Daudar Gora book 2 page 93

Daudar Gora book 2 page 93

Daudar Gora book 2 page 93

DAUDAR GORA 

Book 2 

Page 93

……..Cikin masarautar ma a hargitse suka sameta,dan tuni an is da Malikat Bushirat da aka fara tahowa da ita. Ga Iffah da jini ya balle mawa ta yanke jiki ta fadi itama aka shiga da ita ciki har yanzu likitocin da ke kanta basu fito ba. Tashin hankalin hakan yasa ko wanda suka sarewa kawuna ita da Daneen Ammarah bama a janye ba. Ba'a bari kowa ya ga halin da Tajwar Eshaan ke ciki ba aka shige da shi sashensa. Hakama sauran mayakan da sukaji munanan raunika aketa nufar cikin clinic da su duk da kukan da iyayensu keyi ba'a bar kowa matsowa kusa da su ba, wanda sukaji kananan raunuka ne dai aka zube a harabar masarautar suma ana basu taimakon gaggawa na ruwa da magani. Ga magrib ta gabato. Amma burin kowa dai yaji yaya Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb yake. Yanda suka tada hankalinsu yasa dole sai da Sayeed Fayzul-haq ya fito yay magana da yan jarida akan kowa ya kwantar da hankalinsa Shahan-shan na nan raye, sai dai yana bukatar addu'oin Su...

WASHE GARI

Alhamdullah an wayi gari da dadin rai, dan su Babiy duk sun farfado. Hakama Tajwar Eshaan kaka ya saka masa magani an kuma masa na asibiti da dorin karayar sai dai ace Alhamdullah. Itama dai Iffah an samu nasarar tsayar da jinin kuma cikin da aketama damuwar zai iya lalacewar dai yana nan. Malikat Bushirat ce dai idanun nan da kai kawai ke aiki, sai dai duk abinda za' a fada tana ji. ALLAH sarki Jasrah bata gazaba a yi mata hidima. Jama'"ar gari dama na masarautar da basu san komai akan al'amarin nata ba sunata tausayinta da gain Uwa ta tsafeta ne saboda cikar burinta. Was har addu'a suke mata na samun lafiya. Gawarawakin dangin uwa an tattaresu anyi rami acan daji an biznesu, wanda kuma suka rage tare da uwa an zubasu a kurkuku har sai ALLAH ya bama Tajwar Eshaan lafiya.

   Tako ina labaran abinda ya faru a kasar ruman dinne ke yawo a duniya, wasu na caccakar Shahan- shan akan abinda akai bai dace ba suma mutanen nada yancin kansu, wasu ko na ganin hakan da akai shine dai-dai. To koma dai yaya ne yan kasar ruman sudai hakan da akai yayi musu. Dan babu wata kasa da zata so rayuwa da masu bakin kafirci irinsu uwa.Masu ganin ba'a musu dai-dai ba ma son zuciya ne kawal.

  Lokacin da Iffah ta tartado taci karo da Tajwar Eshaan jikinsa ta fada kawal ta fashe da kuka. Ya rungume kayarsa yana murmushi shima idanun nasa dai sun kada. Sai da tayi mal isarta sannan ta dago, babu zato kawai yaji ta manne lips dinsu a waje guda. Idanu ya zaro itama sai ta zaro nata tare da janyewa tana dariya. Da sauri ya rikota da hanunsa mai lafiyar ya maidota jikinsa yana murmushi.

"Wannan ai mugunta ce a lasama mutum zuma a baki a gudu". Ya fada cikin rada a kunnenta. Dariya ta shigayi a hankali tana boye kanta a cikin jikinsa, da ga haka ya canja wasan a yanda yake bukatar kasancewarsa, duk da kuwa komai da yake na karfin hali ne kawai, dan sam zuciyarsa babu dadi, shi kadai yasan halin da yake ciki akan mahaifiyarsa. Amma yanata kokarin dannewa da gayama ALLAH kukansa.

