RQ
Page 59
A hankali yake shafa gashin kanta har ya samu bacci ya dauke ta. Sosai closeness dinsu ya haifar masa da wani irin yanayi me wahalar fassarawa. Zame jikinsa yayi a hankali ya wuce toilet din ya sakar ma kansa ruwa me sanyi ya dinga ratsa sumar kansa zuwa saman kafadarsa. Kansa a chunkushe yake matukar a yan kwanakin nan, sosai ya tsorata da al'amarin Hajiya zeenatu ganin halin da Ammyn take ciki, be taba tunanin akwai irin wannan kullin ba sai a yanzu, rashin imani ne tsantsa a rabaka da kowa naka domin samun biyan bukatar duniya. Da ruwan a jikinsa ya fito ya zauna akan kujerar dake gefe yana kallon fuskarta, yanayin yadda take fidda numfashi kadai ya tabbatar masa da bata wani jin dadin baccin. Tsaki yaja ya mike bayan ya dan share jikinsa da dankwalin ta sannan ya baza ji a saman kujerar ya zura boxer dinsa ya karasa wajen da take kwance. Rigar jikinta doguwa ce ta atamfa, ya tabbatar ba zata iya cin dadin kwanciya da rigar ba ganin yadda yanayin garin yake da dan zafi duk kuwa da akwai solar da fan tanayi amma garin a chunkushe yake babu iska tana kadawa sosai. A hankali ya juyar da ita ya kama zip din rigar ta baya ya shiga zare mata shi ya kawo mata zuwa kasan cibiyar ta sannan ya juyo da ita. Saurin janye idonsa yayi daga kallon saman kirjinta da yake a bayyane bayan ya janye rigar. Numfashi yaja da dan karfi sannan ya fezar da iska me zafi yana sakin ajiyar zuciya. Ya kai kololuwa a hakuri yana kuma tunanin hakurin nasa gaf yake da karewa, ba dan baya so ya takura mata ba, duba da yadda ta galabaita yau da babu abinda zai hanashi karban hakkin sa a yanzu, sai dai yana da tausayi sosai, ba zai iya kara mata wata damuwar ba, ya kara wahalar da ita ga damuwar Ammy da take ciki kuma.
Juyi tayi ba tare da tasan wainar da ake toyawa ba, taji sanda yake zare mata rigar amma bata kawo wani abu ba, duk a tunanin ta ma mafarki take yi shiyasa ta cigaba da baccin ta hankali a kwance. Gefen ta ya kwanta sannan a hankali ya jawo ta zuwa jikinsa ya manna kirjinta a jikin sa, abinda ya janyo wani irin shock ya furta
"Subhanallah!"
Da dan karfi sai kuma ya samu kansa da yiwa kansa dariya, ya murmusa kad'an sannan ya sake matseta yana jaddada kansa ita din halilin sa ce. Yanayin yadda ya rik'e tan da kuma dan zafin da jikin tan yayi yasa taji ta takura har ta dan sake yinkurin juyawa amma sai ta jita a jikin mutum. Da farki ta manta a inda take kwata kwata, tunanin ta tana gidan Ya Nabeela kwance a gadonta tana bacci, jin ta jikin mutum yasa ta yin saurin yinkurin mikewa amma sai ya hanata, ya sake matse ta kam kam yana chusa kansa a jikin kirjin nata ya shiga sakar mata numfashin sa me zafi. Numfashin tane ya kusan daukewa take kuma sai kwakwalwarta ta shiga hasaso mata a yanayin da yake ciki. Hannun ta, ta kai ta taba kasan rigar ta, taji ta a zame sai tayi saurin kai hannu sama, daga ita sai bra daga sama.
"Na shiga uku."
Tace a ciki ciki kirjinta na bugawa da sauri. Yi yayi tamkar be ji ta ba, ya cigaba da chusa kan nasa hade da sakar mata zazzafan kiss a tsakanin wajen ga numfashin sa da yake hura mata.
"Bacci nakeyi fa."
