**RQ**
Page 66
***A daidai kofar gidan motar tasu ta tsaya, yaran suke sauka da sauri suka shiga gidan.
“Lafiya?” Matar tace da sauri tana kallon su.
“Ina Zainab??”
“Zainab? Bata nan ta fita wajen aiki.”
“Ok, zamuyi searching gidan.”
“Akn me? Me tayi muku?”
Id card dinsa ya zaro ya nuna mata, sannan suka shiga duba gidan suka tabbatar bata nan, suka fito suka samu Kamal yana tsaye ya bada bayan sa
“Tana Office sir.”
“Ok, muje.”
Suka shiga motar suka dauki hanyar Office din.
Tana tsaye tare dashi a compound din company suna magana kasa-kasa, a tunanin su sun samu abinda suke sun gama duk da kasan zuciyar ta na nadamar biye masa da amsar tayin sa da tayi, wanda Adam ya dade yana binta akan ta amince amma taki, sai gashi jiya ta yarda ta amsa wa wanda bata sanshi ba, bata taba sanin sa ma a rayuwar ta ba sai da abu iri daya ya hada su, suka yi taraiya wajen cimma burin su.
Shigowar motar dss din da yadda tayi parking a gaban su ya saka su niyyar fita a Dari, sai dai kafin su farga har sun d’uro sun saka su a tsakiya cikin wani yanayi. Kamal din ne karshen sakkowa ya kalle ta a matukar bacin rai yana kallon wanda suke taren da dama chan hasashen sa ya zama gaskia bayan ya samu waya daga Office din su akan an kama yaran da suka yi aika aikar har ma sun ambaci sunan mutane biyu. Zainab da Muhammad
“Arrest them !”
Kafin ya rufe baki an damke su, aka kuma tura su a motar da ta kasance baka kirin sannan suka fice daga cikin wajen da duk ma’aikatan suka firfito kallon abinda yake faruwa.
***** Ita kadai ce a dakin ta idar da sallar la’asar tana zaune akan sallaya tana azkar taga ya dan motsa kadan, mikewa tayi da sauri domin tana tsoron yayi irin abinda yayi dazu, cigaba da motsin yayi a hankali har zuwa sauran sassan jikin nasa sai dai idanun sa har lokacin a rufe suke. Tana tsaye a kansa tana tofa masa Addua ya cigaba da rage yadda yake matse fuskar zuwa kan a hankali ya dinga bude idanun sa har ya bude su tas a kanta, yadda ta rankwafo a kansa ya bashi damar ganin ta sosai ya kurawa bakin ta dake karanta adduar a hankali ido kafin ya shiga nazarin abinda yake faruwa dashi. Da sauri ya kai hannun sa Ya rike kan da yaji ya sara masa yace
“Ouch!”
“Sannu, Kan yana maka ciwo sosai? Na kira Dr?”
Ta mike yayi saurin riko ta da hannun da babu cannula
“Me nake yi anan?”
Yace muryar sa chan ciki
“Bigewa kayi, bari na kira Dr Mahfouz.”
“Um um karki tafi pleaseee.”
Yace yana yin kalar tausayi, Sai ta tsaya tana kallon sa
“Kiran sa zanyi nace ka farka.”
“Zauna.”
Ya nuna mata gefen sa, a kujerar ta zauna ya juyo da kansa a hankali yana kallon ta
“Tell me, menene ya same ni? I can’t remember anything.”
“Wasu bata gari ne suka kwala maka karfe akan ka, anan.”
Ta nuna wajen ciwon, hannu ya kai wajen da sauri yace
“Ouchhhh.”
Da sauri ta rike hannun nasa
“Da ciwo? Sannu.”
Duk ta rikice, kasa yayi da idon sa yana kallon yadda ta damu sosai, sai yaga ma kamar har ramewa tayi.
“Naje na kira shi?”
“Umm kira shi.”
Yace ganin yadda ta damu sosai, fita tayi yabi bayanta da kallo, sai kuma ya dora hannu a wajen ciwon ya sake tabawa a hankali yana tuna abinda ya faru a ranar.
Dr Mahfouz ne suka shigo tare da wani Nurse namiji, yana ganin shi ya soma dariya
“Ah lallai amarya ta iya kula, banyi expecting ganin ka haka ba.”
“Lallai kam.”
“Ya kan? Akwai wata Matsala ko wani yanayi da kake ji?”
“Akwai, kan yayi nauyi sosai sannan yana ciwo.”
“Dole ne wannan, sai a hankali.”
“Ok.”
“Bashi drugs din Abba,bari nayi ma madam magana a samu abinci a baka kaci, zaka kara samun energy zuwa dare in sha Allahu.”
“Kwana nawa nayi anan?”
“Kwana daya ne”
“Ok, zan iya rama sallolin da suka tsere min ko?”
“Yes zaka iya, ko a yadda kake ma a kwancen, idan kuma zaka iya zama ne toh, but banda a tsaye cox ba’a so ka bawa kan wahala.”
“Ok thank you.”
“You are welcome.”
Ya Nabeela ce suka shigo tare da Khadija, farin ciki fal fuskar Ya nabeela ta karaso gaban sa tana murmushi
“Alhamdulillah kanina.”
“Ya nabee kin ganki kuwa?kuka kikayi?”
“Menene ma ba zan yi ba? Na damu sosai.”
“Kin zata tafiya zan yi ko?”
“Silly boy, bana son wannan maganar, ya jikin naka?”
“Na samu sauki ai, baki ga alama ba?”
“Nasan dai karfin halin ka, da iya pretending dinka,Allah ya kara sauki.”
“Ya jikin Allah ya kara sauki.” Khadija tace
“Da sauki, thank you matar Yaya.”
