Daudar Gora book 2 page 80

Daudar Gora book 2 page 80

Daudar Gora book 2 page 80

DAUDAR GORA 

Book2 

80

……..• KOTU * Yau din ma kotun ta cika sosai,harma wanda basu halarta a jiya ba yau kam sunzo, Sai dai babu Malikat Bushirat. Dan tana can wani irin zazzabi mai masifar zafi da ciwon kai sun lullubeta har sai da Jasrah ta sake kiran likita ya dubata. Ta gama shirya ana gama zaman kotun nan gida zataje, dan ita kam har yanzu a cikin rudani take. Zataje ta sanar da babban yayansu da a yanzu shine kamar uba a wajensu komai tunda ita taki fada mata. Maybe su sai suzo su binciki wane irin TAKUN SAKA ne tsakaninta da surukar tata da har irin wadan nan maganganu ke shiga tsakaninsu. Yanke wannan hukuncin ya sata nufo kotun kamar yanda kowa ya hallara. Iffah tare da su Daneen Ammarah da su Ummu yau ta shigo. Dan suna kammala breakfast sashen Malikat Bushirat taje ta gaishesu kasancewar lyyani da Ummu a can suka kwana. Barrister Abdallah Aas da Abu Zainab kuwa tun a jiyan suka wuce gidajensu da iyalansu. Kaka ma kin kwana yay, sai suka wuce gida shi da Babiy da Hanash akan yau sa dawo. Ya kumayi hakane dan yana so suje su tattauna inda za'a nemawa Daneen Ammarah (Mammy) wajen zama itama. Saboda Tajwar Eshaan ya sanar musu ana yanke hukuncin nan zuwa jibi insha ALLAHU Mammyn (Daneen Ammarah) zata tare gidanta.


  Shine karshen shigowa. A take kotun ta sake nustuwa kayin kowa a kasa har sai da ya kai zaune.Kamar ko yaushe Sayeed Hanifud-Din ya fito hannunsa rike da takardu. Bayan yay gaisuwar girmamawa da Shahan-shan aka fara gabatar da Shariar.


   "Bayan jiya kotu ta gama sauraren bayani da ga bakin Arshaan wata shari'ar mai alaka da juna ta sake shigowa a cikin zaman. Inda muka saurari babban al'ararin da ya rikita kowa har sai da aka yanke wannan zama da alkawarin yau za'a kawo karshen komai. To Alhamdullah domin tabbatar da abinda muka ji a bakin Arshaan. Da wanda muka ji a bakin dattijon nan gamu yau rike da hujjoji. Hujja ta farko zamu saurari recording din da aka shirya saurara a tun farkon shari'ar ta jiya hakan bai faru ba. To a yanzu zamu ji domin sake tabbatarwa. Sannan zamu gabatar da hadiman da sukai aikin kisan gilla ga Sayeed Khairul-Bashar bisa sawar su Jasim, da kuma bokansu mai suna Barbushi dorin jin karin bayani da ga garesu. Hakama bayanan wanna dattijo duk da a jiya Daneen Ammarah ta tabbatar mana da abinda mukaji itama wanna kotu mai adalci ta saka anvi gwaje-gwaje da zasu sake tabbatar mana da komai.,

Shugaban jami'ai bismillah"


