Rumbun Qaya page 72


Health College

Rumbun Qaya page 72

 

Rumbun Qaya

**RQ **


    72


***Drs din ne suka shigo su biyu, da nurse din guda biyu mata, ihun da take ya kara tabbatar musu da zargin su, aka Dr din ya duba ta, yace a barta akan allurar baccin saboda karayar da take jikin ta sannan suka fita.

 Fita Ya nabeela sukayi da Kamal suna magana a tsakanin su, duk jikij Ya nabeela a sanayaye yake, duk abinda mutum yayi koman daren dadewa sai ya dawo kansa, Yanzu wa zai ce hajiya zeenat mace yar gayu da kwalisa ce haka? Rayuwar ta juya mata baya a lokacin da tafi bukatar ta. 

   Sunyi iya yin su, sun mata abinda zasu iyayi mata har akayi mata aikin hannun amma kafar yayi damage, dan har infection ya shiga dan haka dole aka shiga aiki aka yanke ta, ga karaya ga hauka, abun ya hadar mata a lokaci daya, kuma irin haukan nan me me hawa da sauka, me saka surutai amma sarai tana gane kowa da komai. Ta sha bakar azaba bayan an fito da ita daga aikin guntule kafar,Amma ya nabeela ce kawai take tausaya mata. Chan asalin kauyansu aka aika, aka samo wata a cikin danginsu aka bata kudi ta cigaba da zama da ita dan baba tace ba zata iya ba.


****Kwana biyu Daddy ya kara bayan zuwan su, da ya tabbatar babu wata matsala ya tattaro ya dawo gida. Shigowar safe yayi, direct daga airport driver ya wuce dashi gidan su Raihana. Dadah bata nan taje gidan adda maimuna akan maganar muhd sai ammy kadai a falon tana zaune ta idar da sallar walaha Abby ya shiga ciki yana so ya dan huta. Knocking akayi a gate din, ta kalli lokaci taga tara da yan mintuna.


“Lallai Dadah tayi sauri.” Tace tana mikewa, jikinta sanye da hijab da ta idar da sallar ta fita zuwa gate din ta bude sai ta yi sak dan bata taba tunanin ganin shi ba. Da sauri ta maida kofar ta rufe ba tare da tace komai ba, ta koma ciki ta sanarwa Abby sannan ta shige dakin ta. Shi ya fito ya tarar dashi tsaye jikin gate din, ya shigar dashi cikin shima cike da mamakin ganin nasa.


“Kar dai isowar ka kenan?”


“Eh, Yanzu na sauka. Daga airport direct nan na taho.”


“Wai Masha Allah. Sannu da hanya, malam yahya ne ya kawo ka ko?.”


“Yawwa, eh shine, yasan gidan. Ya bayan saduwa?”


“Alhamdulillah wallahi, Ya karfin jikin?”


“Na samu sauki Alhamdulillah, na dan tsaya na sakè hutawa ne.”


“Allah ya kara sauki.”


“Amin, sai naga aisha kamar bata gane ni ba.”


“Hmm, ta gane ka mana. Zata manta ka ne?”


“A ah.” 


“Ta gane sarai, bari nayi mata magana.” 


Ya tashi ya shiga ciki, shi kuma daddy ya cigaba da kallon falon da gidan gaba daya, su da suka tarwatsa wa rayuwa sai gashi Yanzu sune rayuwar su a hade, tare da yaran su kuma. Shi tashi rayuwar be san yadda zai kirata a yanzu ba, kawai gashi nan ne dai.


   A zaune Abby ya same ta, tana ninke wasu kayan Dadah da aka wanke.


“IBRAHIM ne fa Ammy.”


“Na ganshi ai.” Tace tana basarwa.


“Kizo ku gaisa.”


Sakin kayan hannun ta tayi, ta kalli Abbyn sannan tace idanun ta na kawo ruwa


“Mutumin da ya wulakanta ni, ya raba ni da mijina da Yayana da dangi na gaba daya, yaki tausaya min a matsayi na na mace, ya manta karfin alaka ya bare matarsa ta wulakanta ni, shi kake cewa naje na gaisar?”


