Wa ya Kashe Rukayya? Page 6

Wa ya Kashe Rukayya? Page 6

Wa ya Kashe Rukayya? Page 6

WA YA KASHE RUKAYYA*?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.

6️⃣

Aminai ne su biyar ɗin waƴanda suka yarda da juna suka dankawa juna Amanar kansu ta yadda ko iyayansu basu san cikinsu ba, duk abinda ya samu ɗaya kamar ya samu dukkan su ne inma mai kyau ko akasin hakan, sun yarda sun amince babu mai raba su ko shiga tsakaninsu idan ba mutuwa ba, suna tsananin son juna da tausayin juna.

  Suna da banbancin ra'ayi a tsakanin su amma kuma sukan fahimci juna musamman idan Amal ne ta kawo maganar, wani irin so suke wa Amal ɗin wanda baida iyaka, ta kasance kamar ita ce ke jan ragamar ƙungiyar tasu. Suna rayuwar su yadda suke so babu takura duk abinda suke so shi suke yi, iyayansu sun tsaya masu akan komai kasancewar su ƙusoshin gwamnati masu faɗa aji a ƙasar, sam basu da wulakanci amma fa idan ka taba ɗaya a cikinsu tabbas zaka fuskanci tozarci da wulakanci na ƙarshe.

  Tare suke magance matsalolin su ba tare da kowa yaji ba zasu ci su suɗe abinsu. 

A lokacin da suka gama makarantar gaba da primary akai wa Laila aure da ɗan uwanta wanda ya kasance a gidan su ya taso, auran da akaiwa Laila sam bai shafi abotan su ba domin kuwa rayuwa irin ta turawa ake yi a gidan su Lailan wanda kowa nada yancin kansa babu takura. 

  A yanzu tana da ƴarta yar wata bakwai tsarar Amatulla mai suna Fatima amma tana can a Kano gidan iyayanta suna kula da ita dan tunda ta haifeta ko nono bata bata ba wai dan kar nononta ya lalace sai madara ake bawa ƴar.

 Mahaifiyar Amal ta rabu da mahaifinta tun Amal ɗin na yar shekara goma wanda yanzu haka ba ta san a duniyar da yar tata take ba kuma ko ganinta tayi ba lallai ta shaida ta ba tunda shekarun sunja sosai amma ita kam Amal sarai tasan uwarta tasan wacece kawai tana jin zafinta ne saboda yadda tai watsi da ita a lokacin da take tsananin bukatar ta.

A yanzu haka mahaifiyar Amal babbar yar jarida ce da ƙasa ke bala'in ji da ita.

  Mahaifin Amal ya kasance buzu ne wanda yazo daga ƙasar nijar ya ke niman na kansa anan Nigeria anan ne ya haɗu da mahaifiyar Amal har sukai aure iyayanta basa so sam kasancewar su masu rufin asiri kuma ƴar su tayi ilimin boko mai zurfi shi kuma sam basu san asalinsa ba abinda kawai suka sani shi ne shi ɗin ɗan nijar ne.

  Nacewar da mahaifiyar Amal ta yi ne yasa suka hakura sukai masu auran dan karsu rasa tilor yar tasu, inda mahaifin nata ya basu bangare ɗaya a cikin gidan sa suke zaune shi kuma mahaifin Amal ya ci gaba da niman kudinsa.

   Kakar Amal ta shiga ta fita wajan ganin ta raba wannan aure amma Allah bai bata sa'a ba har zuwa lokacin da aka samu cikin Amal ɗin.

  Amal ta taso cikin gata saboda yadda kakanninta ke nuna mata kauna suke kashe mata kuɗi kuma, a lokacin da ta isa shiga makaranta kakanta ya ɗauke ta ya kaita makarantar kuɗi wanda a lokacin sai ƴaƴan wane da wane saboda tsananin kaunar da yake wa jikar tasa, anan ne kuma ta haɗu da abokan nata guda huɗu in da ta zame ta biyar ɗin su sukai wani irin mugun shakuwa na ban mamaki.

Amal na da shekara goma a duniya Allah ya kawo ƙarshan zaman iyayan nata  hakanan babu laifin zaune babu na tsaye mahaifiyar Amal ta tada fitinar sai ya sake ta domin bata kaunarsa bata ko son ta buɗe idanuwanta ta gansa, dole ya rabu da ita badan ya so ba ya sauwake mata inda ya ɗauke ƴar tasa ya tafi da ita yaje ya kama gidan haya suke zaune a ciki, abinda yai matukar batawa kakan Amal rai yace abar shi shida yarsa ai bari ba shegiya bace da ubanta.

  Mahaifiyar Amal ta shiga tsananin tashin hankali akan tafiya da yayi da Amal ɗin gashi bata san inda ya nufa ba, sai da mahaifiyarta ta sake shiga da fita kafin aka samu ta manta da ƴa da uban gaba ɗaya wanda ya kai ya kawo sam bata tunasu kamar an shafe mata tunani akansu.