  Lokacin sallar azhar domin sake Kwantan da hankalin mutane ya fita sallar cikin karfin hali duk da

hanun nasa an masa dorin karaya ne. Ga yankan wukar nan da yay matukar shiga jikinsa sosai, saukin ma dal anyi maganin dafin. Bayan anyi salla an fito ya dan gana da manema labarai da yasa a tara masa. A nan yay ma al'ummar kasarsa godiva da fatan alkairi bisa kokarinsu da addu'oinsu. Ya kuma sake jaddada Iffah matsayin SARAUNIYARSU har yanzu dan bazai amshi mulki ba sai ya samu lafiya. Babu wanda yay jayayya da wannan al'amari. Sai ma Tajwar na jihohi da manyan kasar dake ta layin zuwa dubashi tako ina, tare da sauran mutanen da suka fita wannan gumurzu. Musamman yan kauyukan nan da Hadimai da wasu a jama'ar gari da suka taimaka musu anhadasu da manyan kyautuka, hakama itama SARAUNIYA Iffah ta bisu su dukansu da manyan kyaututtuka da ya sakasu a farin ciki, dan ita dukansu ta hada har matasanta.

    Lokacin da don Malikat Bushirat ke gain bayanin Shahan-shan akan Iffah zata cigaba da rike matsayinsa har sai ya samu lafiya, da lokacin da ake nuna Iffah'r akan karagar mulkin Shahan-shan din randa take zartar da hukuncin kyautukan da ta bama wanda sukaje yakin a matsayin Sarauniya kuka ta dingayi, kuka mai zafi da tsananin kona zuciya. Sosai takejin radadi matuka a cikin kirjinta, ji take inama kafin zuwan wanna ranar ta mutu ta huta. Bayan tasha kukanta ta godema ALLAH ta cema Jasrah a cire mata tvn daga dakin. Jasrah har ta amsa da to Malikat Haseenat ta ce kar a cire. Dan tsaf ta fahimci manufar Malikat Bushirat din. Tana ammakin taurin zuciyar matar nan, ace duk wadan nan abubuwan daka gani basu isheka izna ta saraya ba. Ko dan data haifa ta kasa neman gafararsa ma balle su. Kai ALLAH ya rabamu da irin wanna mummunar zuciyar ta kafuran farko,

    Kullum sai Tajwar Eshaan yabi ta barauniyar hanyarsa dubota. Zasuje da safe shi da Iffah da an idar da sallar asuba. Zakuma suje bayan sallar isha' i. Da ga gaisuwa da tambayarta yaya jiki bai iya kara sake cewa komai. Sai ma ita Iffah'r ce kan dan mata addu'a ta tofa mata, duk da dai kaka nata kokarin bada magani ana mata ko za'a dace. Haka zatayi ta kallon Tajwar Eshaan tana hawaye, amma shi daga kallo daya na gaisheta baya sake yarda ya kalleta har yabar dakin kansa a kasa yake.

