Rumbun Qaya page 67

Rumbun Qaya page 67

 

Rumbun Qaya page 67

**RQ**

       *67*

“Hamma Muhammad?” Tace tana zaro ido

“Yes Raihana, shi da Zainab. Ba shi kadai ba.”

“Innalillah.” Tace a kidime, dan bata taba kawo Hamma Muhammad da irin wannan halin ba.

“It’s ok, ba komai.” Aryan yace ganin yadda raihanan ta rude

“It’s not,dole sai an musu hukunci daidai dasu, kuma ba wai a hannuna ma case din yake ba, dan haka kar ma kace komai.”  Kamal yace yana mikewa daga zaunen. Dr Mahfouz ne ya shigo aryan din na shirin yin magana

“Ashe ka shigo.” 

“Na shigo Dr, Barka da dare.”

Ya mika masa hannu.


“Barka dai, Aiki?”


“Alhamdulillah, ya akaji da patient?”


“Baka ga patient din nawa bane ba? Kamar bashi ba da yake madam tana kusa.”


“Na gani fa, Shiyasa Nima zan yi nawa waje tawa madam din nima tana jirana.”


“Ah ya kamata.” Ya fada suka saka dariya, murmushi kawai Aryan yayi hankalin sa na kan raihana da ta nuna kamar ma bata jin abin da suke cewa.


“Akwai security sosai a asibitin nan ko?”


“Ba laifi gaskia, wani abun ne?”


“No ba komai.”


“Ya jikin naka?”


“Alhamdulillah, please ka cire min drip din nan ya ishe ni wallhi.”


“Yayi half ai, bari mu cire ka huta zuwa safiya sai a maidashi.”


“Ba za’a hakura ba?”


“Ai kana bukatar shi.”


“Ok, zan iya wanka?”


“Yes of course, zaka iya sosai, in dai kana jin karfin jikij naka zaka iya tashi, but sai ka kula wajen kan kar ka jika shi...”


“Ko da yake, ga amarya ma she can help you.” Ya karashe yana dariya. Taji wannan dai, amma sai ta fuske tayi kamar bata ji ba, ta hau dudduba abubuwan cikin ledar gabanta.


“Shikenan, idan akwai wani abu just call the nurses, sai da safe.”


“Ok, sai da safe.” Aryan yace 


“Let me walk you to the door.” Kamal yace suka jera tare, dan dama akwai maganar da yake son tambayar sa amma baya so yayi a gaban aryan din. Suna fita yace


“Come here.”


Ta kowa tayi zuwa gabansa, nauyi da kunyar abinda Muhd yayi ya hanata kallon sa. Ya sani sarai abun sai ya dameta, shi kuma ko kadan be ji komai ba, domin a yanzu baya jin akwai wani abu da zai faru dashi da zai bashi mamaki, komai aka ce mutum zai aikata toh fa zai aikata shi ne. 

  Yunkurawa yayi ya zauna ta gyara masa pillow ya jingina sosai, sannan yace ta zauna a kusa dashi akan gadon, zama tayi ya dora kanta a saman kafadarshi yace


“Kar kiji komai akan abinda Kamal yace, babu wani new abu a wajena akan halin mutanen duniyar nan, kowa zai iya komai akan selfish interest dinsa, so ki manta komai kinji? So nake mu manta da komai da kowa mu fara sabuwar rayuwar mu, away from everything.”


“Duniyar nan kamar rumbu ne da kayan abinci, sai dai an cika shi da kayoyi wanda zaka sha wuya kafin ka kai kasan har ka mori wannan kayan, duk in da kasa kafarka k’aya ce zata soke ka..”


“Haka ne.” Tace a sanyaye tana jan kukan da yake ta neman cin karfinta 


“So ki daina damuwa, na daina nima from the moment da nasan ina dake, I have someone in my life that needs me, tun daga lokacin na watsar da komai.”


“Yanzu ya kake ji? Kan ya daina ciwo.” 


“Alhamdulillah. But it feels so heavy, kamar an dora wani babban dutse akan”


“Sannu, Allah ya kara sauki.”


“Amin. Zaki taimaka min? Nayi wankan?”


“Um.” Ta gid’a kanta.


“Thank you.” Yace yana murmushi 


Tashi tayi ta sauka daga gadon ta nufi toilet din. Wayar sa ce tayi yar kara kdan saboda baya son karar.


“Na wuce sai da safe.” Kamal yace yana dagawa 


“Ok, night.” Ya kashe ya ajiye, sai ma ya kashe ta gaba daya ya sakata kasan pillow. 