  Ba tare da bata lokaci ba kakan Amal yaiwa mahaifiyar Amal ɗin shirye-shirye tafiya ƙasar waje dan ci gaba da karatunta inda ta bar ƙasar ba tare da ta ƙara tunawa da ƴar da uban ba ko sau ɗaya tama mance da su a babin rayuwarta.

Amal taci gaba da zuwa makarantar da take zuwa inda mahaifin nata ne yake kaita da kansa idan an tashi yaje ya dauko ta.

   Ta shaidawa abokan nata halin da ta ke ciki inda suma suka gayawa iyayansu anan mahaifin Rahma ya samu mahaifin Amal ta batun cewa ko zai bashi Amal din ta dawo gidansa da zama a take ya nuna rashin amincewarsa dan gudun abinda zaije ya dawo kamar dai yadda mahaifiyar Amal ɗin tai masa.

  Anan mahaifin Rahma yace ya ɗauki nauyin karatun Amal din daga nan har zuwa jami'a kamar yadda ƴarsa Rahma zata yi.

Tun daga wannan lokacin mahaifin Amal ke ta ciwo a tsattsaye hardai ya kwanta wanda ciwon ya zamo na ajali ya tafi ya bar Amal ita kadai babu wanda ta sani sai Aminan nata guda huɗu da kuma makotan su.

    Mahaifin Rahma ya so ya sake ɗaukar Amal a karo na biyu amma ta ki amincewa ba dan komai ba sai dan tun farko mahaifinta bai amince da hakan ba wanda bata san dalilinsa ba kuma zata ci gaba da girmama ra'ayin sa ko bayan baya raye.

  Dole mahaifin Rahma ya kyale ta badan ya so ba amma daga ƙarshe shi da kansa ya miƙa ta gidan marayu saboda inganta rayuwarta ya kuma ci gaba da ɗaukar duk wata ɗawainiya nata bayan ya danka ta a hannun shugaban gidan marayun wanda shi ne ya zame mata uba sanyin idaniya.

   Amal ta tashi a gidan marayu cikin natsuwa da kwanciyar hankali har zuwa sanda mahaifin Rahma ya zama gwamna inda ya mallaka mata dankareran gida suke zaune ita da mahaifin nata da take kira Father wanda tunda matarsa ta rasu bai sake aure ba daga shi sai yan aiki a gidan a yanzu da Amal ke makaranta. 

  Shekarar mahaifin Rahma biyu kenan a kujerar Gwamna shi da mataimakin sa mahaifin Lailah.

        ************

Bayan sun gama cin abincin sun natsu suka maida hankali kan Amal wacce tace za suyi magana.

Nan Amal ta gaya masu yadda su kai da Ruky jiya da daddare, tunma kafin ta ƙarasa duka suka zabura suka zubawa Ruky ido.

"Ku daina kallona haka, ita gaskiya guda ɗaya ce kuma daga kinta sai ɓata akan me zamu ta aikata kuskure cikin kuskure....."

  Rahma ce ta katseta rai a bace tace "Idan ki kai wannan gangancin na rantse da Allah sai kinyi da kin sani da hannuna zan murɗe wuyanki kuma....."

   Amal ce ta katse su da faɗin "Ya isa ni ba hayaniya nace kuyi ba kawai ina so kowa yasawa ransa cewa mu abokaina na har abada kuma babu mai taba jin sirrinmu har abada kowa ya goge hoton wannan daran a zuciyarsa ku ɗauka komai bai faru ba, kuma har abada Amatulla baza ta taba sanin cewa bani ce na haifeta ba wannan sirrin mun binne shi kenan har abada kar wanda ya sake magana akai ".

A haka duka suka gamsu harma da ita kanta Rukayyan suka rufe maganar suka ci gaba da sha'anin gabansu a inda suka yanke shawarar gobe zasu je su sami Aliyu gaba dayansu akan maganar test din su.

  Laila ce tace bai kamata suje dukkan su ba abarta taje tai masa magana duk yadda sukai shi kenan.

 Gaba ɗayansu sun amince da hakan banda Ahmad da 

 ya kafeta da ido ba tare da yace komai ba.

          ******

Lailah ce ta fito daga office ɗin Aliyu ranta a matuƙar bace ta nufo inda suke zaune suna jiranta.

  Amal ce ta dubeta 

  bayan ta zauna tace "to ya ku kayi da mutumin ne?"

  Iska ta furzar cikin bacin rai tace "ai kun san komi akai da jakki sai yaci kara!"

Nayi iya kok'ari na amman abin ya faskara, 

Kunsan shi da taurin kan tsiya da girman kai kamar shaid'an".

  Wani irin kallo Amal tai mata tana tabe baki.

Rahma ta kwashe da dariya har tana kwarewa saboda kalaman Lailan.

