Rumbun Qaya page 29

Rumbun Qaya page 29

 

Rumbun Qaya page 29

*RQ*


      29****Da sassafe Kamal yazo daukar Aryan ya same shi tare da Adam a asibitin. Adam tun da yazo yaki tafiya babu wanda yake ma wani magana a cikin su amma kuma duk abinda ake bukata da sauri yake tashi yayi. Kallon sa Aryan yayi yasan tafiya zai kuma shi sam zuciyar sa bata yarda da zaman Adam din a wajen shi kadai ba duk da ya nuna damuwar sa amma ba zai iya tantance gaskiyar sa ba


"Kana ganin mu tafi mu bar Adam anan? Shi kadai?"


"Yes akwai jamian mu a wajen duk da ba gane su zai ba, zasu kula da Daddyn har ka dawo."


"Ok, muje."


Suka fice Adam din yana kallon su ba tare da sun masa sallama ba. Shiru ne ya biyo baya tun da suka dauki hanyar babu wanda yayi magana a cikin su har suka kusa zuwa, sosai yanayin Kamal ya koma irin very serious din nan da suka isa gate din cike da mamakin sa Aryan yake kallon komai har suka shiga cikin harabar wajen yayi parking da sauri wasu matasa maza suka karaso suka bud'e masa kofar sannan suka gaishe shi irin tasu gaisuwa.


"Sir Indabawa ya shigo?"


"Yes, anan ya kwana ma."


"Ok... Aryan show them your I'd card."


Hannu yasa a jikinsa ya dudduba be ji shi ba


"Yana mota ko office."


"Ohh..."


"Zamuyi searching dinsa ne sir?"


"Oh yes, kuyi tunda haka dokar tace."


"Ok, zamuyi searching dinka idan ba zaka damu ba."


Kallon Kamal yayi ya gid'a masa kai


"Haka dokar take Aryan, next time don't forget your I'd card ."


Kamal yace yana kallon sa


"It's ok, bismillah."


Duba shi sukayi da yar karamar na'urar su suka tabbatar babu wani makami ko wani abu a jikin sa sannan suka ce babu matsala. 


"Are you for real?" Aryan yace suna tafiya ganin yadda ake saluting Kamal din yana babbasarwa.


"Kai ne kadai ka raina ni ai." Ya bige shi a kafad'a


Office dinsa suka isa, ya daga kai ya karanta sunan da yake rubuce a saman office din sannan a hankali ya furta


"You are unbelievable."


Ciki suka shiga ya nuna masa wajen zama sannan ya zauna a kujerar sa ya hau tattare abubuwan da yake son mikawa su ga Aryan din, sai da ya hade su waje daya tsaf sannan ya taso ya dawo kusa da Aryan din ya mika masa


"Na gama part dina, yanzu saura naka part din, I trust you."


"I will take over in sha Allah."


"Good, ina nan ina jiran ka."


"Wai da gaske kake? Tafiya zakayi?"


"Yes da gaske mana, baka so kasan waye ainahin Kamal din naka?"


"Is there anything da ya kamata na sani? Bayan wannan abun da na gani?"


"Akwai da yawa ma."


"Ok, let see."


"Yawwa, lets go an meet Indabawa, daga nan sai kaga Hajiya Zeenat din."


"Bana son ganin ta, mu hadu a court kawai."


"In kace haka, shikenan."


"Yaushe zaku mika ta kotu?"


"Yanzu maganar da zan oga kenan, sai ya saka hannu sannan. Dole kuma za'a bata damar daukar lawyer."


"Ok. Allah ya bamu sa'a."


"Amin dan saurayi."


"Zaka fara ko?"


"Kayi zuciya mana idan baka so na dinga tsokanar Ka."


"Toh yanzu wannan aikin da yake gaba na zanji ko da wanne?"


"Da dukka mana."


"I can't concentrate ai."


"Shine ma zaka fi samun concentration din ai,guy kasan falalar dake tattare da nisa'u kuwa?"


"Ban sani ba, bana ma so na sani, muje dan Allah."


"A ah wait! nine oga anan ai, kaga hungry boys din can na waje, da nace tak zasu zo su sabe min kai sama."


Dariya Aryan yayi yace


"In ka fasa." 


"Naji tausayin ka ne, kar nayi ma me rabo asarar handsome guy kamar ka, shiyasa kawai."


"Naji, muje dan Allah, a duk serious abu sai ka kawo wasa."


"Na fada maka, kai kadai ka raina ni wallahi, amma ba komai."