Ruwan ta hada me dan dumi sannan ta fito


“Saka key a kofar kamal ba zai dawo ba.”


“Ok.” Tace ta je ta saka key din sannan ta dawo. Da hannu ya nuna mata botir din rigar, ta matso ta taimaka masa ta bude su sannan ta zare masa rigar.


“Thank you.” 


“Zaki ya sauka.”


“Um um ba zan iya ba.”


Yace mata a shagwabe ta kalle shi da sauri ya sake marairace fuska, hannun sa ta rike ta taimaka masa ya sakko a hankali, suka nufi toilet din yana dan cijewa saboda kan nasa da yayi masa kamar zai fado. A toilet din ma kin yi komai yayi, komai tace sai yace ba zai iya ba, haka da daure ta cije tana gogocewa daga kallon sa yana kokarin sakata dole sai ta kalle shin, haka aka gama suke fito yace ta kashe ac dakin saboda ji yayi yana jin sanyi, da sauri ta kashe ta bashi duvet ya rufa, ya dan dauki some minutes sannan ya dawo daidai, ya saka wasu kayan sannan ya zauna akan carpet din yayi sallah a zaune. Yana sallar ta koma toilet din ta gyara shi sannan tayo alwalar tazo ta dauki doguwar rigarta ta saka ta cire na jikinta da suke jike ta kai toilet din, duk in da tayi yana kallon ta har tazo tayi sallar a gefen sa ta idar. Matsowa yayi ya dora knsa a saman cinyar ta, ya rufe idon sa yana jin babu dadi jikin sa. 

  Sun dade a haka shiru babu wanda yayi magana, kowa da abinda yake tunani, ta kasa cire abinda ya farun a ranta, ya adda maimuna zata ji idan taji abun da ya faru? Kowa yasan Dss basu dagawa kowa kafa dan haka tasan dole zasu sha wahala sosai, bata tausaya masa ba ko kadan, saboda abinda yayi ma Aryan din ya chanchanci hukunci me tsauri. 


“Tunanin me kike?”


Yace yana kallon fuskar ta yana daga kwancen, ya dan dade da bude idon sa yaga tana tunani.


“Emm, ba komai.”


“Menene date din yau?”


“30th.”


“Yaushe zaki je clearance?”


“On 2nd.”


“Ok Allah ya kaimu.”


“Amin ya Allah.”


“Abinci?”


“Umm, zanci kadan.”


“Ok.” Kallon kansa tayi, yaji dadin kwanciyar bata so tace ya tashi, 


“Na tashi ko?”


“Un.” Tace tana murmushi 


“Dan kara ko 5min ne sai ki bani abinci.”


“Toh.” Tace ta zauna suka sakè yin shiru, yana rike da hannun ta daya yana wasa dashi, sai da aka kusan mintuna biyar din sannan ya tashi a hankali ya jingina da kujarar ta tashi ta je ta zuba masa abincin tazo ta zauna a gabansa ta tankwashe kafarta ta shiga bashi abincin a hankali. Yaci sosai har tayi mamaki, sannan ta kwashe plate din ta je ta ajiye ta dawo tace ya koma gadon.


“Um um, nan ya ishe mu. Bani pillow kiga.”


“A kasa?”


“Um, carpet din ai yana da girma, kuma yana da laushi.”


“A ah ni dai, please ka koma saman, ba zaka ji dadin kwanciya anan ba.”


“Kiyi hakuri ki barni anan,pleasee.”


Tsayawa tayi shiru, bashi da alamar tasowar 


“Miko min pillow din kizo mu kwanta.”


Zuwa tayi ta dauko ta kawo masa, ya kwanta a hankali sannan ya mika mata hannu, ta tako ta zauna a gefen sa tana jin kamar be kamata ya kwanta a kasan ba. 


“Oya kwanta.” Yace yana kulle idon sa. Hijab din jikinta da tayi sallah ta zare ta dora a saman kujerar sannan ta kwanta a gefensa, hannu ya saka ya matso da ita sosai jikinsa ya maida idon sa ya rufe saboda baya son buden idon sosai.

   Cikin bacci taji alamun yana ta jujjuya wa, bude idon ta, tayi da yayi mata nauyi saboda baccin dake kanta ta kalle shi sai taga ya hada zufa sosai ya rike kan yana jujjuya shi.


“Subhanallahi, ciwo yake yi? Sannu.”


Ta tashi da sauri tana rike shi.


“Kai na zai cire Raihanaa.”