Tace muryar ta a karye amma sam yaki dagowa bare ya nuna yaji me take cewa bare har ya iya amsa mata, maimakon haka ma sai ya sa hannun sa ta bayan ta ya shiga kokarin balle maballin bra din yadda zai samu full access da wajen. Kicin-kicin ballewa yake tana kokarin hanashi amma sai da ya samu ya balle su, sannan ya zare ta da dan karfi ya ajiye ta a gefe, da sauri tayi ruf da ciki tana manne jikinta da katifar dukka, dariya ta bashi sosai yadda tayi, amma sai ya kanne dan yanzu ba wai abinda yake gabansa ba kenan, so yake ya rage zafi ko yaya ne. Hargitso ta yayi gaba daya da hannu daya, ya dora gaba daya jikinsa akanta yayi mata rumfa ta yadda babu yadda zata iya hanashi abinda yayi niyya. Daidai saitin fuskar ta, ya kai tashi fuskar har numfashin su na sarkewa waje daya, ya shiga bin fuskar tata a hankali yana zagaye ta har ya kawo kan lips dinta. Kulle idonta tayi da sauri ya kai bakinsa kan nata ya shiga kissing dinta a hankali, duk da idon ta a rufe yake kokarin kare chest dinta take da hannun ta yana jin ta, ya kyale ta sai da ya gama kissing din bakin nata ta sakankance sai jin hannun sa tayi a saman kirjinta yana zagaya su ko ina, jikinta ne ya hau rawa ta shiga kokarin ture hannu tana masa magiya, amma yaki ya cigaba da abinda yake kansa tsaye, sai da ya ga dama dan kansa sannan ya kyale ta, zuwa lokacin gaba daya jikinta rawa yake yi, shi kuwa dama be ma san abinda yake ji ba, da be yi karfin halin kyale ta ba, da babu abinda zai hanashi aikata aika aikar, shiyasa ya hakura ba dan yana so ba. Toilet ya shige ita kuma ta yi saurin maida rigar ta, cike da mamakin Aryan din tamkar bashi ba. Tana kwance ta kulle idon ta, ta kudundune ya fito daga toilet din ya karaso gabanta idonsa ya dan tashi kad'an yayi ja, yace taje tayi wanka, yi tayi kamar bacci take ya sake maimaitawa sannan yace
"Zan ciccibe ki na kaiki fa."
Da sauri ta tashi, sai dai bata jin zata iya sakawa jikin ta ruwa a lokacin dan zazzabi zazzabi take ji, sai kawai taje ta kama ruwa ta dawo ta tarar har ya kwanta ta rakube a gefen shi ta kwanta kamar zata fada k'asa dan tayi masifar tsorata dashi. Mirginowa yayi ya jawota jikinsa a hankali muryar sa a ciki sosai yace
"Ba zaki koma gidan Ya Nabeela ba, nayi kara ai, bana so a samu matsala."
Bata ce komai ba, dan bata da amsar da zata bashi saboda maganar tafi karfin ta. Sai ta kulle idonta tana jin shi yana gyara mata kwanciyar sosai a jikinsa bata ce komai ma. A haka suka karasa daren bata san lokacin da yayi bacci ba.
Ita ta fara tashi ta wuce tayi alwala tana fitowa ta ganshi a zaune yana kallon wayar sa, mikewa yayi ya isa toilet din ita kuma ta gyara tasa Hijab dinta zata tada sallar ya fito yaje ta jirashi. Kayansa ya mayar yazo ya jasu sallar sannan ya fita ya barta a dakin zuwa wajen Hydar. Hankalin ta gaba daya yana wajen Ammy ji take kamar taje ta ganta amma babu hali haka ta hakura ta zauna lamo sai ga kiran Lamido ta daga da sauri tana dagawa ta saka mishi kuka, dama neman wanda zatayi ma take yi sai gashi ya kira, kwantar mata da hankali yayi ya ce yana hanya zaizo tare da me maganin sannan ta dan samu relief.
***Wajen Hydar ya je ya kwankwasa masa sannan ya shiga, suka gaisa ya zauna.
"Ina kanwar tawa?" Hydar ya tambaya yana kallon sa
"Na cinye ta!"
"Haba ka isa? Ai kanwata ba zata cinyu ba sam."
"Wait and see, Lamidon sun tashi?"
"Eh wayar sa ce ma ta tashe ni, sun dauko hanya."
"Good, Allah yasa Isa ya kawo mana motar yanzu, Kamal ma nasan zai dawo in sha Allah yau zamu juya."
"In sha Allah!"
Kwankwasa kofar akayi, Aryan ya tashi ya bud'e, me gadin dake kula da gidan ne, hannu ya bashi sukayi musabiha sannan yace
"Wai Isa ya karaso, suna waje tare da Malam Yahya."
