Rumbun Qaya page 58

Rumbun Qaya page 58

Rumbun Qaya page 58

RQ

  Page 58

*****

A tsaye take a gefen dakin ta, ba kasafai ta fiye fitowa a irin wannan lokacin ba, ta kan zauna a daki a mafiya yawan lokutan musamman idan gidan ya zama babu yaran duk sun fice. Yau tunda ta tashi gabanta ke faduwa kamar wani babban al’amari yana shirin faruwa da ita. Randar dake gefen dakin nata ta bude ta zuba ruwa a buta ta zagaya bayi domin kama ruwa sannan ta dan wasa kafarta ta dauke hankalin ta kuma daga tunanin dake bijiro mata. Fitowar ta kenan tana tattakowa a hankali zuwa kofar dakin nata tana kallon yanayin yadda rana ta bude kwal kamar irin azahar din nan sosai. Sallama taji ta Malam Yakubu yana shigowa cikin gidan, lullubin dake kanta ta ja ta gyara zuwa saman kafadarta sannan ta amsa masa jin kulin ta Ya shigo kai tsaye, a bayansa muryar mace taji da batayi mata kama da ta yan matan gidan ba. Amsa sallamar tayi tana sakè matsawa daidai kofar dakin nata kamar zata shiga. Kanta ne yayi wani irin sarawa tayi azamar dafe shi tana jin jiri na neman kai ta kasa. Da sauri cikin daga murya tace


“Dan Allah karta karaso nan, dan Allah ta tafi bana son ganin ta.”


“Wacece ?” Malam yakubu yace yana nazarin yanayin da ta shiga ganin raihanan


“Ban santa ba, dan Allah ta tafi bana son ganin ta.”  Ta sake maimaitawa tana yinkurin juyawa ta shige dakin nata. Kukan raihana ne ya karu, ta durkusa a bakin simintin kofar dakin tana sakè fashe wa da kukan.


“Tashi tashi, ba kuka zakiyi ba. Abinda nake son ku gani kenan dama, nasan za’a yi hakan, amma ba wai yin kanta bane ba, an riga an raba ta da kowa nata ne, an saka mata wani ciwo me Zafin gaske akan duk abinda ya danganci gida.”


“Zata warke?” Ta tambaye shi cikin muryar kuka


“Sosai ma, ai maganin ne yazo, in sha Allahu karshen abun kenan.”


“Mike muje shashen Asiya ki zauna kinji? Yaran gidan sun tafi makaranta ne amma daf suke da shigowa.”


Tashi tayi tana kallon dakin da ammyn ta shige, babu ko Motsin ta gashi tana son shiga taga Halin da take ciki amma babu dama sam, dole ta hakura ta bishi zuwa bangaren Asiya din, ta zauna a gefen dan karamin gadon dakin na kaba taje ta debo mata ruwa a randa ta kawo mata sannan suka gaisa a mutunce.


****Daga chan jikin wata bishiya Aryan ya tsaya yana magana da Kamal a waya, yana sanar dashi abinda yake faruwa, da zuwan su Adam din da duk information din da ya samu daga wajen yaron da yake tare da Adam din. Ganin Malam Yakubun ya fito yasa Aryan katse wayar ya dawo wajen domin jin yadda akayi da suka shiga


“Abinda dai na sanar daku din shine ya faru, dole sai anyi maganin sannan za’a samu waraka gaba daya.”


“Yanzu ta zamuyi? Barin ta anan yana cike da babban hatsari tunda suka gano tana nan din domin a Yanzu haka suna cikin garin nan ma already, nasan jiran fitowar mu suke kila suyi attacking dinmu, ba zai yiwu mu dauke ta mu tafi da ita va?”


Girgiza kai Malam Yakubu yayi, sannan yace


“Bana tunanin hakn zai yiwu gaskia, baka ga halin da ta shiga ba ne ganin yarinyar nan, ina tsoron ma kada ciwon nata ya tashi dan baki daya yanayin ta Ya sauya, toh ta yaya kake ganij zata yarda tayi tafiya tare daku?”