“Ba zai cire ba, bari na kira su, sannu, ba zai cire ba.”


Ta ce tana mikewa da sauri har ta soma kuka.


“No Karki kirasu, bani maganin a cikin drawer din chan, nasha.” Ya fada da kyar. Wajen su drawer ta yi da sauri ta dauko maganin, ta dauko ruwa ta kawo masa ta ballo ta bashi yasha, still yana rike da kan nasa. Tana durkushe a gaban sa har ya soma lafawa a hankali yana fitar da gumi sosai.


“Kana jin zafi ne?”


Da ido ya amsa mata ta karo ac ta dawo gabansa ta durkusa tana jera masa sannu. Bayan ya lafa gaba daya ta taimaka masa ya koma gadon ta dan rufa masa duvet a kafarsa zuwa cinyar sa, bacci ya dauke shi nan take. Haka suka karasa daren wajen shida na safe nurse din da zata tafi ta shigo ta duba shi ta mayar masa da drip din sannan tace idan ya tashi ga maganin da zai sha sannan ta fita. Sallah tayi dan ta dan makara sannan ta gyara dakin dan kafin masu sharar su zo ta share idan suka zo moping kawai suke su wanke toilet. 


***Gaba daya hankalin Adda Maimuna da na abban su Aminan Ya tashi matuka, musamman da suka samu labarin tafiya da Muhd din a bakin wani abokin sa da suke a tare a lokacin yana daga gefe sai dai shi, duk kiran da zasuyi sunyi amma shiru baa san su waye suka tafi dasu ba. Yanke shawarar sanar da Ammy sukayi da Dadah a kalla idan aka sanar da Lamido zai iya yin wani kokarin tunda an ce SS ne suka dauke shi. 

  Tun jiyan jikin ammyn ba wani dadi sosai shiyasa ko fitowa batayi daga dakin ba, tana kwance kawai dama karfin hali ne kawai amma tana jin jiki ba laifi. Dakin da suke kwana Adda Maimunan ta shigo jiki a mace ta zauna ta gaida Dadah sannan ta duba jikin ammyn.


“Ya akayi Maimunatu? Na ganki haka jiki a mace.”


“Wallahi Dadah, wai muhd ne jiya Wasu da ake zargin yan sanda ne na farin kaya suka zo suka tafi dashi, toh tun jiyan muke saurare amma shiru gashi har an kwana.”


“Innalillah, yaushe? Me yayi musu?”


“Wallhi Dadah muma bamu sani ba.”


“Kai Subhanallahi, toh! Allah yasa ba wani babban abun bane ba.”


Ammy tace tana mikewa daga kwanciyar da tayi


“Toh Allah yasa, amma su DSS ai basa kwansu sai da zakara, dole akwai dalili, amma dai, bari na kira Lamido naji, ko zai iya wani abu akai duk da ba lallai ba Kinsan suna da tsari.”


Dadah tace. Shiru sukayi gaba daya ta dauki waya ta kira Lamido sannan ta saka a handfree


“Tsohuwa me ran karfe, daga tahowa ta har kin fara missing dina ne?”


“Toh ba dole ba, miji baya kusa. Ya hanya ka koma kalou?”


“Alhamdulillah wallahi, ya jikin ammyn?”


“Da sauki Alhamdulillah.”


“Allah ya kara sauki, na kira jiya da daddare inaga kunyi bacci time din.”


“Watakila kam. Yar Matsala ce aka samu, muhd kanin ka ne aka ce jamian tsaro na farin kaya…”


“Sun tafi dashi ko? Na sani Dadah.”


“Toh! Me ya faru?”


Tashi yayi daga in da yake zaune ya fita sannan yace


“An kama shi ne da laifin abinda ya faru da Aryan.”


“Naam!?”


“Akwai yarinyar da suke tare a Office din su Aryan din, to kamar tana son Aryan din ne, shine sukayi irin abun nan da ake cewa tunda bamu samu ba kowa ma ya rasa, Allah ma ya takaita abun ya zo da dan sauki babu asarar rai.”


“Turkashi! Shi muhdun?”


“Wallahi, toh kinga ai babu abun cewa, zasu bincika shi idan har bashi da laifi zasu sallame shi, amma idan har yana da laifi toh fa dole zasu hukunta shi.”


“Ashsha, abu beyi dadi ba, shikenan, sai anjima.”


“Yawwa, zan kira idan ammyn ta tashi.”


