Wata Sakayya page 30

Wata Sakayya page 30

Wata Sakayya page 30

👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽  

😭😭😭😭😭😭 


 *WATA SAKAYYAR*

        (Sai a Lahira)


👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽👩‍🦽


By

            *NUSAIBA* *ALKAMAWA* 

 *PROFICIENT WRITERS* *ASSOCIATION* 

 Wata Sakayya PAGE 30

Turo kofar dakin Mommy tayi domin ta tashi Jidda tayi salla a zaton ta bata tashi ba, tana shiga ta tarar da ita ta idar da salla tana zaune akan sallaya ta ɗaga hannu sama tana addu'a tana hawaye, mugun tausayin ta ne ya kama Mommy, juyawa Mommy tayi tana ja mata kofa amma tunani ne fal a cikin ranta na mainene abinda yake damun yarinyar nan da har take irin wannan kukan, ta daya bangaran kuma tana jinjina hankalin yarinyar da kuma ibadar ta, tasan dai yara kamar ta basu cika tashi suyi sallar asuba ba a lokacin ta sai gari ya waye sukeyi, amma ita gashi ba tashin ta akayi bama ta tashi da kanta, da wannan tunanin ta haye sama, tana kammala adu'o'inta ta nannade sallayar ta kwanta nan da nan kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

"Inaso ki kasance mai hauri da juriya, ki kasance mai juriya da ibada, ki zamanto yarinyar kirki, tabbas idan kikayi haka zakiga haske a rayuwar ki, Allah ya kawo miki sauƙi a cikin alamuran ki,  Ubangiji Allah yayi miki Albarka, ni zan tafi","Ammi dan Allah karki tafi karki kuma tafiya ki barni kinji Ammi na" amma ina batt! ta bace, Ammi! Ammi!! haka ta rinka kwalla kiran sunanta tana juye_ juye, "Jidda lfy kike kuwa" a firgice ta farka daga baccin da takeyi mai cike da mafarkai, "tashi maza kije ki wanko fuskar ki daga nan ki same ni a kitchen" da yaransu na kurame ta amsa mata da to, tashi tayi ta shiga toilet tanawa mahaifiyar ta addu'a, tana fitowa taje ta samu Mommy tana hada breakfast, "yauwa Jidda matso kusa ki tayani, daga yanzu kullum da safe zakina zuwa mu dunga yin girki tare dan naga kamar babu abinda kika iya" murmushin jin dadin furucin Mommy tayi dan gaskiya itama tanaso ta koya, har kasa ta ɗuka tana gaishe da Mommy da yaran su na kurame wacce take gani kamar mahaifiyar tace, cikin sakin fuska ta amsa mata tana tambayar ta ya ta tashi, alama tayi mata da itama tana lfy.

A haka suka fara girkin Mommy na nunnuna mata abubuwan daya kamata,  har suka kammala girkin  a tray ta jera abincin, "ga wannan ki kaiwa dan mama sannan kizo ki dauki naki ni zan wuce sama, daga mata kai tayi sannan ta dauki abincin ta wuce dakin dan mama, a zaune ta samesa yana cike wasu takardu da sallama ta shiga dakin, chan kasan makoshin sa ya amsa wanda sautin muryarsa ba fito ba, gaishe sa tayi amma ko kallon ta baiyi ba, sai gajiya tayi da tsugunnon sannan ta mike ta isa gabansa ta ajiye tray din tana kokarin tashi taji the yace, "kee! kaimin takarɗun nan kan bedside drower" hannu biyu ta sa ta amshi tana mikewa, tana tafiya tana kokarin budewa ne takardun duk suka tarwatse, da rawar jiki ta fara kwashe wa tana addu'ar Allah yasa karya gani, rubutun daya ja hankalinta ta fara karantawa DR...tsawar da dan mama ya daka mata ce ta hanata karasa karantawa, a firgice ta ajiye su tana zazzare ido, "waike wacce irin shashashace da babu abinda kika iya a rayuwar ki sai shirme, dalla wace min da gani kafin na babballaki wawiya kawai! cike da sanyin jiki ta matsa daga wajan ta koma wajan zamanta, "ni Jidda wai wazai soni a duniyar nan, kowa ya tsane ni bayan babu abinda na tare musu kodan Allah yayoni nakasasshiya shiyasa kowa ke kyamata, mutum uku ne kawai suke sona a wannan duniyar daga inna Asabe sai Baba Garzali da kuma Mommy nan gidan.

