Daudar Gora book 2 page 81

Daudar Gora book 2 page 81

Daudar Gora book 2 page 81

DAUDAR GORA 

Book2 

81


...._..Wani irin wawan tsaki Iffah taja mai masifar karfi ta dauke kanta. Babu alamar ko dar tattare da ita ta cigaba da shigowa cikin dakin, kai tsaye gaban mirror din ta ta nufa, dai-dai tana cire bangles din hannunta batare data sake duban inda Uwa ke zaune a harzuke ba ta furta, "A haduwa daya kawai harkin tsorata kin bayyana kanki karamar agwagwa mai wanka da ruwan dagwalon gulbin wasu. Ai nazata karfin ikon naki zaisa ki cigaba da kawomin harin a cikin barci?".


"Idan tunaninki ke kin iya to da sauranki". Uwa ta fada cikin tsananin kaushin murya mai fita da dacin da ke har a kasan ranta. Wata yar dariyar rainin hankali Iffah tai tare da juyowa, ta dan jingina da mirror hannayenta harde a kirjinta. gaba da idanunta sun canja kamanni mai firgitarwa. Sama da kasa take kallon uwa da itama nata idanun ke jazur kamar garwashin wuta."Tsohuwa iyawa ba yawan shekaru bane ko kwarewa a mishirikanci. Karkiyi wasa da wannan dagwalon tabon dan shi zameki zaiyi ya kaiki kasa wanwar. Da ace iyawar taki ta cika iyawa, da kin iya a gabar da Iffah bata san komai ba sai UBANGIJIN da ya halliceta. Indai har wannan jinjirar yar kwanaki uku da haihuwa zata bacema ganinki da jinki, basirarki ta toshe a gabar da kike gab da isa ga nasararki ki sake dawo da ita a inda karfin ikonta ke a saman naki to ki sake tabbatar da k ba komai bace face batacciya mai jahilin tunani. Ni wlhy da ga lokacin dana san kana gaba daya sai kika kara komawa kasa wanwar a karkashin kasan tsinin takalmana. Ashema ke karamar kwaruwa ce tunda har sai kin jinginu jikin raunin wasu a fagen cimma burinki. Ashe ke ba komai bace face makaskanciya da dan yanzu UBANGIJI yace mutu dole ki amsa kira a shafe babinki kamar yanda aka shafe na uwar data haifeki harta nuna miki wanna hanyar shiga wutar. To wai ni banda ke din jahilar dabba ce a cikin kaskantattun dabbobi a wannan shekarun naki kike tunanin mulkar kasa irin ruman wai harma da duniya. Oh oh lallai kin cika babbar aladiya wih...


"K! Karamar halittar da muka samar da samarwarmu!!…


"K! Babbar dakikiyar da ALLAH ya halitta domin zama makamashin wutar jahannama in har bata tuba ba!!!!'". Iffah ta katseta a tsananin tsawacen da har sai da ta zabura acikin kujerar tsafin nata. Cikin rufewar ido da nunata da dan yatsa ta cigaba da fadin "La'ananniya gatalalliya butulu. K! Har wacece da kika isa samar da koda halittar kwarkwata tsinanniya mai kwana da tashi da tsinuwar UBANGIJI tattare da ita.Why wihy ina miki gargadi na karshe, da ga yau idan

kafarki ko wanna kujerar tsafin naki ta sake rabar inda nake sai na sabauta miki rayuwa. Sai na miki kisan gilla irin wanda ya kamata ama mushirikai batattu irinki a doron kasa". Ta wani irin rarumi wani dunkulallen abun fulawa na tangaran irin mai tsananin kaurin nan bakinta da bismillah ta wulwula sai gashi ya tarwatse a saman fuskar Uwa. Yanda kasan ta jefa wuka mai kaifin masifa ko mayen karfe sai ga hancin uwa a kasa ya gundulo gaba daya namansa. Dama gashi katon gaske mara fasali. Wata irin gigitacciyar kara uwa ta fasa jikinta ya hau kakkarwa ta dafe fuskar da tai faca-faca da jini da duka hannayenta biyu. Wani Iffah ta sake rarumowa, tana ambatar bismillah kafin ta wulwula uwa ta bace kamar walkiya, sai hancinta da digo-digon jininta da ya faffalatsa kasan harma da bango. Bata fasa wulwulawa ta jefa ba sai ko a keyar uwa da ke kokarin ficewa ta jikin bango ta salon tsafinta.


