Rumbun Qaya page 30

Rumbun Qaya page 30

Rumbun Qaya page 30

RQ

Page 30


****Yana tsaye gaban mirror yana feshe jikinsa da turare yana dan duba gefen wuyan sa da yake ganin kamar ya fada sosai a yan kwanakin nan saboda rashin nutsuwa. Adam ne ya turo kofar ya shigo kamar me jan kafa sai dai yanayin sa ya nuna alamun yasha wani abun. Wani kallo Aryan ya bishi dashi har ya karaso ya tsaya daga gefen sa yana yage baki yayi wata doguwar hamma idanun sa da suka yi mugun kadawa sukayi ja ya zube su akan Aryan din. Saurin ja baya yayi jin warin giya sannan ya zaro ido cike da mamakin Adam din yace


"Giya Adam?"


"Manta da wannan, alfarma nazo nema a wajenki."


"Alfarma?"


Gid'a kan sa yayi


"Kwarai, ka taimaka ka kaini naje naga Mom please, ka yi mun wannan alfarmar kwaya daya tak, nayi maka alkawarin baka wani bayani me matukar amfani a gareka."


Murmushi Aryan yayi kawai, yayi masa kallon mara hankali sannan yace


"Yanzu Adam akwai wani taimako da kake ganin zaka iya yi min kuma ba amince maka?"


"Ka gane? Ka ajiye duk wannan aside muyi magana ta fahimta nayi alkawarin taimaka maka amma ina son sanin in da uwata take mana, haba mana ka tausaya mun ita kadai gareni."


"Kai kana da ita ma, ni fa? Ina tawa? Wannan abinda kake nema a wajena ba hurumin ka bane ba, ka jira mu hadu a kotu kawai."


"Ba zaka dai taimaka min ba kenan ko?"


"Ba zan iya ba , babu wani abu wai shi taimako tsakani na dakai."


"Shikenan, shikenan zamu gani."


"Babu abinda zamu gani sai alkhairi. Na riga nayi latti already kazo kuma ka kara sani yin wani,."


"Shikenan, ba damuwa zamu gamu ne."


Jakar sa Aryan ya dauka ya saba a kafad'a ya nuna masa hanya alamar ya fita, yayi kwafa sannan ya fita shi kuma ya rufe kofar sa ya jefa key din a cikin aljihun sa yayi gaba da saurin sa dan abinda yake gaban sa yau yayi yawa gashi har lokacin na neman kubuce masa.


***Ana i gobe zatayi monthly clearance dinta ta shigo Kanon ita da Hamma Hydar. Gidan Addah Maimuna ta wuce shi kuma ya shiga sabgar gaban sa saboda dama akwai abinda yake da niyyar yi a Kanon gashi kuma dama Abby yace dole duk karshen wata su dinga rakota shi da Bobbo Sadeeq wanda dai yake available a lokacin. Kayan ta kawai ta ajiye suka fito tare da Amina ta rakata cafe tayi printing schedule dinta sannan tayi photocopy na clearance letter din ta hade su waje daya sannan suka dawo gida. Sake gwada dialing number Oga Kamal tayi amma still a kashe, tun kwana uku da suka wuce take kiran shi amma bata shiga a kashe, da farko ta dauko ko bashi da charge ne ko wani abun dai haka sai ta share kawai, amma ganin ta cigaba da kiran kuma still a kashen sai taji duk babu dadi, taga missed calls dinsa a ranar amma ko sanda taga missed calls din bayan wajen awa biyu da kiranta ne dan tana chan falo tare da Abbyn ta ranar ya dawo daga tafiyar da sukayi shi da Lamido da bata san ina ba, shiyasa ta makale masa ta ki barin sa hatta abinci tare suka ci. Dalilin da yasa ta damu ta cigaba da kiran nasa taji ko lafiya amma shiru. Yanke shawarar kawai ta biya gobe ta office din ta duba shi daga I'd card dinta yana chan ta barshi idan yaso sai ta dauka daga nan ta wuce kumbotson. Da wannan shawarar ta kwanta ta kuma tashi ta shirya cikin NYSC khaki dinta da suka sha guga ta saka wani farin sneakers me adon stones ta bar jacket din a bud'e ba tare da ta saka buttons din ba sa saboda ta dan matse ta, tayi rolling da white medium veil da ya kara haske farar fatarta sannan ta fito. Sune zaune dukkan su a falon lokacin karfe tara daidai Muhammad ya kura mata ido yana kallon ta cike da yabawa sai dai be yi magana ba, Amina ce ta hau yi mata tafi dan yau ne karon farko da taga tayi complete dressing din dan last month da taje clearance din bata san 