" Shi kansa Dan mama ya rasa mai yasa yake mugun jin haushin ta, saboda tana da rawar kai wata zuciyar ta basa amsa kai tsaye, tsaki yaja yana mayar da kallon sa wajan da yake, "inkin gama kallon nawa kije ki soya min egg push"  tashi tayi tana daga masa kai ta shiga kitchen din kamar gaske, karewa kitchen din kallo tayi tana tunanin ta ina ma zata fara tasan dai ana zuba mai, kwasko ta dauko ta zuba man gyada mai uban yawa sannan ta kunna gas kamar yadda taga Mommy tayi dazu da safe sannan saita dauko kwai ta fasa akan man da ya dau zafi, albasa ya dauko aiko a yankan farko wukar ta shaibe ta, azabar da taji yasa ta fara yarfe hannu aiko ta tankwabi kaskon ya fado inda Allah ma ya taimake ta man bai konata ba, hawayen baƙin ciki ne ya zubo mata, baƙin cikin abu biyu takeyi , ga yankewa ga kuma barnar da tayiwa bayin Allah, da sanɗa ta fito daga dakin ta nufi dakinta ta samo kyalle, koda dan kwalin tane ta yago, bude kulolin abincin da aka kawo masa ya farayi amma sai yaga babu ruwa a ciki danshi a ka'idar sa saiya fara shan ruwa sannan zai fara cin abinci, ga Jidda shiru_ shiru bata dawo ba balle ya aiketa ta dauko masa, tura kekensa yayi ya nufi kitchen din yana zuwa ya bude fridge ya dauko ruwa har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya kara kutsa kansa cikin kitchen din dan yayiwa Jidda magana akan dadewar da tayi, yana shiga santse ya debi keken sa aiko ya fado daga kan keken yana fadowa ya bige da drowar kitchen din kokarin tashi yakeyi amma yaji bayansa ya rike saboda buguwar da yayi ga ciwon da yake jikinsa.

"Daddy Al'amin lfy naga kanata sauri bayan kuma nace maka inaso zamuyi magana mai mahimmanci da kai ","nima dai gaskiya ban sani ba amma dai koma mine ki bari na dawo saimu tattauna, yanzo Hajiya Inna ce take kirana da gaggawa","amma ai maganata tafi ta Hajiya Inna mahimmanci daka bari munyi saika tafi gurin nata","mahaifiyata ce fa kinsan tana da matukar mahimmanci a gurina amma kike danganta kan ki da ita" yana gama fadin haka bai jira yaji abinda zata ce ba ya fito cikin sauri, kwafa tayi tana bin bayansa da harara, lallai aikin boka na kan tsauni ya fara lalacewa, zaka dawo ka same ni ai, aikin banza kawai, mai banzar uwa kawai.

Yana shiga gidan ya nufi dakin mahaifiyar sa cikin sauri, Hajiya Inna na ganin sa ta fashe da kuka, rarrashinta ya farayi duk da baisan mai yasa ta kuka ba, "lfy kuwa kike kuka?","dan nan auran Rabi'atu ne ya mutu watanni hudu da suka wuce,  ta auri miji marar tausayi marar imani, sai gallaza mata yakeyi daga karshe shine ya bata takardar saki, banyan yayi mata shegen dukka, to yanzu ta gama iddarta harma ta samu natsuwa shine a karo na biyu nakeso na hada ku aure, saboda inaso zumuncin mu ya kara karfi kuma naga kai dan uwanta ne bazaka taba wulakanta ta ba" tunda ta fara magana ya zuba mata ido da farko data fara basa labarin mutuwar auran Rabi'atu yana mamakin ko mai yasa take fada masa duk wannan, a yanzu kam ya fahimci dalili, rass haka yaji maganar shifa gaskiya a tsarin sa bashida tsarin zama da mata biyu, kuma yasan matar sa Hassana da baƙin kishi kada taje ta kashe musu yarinya da bakin kishinta maimakon kara ɗonkon zumunci sai zumunci ya rabu, to taya ma zai aure Rabi'atu bayan dukkan su yan uwan junane kuma yasan dama chan Hassana da Rabi'atu ba jituwa sukeyi ba, maganar Hajiya Inna ce ta katse masa tunanin daya lula.

KASH!! 🤦🏻‍♀️Akace Laifin dadi karewa. 


SHARE FISABILILLAH.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post