"Naji, lets go oga kwata-kwata."


"Muje." Yace yana mikewa suka fita daga office din.


Sun dade sosai a office din Indabawan suna magana dan har azahar basu bar wajen ba ana sukayi sallah sannan suka fito. Kan Aryan yayi masifar daukar charge dan yana bukatar yayi zama sosai ya duba dukkan shaidun da suke hannun sa, dan ya lura akwai abubuwan da basu gama bayyana ba Wanda suke bukatar nutsuwa sosai kafin su soma shari'ar. A gidan sa Kamal ya sauke shi amma sai yaki shigowa, har Aryan din ya soma tafiya ganin Kamal din be fito daga motar ba ya sashi dawowa baya


"Ba zaka shigo ba?"


"Eh, tafiya zan."


"Muje mana mu karasa duba abubuwan nan sai mu fito anjima."


"A ah, ka ajiye su kawai ka fito na sauke ka a office."


"It's not safe ai na bar komai anan, ina ganin muje kawai na kai su gidan Ya Nabeela sai mu wuce office din."


"Ok, hakan ma yayi."


Fasa shiga gidan yayi suka koma tare ya kaishi gidan Ya Nabeela ya bata takardun da komai yace ta ajiye sannan suka fito a tare ta nufi asibiti wajen Daddy su kuma suka wuce office din.

  


***Kamar yadda suka dauki kwanaki basu shigo office din ba, haka suka tarar da ayyuka masu tarin yawa.

    Zainab ce ta yi knocking sannan ta turo kofar ta shigo tana yauki da rangwada ta gaishe shi a ladafce ya amsa kansa akan aikin da yake yi ba tare da ya dago ba.


"Hope babu wata matsala sir, kwana biyu baku shigo office ba."


"Babu, akwai wani abu ne?"


"No babu komai,zuwa nayi dai naji."


"As you can see I'm very busy, so please..."


"I can help you." Ta tare shi


"It's ok, zan iya. Zaki iya tafiya "


Tsayawa tayi tana wasa da hannun ta, ba tare da ta fitan ba, so take ta tambaye shi Raihana amma tana shakku, dagowa yayi jin bata fita ba ya kalle ta, tayi saurin cewa


"Sir Raihana fa? Ta daina zuwa ne?"


"Zainab please go out."


Yace mata politely yana kokarin hana kansa yi mata wulakanci 


"Ok sir, kayi aiki lafiya, idan kana bukatar wani abu ina waje."


Shiru yayi mata haushin nacin ta na tike shi, juyawa tayi ta fita ya ja tsaki da karfi. Ta fara isar shi da shegen iyayin ta.

  

  Akan aikin suka dukufa suna kokarin resolving komai sune har bayan magriba suna office din. Sallah suka fito yi da mamakin sa, sai yaga Zainab a zaune babu kowa sai ita. kallon juna sukayi shi da Kamal da ya fito daga office dinsa shima sannan ya kalle ta.


"Baki tafi ba wai?" Kamal yace da mamaki


"Eh, akwai wani aiki da nake karasawa ne."


"Ko wanne aiki ne ba za'a barshi sai gobe ba Zainab?"


"Aikin me muhimmanci ne Sir, shiyasa."


"Still dai, gashi har duhu ya soma yi, ki jira idan zamu fita kawai sai muyi dropping dinki a gida dan samun napep idan dare ya fara yana wahala"


"Ok sir, nagode." Tace fuskar ta dauke da murmushin jin dadi, ta saci kallon bangaren da Aryan yake taga ya bata fuska


"Muje kar mu rasa jam'i." Yace kawai ba tare da ya saka musu baki a maganar tasu ba.


  Tana zaune kamar mayya suka dawo daga sallar, ko motsawa batayi daga wajen ba kar ma su tafi bata sani ba dan ta samu opportunity me kyau da ba zatayi wasa dashi ba,shiyasa ko sallar bata tashi tayi ba tana zaune har suka dawo kowa ya shige office dinsa. Wajen minti talatin sannan Kamal ya fito ya shiga office din Aryan din yace su wuce.


"Kuje kawai zan taho idan na gama."


"A ah, motar ka fa tana asibiti, muje kawai ka ajiye mu a gida ka tafi da motar tawa ma hadu gobe idan Allah ya kaimu."


"Kaga akwai abubuwan da ban karasa ba, musamman harkar shigar da lissafin nan, kwana biyu na samu saukin sa."