  Bayan shugaban jami' ai yay gaisuwa ga Shahan- shan shima ya cika umarnin kotu na saka recording din da aka nada a zaman su Miran Jasim cikin kurkuku batare da sun sani ba. Kotu tai tsit kowa na sauraren kasancewar an saka speaker mai karfi a kowacce kusurwa kowa radam yake ji. Rikicin Miran Jasim da Miran Arshaan tun da ga ranar farkon kasancewar tare a cikin kurkuku daki-daki suna fallashe kansu da zagin juna da tsinema juna har zuwa jiya da safe. Tiryan-tiryan sai ga abinda Arshaan ya fada na fitowa harma da wanda bai fada ba. Jikin kowa da ke kotun duk sai ya kara sanyi. Yayinda aketa la'antarsu da ALLAH wadi da mummunar hallayar tasu duk da fa suma yan zaman kotun akwai masu wasu boyayyun al'amuran a cikinsu suma. Sai dai tunda tasu bata fitoba mai sauki ce. An fito da boka Barbushi shima da tunda aka kawosa masarautar aka rabashi da duk kayan tsafinsa aka aske masa kai da basa kaya bayan an sashi wanka. Gaba daya sai kamanin nasa suka canja kamar bashi ba. Sai faman sinne kai yake kuwa da satar kallon su Miran Jasim kamar yanda suma suke masa kallon mamaki. Shima yay gaisuwa ga Shahan-shan sannan Sayeed Hanifud-Din ya fara jefa masa tambayoyi.


"Kane mushirikin da ke basu tsubbun da zasu cutar

da mutane ko?".


"Ina neman afuwa kuskurene ranka ya dade".


"Tun yaushe kake tare da su?".


"Mun kai shekara goma sha takwas".


"Kace ka dade kana basu lakanin kashe mutane da

musu illa?"


 Shiru ya kasa cewa komai, 


Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da fadin, "Kotu na bukatar jin duk tsiyatakun daka jagorancesu aikatawa".


  Cikin rawar murya data baki ya shiga zayyane komai. Da ga karshe ya dora da fadin, "Naki fada musu gaskiya ne tun farko saboda karsu daina bani kudin da suke bani. Amma ni nasan anfi karfinsu a duk inda suke kai hari. Bakuma zasu samu cikar burinsu ba har abada".


  Ba wanda suke a kotun ba hatta Miran Jasim da Miran Arshaan wan irin kallo suke masa mai ban mamaki, sai dai ko sau daya yaki yarda ya dubesu shikam, Bayan shi an fiddo hadiman da suka kashe Sayeed Khairul-Bashar. Inda suka zayyane komai har yanda Miran Jasim ya sakasu aikin, da yanda suka sacesa lokacin da yake fitowa da ga sashensa zaije sallar asuba. Sun azabtar da shi matuka, dan azabtarwarce ma ta kaisa ga rasa rayuwarsa. Sosai wasu ke kuka, iyalansa kam su kadai suka san irin zafin da sukeji a zukatansu. Babu abu mafi ciwo sai gain amintaccen hadiminsa a cikin wadanda suka halakashi.


 Sayeed Hanifud-Din ya ja numfashi da fesarwa yana mai sake fuskantar kotu. "To Alhamdullah wanna kenan. Sai kuma gwajin kwayoyin halittar da wanna kotu ta bada akai mata tsakanin Zawjata-almilk da mahaifanta guda uku, inda gwajin ya tabbatar da Zayyan ibn Abbas da Ammarah bint Abdul-majeed Ally Qutb matsayin mahaifanta na gaskiya. Wadan nan sune gwaje-gwajen, gashi za'a jaranto.", tiryan-tiryan ya karanto komai, a take matasan nan da Iffah yanzu ta jawo jikinta suka cika kotun da kabbara. Da kyar aka tsawatar suka lafa.Miran Jasim kam sai kawai yaji ya fashe da kuka tsabar yanda zuciyarsa tai wani irin kunci da takurewa waje daya a kirjinsa,


 Bayan shirun da kotun ta dauka kowa ya zuba ido da baza kunne na jiran yanke hukunci ga Shahan- shan da kuma makarrabansa da ke zaune yau a kusa da shi domin yanke hukuncin. Yaja tsahon mintuna hudu shiru kafin yaja numfashi mai sanyi, cike da nutsuwar nan tasa da kamewa ya motsa tausasan lips dinsa idanunsa kyam akan Iffah ta cikin bakin gilashin daya sakaya su. Tana kwance ne a jikin kafadar Malikat Haseenat idanunta a lumshe da alamar har yanzu batajin dadin. Janyewa yay a hankali ya maida ga takardun gabansa ya sake motsa lips dinsa.