Zama yayi a kusa da ita, ya riko hannun ta.


“Na sani, nasan duk wannan. Na kuma fi ki daukar zafi a lokacin da na dawo, amma ya zamuyi da kaddarar mu? Ta hakan zamu sakawa Allah tarin ni’imomin da yayi mana? Ko bama wa Allah laifi ya kuma yafe mana? Ba wannan ba ma, yaran sa. Karki manta dawainiyar su gare mu. Ko dan Aryan da Kamal, IBRAHIM ya Chanchanci second chance, shi kansa fa ba wai dadin rayuwar yaji ba, dan Allah Kiyi hakuri Kizo muje, ki bashi damar neman gafarar ki tun kafin lokaci ya kure masa, domin idan mun ga yau ba lallai muga gobe ba.”

< /p>

Hawayen da take rikewa ne ya zubo, ba zata iya musu da Abby ba, bata saba ba bata iya ba. 


“Daure Maman Raihana,nasan ki da hakuri da yafiya.”


“Itama Zeenatun zaka ce na yafe mata ne?”


“Lala, wannan ko ni kika ce kin yafe mata wallahi sai mun yi sharia, duk da ko a yanzu duniya ta koya mata hankali. Amma da sauran ta. Domin wata shariar sai a  lahira.”


“Na zata zaka ce.” 


“Ban isa ba.” Yace yana murmushi. Tashi tayi yayi gaba ta bishi a baya. Ta wuce kitchen ta dauka ruwa da juice sugar free ta doro a plate ta kawo falon.


“Sannu da zuwa.” Tace bayan ta ajiye sannan ta zauna a gefen Abbyn


“Sannun mu, ina wuni?”


“Lafiya lou, an dawo lafiya?”


“Alhamdulillah, ya yara?”


“Lafiya lo.”


“Sai kaji labarin dawowar aisha, ko basu sanar da kai ba.”  Abby yace yana son kawo zancen da zai yi tsawo


“Na sani, nayi matukar farin ciki.”


Mikewa ammy tayi zata koma ciki, da sauri Daddy ya dan zamo saura kiris ya zube a kasa


“Ina neman alfarmar ki yafe min duk abinda nayi muku abaya, dan Allah ba dan ni ba.”


“Allah ya yafe mana baki daya.”


Tace ta wuce ciki. Bin ta da sauri Abby yayi, suka shiga dakin sannan yace


“Haba ammyn yara, haba Aishatu.”


“Me nayi kuma?”


“Yadda kika amsa ne, sam be ji dadi ba. Kuma da kin dan kara zama.”


“Ba muharrami na bane da zan zauna muyi ta musayar wayu ai, kaga kuma Yanzu akwai surkuta a tsakani.”


“Aisha!!”


“Gaskiya fa.”


“Allah ya shirya min ke.” Ya fita yana murmushi. Yasan duk abin nan tana yi ne kawai domin ran ta a bace yake, dan yasan tafi jin haushin abinda Daddyn yayi mata akan na hajiya zeenat. Saboda ita dama chan tasan zata aikata fiye da haka, amma me yasa daddy zai wulakanta su, ya ajiye duk alakar nan ya rufe idon sa ya kore su.

  Duk a kunyace Daddyn yake, ya kasa sakewa sam tunda suka shiga ciki, kwata kwata be ji haushin abinda Ammyn tayi ba, ya chanchanci fiye da hakan, dan yayi musu abinda yafi haka. Dawowar Abbyn ta dan sa ya sake har suka shiga hirar rayuwa da sauran abubuwa, wanda ya dauke su lokaci me tsawo,har Dadah ta dawo suka gaisa ta shiga ciki, ta samu ammy tana ta faman fushi akan zuwan Daddyn, baki ta bata ta dan kwantar mata da hankali sannan tace ta taimaka su hada musu abincj musamman tunda daga tafiya yake kuma doguwar tafiya. Kitchen din suka shiga ta baya, daidai lokacin me taya ammyn Aiki tazo, sai ta koma ciki ta barta da Dadan tana guiding dinta suka dafa abincin me dan karan dadi.


