Abban Sojoji Takun Karshe chapter 95

Abban Sojoji Takun Karshe chapter 95

Abban Sojoji Takun Karshe

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ARSHE🔥*

Bayan *Jahad* ta fito daga toilet, hijab ta ɗauko cikin wardrobe ta zura ajikinta,wurin gadonsu ta koma ta haye sama tare da kai hannu tana bubbuga hosana,

   "Get up hosana,Time ɗin sallah yayi,"

  hosana bata motsa ba,sae ma cigaba da jan minsharinta da tayi,

  "Hosana ki tashi mana!ba zaki tashi ba wai,kullum sai kin bani wahala idan nazo tashin ki daga bacci"tayi maganar fuskarta a ɗaure,

  Hosana kuwa,gyara kwanciyarta ta ƙara yi,har wani ƙara jan minsharin takeyi da ƙarfi don ma jahad tasan cewa tayi nisa a baccinta,alhalin tun a first call da tayi mata ta farka,

    A ƙule jahad tace"kada Allah yasa ki tashi,kuma saina faɗa ma ya Omar cewa baki yin....."tunkan taƙarasa maganar,hosana ta diro daga saman gadon da gudun gaske ta nufi toilet ta buɗe ta shige ciki,dariya jahad tayi sosai kafin ta sauka daga saman gadon ta koma ta shimfiɗa carpet ta kabbara sallah,


Sehrish kuwa tana a ƙudundune cikin bargo tayi lamo tana faman sauke ajiyar zuciya,kokwanton abunda ya faru tsakaninta da Sgr takeyi,ta kasa gasgata abunda ya faru last night,shin dagaske ne ko kuwa mafarki ne tayi,Don tasan cewa hakan zai yi wuya ya kasance gaskiya,Abun ya matukar ɗaure mata kai,ya caza mata brain ɗinta,tana cikin wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita,


*Junaid Romeo*


Bude ƙopar bedroom ɗinsa yayi tare da fitowa daga ciki,Still kayan baccin jiya ne ajikinshi,ya kara wayarshi a saman kunnanshi,hakan na nuni da cewar waya yake yi,Ashagwa6e yake magana yana faman tura baki,

  "Abba pls come back Soon,nafiso na ganka a kusa dani,"ya ɗan yi maganar yana bubbuga ƙafarshi ƙasa,

  On the other hand,Abbansu yace"ka ji tsoron Allah junaid!Nafa gano ka,So kake in dawo gida,saboda ayi maganar aurenka ko"?

  Murmushi junaid ya saki yana ɗan sosa ƙeyarshi da ɗayan hannunshi"eh dan Allah Abba,nidai duk atakure nake,Allah jina nake kamar a prison,Ayi mun aure kawai in ana son zaman lafiya,"

  Abba yace"idan ba'ayi maka auren ba fa"?

   Ƙuƙuni ya shiga yi ƙasa ƙasa yana cewa"zan addabi kowa ne,in kuma kama ɗaki a hotel....."

Bai ƙarasa maganar ba,Jin dariyar Abbansu ta cikin wayar,ashe duk yaji abunda yake cewa,  

   "Junaid wa kayi mawa?kasan cewa yayyenka gaba ɗaya soldiers ne,Wlh kayi kuskuren yin badai dai ba,kai kasan inda za'a kai ka,".  

  Jin wannan maganar ta Abba yasa shi ɗaure fuskarshi,

  Yana tafiya yana waya,da alama part ɗin Sgr zai wuce,saboda can ya nufa,

  Lokacin daya shiga falonsa,babu kowa,a saman sofa ya zauna,sai da ya kammala yin wayar da Abba,Su kayi sallama,Sannan ya miƙe tare da wuce wa bedroom ɗin Sgr,

  Sallama yayi mashi,jin shiru yasa shi shiga cikin ɗakin kaitsaye,a kwance ya same shi saman katafaren gadon nashi,ya lullu6e jikinshi har zuwa chest ɗinshi,jallabiya ce sanye ajikinshi,tun daga kan yadda yake yin baccin nashi zai tabbatar maka da cewa,yana cikin kwanciyar hankali da natsuwa,

  Lalla6awa Junaid yayi ya ƙarasa kusa da gadon,yana ƙoƙarin hawa idanuwanshi suka sauka asaman bargon Sgr,turus yayi ya tsaya yana kallon ikon Allah,Ya jima yana tunanin kome ya jawo hakan,abu dai gashi nan kana ganinshi ta cikin bargon,hawa sama yayi har zuwa saitin fuskarshi sannan ya tsaya tare da furta sunanshi a hankali"Babban yayanmu,"shiru bai amsa mashi ba,ƙara ɗaga murya yayi'babban yaya,"

  Hannu ya kai tare da shafa gefen fuskarshi ya sake cewa"Babban yaya..,"

  Har cikin dodon ears ɗinsa yaji kiran nashi,daƙyar ya iya ware blue eyes ɗinshi,biji biji ya fara gani kafin idanuwan suka ɗan washe,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunan shi"Junaid,"

  Murmushi junaid yayi tare da cewa"nazo ne don na takura maka,Jiya na jira naga dawowarka,amma baka dawo gida ba,har bacci ya ɗauke ni,'_

  Zuba mashi ido Sgr yayi yana kallonshi,

   Hakan yasa junaid ya ɗan tsuke fuskarshi yace"haba yaya rafayet,in zauna in tayi maka zuba kamar parrot maimakon ka mayar mun da martani saika zuba min ido kana kallona,"

   a hankali ya lumshe idanuwanshi kafin ya sake ɗan waresu akan Fuskar junaid ɗin,

  "Me kake so ne"?

Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"Yanzu babban yaya sai inason wani abu zanzo wurinka?jiya fa na dawo daga tafiya,ko farin cikin ganina ma baka yi ba,"

  Ruƙo hannunshi Sgr yayi tare da janyoshi ya kwantar da kanshi saman ƙirjinshi,yana ɗan shafa bayanshi yace"Am glad to see you,Ya gajiyan tafiya,?kayi mun tsaraba"?

  Ashagwa6e junaid yace"Eh mana,munyi tsarabar fura,da zuma,da sauransu dai,idan kanaso zan yi ma rishi magana ta dama maka fura kasha,Wlh akwai daɗi sosai,nima in nasha kunne na har rawa yake yi,'

   Ya ƙarasa maganar tare da ɗagowa daga jikinshi,da buɗar bakin Sgr sai cewa yayi"you mean tafi abun da nasha last night daɗi"?

A ruɗe junaid yace"babban yaya,me kasha jiyan?Ae ni bansan shi ba balle in san cewa ko yafi furar daɗi,

  Shi kanshi baisan ya furta hakan ba,it was just slip of the tongue,saboda ya kwana da abun aranshi,kuma yanzu haka ma shi yake tariyowa acikin brain ɗinsa,abun ya tsaya mashi arai,yadda har surar jikinta taja ra'ayinshi har ya fita hayyacinshi ya fara romancing ɗinta,ƙiris ya rage jiya ayi abun kunya,

(Allah yaso bai ƙarasa headquater ɗin ba,da shikenan an buge boss,(in jini ba,don na lura wasu in ina kara wannan bayanin suna tsammanin cewa Sune sukeyin zancen zucin,sometimes ina ƙarawa da nawa bayanin)


"Yaya rafayet,"junaid ne ya ambaci sunanshi,ganin ya shiga zurfin tunani, hankalinshi yayi wani wurin,mayar da idanuwanshi yayi kan junaid tare da cewa"don't disturb me pls,Inaso na ɗan huta junaid,"

  Ranshi ya ɗan sosu,jiki asanyaye ya juya zai sauko daga saman gadon,Sgr ya dakatar dashi"Wait,'ɗan tsayawa yayi tare da juyawa yana kallonshi,

  "Tell me what do u want from me"?

Shiru junaid yayi yana lissafin adadin kuɗin da zai kar6a a wurinshi,Don sunyi da jahad zasu fita yawo,gashi ƴan kuɗaɗen acct ɗinsa duk sun ƙare,Yayi broke,'

  ɗaga yatsun hannunshi yayi yana yin lissafin,hakan ba ƙaramin dariya yaso yaba Sgr ba,dama sai da ranshi ya bashi cewar wani abu ne ya kawo shi bedroom ɗinshi,tunda sassafe ko wanka bai yi ba,balle aje ga maganar breakfast,A tsiyacen shi yazo,

  "Zan koma bacci,tunda naga lissafin na ka bamai ƙarewa bane,"

  Da sauri yace"pls babban yaya kada ka koma bacci,yanzu ma daƙyar na tashe ka,". 

  ta6e lips ɗinshi yayi tare da nuna wurin dressing mirror ɗinshi da hannunshi,Yace"idan kuɗine kake buƙata a wurina gasu can ka ɗauki iya yadda kakeso,idan ma na cikin nan isn't enough for u,Zan ƙara maka ta acct,hope hakan yayi maka"?yayi tambayar yana kallonshi,.  

  Washe baki junaid ya shiga yi yana cewa"Babban yaya nagode sosai,wlh duk gidan nan kafi kowa sona,har Daddy ma kafi shi sona,"

  Harara Sgr ya ɗan jefa mashi kafin yace"Saboda ina baka kuɗi ko"?_

  fashewa junaid yayi da dariya,tare da saukowa daga saman gadon ya nufi wurin dressing mirror,


Mayar da idanuwanshi yayi ya lumshe su,shikaɗai yasan irin feelings ɗin da yake ji,kamar yayi hauka,Kuma shi irin mutanan nan ne,waɗanda basa wasa da lafiyar jikinsu,Komai yaji jikinshi na bukata yinshi yake yi don ya samu cikakkiyar lafiya,shiyasa gashi nan ta ko'ina masha Allah,tun daga kan skin ɗinshi zakasan cewa ba ƙaramin gyara take sha ba,haka sumar kanshi,da sauran parts na jikinshi,yanzu kuma ga wani new abu da yake bukata Urgently,


Zuƙunnawa junaid yayi agaban drawer ɗin,ya buɗe middle ɗinta,Dollars ne ya gani a jere,cike fam da ita,har wani ƙyalli kuɗin sukeyi acikin idanunshi,murza hannunshi ya shiga yi,har wani ƙaiƙayi suke yi mashi,Bandir ukku ya ɗauko ya tura su daƙyar cikin aljihun wandonshi,duk da haka basu isheshi ba,sae daya ƙara da naira,A gida na ƙarshe daya buɗe ajikin drawer chest din,kuɗin nigeria ne,Suma ya ɗauki Bandir uku na dubu dubu kusan dubu ɗari uku kenan,Ya turasu cikin ɗayan aljihun daƙyar suka shiga,Bayan ya kammala ya rufe mashi ita,yana ƙoƙarin miƙewa,idonshi ya sauka akan hoton daya faɗo ƙasan tiles,baisan daga ina hoton yake ba,duk a tunanin shi hoton Babban yayansu ne,

  Zukunnawa yayi tare da kai hannu ya ɗauki hoton da ya kife,ya juyo dashi yadda zai ganshi da kyau,

  Da karfi ya furta"Sehrish!"miƙewa yayi tare da tunkarar wurin gadon hannunshi ruƙe da hoton yaci gaba da cewa"wlh itace," jin sambatun da junaid keyi ne yasa Sgr ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da wurga eye balls ɗinsa wurin junaid dake tunkaroshi

   Zama yayi daga gefen gadon fuskar nan tashi awashe cike fal da farin ciki,ya kuma yace"Wlh itace,Yaya rafayet ina ka samu hoton rishi tana ƴar ƙarama,"

  "Junaid what are u talking about"?yayi tambayar a yayin da yake ɗan miƙewa zaune,tare da jingina bayanshi akan gadon,

   "Sehrish mana!wadda take yi maka aiki,"

  Cike da mamaki Sgr yace"Kana nufin itace a pic ɗin"?

