Rumubun Qaya page 60

Rumubun Qaya page 60

Rumubun Qaya page 60

RQ

   Page 60

****Kuka wiwi suke daga ita Har ammyn, su kansu yan mazan dauriya ce kawai da taurin zuciya irin tasu ta maza amma dukkan in su jikin su yayi wani irin sanyi. Mikewa Aryan yayi, zai fita Lamido ya dakatar dashi.

“Please karka tashi.”

“Wai abu zan duba a waje ne.”

“No ka zauna, dukkan mu daya ne kuma na tabbatar ammyn na cike da farin cikin ganin ka.”

Zama yayi ya fasa tashin amma duk nauyi ya cika shi ga kuma kukan da raihana take yana taba shi sosai. Tashi tayi zaune da kyar dan har lokacin jikinta babu gwari, kokarin kokawa suka dinga yi da malam dan haka duk jikinta ciwo yake mata sosai. Matsawa Lamido da hydar sukayi gabanta bayan ta zauna sai ta yafito Aryan da hannun ta


“Zo d’ana.” 


Wani abu ya daki aryan, a lokaci daya tunanin mummyn sa ya dawo masa. Sai yaji yana jin tausayin kansa da kansa, domin yasan shi tasa mahaifiyar ba zata taba dawowa ba. Matsawa yayi kamar yadda su Hydar din sukayi gabanta, duk ta shafa kansa tana murmushi. Kamar Aryan sak da na Khadija, babu in da ya barta a kamanni da dabiun ma sai dan abinda ba zaa rasa ba. Ko na a gayawa ammy shi din waye ba, tasan jinin aminiyarta ne, ballantana kamannin sa sune tun na kuruciya be chanja mata ba, sai dan abinda ba zaa rasa ba. Shi Ya fara zame wa da wayo da wayo ya bar musu dakin sai kuma asiya ta biyo bayan sa itama yanin suna da bukatar gamawa da mahaifiyar su. Sadeeq ne babu da Abby, wanda duk cikin su babu wanda yasan wainar da ake soyawa, sai kuma uwa uba Dadah da ba’a san kalar farin cikin da zata shiga ba. Da laasar sakaliya suka baro garin bayan Aryan fa hydar sun yiwa malam yakubu da isa harda asiya e sha tara na arziki, sannan Aryan ya basu complimentary card dinsa yace suzo Har gida su same shi. Sunyi ta godiya a haka suka rabu da niyyar idan ammyn ta warke sumul zasu dawo dukkanin su, zuwa na musamman wajen malam yakubun asan ahinda ya kamata ayi masa dashi da ahalin sa. Mutanen gidan basu ji dadin tafiyar ammyn a haka ba, tunda mafi akasarin su basa nan, Wasu sun tafi suna chan kauyan su kanwar malam yakubun yaran kuma sun tafi makarantar islamiyya.

  Hydar, Aryan da Malam Yahya mota daya suka hau kamar yadda suka zo, raihana ta gudu motar Lamido, ita da ammy da malam a motar. Tana lura da ammyn duk bata da sukuni shi kansa malam din ya lura ya kuma san dalilin hakan shiyasa yace kar su saurareta su tafi kawai idan sun isa lafiya sai a sakè yi mata adduar. Haka akayi kuwa, dare suka shigo Kano Aryan yace su wuce gidan su amma sai Lamido yace a ah, a kaita gidan adda maimuna, shiru aryan din yayi yana nazari, duk da kanwarta ce adda maimuna Amma be kamata akai ta gidan a yanayin nan ba. Magana yayi ma hydar idan ma gidan su ne Lamidon baya so aje toh akwai gidan sa dan Allah akai ta chan zaifi. Magana hydar din yayi ma Lamidon Ya tunasar dashi fa ba dan Aryan din ba da basu san ina ammyn take ba. Sai kuma abin ya dawo masa yace toh sannan aka wuce gidan Aryan din dake kusa da tsohon gidan su wanda yake har yanzu. Baba maigadi na zaune a gate yaji tsayuwar motoci, duk da kwana biyu ma Aryan din ya rabu da zuwa gidan yana chan main house din Amma yayi tunanin shine, lekowa yyai ganin motar yasa shi saurin janye gate din suka shiga sannan Lamido ma ya shigo da tasa yana karewa gidan kallo. 