"Yawwa Masha Allah, dama yanzu muke maganar."
"Ai naga mutumin ba baya ba, he's very hard working."
"Yeah sosai, bari na je wajen sa."
"Ok zan fito yanzu nima."
Tare suka fito da maigadin suka tarar da Isan a waje tare da Malam Yakubu da Awaisu, key din motar ya karba bayan sun gaisa sannan yace su shigo ciki, ya kaisu dakin Hydar sannan Malam Yakubu ya kira Asiya yace zai shigo ta fadawa Innar Yara. Wajen Maalm Yahya Aryan ya karasa suka zauna ya tambaye shi yadda akayi jiyan bayan su Adam din sun zo wajen motar, guduwa yayi ashe ya buya be fito ba sai bayan magriba bayan ya tabbatar sun tafi. Shiru kawai Aryan yayi yana tunanin abinda ya kamata yayi next for now yasan ya gama da babin Adam da duk iskancin sa
Wajen sha biyun rana Lamido suka karaso tare da malamin, lokacin duk sun shirya sun yi wanka suna jiran zuwan nasa, Kamal yace ba zai samu zuwa ba saboda a jiyan suka bar Kano tare da su Adam dan haka duk yadda ake ciki suyi waya kawai. Raihana na jin malamin yazo ta hau murna, zata fita ma Aryan ya riketa yana mata wani irin kallo, sunkuyar da kanta tayi k'asa cike kunyar sa, yana sane yake mata hakan dan ya lura gaba daya taki yarda ta hada ido dashi tun abinda ya faru jiyan
"Ina zaki fita haka babu ko mayafi?"
"Hamma Lamido zanje na gani."
"Ba shi kadai bane ba, ko so kike a kalle min mata?"
Komawa tayi ta zauna yayi murmushi ya fice. Gaisawa sukayi da Lamido da malamin me cike da kamala. Malam Yakubu ne ya jagorance shi zuwa in da Ammyn take, sukayi sallama bayan sun gyara jikinsu sun rufe sannan suka shiga, hannun sa dauke da Babbar jarka cike da ruwan addu'a, yana shiga Ammy ta mike zata gudu yayi saurin tura kofar yana murmushi
"Bakaken shaidanu ne wallahi Malam, kaga sun ganni zasu gudu, suna matukar tsoron ayar Allah, domin kona su take kurmus, wannan ruwan da kake gani, ruwan addu'a ne da aka karance masa ayoyin alkurani me girma, idan ana zuba musu tamkar ana sheka musu tafasashen mai ne, amma in sha Allahu an zo in da za'a samu waraka, da yardar Allah zata samu sauki."
"Allahu yasa."
"A kujerar Malamin ya zauna sannan ya umarci Ammyn ta zauna, Asiya da duk ta tsorata tayi tsuru tsuru kamar za'a ce kyet ta gudu, amma haka ta daure ta zauna daga gefen amma sai Ammyn taki, cikin daga murya ya daka mata tsawa.
"Zauna!!!"
Da sauri ta zauna tana kin yarda su had'a idanu kwata kwata saboda tsabar tsoron sa da take nan take.
Fita waje Malam Yahya yayi, ya matso yace ta mike kafa, ta mike a tsorace, sannan yace Asiya ta gyara mata Hijabin ta baya goshin ta ya bayyana, gyara mata tayi,yayi bismillah ya dibi ruwan ya zuba mata a saman kanta zuwa saman fuskar ta. Wani irin razanannen kara da ta saki sai da gaba daya gidan ya dauka, da sauri Aryan ya koma dakin da Raihana take, domin tana bukatar shi a lokacin. Cigaba da zuba mata ruwan yayi tana ihu da kururuwa kafin su fara magana daya bayan daya, tun yana irga su nawa ne a kanta har ya fara sarewa, ba karamin wahala tasha ba, domin duk abinda aka hada da bakaken shaidanu akwai matukar wahalarwa domin suna da masifar taurin kai, ba dukka ya samu suka fita ba a lokacin, sai dai yaci karfin su sosai, kuma ya karya lagon su ya kona da dama a cikin su, abu daya yafi tsaya masa a rai, inda suka tabbatar masa sai da aka yanka musu jinjiri sabon haihuwa akan aikin nata. Shekaru da dama suna tare da ita, sun hanata sakat sun saka mata ciwo, sun sakata manta kowa da komai da ya jibance ta, sannan sun dora mata ciwon kai me tsananin gaske.