Dafe kai Hydar yayi da ya zama kamar ruwa a cinye shi a wajen saboda fargaba da tashin hankali, da kyar ya iya bude baki yace


“Ina ganin ni da kanwata ne bata so ta gani, hakan ba zai shafi Aryan ba nake gani ko?”


“Eh toh, bansan wanne irin Aiki akayi ba, amma idan gaba daya ne bana jin har shi din ma zata amince, sai dai mu gwada, bana kuma son mu kara dagula al’amarin ne.”


“Gaskiya ne.” Aryan yace yana dora hannun sa a saman kafadar hydar, wai yau shine yake kokarin kwantar ma wani hankali. Wani messege din ne ya kara shigowa wayar sa, dama abinda yake jira kenan, dan matsawa yayi kadan sannan ya bude


_”Oga suna planning shigowa ciki yanzu, muna tare da thugs ne kuma an basu umarnin daukar Madam ko Hajiyar da kuka zo gani.”_


“Adam!” Aryan ya furta a hankali yana kallon hanyar, baya son mutanen wajen su shiga Matsala saboda su, dan rayuwa suke me dadi da inganci ba irin tasu ba me cike da tashin hankali da tsantsar cin amana. Matsawa yayi wajen hydar yace ya taso suyi magana, Ya sanar dashi abinda yaron yace sannan ya dora


“Menene abun yi? Bana so mu zamar ma bayin Allah nan matsala, dan na tabbatar a yadda Adam yakeji zai iya zasu aikata komai.”


“Akwai matsala, Ammy ba zata yarda ta bimu ba, kana ganin muka barta anan zasu barta ne?”


“Ba zai yiwu mu barta ba, dole zamu sake taking risk din kawai. Zan shiga a matsayin likita da zan duba ta, idan ta amince sai mu ce zaa kaita asibiti ne, daga nan sai muyi kokarin fitar da ita daga garin.”


“Ayi hakan, Allah yasa ta amince.”


“Amin.”


“Malam dan Allah ina zamu samu mota?” 


“Anan? Eh toh, akwai nan makocin mu Isah da yake haya zuwa cikin gari, dazu naga ya dawo ko hutawa yake? Sai dai idan shi zaa yiwa magana.”


“Ayi masan dan Allah. Ba zai yiwu mu bar mahaifiyar mu anan ba domin rayuwar ta na cikin hadari sosai, ina ganin zamu sakè gwada saar mu ne kawai, na gwada shiga din a matsayin likita ko zata amince.”


“Toh Bismillah, muje ciki, kai kuma ko zaka yi sallama gidan chan muji ko Isan zai sake fita.”


“Yawwa ayi hakan, bamu da time.”


Aryan yace a dan gaggauce 


Ciki suka shiga zuwa dakin nata, tana kwanci kanta na jujjuya mata kamar zai fashe ga wani jiri wanda a kwancen ma yin sa take yi suka shigo.


“Innar yara jikin ne?” Malam Yakubu yace yana da jikin labile


“Eh malam, kai ne kamar zai fashe. Don Allah a samo min magani.”


“Tashi ga likita nan yazo, abokin Hamisu ne nan na makota, tashi ya duba ki idan zai yiwu sai ya rubuta maganin idan ba zai yiwu ba sai mun bishi Asibitin su chan cikin gari.”


“Toh.” Tace tana mikewa zaune, suka hada ido da Aryan din ai da sauri ta kwala kara, fita yayi shima da sauri har yana cin tuntube da kofar. Asiya ce suka fito tare da Raihana da sauri, ganin aryan yasa raihana yin wajen sa ita kuma Asiya ta shiga dakin Ammyn.