“Mu shigo?”
Dr Farouk tare da su Amna yace bayan sun turo kofar
“Ashe kuna kusa ma, kace baku fito ba.”
“Tsokanar ki muke, kanina. Sannu ya jikin?”
“Alhamdulillah, da sauki.”
“Allah ya kara sauki.”
“Me Raihana take a waje ne?”
Ya nabeela tace tana kallon khadija bayan ta gaida Dr Farouk din
“Na ganta kuwa a zaune, kun zo kun cika dakin ku bar mutum da matar sa.”
“Kunya ce da ita kasan, zuwa zamuyi mu fita mu bar su, kanina muna falon sai anjima zamu wuce.”
“Ok.”
Ya juyar da kansa gefe. Fita sukayi Ya nabeela tace Raihana ta shiga ta zauna da shi ko zai bukaci wani abu. Duk a kunyace take haka ta koma ciki da sallamar ta, be juyo ba ta zauna a kujerar, kan nasa ne yake masa wani irin ciwo shiyasa yaki juyowa kar ta ga halin da yake ciki. Sai da ya dan lafa masa sannan ya juyo suka hada ido
“Zanyi sallah.”
“Tom, ko zaka fara cin abinci?”
“Um um, zan fara sallar.”
“Jikin ka yayi weak, ka fara cin abincin please sai kayi sallar.”
“Ok, bani kadan.”
Kadan ta zubo masa bayan ta zuba masa fav tea dinsa ta kawo masa ya fara shan shayin saboda cikin sa ya dan warware sannan yaci abincin kadan yace ya koshi. Toilet din ta shiga ta dauko wani dan karamin bawo ta zubo ruwan a bucket ta kawo dakin dan ko da ya yunkura zai tashi jiri ne ya kwashe sh, taimaka masa tayi yayi alwalar daga zaunen yayi dukka sallolin dake kansa sannan ya koma ya kwanta ta gyara masa pillow. Gefen sa ya nuna mata, ta zauna ba musu ta zauna ya dawo da kansa saman cinyar ta sannan ya hade hannun su waje daya ya rufe idon sa yana jin kamar ana tsira masa allura akan nasa.
***Bayan isha su Ya nabeela suka musu sallama suka tafi, suka biya suka ajiye khadija dan kamal yace zai yi dare. Bacci Aryan din yake raihanan na kusa dashi dan hanata tashi yayi ko da su Ya nabeelan suka shigo sallama tana kusa dashi knsa na kan kafarta kuma ko motsawa be yi ba bare ya bata damar tashi.
Kayayyakin da ke ajiye a dakin ta gama gyarawa ta dan tattare wajen duk da babu datti an zo anyi sharar yamma amma kuma tana bukatar taga wajen neat, Hamma Hydar ya dawo da yamma yayi musu sallama shi da Babbo sadeeq saboda zasu koma wajen aiki Abby dai yana nan da Dadah da Ammy saboda zuwa wajen malam sannan sun fara neman gidan da zasu zauna zuwa a gama maganin saboda ba zai yiwu suyi ta zaman gidan adda maimuna ba, gidan Aryan kuwa dama tun a ranar suka kwashe kayan su.
Tana zaune jigum ita kadai tana dan duba wayar ta akayi knocking a kofar ta zata ma Dr ne ta dan gyara mayafin ta da ya dan yi baya sannan tace a shigo. Kamal ne, waya yake amsawa ,shigowar ya saka shi katse wayar yayi sallama ta amsa ya yi mata murmushi
“Sannu da zuwa.”
“Yawwa, sannu ya mai jikin?”
Yace yana karasawa wajen gadon yaja kujerar ya zauna
“Da sauki.”
“Sai Yanzu zaka zo ka ganni?”
Aryan yace yana bude idon sa
“Ashe kana jin mu.”
“Maganar kace ta tashi ni.”
“Nazo dazu kana bacci, sai na wuce Office.”
“Agogo sarkin Aiki.”
“Aikin dole ne, ya jikin naka?”
“Da sauki, as you can see.”
“Allah ya kara sauki.”
“Me kayi a Office din?”
“Arresting suspects din da suka yi maka wannan illar?”
“Are you for real!?”
“Ka zata wasa nake? I’m serious Yanzu haka suna hannu, dan ma yanzu ba anan nake ba, but nayi handing over case din wajen wanda nasan bazai musu ta dadi ba.”
“Lallai, kayi kokari.”
“Ba zaka tambayi su waye ba?”
“Mts! Na gaji ne kawai, ko ma waye dai ba shikenan ba? I’m alive wannan kadai Ya isa.”
“Be isa ba, ran ka suka nema, idan kuma da abun yazo da tsautsayi fa?”
“Be ma zo ba.”
“Still dai, you have to be very careful, Yanzu ba kai kadai bane ba, bamu sani ba ma ko akwai unborn nan tafe.”
Da sauri ya kalli raihana, tayi maza ta kauda kanta, murmushi yayi kawai
“Nayi mamaki matuka da na ga wadanda suka saka yaran,
“Su waye?”
“Muhammad da zainab.”
“Muhammad? Zainab?”
Ya maimaita sunan yana son tuno su waye ma haka?
“Zainab ta Office suka hada kai da Muhammad, cousin din Raihana.” Yayi kasa da murya da zai fadi cousin din, da sauri raihana ta dago dan taji, suka hada ido da Aryan din da Shima ita ya kalla don be so taji ba, amma yanayin ta ya nuna ta jin.
.
*
*RUMBUN QAYA🔥
*DAUDAR GORA*🔥
*IDON NERA*🔥
*A RUBUCE TAKE*🔥
*KI KULANI*🔥
*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*🔥