A hankali ta soma dawowa hayyacin ta, ya kira sunan ta na asali Aishatu,ta amsa masa da k'yar dan ko ina a jikinta ciwo yake mata, fita yayi ya barsu ita da Asiya ta sauya kayan ta, ta kwanta zazzabi me zafi na rufe ta.
A cikin zulumi ya samu su Lamido da Hydar a waje, sai ga Aryan ya fito tare da Raihana sanye da Hijab, kallon ta malamin yayi sannan yace
"Wannan ce Raihanan?"
Gida masa kai tayi Lamido yace eh itace
"Ki dinga azkar kinji? Akwai aiki babba akan mahaifiyar ku, dole sai kun dage da addu'a kar a dinga yin tufka ana yin warwara, suzo suna shafar yayanta, domin yanzu matsafa turke suke yi a jikin uwa,sai suje suna shafar yayanta suna wucewa."
"In sha Allahu Malam, yanzu ya jikin nata."
"Alhamdulillah, amma dole ne sai mun dage, sai munyi addu'ar nan kullum a kalla mu dauki wata guda munayi, domin ba karamin aiki akayi akanta ba, baiwar Allah an cutar da ita, sun zuba mata kaya sosai a jikin ta, domin duk wanda nace ya fita sai yace kayansa yake kwashewa, zan dauka sun tafi sai na sake zuba ruwan sai na gane makalewa yayi."
"Wanne irin Kaya Malam?"
"Cututtuka ne, idan kaji sun ce kaya toh sun saka ma mutum cuta, idan kuka tambayi wadanda ke tare da ita zasu gaya muku abubuwan dake faruwa da ita wanda duk su suke saka mata."
"Mun gode Malam, yanzu muna so mu tafi da ita, amma muna tsoron kar ta rikice mana."
"Babu matsala, tare zamu tafi baki daya ai, in sha Allahu babu abinda zai faru, domin ko a yanzu fa anci karfin su, sai dai nasan naci irin nasu, zai yi wuya su hakura a Zama daya, sai an kusan kone su kurmus sannan zasu hakura."
"Mun gode Allah ya saka da Alkhairi "
"Amin Amin, zan dan shiga gari wajen wani tsohon aboki na, idan kun gama shiryawa sai ku kirana nazo mu wuce."
"Toh Malam, muma yanzu zamu fara shiri dama abinda ya zaunar damu kenan."
"Ba laifi hakan, Malam Ibrahim sai ka kirani idan kun gama."
"Toh Malam, muje na sauke ko toh."
"A ah, je kaga mahaifiyar ka, ni zan iya karasawa da kaina ba wani nisa bane ba."
"Isa yana waje ai, ga Malam Yahya sai su sauke ga Malam."
Aryan yace yana bin bayan sa, yasa Isa ya tafi kaishi tare da Malam Yakubu da suka kulla sabuwar alaka da Malamin.
Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Lamido, Hydar da Raihana. Kowa na tsoro da shakkar zuwa wajen Ammyn, duk da shi Lamido be ga yadda tayi ba, amma kuma yana cike da zulumi, sai dai a matsayinsa na babba shine zai shige gaba, sai kawai ya kama hannun Raihana suka nufi dakin Hydar da Aryan suka taka musu baya. Tana kwance Asiya ta lullube ta da zani suka shiga, taji shigowar su amma bata dago ba, bata kuma yi komai ba sai dai bata kalle su. Hawaye Lamido ya sharea boye da ya tabbatar da Ammyn tasu ce, ta chanja sosai kamar ba ita ba. An zalunce su zalunci mafi girma, be taba jin da gaske yana son ganin bayan Hajiya Zeenat irin yau, ko zaman prison din da Abby yayi be kai zaluncin da akayi ma Ammyn ba. Hannu tasa ta yafito Raihana dake faman kuka wiwi, ta shiga jan jikinta da sauri zuwa wajen Ammyn, ta fada jikin ta sannan ta fashe da wani irin kuka me cin rai.
***Kun jini shiru jiya glasses dina ne ya karye sai da na sake wani. In sha Allahu zamu koma posting din safe zuwa Monday. For now dai ku dinga expecting dina around magriba zuwa Isha. Nagode!