Rumbun Qaya Page 37

Rumbun Qaya Page 37

Rumbun Qaya  Page 37

Rumbun Qaya  Page 37


***Wajen sha biyu da rabi bayan Ya Nabeela ta tafi, Kamal kuma ya fita falo yana waya da Khadija ya zama sai Aryan kawai wanda yayi shirin kwanciya ya saka kayan bacci ya kwanta a gadon hannun sa rike da wayar sa da yake ta faman jujjuya ta zuciyar sa na raya masa ya kirata. Baya so ya kira ya katse mata bacci ko matar dazu ta kara dagawa amma kuma yana son sanin ya jikin nata. Bin shawarar zuciyar sa kawai yayi ya kira ya saka wayar a handfree sannan ya dora ta akan chest dinsa. Cikin bacci Raihana taji ana kiran ta,zazzabin ya dan sake ta har ta tashi tayi sallolin da suka tsere mata ta dan sha yoghurt shine ta sake komawa. Cikin muryar bacci ta daga wayar tace hello, sai da yaja numfashi sosai ya sauke sannan yace


"Bacci kike?"


"Um um, na tashi." Ta amsa tana dan bud'e idonta kad'an.


"Ya jikin naki?" 


"Da sauki."


"I called you dazu, Mama ta dauka tace baki jin dadi."


"Ok Daadah ce, da sauki alhamdulillah."


"Sannu, Allah ya kara sauki."


"Amin. Nagode." 


Shiru ne ya biyo baya, be san me zai kuma ce mata ba,amma kuma baya son ya katse wayar, 


"Sai da safe?" Tace jin yayi shiru


"A ah, karki kashe please, ko ba zaki ce komai ba ki barta kawai."


"Ok." Tace a sanyaye dan yadda take jin jikinta so weak bata da energy din da zata yi doguwar magana. Kusan minti goma wayar na kunne sun yi shiru suna sauraron bugun zuciyar juna. Turo kofar Kamal yayi ya shigo yana cewaa


"Sai da safe babyna, bari na kwanta kar na makara." Dago kai Aryan yayi ya kalle shi yaga sanda yayi mata blowing kiss ta wayar sannan ya kashe wayar yana murmushi


"Oh bakayi bacci ba wai?" Yace yana kunna hasken dakin sosai


"Umm ban yi ba."


"Ok bari na watsa ruwa na kwanta,babyna tana gaishe ka."


"Naji." 


Dariya Kamal yayi ya wuce toilet


"Oga Kamal ne?"


Tace jin muryar sa


"Eh shine."


"Ya dawo ashe, ina ta kiran wayar sa switch off."


"Ok, eh sunje umrah ne, shiyasa."


"Ok zan kirashi mu gaisa, yana da kirki."


"Nifa, bani da kirki?"


"Umm." Tace tana turo baki, da sauri yace


"Bani da kirki?"


"Toh kai ne ai."


"La'ila, shaidar da zaki min kenan."


"Oga Kamal dai yafi ka."


"Toh ni da wannan me kafar kamar mirkin lema, waye yafi kirki.?"


"Wa?"


"Ban san shi ba, wani da ya kawo ki office ranar."


"Oh, Hamma Muhd?" Tace tana murmushi


"Shi,Hamman ki ne?"


"Eh, dan gidan Adda Maimunan mu ne, gidan da nake zaune a Kano."


"Oh okh, na gane."


"Ka ganshi ne?"


"Eh na ganshi, kina masa murmushi."


"Okh, bamu ganka ba."


_"Ina zaku ganni kuna cikin soyayya."_ yace a ransa, a fili sai yace


"Ni na ganku ai."


"Waya kake?" Kamal yace yana fitowa daure da towel cike da mamaki


"Umm, waya nake." 


"Da wa? A wannan tsohon daren?"


"Ina ruwan Ka? Kai ma ba yanzu ka gama wayar ba."


"Ni ai matata ce, kai fa? Bari naga sunan." Ya nufo shi, tashi zaune Aryan yayi da sauri yana hararar sa


"Corper ce, shikenan."