“Menene? Me ya same ta?” Ta hada tambayar waje daya tana kallon sa hankali a tashe


“Calm down kinji? Babu komai muna son ganin mun fitar da ita daga nan ne, but hakan ba zai yiwu ba sai bata ganin mu dukka, sai munyi hakuri mun bi komai a sannu, zo muje naga ko Hydar ya samu motar, idan yaso sai su, su dauke ta kawai mubi bayan su. Time yana kara kurewa.”


Hannun ta ya kama suka fito wajen suka tarar da Hydar da Isan a tsaye ana magana har ya jawo motar ma, 


“Dama mota na shigowa nan?”


“Eh Amma ta chan baya ne, sai anyi zagaye idan mutum ba a garin yake ba, ba zai gane ba.”


“Haka ne, saura babura guda uku dan Allah, dan ba zai yiwu mu koma wajen motar mu ba.”


“A cikin gidan nan ma ba zaa rasa babura ba, kaga biyu nan nasu Awaisu, bari na zagaya baya na kirawo shi sai Isuhu ya dauko nasa shima.” 


Isan yace yana barin wajen da sauri dan ya hasaso zai samu kudi sosai a wajen su, shi dama kuma mayen kudi ne kowa yasan shi. malam yakubu ne ya fito Aryan ya fada masa abinda ya tsara kawai, hakan kuwa akayi, suka hau  suka bar wajen sannan aka fito da ita tare da Asiya da Matar kawu Liman na gidan sai malam yakubun a gaba.

Ba hanyar da su Aryan din suka shigo ba tanan suka bi ba, hanya ce sosai babba kuma sai dai zagaye ne. Wayar sa ya dauka ya kira Adam domin baya so ma yaje musu wajen da yan iskan da ya dauko ya sake tayar musu da hankali duk da su  din ma ba baya ba, mafarauta ne a garin idan ka cire gidan su Malam Yakubun da yan tsirarin gidajen. 


“Kar ka wahalar da kanka shiga cikin dan mu tuni mun wuce,kuma wallahi wallahi idan wani abu ya faru,sai na nuna maka na fika sanin duniya na rantse da Allah.”


“Kai karamin dan iska ne, idan ka isa ka tsaya a in da kake, kaga yadda zan sa karnuka su yagalgalaka na rantse da Allah, kuma Yanzu ma ba hakura nayi ba, zan biyo bayan ku idan har zaka dauke min mahaifiya babu abinda ba zan iya aikata maka ba.”


“Idan ka fasa Adam, kasan daidai nake da kai, dan haka duk abinda zakayi kayi, mahaukaci kawai. Sai nayi maganin ka.” 


Ya katse wayar ya maida ta aljihun gaban rigar sa. Bayan motar suke bi har suka fita daga lungunan suka hau main titin, wani abokin sanaar Isan suka hadu dashi zai koma gida isa ya tsaida shi ya dauki su Aryan din a motar sa su kuma su Isuhu suka koma bayan Aryan din ya basu kudade masu kauri suna ta godiya.


Aryan ya riga yasan Adam sai sun biyo bayan su, ya kuma san a lokacin daf Kamal yake da shigowa tare da yaran sa, hakan ya bashi relief duk da yasan dole sai ya koma ya tabbatar da basa garin kamar yadda yace masa Amma yana da yakinin ba zai yi musu komai ba ko dan gargadin da yayi masa kuma yasan tabbas Hajiya zeenat na wajen sa dole zai bi a hankali tunda Yanzu be samu abinda yake so din ba.