  Jinjina kai junaid yayi"ƙwarai kuwa itace,"

  Cike da mamaki Sgr ya kuma tambayarshi "taya akai ka gane cewa itace?cos i even asked her last time,amma ta sanar dani cewa ba ita bace'

  Junaid yace"ae duk cikinsu,babu mai ɗigon tawada asaman wuyanshi sai ita,duk sauran basu dashi asaman neck ɗinsu,Idan ka kalli hoton nan dakyau,zaka ga ɗigon baki asaman wuyanta,'. 

  "Lemme see"ya buƙaci ganin hoton,da sauri junaid ya mika mashi,hannu yasa ya kar6a,sannan ya ƙura ma hoton ido yana kallonshi,ɗigon tawadar ya gani asaman wuyanta,closing eyes dinsa ya ɗanyi,yana tariyo kallon da yayi ma ƙirjinta adaren jiya,har izuwa saman wuyanta,tabbas yaga black point ɗin nan,amma abun ya daure mashi kai,ta yadda har ita kanta,bata gane cewa ita bace a hoton,

Buɗe idanuwan nashi yayi akan fuskar junaid sannan atsanake yace"Junaid,dama kallonta kakeyi?" cike da tuhuma yayi mashi tambayar,

  Sunnar da kai junaid ya ɗan yi yana sosa ƙeyarshi yace"Nifa ba kallonta nake yi ba,tun lokacin baya ne,kafin ta bayyana amatsayin mace,muna da kusanci sosai da ita,shiyasa ma har nayi mata wannan kyakkyawan sanin,"

   "Its okey" ya furta hakan,tare da mayar da idanuwanshi kan hoton,Abun ya daure mashi kai,sai lokacin ya shiga tunanin ko meyasa Uncle Abusufyan ya basu hotonsu shi da Omar?

  Muryar junaid ce ta katse shi da cewa"Ka taso muje dining muci abinci pls,nasan kana jin yunwa,'

  Runƙo hannun Sgr yayi,har sai da ya samu ya sauko daga saman gadon,Sannan suka fito atare,har lokacin hoton na hannunshi,daga bayane ya zura shi cikin aljihun jallabiyarshi


Saukowa downstairs suka yi,tunkafin su ƙarasa dining ɗin,suka hango Uncle Abusufyan tare da Marshal Omar,ga Jahad da Hosana ma,duk suna azaune suna cin breakfast ɗinsu,Azmee ce atsaye take yin serving ɗinsu,

  koda suka ƙarasa,da sauri su jahad suka gaisar dashi"babban yaya ina kwana,an tashi lafiya,"?

"Lafiya,sannunku"ya ambaci hakan kafin ya samu wuri ya zauna,junaid ma ya zauna a kusa dashi,

   "Big bro,jiya na jira dawowarka gida baka dawo ba,ina fata kana cikin ƙoshin lafiya,"acewar Marshal Omar,

  "Am ok,"ya bashi amsa atakaice,dama fushi yake yi dashi saboda yaso su dawo gida atare,Amma Omar yace sai ya ɗan ƙara kwanaki,

  Juyawa ya ɗanyi tare da kallon Abusufyan,wanda shima kallon nashi yake yi,jira yake yaga iya gudun ruwan nashi,zai gaisar dashi ne?ko kuwa jira yake yi shi ya gaishe da shi Ne?

   a hankali ya furta"Uncle,ya gajiyar tafiya,jiya kun dawo time ɗin bana nan"

  Murmushi Abusufyan ya ɗan saki tare da cewa"lafiyalou Alhamdulillah,gajiya tabi jiki,'

  Matsawa azmee tayi ta ɗauki plate ta shiga zuba masu abincin da zasu ci,

  Hosana tace"Daddy,rishi fa?kada acinye ita bata ci komai ba,"

  Jahad tace"bacci takeyi tun ɗazu,kuma har tashinta nayi tazo muci abinci,amma tace mun in ƙyaleta,bata jin daɗin jikinta,'

  "Me ya ke damunta ne"?Omar yayi tambayar,

  "Nima bansani ba,tunda asuba dai kamar bata da lafiya,duk ta canza mun,har tambayarta nayi meke damunta amma bata sanar dani ba,"

  Abusufyan yace"bai kamata a ƙyaleta ba,yakamata ku kirata tazo muji menene matsalarta,"

  Jiki na rawa junaid ya miƙe zaije kiranta,karaf idanuwanshi suka sauka kan fuskar Sgr,wani irin kallo ya wurga mashi mai kama da harara,batare da kowa ya lura ba,komawa junaid yayi ya zauna,tare da cewa"Jahad kije ki kirata mana,"_

  "Amsa mashi tayi da toh,kafin ta mike cikin sauri ta wuce bedroom ɗinsu,

  Cike da zolaya Marshal yace"Wato har ka fara bata Command ko"?_

  Kunyace ta rufe junaid,har ya kasa shan Tea ɗin da ya ke sha cikin cup,Satar kallon Abusufyan yayi,Suna haɗa ido nan fa ya ƙara kame kanshi,

Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba,Hosana tace"Ya Omar,wai yaushe ne abun nan?kace idan kuka dawo za'ayi magana nifa na kagara wlh,"

  Gabanshi ne ya fadi rass,Hankali aɗan tashe ya ɗago ya kalleta,ko ajikinta sae ma tura pancake takeyi acikin bakinta,wata irin kunyace ta rufe shi,.  