"Amfanin Raihana kenan, da tana nan da tuni tayi."


"Zaka fara, shikenan muje kawai."


"Kai kuma baka san gaskiya, ka tsaya kallon ruwa dai, kwado yayi maka kafa."


"Wai dan Allah me yasa kake min haka? Ni menene nawa tsakani na da yarinyar nan ne wai? Aiki take kamar kowa nothing more."


"Kaga duk zagaye-zagayen ka ba zai maka ba, ni dai ba bako bane bare kace zaka ninke ni bai bai, nasan komai har kiran ta da kayi."


"Ya Allah, ita tace na kirata?"


"Ni na sani, kana wasa da aikin detectives ne?"


"Aikin munafukai dai, na ji na kirata kuma saboda kai ne, babu kuma wata doguwar magana da ta hada mu, bayan gaisawa, hakuri kuma na riga na bata sannan na bata abinda take so na monthly clearance din ta, me ya rage kuma?"


"Call her, kace ta dawo you need her."


"Wa? Ina ba dai ni ba."


"Ba in da ego dinka zai kaika, man accept your defeat kawai dan wallahi nasan kana son yarinyar nan, ban taba ganin kayi ma wani irin abinda kayi mata ba, amma ki fadin ka ya hana ka gane."


"Ya Allah, yanzu me ya kawo duk maganar nan? Soyayya CE irin ta yarinta, irin ta yaya da kanwar sa, babu wani abu kuma,."


"Shikenan, zaka ce na fada maka kila a lokacin da bashi da amfani."


"Let's go please."


"Yes muje, dayar girlfriend din taka tana jiranka kar ta gaji da jira."


Fasa abinda Aryan din yake shirin yi yayi, ya tsaya yana kallon Kamal din


"Girlfriend kuma?"


"Zaka ce baka gane duk moves din ta ba?"


"Ya Allah, me ka maida ni me wai Kamal? Huh?"


"Oho, muje madam dita tana jirana kar hakurin ta ya kare."


"Kana da matsala."


Yayi gaba kawai Kamal din ya bishi a baya yana murmushi,duk taurin kansa da ki fadin sa ba zai hana shi fada masa ba, da bakin sa ya furta yana son ta, kila lokacin a rikice yake ne, yayi subutar baki amma dai ko ma menene ya riga ya furta, kuma yaga komai a idon sa, kuma yana da yakinin sune zasu dawo da alakar Abby da Daddy da ta dade da watsewa, hakan yake fata shiyasa kuma ba zai taba hutawa ba sai yaga hakan ya tabbata.


   Kamal ne yake driving din, Aryan na gefen sa, ita kuma tana baya daga side din Aryan din, dadi kamar zai kasheta yau gata ga shi a mota suna tafiya. Babu me magana a ciki sai radio da Kamal ya kunna kawai a kalla zata rage shirun motar. Direct gidan sa ya fara kai su, Aryan ya dube shi da sauri


"Baka sauke Zainab ba?"


"Ai nine a hanya oga, ka sauke ta a gida."


Bud'e kofar yayi ya fito da sauri ya tare Kamal din


"Ya zakayi min haka?"


"Me nayi kuma?"


"Ni ba zan iya kaita gida ba, ta sauka ta hau napep daga nan."


"Kasan dai ba'a fiye samu ba anan."


"Toh ka san yadda zakayi da ita ni zan hau napep din kawai."


"A ah Aryan, ka taimaka dan Allah, mace ce fa."


"Ita bata da kamun kai ne da zata zauna tana jira maza su kaita gida?"


"Taimaka dai toh, kar Madam ta leko ta ganta ma ni na shiga uku."


"Ka gama dani wallahi." Ya bud'e motar ya shiga, tayi saurin bud'e kofar bayan ta dawo gaba ta zauna. 


"Sai da safe." Kamal yace ya daga musu hannu yana boye dariyar sa


"Ina ne unguwar?"


"Naibawa."


Be ce komai ba, ya maida hankalin sa akan tukin, tana ta satar kallon sa amma ya hade fuskar sa tamau sai uban sharara gudu yake kamar zasu tashi sama.


"Sir hope ban takura maka ba."


"Mm." Yace a gajarce


"Ok thank you so much, nagode sosai."


"Ok." 


