa.


“Na lura kamar ana bin mu tun dazu, ganin yadda suke kokarin bin bayan mu sai da kafa ba tare da sun zo sun wuce mu ba duk kuwa da yanayin tafiyar da muke a hankali.”


Murmushi Aryan yayi, hydar ya waigo yana bukatar karin bayani


“Nasan suna bin mu, Adam ne tare da yaran Hajiya Zeenat.”


“Ka sani?”


Gida kai Aryan yayi, 

“Yaji convo dinmu da Kamal, na ganshi ta jikin window din kitchen sanda yake eavesdropping ma conversation dinmu, shisa na bashi damar yaji komai dan nasan dama abinda zai yi kenan, zai biyo mu not knowing zai fadama trap ne.”

“Woaw! I’m impressed.” Hydar yace yana murmushi, be san Aryan din yana da basira haka ba, dan wani kallo yake masa duk da yaga kokarin sa sosai ko akan case din Abby Amma be dauka haka yake ba. He act calmly kamar ba wani abu bane ba ma. Menene trap din? Menene kuma plan din da Ya shirya?

“Malam Yahya muje kawai, ka lura sosai da moves din su, hydar watch from your side,” 

“Ok.” Hydar yace yana kallon mirror side din shi ya kara tabbatar da, da gaske bin sun suke. 

 A nutse suke tafiyar duk kuwa da doguwar tafiya ce, yana cikin plan din Aryan din dan ya riga yayi calculating hour nawa zasuyi covering akan speed din da suke kai. Wani messege din ne ya sake shigo masa, ya kalli wayar sannan yace 

“Taka motar nan malam yahya.”

Take motar malam yahya yayi suma sai suka taka tasu, abinda ya bawa raihana matukar tsoro, tayi saurin riko shi tana matsowa jikin sa sosai. Riko ta yayi ya sakata a jikinsa ta makalkale shi. Hannun ta ya kama ya saka cikin nasa ya damke yana mata dariya. 

  Idan kana neman kwararre a tuki ka samu malam yahya ka gama, dalilin da yasa Aryan ya zabi tafiyar tare dashi kenan dan yasan dama hakan zata faru. Kokarin bace ma su Adam din suke amma suma sun rike wuta gashi dama hanyar ba kowa sai yan motoci jefi jefi.

   Daf da zasu shiga garin ne wajen wani karkacewa da titin yayi Aryan yace malam yahya ya dauke hanya, abinda ya jawo suka bace wa su Adam, wani irin ihu Adam yayi kamar zai damki kan sitiyarin ya buga jikin dashboard cikin bacin rai yace driver ya sauka daga titin ya gangara kasa. Gangarawa suka yi ya hau duddubawa dan basu ga alamun hanya a wajen ba, sai wannan dai titin guda daya tal da suke kai.

   Tafiya suka soma yi a cikin garin har suka iso garshen dan titin da babu kwalta akansa, parking sukayi daga chan gefe sannan suka fito, a kaida machine ake hawa daga nan sai a shigar da kai garin amma sai Aryan yace su taka a kafa har su karasa dan baya so raihana ta hau bayan machine din,

“Idan da nisa nake ganin gwara mu hau Aryan. “

“Daga nan zuwa gidan malam yakubu akwai nisa?”

“Malam Yakubu wanne?”

“Wani farin bafulatini, ya zauna a cikin gari kafin ya tattaro ya dawo gida.”

“Oh na gane, gidan Baffan Kudu yake nufi, da yar tafiya gaskia musamman Yanzu da tsuka tayi yabanya hanyoyin sun zama masu wahala dan idan ba kwakwaran sanin wajen kayi ba sai ka bata.”

“Ai ban ma san wajen ba, zuwan mu na farko kenan.”

“Ina ganin mu hau kawai su kaimu Aryan.” Hydar yace 

“Ok, baba kai sai ka dauketa.” Yace yana nuna wani dattijo a cikin masu baburan. Girgiza kai hydar yayi, ya d’ane bayan machine dinsa. Taimaka mata yayi ta hau ya karbi jakarta ya saka a tsakiyar machine din tsakanin ta da baban sannan yace su yi gaba sai wanda zai hau yabi bayan su maana tana gaba yana bayanta kenan. Shi dai hydar be ce komai ba, burin sa kawai su isa, jikinsa yayi masifar sanyi ga wani irin tsoro, tsoron kar su tarar da labari mara dadi ko ace ba nan bane, duk da Aryan ya tabbatar masa da mutumin shine ya dauki ammyn kuma shine Hajiya zeenat take zuwa gani a lokacin.

***Babban gida ne da ya amsa sunan babban gidA, baki daya kauyen babu gida me girma da tarin mutane irin sa ba. Malam Yakubu shine Yanzu a matsayin babba a ahalin gidan kuma shine ya tatttara yanuwansa dukka ya hade kansu bayan ya tattaro ya dawo a lokacin da ake harin rayuwar sa. A duk safiyar duniya bayan sun dawo daga dubo gonar su su kan zauna a kofar gidan a shinfida babbar tabarma su zauna su sha fara ko kunu da gaya ko koko duk dai abinda ya sauwaka kafin kananan ciki su wuce zuwa aikin gonar na ranar zuwa dagawar rana su sake tattaro wa su dawo gida suci abinci tare. Babban abinda mutane da yawa basu gane ba shine cin abinci tare yana matukar kawo shakuwa tsakanin yan uwa, miji da mata da sauran su. Babban Dalilin da yasa suke da matukar hadin kai kenan suna kuma girmama Malam Yakubu a matsayin sa na babba suna kuma mutunta duk wani abu da ya jibance shi. Karar shigowar mashinan ya sa suka maida hankali wajen ganin su waye suka zo? Ganin baki ne yasa suka ajiye abinda suke a gefe. Gaban malam Yakubu ne ya fadi, daidai lokacin da raihana take sauka daga machine din, bata da maraba da Ammy sam, nan take ya gane su waye da kuma abinda ya kawo su.