"Corper? Innalillahi wallahi yaron nan sam baka hadu ba, Raihana ce wai? Bani wayar." Ya fuzge yana dariya


"Kanwata ashe kece?"


"Sir barka da dare."


"Barka dai, ya gida ya kwana biyu?"


"Lafiya lou wallahi, nazo aka ce min kayi tafiya."


"Eh wallahi, sorry ban fada miki ba, ya gidan?"


"Lafiya lou."


"Me yake ce miki da wannan tsohon daren?"


"Ba komai." Tace tana murmushi


"Karki yarda wallahi, haka kawai ya hanaki bacci shi ba wani abu zai fada miki ba."


Dariya tayi k'asa k'asa, sannan tace


"Toh sai da safe."


"A ah karki kashe, bansan ko be gama fadar abinda zai fada ba, gashi sai da safe."


Ya mika wa Aryan din wayar ya karba yana yin hanyar fita daga dakin. 


"Da kayi zaman ka ma, ni bacci na zan ba Jin abinda zaka ce zanyi ba."


"Kana da matsala wallahi."


Ya fice gaba daya, falo ya je ya zauna yana duba wayar sai yaga ashe ta kashe ma, tsaki yaja ya kwanta ya dora kansa a saman hannun kujerar ya cigaba da juya wayar, ko haushi taji dan yace mata corper? Dialing number ya sake yi amma sai yaji switch off, ya mike yana kashe tasa wayar ya koma dakin. Har Kamal ya kwanta ya rage hasken dakin, pillow ya dauka ya nufi kan sofa ya kwanta.


"Har ka gama wayar?"


"Bayan ka kore ta, ta kashe ai."


"Toh akan me zaka hana yar mutane bacci, kai ba kalaman soyayya kake karanta mata ba, sai umm da a ah kawai."


Juya bayan sa Aryan yayi dan ya cigaba da sauraron Kamal din tsaf zai tashi ya bar masa dakin.


"Goodnight." Yace masa kawai ya ja duvet ya rufe har kansa. Dariya Kamal yayi ya ce


"Sai da safe angon corper."


****Da safe Raihana ta tashi da karfin jiki, kafin ta gama shiryawa ta fito falo har Hamma Hydar ya shigo ganin ta, yana tsaye suna magana sai ga Babbo Sadeeq tare da Lamido, ganin jikin nata da sauki yasa su jin dadi suka mata sallama kowa ya wuce office. Dakin Daadah ta shiga bayan ta dan chachakali breakfast ta sameta tana yin sallar walaha, ta zauna ta jira ta idar ta juyo tana kallon ta


"Nazo dazu kina ta bacci ai, ya jikin naki?"


"Da sauki sosai."


"Allah ya kara sauki, kinci abinci?"


"Eh nasha tea."


"Magungunan ki fa?" 


"Nasha suma."


"Toh yayi kyau."


Shiru tayi tana nazarin ta tambayi Dadahn ko kar ta tambaya, tana jin kunyar tambayar amma bata da wata kawa da ta wuce Daadahn dole ita zata tambaya.


"Umm..Daadah."


"Na'am?"


"Misali, idan mutum yana kiranka yana nuna ya damu da kai amma be ce yana son ka, me yake nufi?"


"Eh toh, kinsan kowa da yadda yake nuna soyayyar sa, amma dai duk wanda ya damu da kai toh alamu ne ko da be furta ba."


"Ok."


"Me ya faru?"


"Dama Aryan ne..."


"Kin tuna min ma, ya kiraki kina bacci."


"Eh ya fada min."


"Ok, ya sake kira kenan."


"Eh."


"Toh abinda nake so dake, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, sannan kiyi addu'a, saboda mahaifin ku ya dau zafi akan maganar da duk ta shafi gidan nan, amma kiyi addu'a nima zan tayaki, bamu san abinda Allah ya tsara ba."


"In sha Allah."


"Yawwa, karki tada hankalin ki, duk kuma abinda iyayenki suka zartar a kanki in dai be sabawa shari'ar musulunci ba toh kiyi musu biyayya."


"In sha Allah Daadah, nagode."