"Kin ganki kuwa Adda Raihana, wow."


"Kai Aminatu banda sharri."


"Dan Allah Mama batayi kyau ba." 


"Tayi mana, amma wannan mayafin be yi karami ba Raihana?"


"A ah be yi ba Mama, haka ake sawa fa." Amina tace da sauri


"Ko da yake jacket din da tsawon ta kuma." Adda Maimunan tace


"Yawwa, Allah muma ya nuna mana sanda zamu saka kayan nan wai za'a ga yanga."


"Sai kace kyau zasuyi miki."


Muhammad yace yana hararar ya


"Ai dama ko kowa zai ce nayi kyau ai banda kai Hamma, amma wallahi ni na san zan yi kyau."


"Tafi chan, wata mummuna dake."


Dariya suka kwashe dukka, ta zumburi baki tana hararar sa ta gefe, ita dai Raihana dariya kawai take yi


"Adda na tafi, zan fara biyawa ta office dinmu na dauki I'd card dina sai na wuce,."


"Toh sai kin dawo Raihana."


"Muje na sauke ki kanwata."


"Nagode Hamma."


Gwalo Amina tayi masa ya jefa mata pillow da yake kan kujerar ta chafe tana dariya


"Zan dawo zan kamaki ne yarinya. Da kanki kamar goriba a wajen."


"Irin kanmu daya." Tace ta gudu da sauri ta shige ciki. Girgiza kai kawai yayi, yabi bayan Raihana da tuni ta fita yana jin sa ontop of za world. Da sauri ya karasa ya bud'e mata motar ta shiga ta zauna sannan ya dawo wajen zaman driver ya shiga ya zauna yana shak'ar kamshin turaren me sanyin kamshi. Kusan minti biyu suka dauka ya kasa tada motar dan wani irin feeling ne yaji yana shigar sa akanta, karo na farko da yaji wani abu ya darsu a ransa game da ita. Sai da ya daidaita nutsuwar sa sannan ya kunna motar bayan ya sakar mata murmushi, ya saita radio din motar ya kamo cool FM ya dan rage volume din sannan suka bar layin.


    Duk da saurin da Aryan yake yi sai da ya makara sosai, bacci ne be yi da wuri ba jiya yana wani bincike shiyasa ya makara gashi akwai meeting din da zasuyi anjima da directocin companyn su dake wasu states din sannan zasu je su duba Daddy da jikinsa dan sai jiya suka samu labarin abinda ya faru daga bakin Aryan din dan duk kiran da suka yi masa bayan labarin ya bazu be dauka ba, dan bashi da nutsuwar da zai iya yi musu magana a lokacin. Har ya hau sama ya zauna a office ya manta da important files din na cikin mota, tsaki ya dan ja kad'an ya tashi da sauri ya sake fitowa ya sakko kasan daidai lokacin da motar Muhammad ta shigo compound din tayi parking a opposite motar sa. Da farko be lura da wadda ke cikin motar ba, sai bayan ya bud'e tasa motar ya dauki abinda zai dauka ya fito kawai idanun sa suka hango masa ita a gaban motar tana magana da wani handsome saurayi suna ta faman zabga murmushi. Wani das yaji gaban sa ya fadi, maganganun  da Kamal ya fada masa suka shiga yi masa bita aka