“Sani matsar da kayan nan gefe, sannun ku da hanya.”

“Yawwa.” Suka amsa a tare sannan suka zauna a gefen tabarmar bayan sauran duk sun tashi, gefe Raihana ta samu ta tsuguna ya cigaba da satar kallon ta ganin tsananin kamar tasu. Gaishe shi sukayi sannan aka gaisa da sauran yan uwan sai malam Yakubu yace duk su koma bakin aikin su, su basu waje. Ba musu kowa yayi nasa waje ya rage sai su kadai.

“Yan samari ban gane daga ina ba.”

“Daga kano muke.” 

“Toh toh Masha Allah, me ke tafe daku.”

“Munzo akan maganar mahaifiyar mu ne dama.” Aryan yace 

“Madallah, jini na karya ba, tun da kuka nufo mu nake kallon fuskar innar yara da wannan Baiwar Allar, kamar ta baci matuka. Ya gida ya hanya?”

“Alhamdulillah.”

“Anzo lafiya dai ko?”

“Alhmadulillah.”

“Toh Madallah, me kuke son sani game da mahaifiyar taku?” Ya tambaya 

“Munzo ne muji idan tana raye, muna so mu ganta.”

“Menene sunan mahaifiyar taku?”

“Aisha Nasir.” 

“Madallah, tana nan da ranta kuma a yanzu haka ma tana cikin gidan nan.” Ya nuna gidan nasu da hannu.

“Alhamdulillah! Suka hada baki wajen fada. Kallon rashin sani da fahimtar abinda yake wakana raihana take musu dan Itafa bata fuskanci komai ba.

“Zamu iya ganin ta ?”

“Sosai, me zai hana? Sai dai wani hanzari ba gudu ba…”

Duk sai suka tsaya suna kallon sa cikin tarradin abinda zai fada

“Mahaifiyar ku na raya kuma cikin koshin lafiya, sai dai ta gamu da wani iftilai a shekarun baya in da mota ta kade ta har ta kai kan ta yayi mugun buguwar da ta manta komai da kowa da ita karan kanta. Bata san wacece ita ba bare tasan komai akan rayuwar ta. Anyi mata magani a lokacin daidai gwargwado sai dai duk lokacin da mukayi mata maganar gida da dangin ta takan birkice mana tamkar ana saka guduma ko karfe ana buga mata kanta. Haka zatayi kwana da kwanaki tana ciwo na fitar hayyaci, da muka gano haka sai muka daina yi mata maganar, tun daga lokacin shikenan ta samu sauki, muka cigaba da rayuwar mu tamkar babu abinda ya faru.”

Shiru sukayi kamar ruwa ya cinye su, sai raihana da ta saka kuka a durkushen da take.

“Yanzu menene abun yi?” Aryan yayi ta maza ya tambaya

“Sati biyu da suka wuce na samu wani babban malami munyi maganar, domin tabbas ba kalou ba, anan ne yake tabbatar min ko dai anyi mata sihirin da aka raba ta da gida da danginta ne aka kuma saka mata tsanar su da tsanar waiwayar gida tunda bata shiga yanayin sai idan an mata maganar, dole sai anyi mata maganin sihiri idan har akwai shi toh sai an cire shi sannan zata iya dawowa daidai ta iya waiwayar danginta.”

“Ya Allahu!” 

“Minti daya bari na daga waya.” 

Aryan yace yana tashi ya matsa gefe shi kuma malam yakubu Ya cigaba da yiwa su hydar bayani. Kamal ne ya kirashi sukayi magana sama-sama sannan ya kashe, sakon ne ya sake shigo masa ya duba sai yaga yace sun samu shigowar garin gasu a inda ma sukayi parking din motar su. Komawa yayi ya zauna kusa da hydar sannnan yace masa

“Sun shigo suna wajen motarmu.” 

Kallon sa Hydar yayi da idanun sa da suka dan chanja kala, gida masa kai Aryan yayi sannan ya kalli malam yakubu

“Baba dan Allah toh ko zaa shiga da ita ciki? Idan yaso ko maganar ce kar ayi mata tunda nasan ba gane ta zatayi ba.”

“Abinda zan ce kenan, taso yan mata muje ciki, ya sunan ki.”

“Raihana.” 

Jerawa sukayi tare da Aryan din har kofar gidan 

“Please karki yi kuka, komai zai wuce zamu san yadda za’a yi,just be strong kinji? For me.”

Gida masa kai tayi, ya tsaya daga kofar ita kuma tabi bayan Baba Yakubu zuwa cikin gidan kirjinta na dukan uku uku.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post