Wa ya Kashe Rukayya? Page 7

Wa ya Kashe Rukayya? Page 7

Wa ya Kashe Rukayya? Page 7

WA YA KASHE RUKAYYA?

*DAGA ALƘALAMIN*

*FIDDAUSI SODANGI*

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

1 Ƴar gata 

2 Aliya

3 Waheeda

4 A zumuntar mu

5 Real Amani

6 Kwadayi mabudin 

7 wahala.

8 Jawaheer

9 Ni da surukata.

10 Makira.

11 Ruguntsumi.

 12 Gimbiya Ameenatu

 13 Mugun tsartse.

  14 Muhibba.

  15  Dan hakin daka raina.

 16 Zamani.

  17 Mugun makoci.

  18  Har a zuciya.

  19 Kai ne gatana.

  20  Maryama.

  21 Kaine sanadi.

  22 Kaddara ta riga fata.

  23 Aminiyata ce.

24. Gobara daga kogi

25. Wa ya kashe Rukayya.

7️⃣

"Gaskiya Lailah kin iya shirya tatsuniya, shi *ALIYU YUSUF ALKALI WAZIRI* shi ne ya karbi kuɗi a hannunki? Da ace baki faɗi kalmar kuɗi a kalamanki ba da zan iya yarda tunda namiji ne shi matashi wanda baida aure ba zanyi wani mamaki ba dan yayi wani abu makamancin hakan, amma kuɗin da ki ka ambata shi yasa ni kokonto harma na karyata zancanki kai tsaye."

Bakinta na rawa tace "ALKALI WAZIRI......."

"Kwarai kuwa dake baki san waye shi ba ki ka lafta masa wannan uban karyar? Allah ma ya rufa asiri ni ki ka gayawa ba wani ba da ya zama babban matsala a gareki."

"Mallan Musa wai kana nufin ɗan gidan ALKALI WAZIRI ne dai dana sani?".

  Ta yi masa tambayar kamar ba ita bace ta gama rusa kuka ba kamar zata mutu.

  "Shi fa, kima gaggauta tuba dan wannan babban sabo ne ki ka aikata dan nasan karya ki ke, hala dai son shi ki ke ne ko kuma kece ɗin ki kai masa tallar kan naki yaki amincewa da muraɗin ki shi ne ki ke so kiyi masa wannan mummunar sharrin?".

   Kamar mai duba har hanji yai maganar ba tare da sakayawa ba.

"Ni..ni..ni da aure na zan so wani? Allah ya kiyaye ba haka bane kawai dai shikenan ya wuce".

Nasiha yai mata mai ratsa jiki gaba ɗaya kunya ya gama lullubeta haka nan ta bar office ɗin jiki a saluɓe.

Kaf miyan bakin Aliyu ya kafe da k'yar ya iya tattaro numfashin sa guri d'aya ya bar jikin kofar office din Malan Musa dama yaje ya nuna masa abu ne har zai shiga yaji ana ambatar sunan sa shine ya tsaya yana sauraransu tun daga sanda ta fara magana har duka nasihar da malam Musa ɗin yai mata a kunnansa ne.

Idanuwan sa sam babu k'yawun gani 

Cikin wani irin tafiya mai kama dana bijimin sa ya bar wajan.

           *******

   *BAYAN WATA UKU*

A yau su ka zana jarabawarsu ta karshe a Jami'ar ta AMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA. Bayan tsawon shekaru biyar da suka kwashe suna karatun.

Shi kenan sun gama da A.B.U Zaria sun haɗa degree ɗin su LL.B nan da wani lokaci kaɗan kuma zasu tafi Nigeria Law school inda zasu yi shekara ɗaya daga nan shikenan zasu zama cikakkun lauyoyi tare da kwalinsu na B.L Headquarters ɗin na Abuja sannan kuma akwai a Lagos, Kano, Enugu, Yola, Bayelsa but su sun zabi da suyi a Kano saboda shi ne Jaharsu ta haihuwa komai zaizo musu da sauki suna gaban iyayansu.

Amal ce kaɗai a gidan duk sauran sun fice kowa fitar sa daban ya yi ita kam tace a gida zatai shagalinta kafin gobe su gudanar da babbar party da suka hada a wani babban hotel anan Zaria kafin jibi su tattara su bar garin Zariya zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.

Gaba ɗaya k'arar mp da ta kunna ya cika gidan in banda karar kiɗa babu abinda ka ke ji sai faman tik'ar rawa ta ke tamkar zata karye daga ita sai wata yar _vest_ da guntun wando wanda da kaɗan ya wuce guiwarta.

 Hankalinta k'wance ta ke rawar da gani kasan tana cikin nishad'i, wani irin rawa take tana juyi tamkar wata bebin roba.