 Duk da yasan ya kamata ace Ya tafi ko dan gajiyar da ya kwaso, amma Ya kasa tafiya. Idan yaje gidan ma be san me zai yi ba, dan gaba daya gidan yayi masa baki yanzu.


“Kasan abinda ya faru da zeenatu kuwa?”


Girgiza kai daddy yayi


“Me Ya same ta?”


“Kamal be sanar da kai ba ko nabeela kenan.”


“Gaskia.”


“Ai tsautsayi ta hadu dashi, ko nace Kaddara. Mota ta bige ta kuma me motar ya gudu, in ta kaice maka labari Yanzu haka ma an yanke kafar, sai dai suna zargin kamar Har da ciwon hauka yana damun ta. Ni dai ban je na ganta ba, haka dai na samu labari.”


“Abinda ya chanchanta gareta kenan, ni bani da wani information akan ta da rayuwar ta tun bayan da na tafi, tun da zamu wuce na rubuta takardar saki na bawa Kamal nace ya bata, idan ta fito daga prison din dan na tabbatar sai ta fito, daga nan bamu sake maganar ta da kowa ba, dan sun san bana so.”


“Ta fito din kam, sai dai tun ranar da aka fito din baa sake sanin in da take ba, Ana zargin kamar dauke ta akayi, sai gashi kuma yan sanda sun kawo ta a karye cikin mawuyacin hali.

 


“Abinda ya dace da ita kenan Barr. Matar nan ta cutar da rayuka da yawa, tabbas nasan a karshe mutuwar wulakanci zatayi.”


“Kaje ka ganta.”


“Zanje, ko dan naga yadda rayuwa ta maida ita. Amma tare da kai zamu da hajiya aisha.”


“Aisha zata kuwa?”


“Zata, kasan ta da saukin kai.”


“Yanzu ai tayi tauri.” Yace yana dariya


“Rayuwa ce ta maida ita hakan.” 


Shigowar da tayi yasa su yin shiru, ta ajiye musu flasks din abincin. Sannan ta sakè fita. Tare suka ci abincin, wanda rabon daddy da yaci abincj me yawa irin haka ya manta, sai yaji kamar an dawo rayuwar su ta baya ne, babu abinda ya faru.


“Allah ya jikanki Khadija. Allah yasa kina aljanna.” 


Yace a sanyaye, 


“Amin ya Allah.”


Sai da akayi sallar azahar sannan ya fito ya tafi, ba a san ransa ba, ya wuce gidan nasu da babu kowa a yanzu sai masu aiki saboda kula da gidan, wanka yayi yana komawa dan ko wayar sa be kunna ba sai ya huta sosai. Kwanciya yayi ya dan yi bacci zuwa laasar sai ya tashi.


Kafin ya tashi Ya nabeela da yaran da khadijan Kamal sun iso gidan, suka yi zaman su a falo dan sun san bacci yake yi. Suna zaune bayan an idar da laasar sai gashi ya fito, cike da mamaki yake kallon su, su amna suka tafi da gudu suka rungume shi ya daga su sama yana dariya. 


“Maimakon ku tashe ni.” Yace yana karaso wa falon rike da yaran


“Munsan hutawa kake, kuma ba sauri muke ba.”


“Lallai kun kyauta. Sannun ku da zuwa.”


“Ina wuni?” Khadija ta gaishe shi a tsugune


“Lafiya lou ‘yata. Kuna lafiya?”


“Alhamdulillah.”


“Daddy barka da yamma.”


Ya nabeela tace tana murmushin jin dadin yadda Daddyn ya chanja


“Barka dai Nabeela, kuna lafiya?”


“Alhamdulillah wallahi, ya karfin jiki? Allah ya sa kaffara ne.”


“Kalle ni fa, ke kin ga alamun ciwo? Ai na warke sarai wallahi. Alhamdulillah.”


“Allah ya kara sauk.” Suka hada baki da Khadija suka fada 


“Amin, Allah yayi muku albarka.”


“Dr yace yana maka sannu da zuwa Daddy.”


“Likita bokan turai, Nagode masa.”


“‘Yata kuna lafiya dai ko? Babu wata matsala?”