  Shi kanshi Abusufyan,kunyarce ta rufeshi,sai faman jujjuya fork yake acikin plate,ya kasa cin Abincin,

  Sgr kuwa har ɗagowa yayi ya kalli Hosana da tayi maganar,

  Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,jurewa kawai takeyi,

  Junaid ne yayi ƙokarin dakatar da ita ta hanyar yi mata raɗa acikin kunnanta,

  "Hosana waike baki da burki ne?meyasa zakiyi mashi haka,Duk kinsa sunji kunya,daga shi har Daddy ɗin naku,bai kamata kice haka ba,"_

  Turo baki ta ɗan yi tare da cewa"zunubi na aikata ne?kawai kawai saboda nace....."bata ƙarasa maganar ba,sakamakon kallon da taga Omar yayi mata,nan take ta shiga taitayinta,

After some minutes,Jahad ta shigo Dining area ɗin,tunkan ta karaso Junaid yace"ina rishi ɗin take ne"ganin ta dawo ita kaɗai batare da Sehrish ba,

  "Tana aciki,yanzu zata fito,"ta karasa maganar tare da samun wuri ta zauna,

A hankali ta zuro da kafarta,har yanzu jallabiyar ce ajikinta,ta laga gyale akanta,ƙafarta kuma na sanye da flat shoes,jikinta sae kerma yake yi,saboda zazza6in daya rufar mata,amma bata so kowa ya gane halin da take ciki,hakan yasa tun kafin ta ƙaraso wurinsu,ta daidaita natsuwarta sosai,sannan ta shigo dining area ɗin,takun takalminta ne ya janyo hankalinsu,duk suka juyo suna kallonta,gabanta ne ya faɗi Rasss ganin Sgr zaune,aikuwa a ruɗe ta juya zata koma ciki,.  

  Abusufyan ya dakatar da ita,ta hanyar ambaton sunanta"Sehrish,"tsayawa tayi cak,batare da ta ƙara ɗaga ƙafarta ba,wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,kafin a hankali ta juyo ta ci gaba da tafiya,hankalinta duk yabi ya tashi kamar taga wani mugun abu,

   Wurin Abbansu ta tsaya,tare da gaisar dashi,"daddy ina kwana,". 

  Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"lafiyalou Daughter,meyasa baki fito ba tun ɗazu,"?

   "Bana jin daɗin jikina ne,Amma naji sauƙi yanzu"

   "Alhamdulillah,samu wuri ki zauna,"cike da kulawa yayi maganar,

  Gabanta sai faɗuwa yakeyi,ta rasa ta ina zata zauna,inda bazata fuskance shi ba,balle har su haɗa ido,

  Ganin taƙi samun wuri ta zauna sai ƴan dube dube takeyi,Hakan yasa Omar nuna mata gefenshi yace"Zo ki zauna,"hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,saboda yana a left hand ne kuma suna fuskantar su Sgr dake ta dama,kuma kujerar da zata zauna,ita ke fuskantarshi,jiki a mace ta ƙarasa gefen Marshal ta zauna,muryarta na kerma ta gaisar da Marshal"ina kwana yaya Omar,"

  Da fara'a a fuskarshi ya amsa mata,"lafiyalou sister,ya jikin naki,"

  "Da sauƙi,"ta bashi amsa,

"Allah ya ƙara sauki,"

  "Ameen"

"Yaya rafayet,ina kwana,"daƙyar ta iya gaishe shi,sai dai ko kallo bata ishe shi ba,balle har tayi tsammanin zai amsa mata gaisuwarta,lokaci guda ta gane dalilin dayasa yaƙi amsa mata gaisuwar saboda bashi ta fara gaisarwa ba,a matsayinshi na boss ɗinta,wanda ke asama da mahaifinta,

  "Bro baka ji ana gaishe dakai bane"?acewar Omar

   Batare daya ɗago ya kalleshi ba yace"Naji,"yayi maganar tare da ɗaukar cup na coffee yana sha,

  Murmushi marshal yayi,saboda ya gane reason ɗin dayasa yaƙi amsa gaisuwarta,

   Zagayowa azmee tayi kusa da ita,ta ɗan duƙa saitin kunnan sehrish tace"Amaryarmu,me kikeso a zuba maki ne?farfesun nama ko Snacks,"?

    Murmushi sehrish tayi har dimple ɗinta ya lotsa,sannan tace"Aunty azmee pls kidaina zolayata,yanzu idan yaji fa?ni zaki jamawa,"cikin raɗa tayi maganar don kada suji mai take cewa,

  Azmee tace"Shikenan Mrs rafayet,na daina,yanzu dai me kikeso"?

  Sehrish tace"farfesun zaki samun,saboda bakina babu daɗi,"

  Su6ul da baka azmee tayi wurin cewa"kice mun kusa samun ƙaruwar baby kenan,"karaf maganarta ta sauka akan kunnan Sgr,kuma cikin whispering tayi maganar,amma wani iko na Allah yaji abunda tace,ko kuwa yayi amfani da motsin la66anta ne Oho,

  Kamar daga sama taji yace"Keee!"a ɗan firgice azmee ta ɗago,ba ita kaɗai ba hatta su Uncle sai da suka ɗago suna kallonshi,ya haɗe fuskar nan babu annuri acikinta,.

    Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da tabar wurin,Jiki asanyaye azmee ta juya da sauri tabar wurin,

  Sam sehrish bata ji daɗin hakan ba,duk sai taji babu daɗi,bata so Sgr ya kori Azmee ba,agaban kowa da kowa wannan kamar Cin fuska ne,Su kansu sauran dake zaune a dining ɗin basu ji daɗin hakan ba,shiru kawai su kayi,tunda basu da yadda zasuyi dashi,

   Ganin ya sallami Azmee yasa ta shiga ƙoƙarin yin serving ɗin kanta,plate ta ɗauko acikin jerin plates ɗin dake ajiye saman table din,Warmers din tashiga bubbuɗewa harta buɗo wadda ke ɗauke da farfesun naman kaza,serving spoon ta sanya,ta shiga ɗibarta tana zubawa acikin plate din,sai da tacika shi,sannan ta rufe warmer ɗin,

Sosai ta shiga shan farfesun,har wani lasar baki takeyi saboda daɗinshi da takeji,cinyar kaza ta ɗauko tana ƙoƙarin kaiwa bakinta,Sgr ya ɗago da idanuwanshi,karaf suka shiga cikin nata,nan take tasha jinin jikinta,kasa ƙarasa kazar tayi cikin bakinta,cak ta tsaya,tana kallonshi,

  Wannan karon kallon da yake yi mata yasha bambam da irin kallon daya saba yi mata a baya,gaba ɗaya sun shagala da kallon junansu,babu wanda ya lura a wurin,tunani tashiga yi komai yasa yake kallonta har haka batare da ya janye idanuwanshi ba?

  Shikuwa gogan jira yake ta kawar da idonta daga kallon da takeyi mashi,kada raini ya fara shiga tsakaninsu,saboda abunda ya faru jiya,musamman da ta ganshi tsurararshi babu kaya a jikinshi,

   ƴar harara ya watsa mata,tare da janye idanuwanshi daga kanta,kawar da nata idon tayi,mayar da cinyar kazar tayi cikin plate,gaba ɗaya taji komai ya fita ranta,ba don ta ƙoshi ba,ta miƙe zata bar dining ɗin,

  "Whe're u going"muryarshi ce ta dakatar da ita,

   daƙyar ta iya buɗe baki tace"Na koshi,"

  Zuba masu ido Abusufyan yayi yana kallonsu,

    "Koma ki zauna,"Yayi maganar yana nuna mata seat ɗinta,Tamkar ta fashe da kuka haka taji,juyawa ta dan yi suka haɗa ido da daddynsu,kafin ta zauna,taci gaba da shan farfesun da ta rage,

  Hannu yasa ya yago tissue,yana goge mouth ɗinsa,kafin daga bisani ya miƙe ya wuce part ɗinsa,

   Sai da ya bar wurin sannan,ta samu natsuwa,

  "Daddy,ya maganar zuwa kano?sehrish ta faɗamun cewa,da zarar kadawo daga damaturu zaku wuce kano,Wurin neman Oumman mu,"jahad ce tayi maganar,

  "In sha Allah gobe nake son tafiya,tunda Asuba before ku tashi daga bacci ma"

  Yana kai ƙarshen maganarshi,Hosana tayi saurin cewa"daddy,pls dani za'a tafi,wlh inason zuwa kano,"

  Harara marshal ya ɗan wurga mata kafin yace"a haka za'a tafi dake?me kika sani?Faɗamun a wata unguwa kuka zauna a kano"

   Wurga ido sama tayi tana ƙoƙarin tunano anguwar da suka zauna a kano

  Yatsina fuska tayi tare da cewa"Dawanau ko"?

me zasuyi in ba dariya ba,gaba ɗayansu suka fashe da dariya,ɗaure fuskarta tayi,don ita ba ta faɗi don ayi mata dariya ba,bilhaƙƙi da gaske take ita,

  Jahad tace"kai  hosana dawanau fa kika ce?Anan ne muka zauna?,' murguɗa mata baki tayi batare da ta ƙara cewa komai ba,

   "Daddy dan Allah ka tafi dani,nafi kowa son naje,"acewar sehrish,

  Mayar da idanuwanshi yayi kanta tare da cewa"Kin tambayeshi ne?ko kin manta yadda muka yi dake,"_

  Jin haka yasa ta ɗan ɗaure fuskarta don tasan cewa,daƙyar ne Sgr yabarta ta tafi kano,

  "Ki je ki tambayeshi,idan ya barki tun yau ki fara shiri don da asuba zamu tafi,idan kuma ya hana to zan tafi da jahad ne"

   Tuni idanuwanta suka ciko tab da kwalla saboda tasa ran zuwa kano,

  Mikewa tayi daga saman kujerar tace"shikenan daddy,zan tambayeshi,Allah yasa yabarni,"ta ƙarasa maganar tare da barin wurin da sauri ta wuce ciki,

Bayan sun kammala yin breakfast ɗin,kowa ya kama gabansa,

A 6angarensu Aunty babba,tafiya ta kankama,Domin kuwa tun yau sun kammala shirinsu na tafiya Enugu,sun kimtsa kayansu da zasu tafi dasu,da asussuba zasu bar Abuja,da farko zasu fara sauka a hotel ne,a washe garin ranar zasu wuce,Cikin dajin da Bokan yake,taci alwashin cewa Sai taga bayan Hosana,saboda itace silar tonuwar asirinta,kuma A sanadinta ne tarasa igiyar auranta ɗaya,Bayan haka kuma taci alwashin saita Sanya soyayyar Abra acikin zuciyar Sgr,fiye da yadda ya Ke son iyayenshi,