_"Tana da saurayi."_ 


  yaji muryar Kamal din kamar tayi masa rada a kunnen sa. Tsayawa yayi chak yana kallon su ya ma manta shaf da abinda ya kawo shi wajen, Muhammad ne ya fito da sauri ya zagayo ya bud'e mata kofar sannan ya ware hannuwan sa alamun bismillah sukayi dariya a tare, muryar ta, ta shiga cikin kansa sanda tace


"Kana da abin dariya Hamma."


"Honey?" 


Kunnen sa kawai yaji tace ba Hamma ba, ji yayi kamar ya karasa ya same su ya faffalla musu mari a wajen da suke tsaye. Daga masa hannu tayi yayi reverse ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya tana jin kamar be dace ace tazo ba, kamar bata da zuciya ita kuwa? Korar kare fa Aryan yayi mata Amma shine ta zo? Wata zuciyar ce tace mata ai bashi kika zo gani ba, kuma Kamal yayi miki halacci babu laifi dan kin tabbatar da lafiyar sa. Da wannan shawarar ta amince ta nufi building din kanta tsaye duk kuwa da wani abu me kamar tsoro tsoro yana neman dakushe ta. Bayanta yabi kawai ganin ta wuce ba tare da ta lura dashi ba. Tana shiga su Zainab suka yo mata cha da ido, ta gaishe su normal kamar babu komai sannan ta yi hanyar office dinsu dan ta fara daukar I'd card din nata kar ta manta. Babu kowa a office din nasu ta bud'e drawer ta, ta hau duba I'd card din a in da take zaton ta ajiye shi, sai dai baya nan ta sake dubawa sosai tana cikin dubawa Abdulhakeem ya shigo suka gaisa sannan ta tambaye shi ko sun ga I'd card din ta


"Kamar yana wajen oga Aryan gaskiya, saboda ranar Abdallah ya ganshi sai ya dauka ya kai masa."


"Innalillahi, ai da kun ajiye min a wajen KU."


"Ai yazo ma, kije kawai ki karba a wajen sa"


"Ba karbar bace ba ai, ta ina ma zan fara shiga office dinsa?"


"Ba zaki iya zuwa ki karba ba wai?"


"Gaskia, gashi LGI dinmu idan babu I'd card din nan ba zai maka clearance ba"


"Ba dai Tanko bani ba? Shine LGI din naku ko?"


"Shine."


"Wai, ai kuwa idan kina son kanki da arziki kije ki karba gaskiya, in ba haka ba zaki samu matsala."


"Toh ka taimaka ka karbo min dan Allah, zanje na gaishe da Oga KAMAL idan na fito sai na karba na tafi."


"Oga Kamal ai yayi tafiya, baya nan wallahi."


"Haba dai? Ina ta neman wayar sa bata shiga."


"Wallahi baya nan kuwa.'


"Toh ko baya k'asar ne?"


"Eh toh, watakila dai, babu wanda yasan ina yaje a cikin mu gaskiya."


"Toh da sauki ai, dama na dauka ko ba lafiya ne naga ina ta kiran sa switch off, tunda tafiya yayi toh alhamdulillah, yanzu ka taimaka ka karbo min I'd card din ina jiranka dan Allah."


"Ok bari naje."


"Yawwa nagode." Ta zauna sosai shi kuma ya fita. Aryan na zaune yaji an kwankwasa yayi saurin kallon kofar a tunanin sa itace, come in yace yana sauke kansa sai kuma ya sake dagowa jin Abdulhakeem ne


"Ya akayi?"


"Sir dama sister Raihana ce tace nazo na karbar mata I'd card dinta."


"Wacece?" Ya fada kamar be gane ba


"Wannan corper din sir."


"Kace tazo ta karba da kanta."


Ya maida kansa kan aikin da yake yi.