“Babu komai Daddy.”


“Toh Masha Allah, haka nake son ji”


“Miko min wayata a ciki Nabeela, nasan an kikkira ni.”


Tashi tayi ta dauko masa wayar sannan ta dauko kayan abincin da suka dafo masa ta kawo tsakiyar falon. Kamal ya fara kira sannan ya kira Aryan sai brothers dinsa da abokan hurda wanda yaga sakon su. Har dare su Ya nabeela na gidan sun tattauna maganar hajiya zeenat da Adam ma daga nan yace zai je ya ganta gobe daga nan ya wuce company.


****Washegari Khadija da Ya nabeela suka tafi garin su Kamal, wuni Ya nabeela tayi ta juyo in da ita kuma Khadijan zatayi musu kwana biyu daga nan taje gidan su itama tayi kwana biyu sai ta bi kamal din domin zai kwana biyu kafin ya dawo wanda yake saka ran dawowar sa ce gaba daya. Yana so ya dawo da babansa cikin kanon ma kusa dashi sannan ga Daddy ma yana so ya dawo su cigaba da rayuwa tare su cigaba da gina company su.

    ****Tana cikin tsananin azaba lokacin da Daddyn ya karaso, kuka take wiwi tana jin kamar a karasa guntule kafar a huta saboda ciwon da take mata na balai, a nutse take yau ba kamar kullum ba, abun ya dan sake ta dan dama zuwa yake yana tafiya. Sarai ta gane shi sanda ya shigo, sai ta rude ta fara kokarin mikewa, da sauri aka rirrikete akakwantar da ita saboda ba zai yiwu ta tashi a haka ba, ga hannu a nannade ga kafa a nannade da wanne zata iya? Karaso wa yayi ciki har gaban gadon ta da yake dakin mutane da yawa ne duk kowa ya basu hankalin sa yana kallon su. A tsaye ya tsaya daga gefen gadon yana kallon yadda ta koma cikin dan kankanin lokaci Allah ya chanja mata kamannin ta baki daya. Bubbuga kanta ta hau yi a jikin karfen gadon ya girgiza kai yace


“Ya jikin nata!?”


“Da sauki toh, an gode Allah.”


Be ce Allah ya kara sauki ba, ya zura hannun sa a aljihu ya ciro envelope guda biyu ya ajiye mata a gefen gadon yana kallon yadda take kallon sa amma ta masa magana, ya lura kamar bata iya magana ma gaba daya sai dai yunkurin yi din.


“Allah yayi miki abinda kikayi ma Bayin Allah da yawa zeenatu, ni IBRAHIM na sakè ki saki uku,ga takardar nan Allah ya sa wannan shine silar shiryuwarki idan zaki shiryu, dan bana jin zaki taba shiryiwa a rayuwar ki.”


Wanda suke gefen gadon suka yi saurin toshe baki cike da mamakin mutumin, ace mace na wannan mawuyacin Halin amma ka saketa har saki uku? Lallai maza mugaye ne. Yana jin kananun maganganun da suka soma tashi a dakin, da ihun da ta saka amma yayi biris, ya fice da sauri yana jin zuciyar sa fes kamar an zare masa babban nauyi da ya to kare zuciyar.

“Lallai maza sai a bar su, Yanzu saboda ta gamu da wannan kaddarar shine zai guje ta?”


“Ai haka Halin maza yake, sai dai Allah ya bi mata hakkin ta.”


Maganganu dai kala kala hadda nurses din ma da akan idon su abin ya faru. Matar dake kula da ita ce ganin maganganun sun yi yawa tace


“Idan kunsan abubuwan da ta aikata, bana jin zaku iya cigaba da zama da ita a dakin nan, wannan matar da kuke gani, tayi abinda zaa kirashi da karshen zalunci, samun muguwa azzalumar mace irin zeenatu sai an tona, dan haka kar kuyi saurin yanke ma mutum hukunci, abinda alhaji Ya aikata shine daidai.”


Tsit kake ji babu wanda ya sake magana, sai yan kananu dake tashi kasa kasa, sai kuma aka koma tunanin irin abin da tayi har haka amma dai babu amsa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post