  Tashin hankali!Rayuwar hosana na cikin haɗari,

Shin ina hayaam dake a kwance gadon asibiti cikin mawuyacin hali,har yau ba ta dawo cikin hayyacinta ba,Gashi likitocin sun nemi wani makusancinta sun rasa,babu wani atare da ita,baiwar Allah,bamu son ya zata ƙare ba,

Gab da sallar magrib,Wayarta dake ajiye saman gadonsu ta shiga ringing,a lokacin tana acikin toilet,Jahad ce kawai acikin bedroom ɗin nasu,tayi zaman cin tuwo saman gadon,ta ƙura ido tana kallon k-drama acikin system dinsu,Hannu tasa tare da daukar wayar Sehrish,ta duba mai kiran nata,Sunan Aunty azeema ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,picking tayi tare da manna wayar a kunnanta,

  "Assalamu alaikum,mommy azeema"

On the other hand azeema tace"Daughter,kin ga saƙo na"?_

Murmushi jahad tayi kafin tace"Aunty azeema yanzu baki gane muryoyin mu?Jahad fa ce ba rishi ba,"

  Hajiya azeema tace"wlh naso in ɗauki muryarki,Ashe second daughter ce,To ya kike"?

  "Lafiya lou Alhamdulillah ina lafiya,"

  "Madallah,Amaryar junaid,"

Cike da jin kunya jahad tace"Aunty azeema waya faɗi zancen nan,"

   Dariya hajiya azeema tayi kafin tace"oh kin manta matsayina a wurin daddynku ne?Ae shi da kanshi ya sanar dani,kuma naji daɗi wlh,Junaid zai samu kamilar mace wadda zata kula da rayuwarshi,"_

  kayataccen murmushi jahad ta saki,ba ƙaramin daɗin maganar taji ba,

   "Ina fata zaki kula mana da bugun zuciyar mu?

  Dariya jahad tayi tana faɗin"in sha Allah,zan kula maku dashi,"

  Hajiya azeema tace"Yawwa My daughter,but akwai abunda nakeso na tattauna tare dake game da junaid!amma ki bari zan kira wayarki,ko zuwa anjima ne,"

  "To Aunty Allah yakaimu anjiman lafiya,"

  "Ameen daughter,ina sehrish ɗin take ne?inaso nayi magana da ita ne,"

  Jahad na ƙoƙarin bude baki tayi magana,sai ga sehrish ta fito daga toilet din,jikinta sanye da bathrobe,wankan marece tayi,dama duk in tana period,kusan sau uku take yin wanka,'

   Ganin wayarta a hannun jahad yasa ta tunkarota tana tambayarta wanene ya kirata,

  Mika mata wayar jahad tayi"kar6i nan,Mommy azeema ce keson magana dake"

  Jiki na rawa ta kar6i wayar,da sauri ta koma gaban mirror,ta zauna saman kujerar,sannan tayi mata sallama,

  "Daughter,ya ake ciki ne?ina fata kinga saƙona ko"?

..Sehrish tace"nagani,junaid ya kawomin su,nagode sosai,"

  "Yawwa,Zaki ga turarurruka aciki,Tun yanzu zaki fara amfani dasu,akwai wasu sirrika atattare dasu,sannan akwai mayuka na gyaran fata,dana gyaran gashi,Original ne,Cikin one week,kina fara amfani dasu zaki ga sauyi a jikinki,Sannan akwai sauran kayan da ba yanzu zakiyi amfani dasu ba,suna da haɗarin gaske,su kansu turarurrukan nan,Shu'umaine na gaske,Fisgar mutun sukeyi kamar magnet,ƙarfi ne dasu,duk in zaki shafasu ki bari sai in zaki part ɗinsa,idan ba haka ba gaskiya za'a iya samun matsala,"

  Natsuwa sehrish tayi tana sauraronta,sun jima suna waya kafin daga bisani su kayi sallama,

   Kasa yin amfani da turaren tayi,tsoranshi ma take ji,tunda taji ance fisgar mutun yake yi,kada ta jama kanta bala'e tana zaman zamanta lafiya,

   bata shafa turaren ba,Amma ta fara amfani da mayukan gyaran jikin,

  Shaf shaf ta shirya cikin Doguwar riga ta material black colour,mai zanen manyan flowers a jikinshi launin ash,rigar tabi shape ɗin jikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba gaban mirror ta koma ta zauna,powder ta murza a fuskarta,Sannan ta shafa man baki,la66anta sae salƙi sukeyi,

   Bata yafa komai akanta ba,Iya sumar kanta ce data sauko har gadon bayanta,high hills ta zura a ƙafarta,

  Kama hanyar fita daga ɗakin tayi da sauri jahad tace"Ina zuwa?

  "Zanje part ɗin babban yaya ne,Inaso na gyara mashi ne,"

  Murmushi jahad ta saki tare da mayar da idonta kan system ɗin gabanta,

  "Kinyi kyau sosai,kada fa ki zautar mana da babban yayanmu a rasa gane kanshi,"

  dariya sehrish tayi batare da tace komai ba,ta fuce daga dakin,

Babu kowa a falon,da alama duk sun tafi yin sallar magriba ne,tana cikin tafiya,kwatsam taji an ruƙo sumar kanta ta baya,a firgice ta juya don taga wanene,Gabanta ne ya faɗi rass!ganin Haroon kamar wani maye haka ya kama dogon gashin kanta,yakai shi izuwa saitin hancinsa yana shinshinar ƙamshinshi,

  A wani irin tsorace sehrish ta buge hannunshi,sam batasan cewa zata hadu dashi ba,da batayi kuskuren fitowa daga dakinsu ba,batare da ta sanya mayafi ba,

   Fuskarta a daure tace"Dan Allah menene haka"?

  Shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"Shauƙi,"

  Harara ta watsa mashi,aranta tace"Mai hali bai ta6a canzawa dama saida raina ya bani cewa karyane tuban da yace mun yayi,"

  Guntun tsoki taja,da hanzari ta juya zata wuce saman stairs din,aikuwa da sauri ya sha gabanta ƙiris ya rage ƙirjinta ya daki nashi,hakan ba ƙaramin daga mata hankali yayi ba,

  "Ka bani wuri na wuce,banason wannan rashin wayon naka,Bakasan cewa ni matar aure bace,"

  Ta6e bakinshi yayi tare da cewa"And then so what idan ke matar aure ce?Nafa son komai,auren yarjejeniya ne,mutumin nan fa da kika kwallafa rai akanshi ba sonki yake yi ba,Ni ne mosayinki,inason ki sosai,kuma ashirye nake dana aureki da zarar ya sake ki...."

  Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta,tuni idanuwanta suka cicciko da kwalla,ta tsani taji ance mata haka,

  Ranta a matuƙar 6ace tace"Wlh koda ace mazan duniya sun ƙare duka kaf babu su,kai kaɗae ne ka rage sai dabbobi a cikinta,to na ƙwammace in auri Biri da in aure ka,"

  Waro ido waje yayi yana kallonta a hasale yace"Ke!ni kike gayawa wannan maganar?baki da hankali ne?ki rasa dawa zaki haɗani sai biri,kina nufin cewa biri yafi ni mahimmanci a wurinki"?

   "Ƙwara shi dabbane,kaifa mutunne mai hali irin na dabbo...."_

  Bata ƙarasa maganar ba,a fusace haroon ya sanya tafin hannunshi ya ɗauke ta da mari,Sae dai kafin ya janye hannunshi daga saman kuncin ta,yaji shima an dauke shi da wani irin zazzaffan mari,Kuma kafin yayi wani yunƙuri yaji tafukan hannaye again har biyu asaman fuskarshi,Tashin hankalin 

Wasu irin baƙaƙen taurari ya gani acikin idanuwanshi,tsabar raɗaɗin da ya ji ne yasa shi sakin ihu,yana tangal tangal zai fadi,gaba daya duk yabi ya susuce,har fitsari sae da ya saki a wondonshi,saboda tsabar raɗaɗin daya ji,

    A galabaice yace"Na shiga uku!Meke faruwa dani ne!dan Allah ataimakamin duhu cikin idanuwana,"

   Shessheƙar kuka kawai sehrish keyi hannunta dafe da kuncinta,mutum biyu ne suka mari haroon,shigowarsu kenan Suka ganshi ya sharara mata mari,aikuwa da gudu Abusufyan ya ƙaraso ya kwashe shi da mari,Marshal Omar kuwa,Hannu biyu yasa ya ɗauke shi da Mari ta baya,hakan yasa yaji duuuuum acikin kunnanshi,babu wani sauti kwata kwata,kamar ya kurmance,

  Ruko hannunta Marshal yayi"kiyi haƙuri kinji,dan Allah ki daina kuka," side hug yayi mata yana dan bubbuga bayanta,Abusufyan kuwa sam ya kasa magana sai faman huci yakeyi,ranshi yayi mugun 6aci,

  "Banaso Sgr ya shigo yaji wannan aika aikar da haroon yayi,don wlh sai ya ɗanɗana kuɗarshi,Sehrish ki wuce bedroom ɗinku,ki barni dashi,zaici ubanshi ne,"

.. Cikin shessheƙar kuka tace"Part din babban yaya zanje in gyara mashi"

   Tayi maganar tare da wuce wa upstairs da sauri tana ci gaba da yin kukan,

 "Uncle,dan Allah ka shiga daga ciki,Ni zanji dashi,"

  Jinjina kai kawai Abusufyan yayi tare da juyawa yabar falon,

   Kwakkwaran damƙa Marshal yayi ma wuyan rigar haroon dake a zube ƙasa yana birgima,ɗaɗɗago dashi yayi ya jashi,har izuwa ɗakin da suke hukunta mai laifi,lallai haroon ya ta6o ma kanshi,

Lokacin da sehrish ta faɗa cikin palourn shi,Saman sofa ta zauna tana cigaba da yin kukan,taji zafin marin da haroon yayi mata sosai,abun ya tsaya mata aranta,tsanarshi ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarta,ta jima a zaune batare da ta motsa ba,har aka kira sallar isha'e,sae bayan da aka kammala sallar sannan ta miƙe ta wuce cikin bedroom ɗinshi,toilet ta fara shiga ta gyara mashi,kafin ta dawo bedroom ɗin nashi tana gyarawa,har lokacin bata daina yin shessheƙar kukan ba,

Bayan ta kammala gyara mashi part ɗin nasa,kasa tafiya tayi saboda a ƙagare take daya dawo,saboda tayi mashi maganar zuwansu kano,Addu'arta Allah yasa yabarta taje,

  Safa da marwa ta shiga yi acikin bedroom ɗin nashi,gajiya tafara yi da yin yawon,wuri ta samu daga gefen gadon ta zauna,gyangyaɗi ta fara yi a ƙarshe bacci ya kwasheta,bata ƙara sanin meke wakana ba,