Duk sunji komai babu bukatar maimaitawa, adda maimuna har ta soma kuka dan bata taba tunanin zai aikata hakan ba, har son da yake ma raihanan ya kai yayi risking life dinsa haka? Kunya da nauyin ammyn ya rufe ta lokaci daya, mijin yarka aso a salwantar wa da rayuwa.


“Yayi wauta sosai yaron nan, na tabbatar yarinyar da aka ce ita taja raayin sa, wannan wacce irin Kaddara ce haka?”


“Be kyautawa kansa ba, ya kuma cuci kansa.”  


“Um um, karki cika magana kije Kiyi masa baki, addua zakiyi masa, tsautsayi da Kaddara dai.” 


Ammy tace


“Sa kai ne da dorawa kai, idan ba haka akan da aka fara hana aure? Shi bashi da tawakkali? Eh?”


“Ya isa dai, duk ma me zaki ce a yanzu cikin bacin rai ne, ki sawa zuciyar ki sallama.”


“Dadah ya zanyi? Laifi ne fa babba ya aikata, Yanzu da wanne idon zamu kalli mijin Raihanan? Ita kanta da wanne ido zata kalle shi ace dan uwanka na neman ran mijinka?”


“Abun da ya riga ya faru dai ya faru, yanzu addua zamuyi Allah ya fitar dashi kawai, amma kuskure an riga an tafka shi.” Dadah tace ganin yadda Adda Maimunan ta shiga damuwa 



Tashi tayi ta fita ta samu Baban su Aminan ta fada masa abinda yake faruwa, shima ya kadu sosai da laifin da aka ce muhd din ya aikata, be kuma taba hasaso zai iya aikatawa din ba. Ya dauka komai ya wuce Ashe abun yana ransa, ya biye ma dokin zuciya ta kaishi ta baro shi. 



*****Har su Ya nabeela suka zo da wata cousin din Mummyn su be tashi ba, gida Raihana tace zata je ta dan dawo ta bar su Ya nabeelan a tare dashi. Gidan sa ta fara zuwa ta dauko masa yan kayan sa ta dauki nata hade da khakhi dinta saboda clearance din gobe, sannan ta wuce gidan Adda maimuna. Kunya da nauyinta ya hana adda maimuna yadda su hada ido, ita bata ma sun san maganar ba sai da ta shiga daki wajen ammy sannan take fada mata, abinda ma ya hanasu zuwa yau da wuri kenan suna tunanin idon ta zasu kalli Aryan din


“Yace ba komai Ammy, ni kaina baki ji yadda naji ba, na dauka zai yi fushi sosai amma ko kdan be damu ba.”


“Amma ai duk da haka sai yaji babu dadi, a hari ranka fa? Mutum ya kai makura a kinka fa kenan.”


“Nima haka na gani. Kuma wallahi Sir Kamal ba zai kyale ba, yanayin sa kadai ya nuna ba sassauci, sai hakuri Kinsan yanayin aikin nan nasu, ba ruwan su da alaka ko waye kai.”


“Shine dama matsalar, sai hakuri kam.”


“Tafiya zan.”


“Toh, kamar naji an gama abinci tun dazu an kasa kai muku, ki tafi dashi idan Dada zata sai kuje tare, yau kam bana jin dadin jikina amma zan yi magana da Aryan din.”


“Ok tam, Allah ya kara sauki.”


“Amin.”


Tare suka tafi da Dadahn suka tarar da Abby a chan Aryan din ya tashi yana yin breakfast, ta kasan ido ya kalle ta, ta ajiye kayan hannun ta, ta durkusa ta gaida abbyn ya amsa sannan ya gaida Dadah shima sannan yayi musu sallama ya tafi. 

  Duba shi Dadah tayi ta dawo falon ta zauna tare da wannan matar sai Ya nabeela ta mikawa raihana cup din da plate tace


“Karasa aikin ki.” A kunyace ta karba ta fita ita kuma ta zauna a in da ya Nabeelan ta tashi


“Shine kika tafi kika barni?”


Yace yana kallon ta


“Gida naje na dauko mana kayan mu.”


“Wait, wai zama zamuyi tayi anan ne?”


“A ah amma naga babu kayan kuma babu dadi maimaitawa shiyasa.”


“Uhm, da kin bari na tashi sannan kika tafi, ina ta neman ki.”


“Toh gani na dawo ai.”


Tace tana murmushi 


“Tam sannu da dawowa.”


“Kan ya daina ciwo?”


“Um kadan, ya fara amma da ya ganki sai ya daina.”


“Da gaske?”


“Da gaske.”