"Karamar yanyan ki tsaya mana, ki tsaya kiga yanda ake jifan shedan a zahirin rayuwa",. Ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ke kumbura da cika da batsewa ba da. Sai da tayi mai isarta harda fadawa gado. Sai kuma ta dan dafe kanta dake mata ciwo har yanzu. Dai-dai nan akai knocking kofar, damar shigowa ta bada dan tasan hadimarta ce. Ita dince kuwa dauke da madaran da ta saka a dafa mata. Cikin girmamawa ta ajiye a inda ta nuna mata. Kafin ta bata umarnin gyara wajen da jinin uwa ya faffalatsa, sai dai abun mamaki yanzu babu bantalen hancin uwar da alama dai ifiritan aljanunta sunzo sun dauke..





**....






Kamar wadda aka wurwuro kwallo da ga nesa haka ta fado da ga ita har kujerar tsafin nata a tsakkiyar wasu irin bakaken bukkokin bamboo da ke a jajejin. Firgitaccen ihunta da gumzar azabar da take yasa dajin amsawa, kamar busa kaho wasu irin mutane marasa kyawun gani da mummunar suffa irrin tata suka fara tururuwar fitowa. Duk dinsu babu mai kaya a cikinsu, tsirara suke yara da manya maza da mata, sai dan ganyen da suke rufe iya al'aurarsu kawai. Matan ko da ga samansu ma duk a bude yake tun daga yammata har tsoffi. Cikin kankanin lokaci duk suka zagayeta, yayinda wasu tsoffi da bazasu kaita shekaru ba suka rufu a kanta su kusan biyar maza biyu mata uku. Dagata sukai gaba dayanta ita da kujerar, daya da ga ciki kuma yay saurin yafa mata jan kyalle a saman fuskar datai kaca-kaca da jini. Daya da ga cikin dakunan Bamboo din suka shiga da ita, shikam da yar sabuntarsa kuma babba ne, sai dai cike yake da da was irin tarkacen bakaken gumaka da akaima ado da ja. Kujerar suka ajiye tare da fara zagayata suna was irin surutai da dukawa da tashi kamar wanda zasuyi ruku'u. Tuni nacan waje ma sun tattaru a kofar dakin yara da manya a layi, idan wadan can suka fadi surkullen sai su kuma su amsa musu da ga waje suma suna dukawa da mikewa. Gaba daya jajejin babu wani sauti da kakeji sai wanna surkullen nasu. Haka suka dingayi tsahon lokaci kafin a ciki su fara dibo was ruwa dake a manya-manyan randunan kasa na cikin akin suna zubama Uwa da cigaba da zagayeta cikin surkullen. A haka suka wanke mata jinin fuskarta tsaf, hancin dai ya fita babu kyawun gani sai fuskar ta kara munancewa fiye da da can. Amma jinin ya tsaya. Magunguna suka sassaka mata a ciwukan dan duk ta yayyanke dan ba hancin kawai ba. Bayan sun nutsa itama ta daina mummunan nishin da takeyi sai dai har lokacin a wajige take. Cikin mummunar muryar nan tata ta shiga kwala kiran wasu irin sunaye, jif!! jif!! jif!!! Kakejin abubuwa na fadowa cikin dakin, babu alamar toro a tattare da su, sai dai duk suna gabanta a tsaye kawunansu a kasa alamar girmamawa a gareta, Da wani irin zafin rai ta shiga nuni da bakaken hallitun dake ta fadowa. Ta nuna na farko cikin karaji da fadin, "Keje jajjal, da ga yau na baka umarnin, karka sake barin ta-kurya barci lafiya, a zagaye jikinta da kuraje masu warin da babu wanda zai iya rabarta koda danta ne, a dinga firgitata a ido biyu da cikin barcinta".