*SGR*

Around 12 ya dawo cikin gidan,Army trouser ne ajikinshi,sae farar shirt mai dogon hannu,Lokacin daya shiga bedroom ɗinshi bai ankara da ita ba,rage kayan jikinshi yayi kafin ya shiga toilet,bayan ya kammala yin wankan,Ya fito sanye da bathrobe ajikinshi,gaban mirror ya tsaya sai da ya kammala shafe jikinshi da tsadaddun mayukan jikinshi,ya gyara sumar kanshi sosai,kafin ya koma wurin closet ɗinshi,after some minutes ya dawo cikin ɗakin jikinshi sanye da Sleeping dress Red colour,yayi wani fresh dashi,tunanin kiranta yayi a wayarshi don ta kawo mashi dinner ɗinshi before ya kwanta,Yana ƙoƙarin juyawa don yaje ya ɗauki wayarshi daya ajiye saman drawer ɗinshi,wayar ta shiga ruri,da sauri ya ƙarasa tare da ɗaukar wayar,duba screen ɗin wayar yayi sunan*Uncle donald*ne ya bayyana,

Picking call ɗin yayi a natse ya kara wayar a kunnanshi,Cikin harshen Spanish suka soma yin maganar,wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana cigaba yin wayar,fuskarshi asake da alama ba ƙaramin farin ciki yake da kiran ba,

    Sun jima suna magana da uncle ɗin nashi,kafin sukayi sallama,mayar da wayar yayi saman side drawer ɗin ya ajiyeta,sauke ajiyar zuciya yayi tare da kwantar da bayanshi asaman laps ɗin sehrish batare da saninshi ba,lumshe idanuwanshi yayi a hankali ya ɗan waresu,ƙoƙarin juyawa yayi karaf eyes ɗinshi suka sauka akan hannunta,Har sai da gabanshi ya ɗan faɗi rass saboda baiyi tsammanin ganin  mutum a cikin bedroom ɗinshi ba,kuma farat ɗaya bai gane cewa ita bace,A sukwane ya miƙe zaune yana kallonta,cike da mamaki,Hankalinta kwance sae sharar baccinta takeyi,Abun ya ɗaure mashi kai har saman gadonshi,

  Clapping hands ɗinshi yayi,A firgice sehrish ta farka,Sakamakon sautin da taji na tafin da sgr yayi mata,A Ruɗe ta miƙe daga zaune,sumar kanta duk ta yarfo ta saman fuskar ta rufe mata idanuwanta,hakan yasa bata iya tantance wanene ba,Amma ranta na bata cewar mamallakin ɗakinne ya dawo,Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoro ya hana ta janye gashin kanta daya rufe fuskarta don taga wanene,

  Shi kuwa boss man ɗin ya zuba ma sarautar Allah ido,ganin ta kaza yin motsi yasa shi yin magana

   "Bacci asaman gadona"?wani irin wahallan yawu ta haɗiya,

   Muryarta na kerma tace"Am Sorry yaya rafayet,wlh bansan bacci ya ɗauko ni ba,Asaman gadonka,Na tsaya ne saboda inason yin magana dakai,"

   Matsawa yayi kusa da ita,ta maƙure ajikin head board ɗin gadon,

   A hankali ya sanya hannu tare da ruƙo doguwar sumar kanta,Ya yarfar da ita gefe guda,ta sauka asaman kafaɗarta,runtse idanuwanta tayi da sauri saboda bazata iya jurar kallon cikin nashi idanuwan ba,Ƙwayar idonshi ba ƙaramin rikitar da ita takeyi ba,Hada ƙarin ƙwayar idon yasa take jin tsoranshi,

     "Neman me kike yi mun"?yayi tambayar a yayin da yake saukar da idanuwanshi saman lips ɗinta,

  "Dama,na tura maka saƙo ta whatsapp ɗinka,bansani ba ko ka gani,"tayi maganar tare da buɗe idanuwanta,suka sauka kan fuskarshi da sauri ta kawar dasu izuwa saman yatsun hannunta data aza asaman laps ɗinta,

   "I saw it already,naji complain ɗinki,Bayan wannan tashinki da nake yi in midnight,baya takura maki"?

   "A'a,Nima ina samu nayi sallah,"

  Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Okey,je ki kawomin dinner ɗina,'

  Amsa mashi tayi da toh,kafin ta sauko daga saman gadon,tayi mamakin yadda yake yi mata magana cikin sanyin Murya babu wannan faɗan,tayi tunanin cewa,Zai ɗauke ta da mari ne,amma sai taga akasin hakan,

  Har ta kusa fita daga bedroom ɗin nashi ta ɗan dakata da yin tafiyar,ta juya tare da kallonshi a lokacin harya kwanta,

   "Yaya rafayet"ta ambaci sunanshi,

Har cikin kunnanshi,tsayar da idanuwanshi yayi akanta,Yana jiran jin me zatace,

     "dama gobe daddy zai tafi kano,kuma yana so ya tafi tare dani,"

  Shiru ya ɗanyi na wani lokacin kafin yace"dole sai dake za'a je kano ɗin ne? ba wani wanda zai iya replacing ɗinki"?

tunda taji haka,jikinta yayi sanyi,

   Muryarta tamkar zata yi kuka tace"Akwai,"

  Bai ƙara tanka mata ba,kama hanya tayi ta fuce,sai da ta sauko downstairs sannan ta fashe da wani sabon kukan,Ta kwalfa rai akan son zuwa Kano,

*tawaga biyu zasu yi tafiya gobe in Allah yakai mu,Tawaga ta farko zasu tafi neman wani da suka rasa a rayuwarsu,Tawaga ta biyu kuma zasu tafi wurin boka neman sa'a,*😱😳


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post