  Shi da Hydar suka taimakawa ammyn suka shiga da ita ciki Aryan ya kaisu bedroom din sa dake kasa suka zaunar da ita dan jirin ne ya sake dawowa. Sallah suka fita suka yi tare da Malam sannan suka dawo ciki Lamidon da malam

Suka shiga dakin ita kuma raihana ta fito. Sai a lokacin suka hada ido da Aryan da yayi zuru zuru a kwana dayan nan kachal duk ya sauya, irin kallon da tayi masa taga ya rame shima shi yayi mata dan sai yaga har ta fishi ramewa ma ga wani abu me kama da tsoro dan kare a idon ta. Da hannu yayi mata alamar tazo gareshi, ta saci kallon falon babu kowa sai su biyu dan hydar ma ya shiga cikin dakin. A hankali ta isa wajen da yake tsaye daga jikin kafar bene kusa da wani dan corridor. Hannun ta yaja zuwa cikin wajen yana kokarin saka kwasar idon sa a cikin tata


“Menene?” Yace mata cikin muryar tausaya wa. Kamar me jiran kiris sai hawaye shar shar shar suka soma zuba, jan ta yayi ya bude dayan bedroom din suka shiga ciki sannan ya rufe kofar ya jingina a jikin ta yana jawota gaba daya jikinsa. A hankali suka saki ajiyar zuciya dukkan su. 


“Please ki daina kuka,idan kina kuka bana jin dadi, zata samu sauki zata warke, amma sai kin zama strong, idan ba haka ba gidan Ya nabeela zan maidake har sai an gama komai.”


“Na daina.” Tace da sauri tana goge fuskar tata da bayan hannun ta.


“Good girl.” Yace yana murmushi. Murmushin da maida masa itama sai kuma wayar sa tayi ringing. Rike ta yayi da hannu daya ya saka dayan hannun ya jawo wayar daga aljihun wandon sa. Zainab ce take kiran sa, ya kwana biyu rabon da ya shiga office, dazu yaga kiran abdulhakeem be bi ba, yanzu ga na zee. Dagawa yayi yana sakata a handfree 


“Hello sir.” Muryar ta cike da yauki da rangwada ta fito daga cikin wayar tasa. Gaban raihana ne ya fadi, ya dan kalle ta kadan jin yadda ta motsa sosai.


“Ina jinki.”


“Ya gida ya aiki sir?”


“Alhamdulillah, ya akayi? Naga kiran abdulhakeem dazu yanzu kuma ga kiranki, hope komai lafiya?”


“Lafiya lou sir, wasu files ne dama da ake da bukatar kayi signing, sai kuma meeting din da za’a yi tun last week Monday muke ta daga shi, sun yi magana suna so a sake fixing musu wata ranar.”


“Zan shigo Office din gobe, duk abinda ya kamata sai ayi.”


“Ok sir, ka huta lafi…”

  

Kit ya kashe kiran sannan yace


“Zainab ce.” 


Bata ce komai ba, ta zare jikinta a hankali ya kalle ta


“Zanje na duba ammy.”


“Um um, ki zauna ki jirani anan, idan malam ya gama ma Dr Mahfouz ne zaizo ya bata magani, tana bukatar Hutu tayi bacci sosai, so ki barta ta huta kinji? Yanzu zanje na dawo.”


“Toh zanje falo na zauna, bana son zama anan.”


Rike hannun ta yayi zuwa gaban gadon, ya zauna sannan ta dora ta saman cin yarsa domin ya lura rigima take ji, yi tayi kamar zata tashi ya rike ta sosai yayi kissing lips dinta na kasa. Shiru tayi ta nutsu kamar ba ita ba, murmushi yayi kawai ya zaunar da ita a gefen sa sannan ya tashi