"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".


Ya fada yana mai zabura a guje kamar iska ya bace bat. Na kusa da shi ta nuna, shima cikin bada umarnin, "Zurnini kaje ga dan da muka samar mata(Shahan-shan 😱), da ga yau karya sake tunani irin na mutane, a maidashi majanuni, yayta dariya da soshe-soshe. Ya tsani shegiyar matarnan tasa fiye da komai a duniya, nanda kwanaki kadan jininsa halattacene garemu".


"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".


Shima ya fada yana bacewa. Ta sake nuna na kusa da shi shima "Rudde! Kaje ga tsohuwar can (Malikat Haseenat 52 ), ka taya Banou aikinta, da ga nan zuwa kwana uku jininta halattacce ne agaremu".


"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".


"Zambo kaje ga karsugumar shegiyar yarinyar can,ka zukemin gudan jinin da ke jikinta, ka ringa

firgitamin ita da wajiga rayuwarta, har saita san wacece Uwa kafin masana nayi gareta".


"Fadi naki, Cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".


"Gamberu! Ina bukatar jinin shegun iyayen da suka haifi yarinyar nan da umarnin mu (Wa'iyazubillah)".


"Fad naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".


Wani irin mahaukaciyar dariya ta shiga babbagawa da fadin, "Sai na ga bayansu, sai na haukata rayuwarsu, saina gigitasu. Yanda suka hanamu zama cikin alkaryar kasarmu suma basu isa su rayuwuba. Sai na mulki ruman, sai na mulki duniya, zan zama mafi girma a karfin iko. Matsiyacin tsoho (Kaka) gani nan gareka, nice da kaina zan tsireka a tsakkiyar kasar ruman. Hahahahaha!


  Gaba daya na wajen suma suka dauki dariya. Dandanan dajin ya dauki amsa kuwwa. Tako ina dariyarsu amsawa take a cikin dajin..





*****







"Akia, an taba ciwo babu cin abinci, ki daure ko kadan kisha madarar nan sai kisha magani". Jasrah da dawowarta kenan da ga gidansu tun bayan tashi a kotu data tafi sai yanzu take dawowa, ta sanar ma babban yayansu komai yay mata alkawarin zuwa kuma duk da dama Shahan-shan ya tura masa sako, dan yana daya daga cikin mashawartansa ma akan yankema su Miran Jasim hukunci, kasancewarsa babban malami masani. Kai tsaye dakin Malikat Bushirat ta nufi, shine ta iske ta farka. Ganin jikin nata duk babu karfi tai zaman fara bata madara mai dumi akan tasha kafin ta watsa ruwa sai tai sallolin azhar da la'asar da suka wuceta. Amma Malikat Bushirat din taki amsa sam, gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Lallashinta Jasrah ta cigaba da yi har ta samu ta dan sha madarar kadan. Magungunan ma da kyar tasha. Mikewa tai zuwa bayi ta hada mata ruwan wanka sannan tazo ta kamata ta kaita. Fitowa tai ta barta da rokon tayi wanka koda ruwanne kawai ta zubama jikinta kozai danyi karfi. 



    Kamar jira ake Jasrah ta fita aka fara kyalkyala dariya. A firgice ta fara waige-waige sai dai bataga komai ba. Kuka aka fashe dashi kuma. Nama duk ta kidime tuni ta mike zumbur kamar ba itace aka kawo bayin da kyar ba. Sake kwashewa akai da dariya. Sosai jikinta ke wani irin rawar mazari kamar zata amayo zuciyarta ta baki. Tako ina waigawa take amma babu komai sai ita kadai a bayin. Da mugun sassarfa ta nufi kofa da nufin ficewa. Amma ina kofar ta rufe gam-gam babu alamar zata bude, Tanata kiciniyar budewa akai mata wani irin harrrrr!!! Daga jikin kofar sal ga mummunar suffa ta bayyana, baya taja a razane ta kwalla wata irin kara mai tsananin firgitarwa data saka Jasrah dake gyara mata gadon kafin ta fito zabura itama tayo bathroom din a razane….✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post