  A kofar shiga babban garin suka hadu da su Kamal, a waya sukayi magana dan basu tsaya ba saboda jikin Ammyn ya rikice suka ce su hadu a asibitin garin domin suna da bukatar chapke Adam da yaran nasa dan haka suka bi hanyar da su Aryan din suka baro su kuma suka shiga cikin garin. Direct babban asibitin garin suka nufa wanda yake a matsayin zone 1 saboda haka yake da duk manyan kayan aiki da manyan likitoci da suke shigowa daga chan cikin gari suna komawa kullum. Yanzu ma akwai likita saboda haka suna zuwa aka karbe ta aka duba ta sannan aka rubuta mata maganguna ciki har da na matsanancin ciwon kan. Sanda suka gama da asibitin sannan yamma tayi sosai, ba zai yiwu su dau hanyar barin garin ba duba da yanayin nisa garin, Malam Yakubu ne ya nema musu alfarma sauka a gidan bak’i, gidan da wani me kudi a garin Alhaji Ahmad ya gina saboda bakin sa idan sun zo anan yake saukar su. Mukullin ya basu dan a lokacin ma babu kowa a gidan. Chan dakunan ciki aka kai Ammy saboda ma karsu hadu aka ce mata zasu kwana anan ne zuwa gobe su wuce gida, bata kawo komai ba kuma kan nata yayi sauki musamman ga asiya a tare da ita sai ta ware. Daki biyu bayan na ammyn aka bawa su Aryan,Aikuwa ya shafawa idon sa toka yace shi da matar sa zasu zauna hydar shi kadai dan a lokacin kamal sun wuce dasu Adam da suka labe suka kama su a hanya. Lamido kuma ya tsaya kawai a kano dan yasan ko yazo zai sake complicating abun ne tunda ga halin da Ammyn take ciki. Wuce wa yayi kawai rijiyar lemo gidan wani babban malamin sunna da yake maganin ire iren wadannan matsalolin ya same shi ya sanar dashi komai, suka shirya zasu tafi gobe tare daga nan ya wuce hotel ya kwana.

   Lawan ne ya maida su Malam Yakubu gida tare da matar Kawu Liman isa kuma ya zauna suka fita tare da Aryan samo musu abinda zasu ci, suka samu wani restaurant karami suka siyo abinci da gurasa sai tsire da soft drinks da ruwa. Malam Isan ne ya mikawa su Ammyn sannan shima aka bashi nasa hade da kudade masu kauri sannan yayi musu sallama ya tafi akan zai dawo da safe ya dauki Aryan din suje ya dauko motar sa.

Ledar da akayi ma hydar daban Aryan ya mika masa sannan yace


“Sai da safe Yaya.” 


Da sauri Hydar ya riko shi suka saka dariya a tare, yanayin shekarun baya ya dawo musu a lokacin


“Dan wulakanci bari na zakayi?”


“Me zanyi? Zan kwana da kai ne?”


“Kafi karfi na, sai da safe.” Hydar yace yana sakin shi. Murmushi kaawai Aryan din yayi yana jin wani closeness da hydar din kamar a shekarun baya, ya wuce dakin da Raihanan take ciki. A chan gefen katifar dake malale a kasan dakin Ya hango ta, ta kwanta l’amo kana gani kasan ta gaji sosai. Ajiye ledar yayi a kan carpet din dakin ya karasa gareta gami da dagota ya jawota jikin sa yana kallon kumburarrun idanun ta da suka daga saboda kuka. Da yasan abinda zasu tarar kenan da be zo da ita ba, shi a tunanin sa suna zuwa komai lafiya tafiya kawai zasuyi, amma sai aka kuma samu akasi.


“Ina ammyn?”


“Tana dakin ta, ta samu sauki ma ta ware fa, aikin sihiri ne amma in sha Allah komai yazo karshe kinji?”


Gida masa kai tayi, ya share mata fuskar da gefen hannun sa sannan yace ta wanko hannunta tazo suci abinci. Toilet din dake cikin dakin ta shiga ta wanke hannun ta dawo suka zauna Ya bude musu abincin suka fara ci a hankali. Gurasar suka fi ci da naman sannan suka sha juice din ta matsar da ragowar gefe ta koma gefen katifar bayan ta kara wanke hannun ta. Rigar jikinsa ya zare ya makale ta jikin kujera ya bar singlet yazo ya zauna a kusa da ita.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post