“Yanzu zan dawo just wait for me.” Da kai ta amsa masa, ya fita ita kuma ta kwanta lamo akan gadon komai na dawo mata daki-daki. Be jima ba sai gashi ya dawo, kamar wanka yayi dan ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi, dama a takure yake tun a chan din shiyasa ya hau saman ya chanja bayan ya watsa ruwa a gaggauce, sannan ya fita ya karbo abincin da Ya nabeela ta aiko dashi wanda yayi mata waya tun suna hanya. A dinning ya ajiye sannan ya dawo dakin sai kuma ya kara fita da sauri ganin hydar na kiran sa a waya. Malam ne zai tafi suka raka shi waje Lamido yace zai maida shi yaki yace zai tafi da kansa gobe sai suzo tare da ammyn su kawo ta domin akwai Aiki sosai akan ta. Godiya sukayi masa ya tafi suka dawo ciki Aryan yace ma hydar akwai abinci a dinning idan akwai me bukata. Ammyn ya dibarwa Lamido ya bata taci kadan sai ga Dr Mahfouz ya karaso, ya duba ta sannan ya bata magunguna yayi mata alluran da zasu taimaka mata ta huta sosai sannan yace a barta ta huta zuwa safiya. Jawo mata kofar akayi suka dawo falo raihana kuma ta koma dakin da Aryan din ya kaita dazu ta zauna sai ta rasa me zatayi ma. Tashi Aryan yayi ya je dinning ya dauki plate ya zuba mata abincin sannan ya nufi dakin hydar na satar kallon sa kasan ransa kuma yana cike da jin dadi da farin cikin kanwarsa ta samu wanda yake sonta yake kulawa da ita.
****Tana kwance gaban katifar duk abin duniya ya dame ta, sau biyu tana yinkurin guduwa amma da ta zura kafarta take cin karo da kurar nan, abun mamaki yake bata yadda mutum zai yi rayuwa da kura babu abinda ya shafe su kuma. Ruwan pure water da take sha ta kalla, saura uku ya rage, bata san ko zaa sake kawo mata ba, ko kuma haka zata cigaba da zama. Turo kyauren akayi, Ladi ce dauke da abun kari tuwon dawo miyar kuka kamar kullum, shine abincin ba’a taba fashi ko a chanja ba tun da tazo, ta farko bata iya ci sai da taga uwar bari yunwa zata kasheta ta soma dan tsakura shima ba da yawa ba, gashi minti kadan Ladi take bata idan bata ci ba tazo ta kwashe kayanta tayi gaba. Shiyasa ana kawo wa in dai tasan zata ci take yin sauri ta dauka dan ta gama gane rashin mutuncin Ladi kadan daga aikin ta, ta zauna da yunwa, ruwan ma sai kadan ta bata ta shanye sauran tayi magana kuma taci zata chuna mata kura a dole ta hakura take kankan da kai a gabanta duk kuwa da bata san wacece ita da kalar abinda zata iya aikatawa ba, Amma babu komai da zarar ta fita daga wajen zatayi maganin yar iskar matar dan sai ta batar da ita daga doran kasa kamar yadda ta batar da sauran da suka yi yinkurin shiga rayuwar ta.


“Tashi ki yi maza idan kina da niyyar cin abincin kici, ki bani kwanon idan baki da niyya kuma nayi gaba da kayana dan ba ajiye ni kikayi da zan dinga dafa miki abinci kina wulakanci ba.”


“Yanzu Dan Allah ba zaki barni na tafi ba?”


Kallon ta Ladi tayi, kamar ba zatayi magana ba, sai kuma ta matso ta zauna a gefen katifar daf da hajiya zeenat din, kamar tace ta matsa amma sai ta daure dan idan tayi magana tata ce zatayi zafi.


“Kina so ki bar nan?”


Tace tana sunce gefen zanin ta, 


“Ina so sosai wallahi, ki taimaka min na rantse da Allah sai na inganna rayuwar ki, na daga darajar ki zuwa daraja mafi girma a duk garin nan.”


“Toh Madallah, zaki bar nan amma sai na samu abinda nake so, idan kin yi hadin kai toh, idan bakiyi ba na rantse da Allah barki zan gaki ga kurar nan.”


“Zanyi koma me kika ce,wallahi zanyi nayi alkawari.”


“Tah! Ba naje na dawo.”


Ta mike tana yashe baki, ta girgiza kai ta fice da sauri. Dakin Lawwali dake daura da zauren gidan ta nufa tana kwalamar kira, kafin ta karasa ya fito da sauri


“Ya akayi?”


“Matar nan ce mukayi magana, ina ganin abinda alhaji yace ayi Yanzu ne daidai lokacin, taji uwar bari dole zata fadi gaskia akan komai.”


“Allah ko? Bari na dauko abinda ya bani, mun yi waya dashi ma jiya yace zai dan yi tafiya, zamu iya fara aikin muga.”


“Dauko maza, maganin dan iska karen maguzawa, ka daure ta a wuya sai ka shigo da ita, idan tasan wata ai bata san wata ba.”


“Hajiya Ladi ikon Allah, duk an buga dake an barki, me maganin yan iskan gari dana jeji, ke kadai gayya kin tare nan kin tare nan. Manya manya maganin kanana kanana.”


Ya hau yi mata kirari yana dariya 


“Kai dai yi da jiki, na matsu naga idon yar iska. So nake ko banza ta danyi zawo a jikinta, shegiyar mata me zubin karu wai.”


“Haka kika tsaneta wai Hajjaju.”


“Kasan ni bana son rashin mutunci, duk kawaicin yaron nan sai da ta kure shi.”


“Wallahi, bari na dauko.” 


Ya juya dakin ita kuma ta koma tsakar gidan ta jirashi tana cije lebe irin na mugunta. Dauke da camerar ya dawo ya mika mata yace ta rike masa, ya karasa gaban kurar da suka gada wajen mahaifin su ya sunto ta, ya makala mata abu a wuya da baki sannan ya ja ta suka nufi dakin da Hajiya zeenat din take ciki😂

  Ladi ce ta gaba dan haka bata ga abinda yake bayanta ba sai da taji gurnanin da take ji a waje yana matso ta har ta tabbatar a dakin ne, idonta ne suka hasko mata kurar muraran dinta a tsakiyar dakin harshen ta a waje tana kallon hajiya zeenat din.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post