  Amatulla na zaune tana ta wangale mata baki dan abin yana mata kamar wasa uwar nata ke mata.

  Kwalbar kodin ne a hannunta wannan shi ne gwalba na biyu da zata sha amma kuma sam bata bugu ba tana a hayyacinta take komai.

Ɗaya daga cikin ƴar aikin su ce tazo ta ce mata tayi bako.

  Wani irin kyalkyalewa da dariya ta yi tace "ni dince nayi bako ikilima?"

  Ita abin ma dariya ya bata wai bako, ita fa duk iskancin da suke sam babu ruwanta da namiji ita dai barta tasha abinta ya kai mata karo tai baccinta shikenan, haka ma sauran aminan nata a zahiri.

"Shigo da shi kawai ikilima ai shi ya jiyowa kanshi dan ni dai babu kayan da zan sauya a haka zai ganni tunda bani na gayyato saba koma waye".

  Tana maganar ne tana ci gaba da tikar rawar ta tare da kurbar kodin ɗinta.

Cak ta ɗaga Amatulla ta rungume ta tana juyi da ita sai dariya yarinyar ke yi tana zillo.

Yafi minti uku a tsaye a jikin ƙofar yana ƙare masu kallo babu abinda yafi ɗaukar hankalinsa irin kwalbar da ke hannunta. 

Wani irin juyi ta yi tare da ɗaga kwalbar gaba ɗaya ta zuƙe Amatulla na ta kokarin kai hannu amma ta yi jifa da kwalbar tana dariya.

  Ido huɗu sukai da shi ya naɗe hannu a kirji yana kallonta kamar wanda aka kafe a wajan idanuwansa sunyi jajir kamar barkono.

  Wani irin mummunar faduwa gabanta yayi a ta ke cikinta ya juya saboda mamaki da fargaba.

Saura kiris ta saki Amatulla a ƙasa tayi saurin rikota ta mannata a kirjinta ta kankame jikinta na karkarwa domin har ga Allah ya matukar tsoratata.

Wani irin mugun kallo ya ke mata ko k'yaftawa baya yi, jikin sa gaba d'aya rawa yake yi shima ya yi dukkan binciken da zaiyi akanta amma baici karo da inda aka ce tana shaye shaye ba, tabbas ta shammace sa.

 Baya ta ɗanyi kad'an da niyyar artawa ɗaki ta rufe.

"Karki soma!".

  Ya faɗi cikin wata kalar murya mai amo.

Matsowa ya soma yi inda take cikin wani irin taku wanda duk takunsa ji take kamar yana tafiya da numfashinta ne.

  Hannu yasa ya kashe mp din nan da nan ko ina yai tsit baka jin komai sai karan ac da ke aiki a palon.

 Nan da nan kamanninta ya canza alamar tsoro ƙarara ya baiyyana a fuskarta.

 Dakewa ta yi  ta soma yin baya kad'an kad'an, binta ya cigaba dayi har ta kurema bango, tamkar zai shige cikin jikin ta yaja ya tsaya yai mata runfa da makeken k'irjin sa.

Ya fita tsawo nesa ba kusa ba da ace wani zai shigo a lokacin sam bazai yi nasarar ganin taba domin kuwa gaba d'aya Aliyu ya lullube ta da tsawonsa da kuma faɗinsa daga ita har ƴar tata.

Bud'e bakinsa yayi zai mata magana wani irin had'add'an k'amshi had'e dawani irin huci mai zafin gaske ya bigi fuskarta, nan da nan y'an hanjin cikinta suka kad'a gabanta ya yanke ya fad'i rass!! Rass!!

Manyan idanuwanta ta zaro tana duban sa tsoro k'arara shimfid'e a fuskar tata. 

     Cikin wani irin kakkausar murya ya shiga fad'in "Meyasa ki ke wasa da zuciyata Amal? Meyasa ki ke shaye shaye wa ya koya maki? Meyasa? Meyasa?"

  Ya kare maganar da tsawa tsawa.

"Kinyi babban kuskure da wannan abin da ki ke aikatawa, ta yaya za a ce matar Aliyu tana shaye shaye? Banda zuwa party da dukkan abinda kuke aikatawa haba haba, meyasa Amal?"

Gaba ɗaya jikinta rawa ya ke harzuwa wannan lokacin ta kasa cewa komai mamaki name yake ya kasheta a tsaye.

"I love you Amal ina sonki da dukkan zuciyata, nasan kina sona ko baki furta ba nasa ni, ke tawa ce mallakin ALIYU YUSUF ALKALI WAZIRI ce......"

A firgice ta ɗago ta dube sa bakinta na rawa ta furta ALKALI WAZIRI?

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post