Shiru tayi jin yadda ya amsa mata, duk sai tasha jinin jikinta bata sake magana ba, sai da aka zo sannan tace yayi, yayi parking ta sauka tana kokarin yi masa godiya ya fizgi motar kawai.***Da farko Aryan ya dauka wasa Kamal yake masa da yace zai yi tafiya kuma yana so ya nemo shi, be dauki maganar tasa da gaske ba sam wallahi, dan be yi tunanin akwai in da Kamal din zai wani je ba. Kwana biyu kenan yana neman wayarsa amma a kashe take, sannan yaje har gidan sa shima baya nan dan gidan ma a datse yake har da padlock a gate din. Abubuwan ne suka tarar masa sosai sukayi masa mugan yawa, ga kula da daddy, ga aikin companyn su da yanzu babu wani tsayayye a wajen sannan ga nasa aikin da ya fara a office dinsa, yana ta kokarin tattare dukkan bayanan kafin ranar da za'a soma shiga kotun amma gani yake komai ya dagule masa musamman matsalar Daddy da rashin wanda zai tsayawa companyn nasu wanda dama shi da Kamal suke karfin aikin toh duk su biyun basa samun shiga ma bare su san ya ake ciki. Haka yake fama tsakanin asibiti da offices din duk ya sauya tamkar bashi ba, yana kuma kara jinjinawa Kamal namijin kokarin sa. He's very strong kuma very hardworking dan sai yanzu ya kara tabbatar wa. Kokari sosai ya dinga yi ganin yayi copying dinsa dan bazai yarda ya bashi kunya ba, zai yi abinda zai yaba yasan taraiyarsu tayi matukar amfani.


***KURA LGA*


   Tana zaune a dakin bayan ta gama tattare shi ta gyara yar katifar tata da Malam Audi ya siyo mata bayan iftila'in kofar da ya same su kwanakin baya da ya cinye kusan komai na gidan har da kayan ta da take ta boyo da ajiyar su tsawon lokaci tana fatan watarana suyi mata amfani.

  Dago labulen dakin akayi, Atika ce dauke da langa ta shigo ta ajiye a gefen katifar ta gaida ta sannan ta juya ta fita. Jim kad'an sai ga Zuwaira itama da samira a rufe tazo ta ajiye daga gefen wadda Atikan ta ajiye itama ta gaishe ta sannan ta fita. Wannan al'adar su mutanen karkara ce basu da matsala ta rowar abinci duk kuwa da basu da kaloli na abincicikan amma kuma suna dafa shi yadda ya kamata dan haka kuma ko bako akayi yazo ba'a san da zuwan sa ba zaka samu da abincin da za'a bashi ya ci. Tsawon zaman ta dasu basu taba fashin bata abinci ba kuma dukkansu haka suke jere mata abincin ko tace yayi yawa sai sun kawo dole sai dai taci ta rage amma dole ne kowa ta aiko mata idan ta gama daga na safe har na dare abincin har yawa yake mata amma babu fashi, sun dauke ta tamkar itace ta haifi majajen su duk wani girmamawa suna mata suna kuma mutumta ta sosai basu taba yin abinda zai bata mata rai ba. Aminene ce ta shigo daga karshe ita ma da nata kwanon ta ajiye sannan tace 


"Yau su zuwai sun riga innarmu sauke tukunya kenan, toh na kulin mu zaki fara shi Inna."


"Na kulin mu dai, ai shine farko." Atika dake kofar dakin ta dago labulen ta fada


"Inna namu zaki fara, yau nice nayi girkin kici kiji dadi."


"Toh aminene, duk zanci ai na kowa, naji girkin Aminatuwa ko da dadi?"


"Wallahi da dadi Inna, taliya ce yar murji wallahi."


Atika ce ta kwashe da dariya


"Yo har wani birgewa ce a dafa taliya yar murji?"


"Ina laifi ko Inna?"


"Ba laifi kam."


"Inna da dai tuwo tayi ko shinkafa da miya ko dafaduka, amma taliya da manja ina wani wahala?"


"Duk da haka dai nayi kokari, ke da kika dafa ranar nan ai chabewa tayi."


"Ai ranar ne kawai shima dan an dan samu akasi ne."


"Toh yanxu dai duk kunyi kokari, ku kara zage dantse kafin bad'i a mika ku gidan majajenku."


Da sauri suka tashi suka fice cike da kunyar maganar Innan, murmushin tayi itama kawai dan tasan dama maganin musun nasu da anyi maganar aure sai su gudu. Abincin ta jawo gabanta ta bud'e sannan ta tashi ta wanko hannun ta ta dawo ta zauna tayi bismillah ta soma ci a hankali.

  

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post