   "A bisa hujjoji da kwararan shaidu da ji da ga bakin masu laifin wannan kotu mai adalci tayi dubi da nauyin laifukansu da hukunce-hukuncensu masu nauyi daya dace ta musu. Domin saukaka wahalarwa ga kotun ta yankema Miran Jasim da Miran Arshaan hukunci ta hanyar rataya a tsakkiyar al'ummar wanna kasa a dunkule bisa laifukansu.....


   A take kotun ta dauki kabbara cikin motsuwar zukata da tsananin rudani musamman ga Miran Jasim da Miran Arshaan da sukai wata irin zabura. Da kyar aka samu aka lafa ya cigaba da fadin. "Za'a yanke musu hukuncinne a ranar bikin al'ada dake hada kowa da kowa da za'a iya bukata da fatan su shaida Kafin hakan zasu cigaba da zama a cikin kurkuku, zakuma su bayyana dukkan laifukansu a gaban yan jarida. Bama bukatar wata kungiya a duniya wajen mana katsalandan akan hakan, zakuma su biya diyyar ran yarinyar Sayeed Hifzur-rahaman da ta Sayeed Khairul-Bashar ga iyalansa. Hakama zasu biya kudade masu nauyi ga ahalin Fhareedah bint Zayyan da suka wahalar bisa son zuciya. Bokansu an bashi damar zaman kurkuku na daurin rai da rai idan yana da rabon shiriya ALLAH ya shiryar da shi. Hakama hadiman da sukai musu ayyukansu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai suma. Wannan kotu ta sallami wanda ya samar musu da dafin macizai abisa gargadin kiyayewa. Idan ya sake sakaci makamancin wanda yay zai yabama aya zakinta. Haifah za'ai mata hukuncin bulalar aikata Zina tare da zaman kurkuku na shekara goma bisa yunkurinta da hadin bakin son yin kisa. ALLAH yasa mufi karfin zukatanmu, ya yafe mana kurakuranmu mu da zuri'armu da al'ummar mu baki daya". Da ga haka ya mike. Babu wanda ya iya motsawa har sai da ya fice. Kotun tai wani irin harmutsewa kowa na ALLAH wadai da halayyar su Miran Jasim da kuna da tashin hankalin karshen su Miran Jasim da kuna da tashin hankalin karshen su yama hanasu iya duban kowa. Arshaan sarkin rudiya ma kuka yakeyi, dan yayi nadamar biyema Jasim a rayuwarsa duk da shima da nasa kudirin. Amma bai taba samun kwarin gwiwar aikatawa ba sai da suka dunkule. Haka aka wuce da su da kyar da ga cikin kotun aka maidasu kurkukun...




Gaba daya Iffah bawani son hayaniyar take ba yau, dan batajin dadi gaba daya saboda gumurzu sosai tasha da uwa a cikin mafarkinta na daren jiya. Ga yanayin da take ciki na laulayi duk da bata jin wani ciwo kafin jiya da rana. Ta riga su Malikat Haseenat baro kotun ma ita, kai tsaye kuma sashenta ta nufa dan kwanciya kawai take bukata da kadaici, Hannu kawai ta iya dagama hadimanta, kafin a takaice ta shige ta bada umarnin a kawo mata dafaffen madara. Cikin sauri kuwa Amintacciyar hadimarta ta amsa. Ita kuma ta shige cikin takun nan nata sai dai yau tattare yake da kasala.


Da sallama ta shigo dakin da ya sha gyara sai tashin kamshi masu dadi yake. Ta maida kofar ta rufe. Juyowar da zatai gaba dayanta idanunta suka sauka akan Uwa da ke zaune zama irin na izza da kasaita cikin kujerar ta ta gado ko nace ta tsafi tana wani irin cika da batsewa katon hancin nan nata ya sake budewa….✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post