Ruky ce tace "to yanzu ya za mu bullo masa kenan? Nifa wallahi ko kunsan cewa

 guy d'in burge ni ya ke yi dan ya iya d'aukar wanka k'arshe wallahi."

Wani irin mugun kallo Amal tayi mata cikin daka tsawa tace "kar ki k'ara batan rai dan Allah!"

  Ita kanta bata san sanda tai tsawarba haka nan taji zuciyarta na tafasa da kalaman na Ruky.

Rahma tace "meye wani abin burgewa ajikin wannan mai Bala'in ji da kai din ni dai baya burge ni bakuma ya bani haushi". 

       **********

Bayan sati d'aya yau ma kamar kullum sai wajan 8:30 suka shiga makarantar bayan sun san cewa 8am ya ke shiga ko minti daya ka ƙara bazai bari ka shiga ba.

Kai tsaye suka shiga cikin ajin suna takun ƙasaita da tak'ama, gaba d'aya k'amshin su ya bad'e ko ina.

Cingum ne a bakin oga Amal tana tauna abin ta cike da yanga kuma ita ce a gaba suna binta a baya.

Sosai ya bud'e murya yace "karku k'araso nan! Ku koma inda kuka fito,"

Ko kalma d'aya basu furta ba asali ma ko tsakin babu wanda ya yi a cikinsu yau suka juya waje suna wani jujjuya jiki. 

Cikin bacin rai yaci gaba da koyar da darasin sa ransa na suya, shi kam ya shiga uku soyayya da kishin yarinyar nan suna nima su zauta shi bai shirya ba, wai ma ya akai ya faɗa a tarkon yarinyar nan ne shida aikin sirri ya kawo sa makarantar nan amma jibi yadda yake nima ya kare a soyayya. Ya ƙare maganar a zuciyarsa yana mai jan tsaki a zahiri.

Ba tare da sanin sauran ba Laila ta zame ta nufi office din wani malami wanda ya kasance abokin yayanta ne dan ta kudiri aniyar sai ta saka an wulakanta Aliyu a karo na farko batare da shawarar abokan nata ba dan bata ma so wani a cikinsu ya dakatar da ita, ita kaɗai tasan irin cin mutuncin da yai mata ranar kawai faɗa masu ne batai ba dan karsu fassara ta wani iri kuma tasan cewa koma me zata yi dole ne su bata goyan baya baza su taba kwaye mata baya ba a gaban kowa ba sai dai idan sunje gida suyi duk uwar da zasu yi.

Zaune ya ke shida wasu malamai suna tattaunawa ta kwankwasa akai mata izinin shiga sannan ta shiga ta gaishe su nan suka fice suka basu waje dan dama sun gama.

"Lailah ya akai ne, ya karatun ya kuma shirin fara jarabawa ana karatu dai ko?"

Kuka ta fashe da shi sosai ta kasa magana.

Da sauri ya katseta a rud'e ya shiga tambayarta me akai mata?

 Cikin kuka da shasshek'a babu kunya babu tsoron Allah ta soma magana. 

"Malan Aliyu ya tsane mu a cikin makarantar nan, sam baya son ci gaban mu,  baya son farincikinmu da k'wanciyar hankali mu,

Kullum burin shi shine ya takurawa rayuwarmu.

Mun shigo makaranta last week ya kore mu daga ajin sa, yaba da test babu mu kuma yace duk wanda baiyi test d'in shi ba bazai ci jarabawar saba. Daga ƙarshe su Rahma suka ce inje in bashi hakuri ko zai sauraremu ya rubuta mana muyi dan kar muje duka ya koremu.

Na bishi _office_ d'in sa na bashi hakuri yace sai dai in siya test d'in da kud'i,  na bashi kud'i masu yawa yace shi kenan magana ta k'are zai rubuta mana namu.

Rannan ya kira ni _office_ d'in sa bayan naje ya ke cemin shi ya janye zancan kud'i saidai inbashi kaina".

Wani kalar zare ido Malan Musa ya yi yana kallonta cike da maɗaukakiyar mamaki bisa fuskarsa.

Ta k'ara fashewa da kuka mai cin rai duk wanda yagan ta a lokacin sai ya tausaya mata

 Taci gaba da faɗin "kowa yasan ni matar aure ce kuma ina matukar kaunar karatuna

burin mahaifinane in samu ilimi sosai kaima ka sani, wannan dalili yasa nabawa Malam Aliyu kai na saboda kawai ya bamu test d'in nan kada mu fad'i jarabawar sa.

A bin mamaki yau ya tare ni da zancan saidai in k'ara bashi kaina saboda test d'in nan ba abu bane mai sauk'i dazai iya bamu shi haka a bagas.

Na nuna masa sam ban yarda ba tunda abin nasa rainin hankali ne shine wai dan mun shiga lecture d'in shi yanzu ya koremu daga ajin".

 Tak'ara fashewa da wani irin kuka tamkar zata shid'e...........

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post