Juyawa Abdulhakeem din yayi ya sameta a office din ya fada mata abinda Aryan din yace


"Na shiga uku, dan Allah yanzu be baka ba? Wallahi bana son zuwa."


"Wai laifi kika yi masa ne hala?"


"Ba komai, ba zaka gane ba."


"Gwara kije da kanki, ba zai bayar ba wallahi."


"Kai innalillahi." Ta mike jiki a sanyaye ta fito. Da sauri Zainab ta tashi ta tare ta.


"Karki shiga office din Oga Aryan."


"Akan me?"


"Saboda yace kar wanda ya shiga yana busy ne."


"Ni kuma shi yake kirana, please karki bata min lokaci ina sauri ne."


"Bakar mayya."


Zainab din tace taja wani irin dogon tsaki. Sarai ta jita amma sai ta kyale ta kawai ta barta tsaye da bakin ciki. Kamar kirjinta zai fado haka ta sa hannu ta kwankwasa a hankali sannan ta tura bakin ta dauke da sallama tayi kokarin daidaita kanta da nutsuwar ta. Ta kasan idon sa ya hange ta, ta shigo ya yi kamar be ji shigowar ta ba, ya dai amsa sallamar tata a ciki ciki yanda ba zata ji ba. A bud'e ta bar kofar ta tsaya daga wajen kofar ba tare da ta shigo ciki ba tace


" I'd card dina da na manta nazo dauka."


Yadda tayi maganar a dunkule ya sashi daina abinda yake ya dago idanun su, suka sarke da juna, ita ta fara janye nata da sauri ta dauke kanta gefe. 


"Close the door please."


Juyawa tayi ta rufe kofar amma ba ruf ba, ta cigaba da tsayawa a jikin kofar fuskar ta ba fara'a.


"Baki iya gaisuwa ba?"


_"Eh ban iya ba."_ Ta fada a cikin zuciyar ta, Amma a fili sai ta fuske kamar bata ji me yace ba.


"Me kika ce kika zo dauka?"


"Identity Card."


"Shine zaki aiko min wani? Ba zaki zo da kanki ba.?"


"sauri nake ne."


Kallon ta yake tunda suka soma maganar amma ita sam gefe take kallo. Mamakin ta yake sosai kenan fushi take dashi shine ta aiko wani ba zata iya zuwa ba, ko da yake shi yace mata baya son sake ganin ta, kila shiyasa ta aiko din amma kuma ganin da yayi mata a yanzu yasa shi karyata kansa da kansa da abinda yace din a lokacin, tabbas ba har zuciyar sa bane ba, a yanzu da yake cikin irin wannan yanayin yana bukatar ta, amma ta yaya zai fara gaya mata hakan? Taya zai yi sakata ta yafe masa abinda ya fada a bacin rai ta dawo su cigaba da aikin? He need her more than ever, ya tabbatar aikin zai fi tafiya masa daidai idan tana kusa dashi.

   Mikewa yayi daga wajen da yake zaune, ya shiga takowa zuwa gaban ta, ya tsaya daga gefen da ta karkatar ta fuskar ta, kin kallon sa tayi kemaimai ta maida kan dayan side din ya sake biyo ta.


"Fushi kike dani?"


Ya samu kansa da tambayar ta. Kin amsawa tayi ya sake maimaitawa


"I'm sorry toh."


"Sir please zan makara, Kumbutso zan tafi clearance."


Ta fada kanta tsaye tana jin wani sabon confidence musamman da ta jiyo sautin tausasawa a kalaman sa.


"Please kiyi hakuri, nasan na bata miki rai amma kiyi hakuri."


"Please sir zan makara."


Kofar ya kalla sannan ya kalle ta, ya matsa jikin kofar kawai taji ya murda key, ya zare key din daga jiki ya juya ya koma wajen zaman sa ya zauna ya barta a tsaye a wajen cikin tsananin mamakin sa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post