“Umm, ammy na duba ka, da Adda maimuna, ammyn bata dan jin dadi ne shiyasa bata zo ba.”


“Ba komai, tayi kokari ma ai da tazo.”


“Dr Mahfouz yazo?”


“Yazo, yace tafiya zamuyi in ji daddy ko?”


“Naam?”


“Yes, ki fara shiri idan muka tafi sai an ganmu.”


Shiru tayi akayi sallama aka shigo, suka gaisa ta duba mai jiki sannan ta fita. Tana fita Hajiya zeenat ta fado masa. Da sauri ya dafe kansa 


“Subhanallahi, nayi babbar mantuwa. Ina wayata?”


“Gata.” Ta mika masa ya karba da sauri, call log ya shiga ya tarar da missed calls din Lawwali sun fi 50, salati yayi a ransa yayi saurin kiran sa yana saka wayar a kunnen sa 


“Lawan? Kana jina!?”


“Eh Alhaji, ina jinka.”


“Afwan ka kira ni Ashe, wallahi wani dan accident na hadu dashi muna gama waya a daren, akayi admitting dina sai yanzu na samu kaina.”


“Subhanallahi, Shiyasa nayi ta kira shiru, Ya jikin?”


“Alhamdulillah, Ya ake ciki?”


“Wallahi tallahi an samu matsala, tun a daren wallahi ta fice.”


“Ta fita?”


“Wallahi, babu irin duban da bamuyi mata ba, amma wallahi babu ko duriyar ta.”


“Toh! Innalillah.”


“Wallahi ranka ya dade, sama ko kasa mun rasa ta.”


“Zan kiraka.”


Yace sannan ya kashe ya yi saurin dialing number sa


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*



*ZAFAFA BIYAR BACTH A*



1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350

 *(Bilyn Abdul)*



2.. _KAI MIN HALACCI_ 350

*(Miss xoxo)*



3.. _BURI DAYA_ 350

 *(Mamu gee)*


4... _DAURIN BOYE_ 350

*(Huguma)*


5... _SAUYIN KADDARA_ 350

*(Hafsat Rano)*


_Duka biyar 1500_


*___________________________*

    


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*



1... _DAURIN GORO_ 350

*(Hafsat Rano)*


2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350

*(Huguma)*


3... _QAUNAR MU_ 350

*(Mamu gee)*


4... _IGIYAR ZATO_ 350 

*(Miss xoxo)*


5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*



_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*


1... _MIN QALB_ 350

*(Mamu gee)*


2... _SARAN ƁOYE_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _KIBIYAR AJALI_. 350

*(Miss xoxo)*


4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350

*(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*____________________________*



*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*


1... _ALKIBLA_ 350

*(Huguma)*


2... _DALAAL_  350

*(Miss xoxo)*


3... _UBAYD MALEEK_ 350

*(Mamu gee)*


4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350

*(Hafsat Rano)*


5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350

*(Bilyn Abdull)*



_Duk biyar 1500_


*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*


1... _SO DA ZUCIYA_ 350

*(Mss xoxo)*


2... _TAKUN SAAKA_ 350

*(Bilyn Abdull)*


3... _HALIN GIRMA_ 350

*(Hafsat Rano)*


4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350

*(Huguma)*


5... _DEEN MARSHALL_ 350

*(Mamu gee)*



_Duk biyar 1500_


*______________________________*



*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*


1... _BAKAR INUWA_ 350

   *(Bilyn Abdull)*


2... _RAYUWAR MACE_ 350

    *(Hafsat Rano)*


3... _NOOR ALB_ 350

     *(Mamu gee)* 


4... _MASARAUTA_ 350

    *(Mss xoxo)*


5... _KUFAN WUTA_ 350

    *(Huguma)*


_Duk biyar 1500_


*_____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETE )_*


1... _FARHATAL QALB_

*(mss xoxo)* 400


2... _GURBIN IDO_

*(Huguma)* 400


3... _SANADIN LABARINA_

*(Hafsat Rano)* 400


4... _INAYAH_

*(Mamu gee)* 400


5... _BABU SO_

*(Bilyn Abdull)* 400


_Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_


*BATCH F



*RUMBUN QAYA🔥


*DAUDAR GORA*🔥


*IDON NERA*🔥


*A RUBUCE TAKE*🔥


*KI KULANI*🔥


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


IDAN AN GAMA SU DOCUMENTS DINSU DUK DAYA 400 NE GUDA BIYAR DIN 2k 


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥


0022419171

Maryam sani

Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+227 90 16 59 91


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*


*Thanks for choosing us*🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post