"Ah Lallai Raihanatu tayi hankali."


"Kai Daadah."


"Ja'ira, ashe kina son auren."


"Innalillahi, shiyasa fa sai da k'yar na iya tambayar ki,nasan tsokana ta zaki."


"A ah, murna nake dai, yarinya ta girma ta isa aure."


"Shikenan na kad'e har ganye na."


Ta tashi ta fice da sauri.


    Missed calls din Muhd ta gani rututu ko da ta koma dakin ta, har yanzu bata yi masa reply din sakon sa ba, gashi sai sabani suke idan ya kira bata kusa, tausayi ya soma bata a kalla ko ba ta karbi tayin soyayyar sa ba ya kamata ta daga wayar sa taji. Kiransa tayi ringing daya ya daga kamar me jira


"Alhamdulillah." Ya sauke ajiyar zuciya


"Raihana wannan hukuncin yayi min tsauri."


"Hamma ina kwana?"


"Lafiya ba lou ba, kin sani tunani, nayi message no answer, kira no answer. Menene laifi na."


"Kayi hakuri Hamma, bana jin dadi ne, amma na samu sauki."


"Subhanallah, me ya same ki? Ban sani ba ai wallahi, sannu Allah ya kara sauki."


"Amin zazzabi ne kawai ma kuma na samu sauki."


"Kin tabbata?"


"Eh."


"Ok, Allah ya kara sauki. Zan shigo Yolan gobe in sha Allah."


"Na'am?" Tace tana zaro ido


"Eh, ko kar nazo?"


"A ah ban ce ba."


"Kiyi min addu'a, zanzo na ganki muyi magana face to face."


"Toh, Allah ya kawo ka."


"Amin nagode, please zan kiraki anjima karki ki picking dan Allah."


"In sha Allah "


"Nagode, sai na kira, I lov..."


Kit ta kashe wayar ta jefar da ita gefe, ranta ne ya dagule musamman zuwan da yace zai yi, bata so yazo ya sake damalmala komai, tasan yadda ran Abby yake a bace yanzu zai iya yanke kowanne hukunci ma. Bata son shi ko na digo ba kuma zata iya son shi ba, bata tsane Shi ba amma dai, kawai be mata ba, musamman yadda yake magana ba, ba aji ba komai. Flight mode ta saka wayar dan ma kar ya sake kiranta. 


***A tsakiyar falon suka hadu dukkan su dan yi breakfask saboda daddy ba zai iya zaman dinning ba. Ba zasu iya tuna when last sukayi irin wannan zaman ba. Aryan ne ya fito a karshe yana gyara links dinsa, ya karaso ya zauna a gefen Ya Nabeela sannan ya gaida Baba Hassan cikin girmamawa sannan ya juya ya gaisar da Daddy sannan ya Nabeela. Adam ne ya fito fuskar sa a hade yazo zai wuce shi daddy ya kira shi, dawowa yayi ya tsaya daga jikin kujera ba tare da ya russuna ba


"Ba ka gan mu bane Adam?"


"Sauri nake zan fita."


"Kayi breakfast ne?"


"Na koshi."


"Yaushe zaka yi parking din?" Aryan yace yana kallonsa, duk sai suka dawo da kallon su kan Aryan din da yayi magana, yi yayi kamar be san suna kallon shi ba, ya dauki Irish Potato ya tura a bakin sa yana jiran amsar Adam din. Wani kallo yayi masa kafin yace


"Idan kayi hakuri gobe zan tashi ai."


"Good, ina jiranka."


Juyawa yayi bayan yaja tsaki da karfi ya bar wajen. Kallon Aryan Daddy yayi irin kallon neman karin bayanin nan


"Ni nace masa ya tashi."


"Amma me yasa? Da Ka kyale shi ai tunda ba shine yayi laifin ba." 


Ya Nabeela tace, gid'a kai Daddy yayi shima yace


"Ka kyale shi Aryan, be san ko ina ba sai nan, haka be san kowa ba sai mu, mune family dinsa mu kadai ya sani."


"Ba zan iya cigaba da ganin sa ba, idan zai cigaba da zama anan ni zan koma wanchan gidan."


Ya ajiye fork din ya mike, gefen rigar sa Kamal ya ja yaki kallon sa, mikewa yayi shima kawai yace


"Ka kwantar da hankalin ka, zamuyi maganar please."


"Me yasa zai cigaba da zama? Kasan me yake planing? Mahaifiyar sa ce fa ake magana, dole zai ga rashin kyautawar mu, kuma zai yi kokarin taimaka mata, ba zai yiwu muna tufka yana warwarewa ba."


Ya fada a hasale, rike shi Kamal yayi yana girgiza masa kai


"Karka sake daga muryar ka Aryan, waye yayi magana anan? Mahaifin mu ne sai Ya Nabeela, me yasa kake saurin hawa haka? Komai idan aka bishi ta hankali ai zaa fi cimma shi."


"Fushi yake dani Kamal." Daddy yace muryar sa na rawa


"Wannan ba daidai bane ba, baka kyauta ba kuma." Kamal yace 


Sakin hannun sa Aryan yayi yana matsawa nesa dashi, kirjinsa da yake harbawa da sauri da sauri ya dafe, ya runtse idon shi. Be san me ya hau kansa haka ba. 


"Are you ok?" Ya Nabeela ta riko shi tana kallon fuskar sa, girgiza mata kai yayi yana rike da kirjin sa


"Kana shan maganin ka kuwa?"


"Baya sha." 


"Zauna." Tace ta yi saurin dauko ruwa ta zo ta bashi, ya karba ya kafa kai ya shanye tas, sannan ya dafe kansa da hannun sa biyu. Malam Hassan ne ya taso daga in da yake zaune, yazo wajen Aryan din ya dafa shi, ya dago suka hada ido


"Kar ka bari zuciya ta debe ka,ka aikata abinda zaka zo kana dana sani, su iyaye daraja ce dasu, kuma wajibi ne yin biyayya a garesu, kuma dole kayi hakuri dasu a duk yanayin da ka same su."


"Bansan me ya hau kaina ba Baba, ban sani ba."


"Na gane yanayin da kake ciki, amma dole ka sani baka da hujjar da zaka kare kanka ko a gaban Allah, iyaye sun wuce in da kake tunani."


"Kuyi hakuri dan Allah, hakan ba zata kara faruwa ba."


"Wannan itace tarbiyya, karka damu ka nemi gafarar mahaifin Ka sannan ka roki Allah ya yafe maka, ka zama me biyayya da danne zuciya, ka yawaita azkar zaka samu nutsuwar zuciya"


"In sha allah."


"Tashi muje ka karya, ka kuma nemi yafiyar mahaifin ka,komai ya wuce ku fara sabuwar rayuwa, domin kai ma Allah ya baka ya baka 'yaya masu jin kanka."


   Falon me yayi shiru sosai sai karar AC kawai dake tashi a wajen, breakfast din ake amma kowa ransa babu dadi, Aryan dai jujjuya chokalin kawai yake ba tare da yaci komai ba. Dago idanun sa yayi da suka kad'a sosai ya kalli Daddyn


"Dan Allah daddy kayi hakuri ka yafe min."


"Na yafe maka Aryan, duk abinda kayi min kana sani da wanda baka sani ba, na yafe maka, nima ka yafe min halin da na jefa ka a ciki, dan Allah, kai yaro ne me biyayya, kuma ban taba saka ka ko na hanaka abu kayi ba, baka taba ketare umarni na ba, duk kuwa da tarin abubuwan ki da nayi maka."


"Allah yayi muku albarka gaba daya."


Hawaye Ya Nabeela ta goge a fakaice, wannan ranar na cikin ranakun da take burin gani a rayuwar ta, sai gashi ta gani yau, Aryan da Daddy sun shirya. 


"Ni baka bani hakuri ba." 


Kamal yace cikin sigar tsokana, dariya akayi dukka banda Aryan din, da ya mike yace zai ya hau sama, ya haye suka bishi da kallo dukka.

1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Pls Ina neman rumbun qaya from page 12 to in da ake

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post