**

Bayan kwanaki bakwai abubuwa da yawa sun dai-data, musamman masu kananun raunuka sunji sauki sosai, sai wanda suka jigata ne sosa ke cigaba da karbar magani. Baby ma dai da yake buguwace Alhamdullah jikinsa da sauki, dan haka Tajwar Eshaan yace kawai Daneen Ammarah ta tare haka nan. Duk yanda taso zamewa sai da aka shirya wani dan kwarya-kwaryar walima data kayatar. Dan anyita ne irin ta manyan mata masu aji da ilimi. Zuwa dare aka shirya mika amarya dakinta, Iffah kuwa ta dage sai taje. Sai da aka tuna mata itafa SARAUNIYA ce a yanzu, babu yanda ta iya dole ta hakura, amma tanata ima Mamyn (Daneen Ammarah) tabarar wai shikenan ita haka kowa zai tafi ya barta. Ita an kawota gidansu ita kuma za'a maidata gidansu. Itakam data san hakane kawai kowa yay zamansa gidansu. Dariya sosai Malikat Haseenat da Daneen Waheeda keyi da drama din tasu. Dan wata shakuwace ta musamman ta sake shiga tsakanin Iffah da Mamyn (Daneen Ammarah) taja yarta jikinta sosai da sake tabbatar mata da kaunar da take mata dabance a rayuwa. Haka itama Iffah'r tana kaunar mahaifiyar tata matuka duk da bata rayu da ita ba. Sannan tana kaunar Ummu dinta da Baby. Hanash Akhi kam ai shi na musamman ne gareta da Kakanta abin alfaharinta. Kullum cikin lallabasa take shi da lyyani su dawo cikin masarautar da zama ko zata dan ji saukin kewarsu da tayi. Shi dai ya nuna bazai dawo ba. Amma Tajwar Eshaan ya ce ta kawantar da hankalinta zai dawo mata dasu, Ba karamin farin ciki tayi da hakan ba.Dan shima Babiy an gyara masa gidansu sosai dan bazai iya barinsa ba saboda gidan gonarsa.

   Lokacin da za'a wuce da Daneen Ammarah sai gashi tana kuka, ta rungume Malikat Haseenat da Iffah sunata kuka. Da kyar Daneen Waheeda da Malikat Ashwaq suka rabasu aka fita da ita. Yau kuma sai dakin mijinta ban yarta.

   Tarbace ta mutuntawa suka samu da ga su Ummu, kowa halayen Ummu na birgesa, dan mace ce data amsa sunanta cikakkiyar mace jaruma abin koyi da nunawa a duniya ga kowa, Yan kawo amarya basu wani jima ba suka wuce abinsu. Lokacin da ango zai shigo Ummu da kanta tayo masa rakkiya cakin amaryarsa. Zata gudu Daneen Ammarah tace saifa ta zauna sunyi hira. Babu yanda Ummu ta iya dole ta zauna. Sai dai hirar ma dai duk akan rayuwarsu ta bayace data shude. Kuruciyar Iffah da su Arfa Daneen Ammarah har kuka tayi, ta jinjinama hakuri irin na Ummu. Ta kumayi alkawarin kyautata zamansu tamkar yan wan juna har abada. Zasu zama aminan juna bawai kishiyoyi ba. Ganin dare yaja da wayo Ummu ta tattare kwanikan da sukaci abinci ta gudu. Dama shi Hanash Akhi yana can masarauta Iffah ta rikesa wai shine amintaccenta, nan ko duk wayone dan taita gain dan uwanta ne. Dan babu wani abu da yake yi sai idan sun dan shiga fada zatai wani zama mai muhimmanci da manyan masarautar ya kasance a gefenta. Hakan sai ya saka mata zaman lafiya da Tajwar Eshaan sarkin kishi, dan tana ambata maganar Hanash Akhi dinne zai kasance amintaccenta harda kyauta sumba aka bata. Wai hakan shine dai-dai.

    Ummu na fita Babiy sauka yay kasa gaban Daneen Ammarah ya zabga tagumi ya wani zuba mata idanu. Murmushi tayi da jan mayafin jikinta ta rute fuska cike dajin kunyarsa. Ya lumahe idanu da budewa yana murmushin shima, Kafin ya mike tsaye ya yaye mayafin gaba daya ya kama kafadunta ya mikar da ita ya rungume abinsa. A tare suka dinga sauke ajiyar zuciya, sai kuma hawaye na tsananin kewa da tuna baya.

   "ALLAH na gode maka daka maimaitamin wannan rana a rayuwata. Ka gamamin komai UBANGIJINA daka bani mafi tsadar nan a cikin mata matsayin matata"

    "Ni zan godema ALLAH da samunka matsayin miji kuma uban yayana Zayyan. Tare da yar uwa jaruma Saliha irin Jumaymah. Yanda kuka sharemin hawayena, da zama silar canja labarin da ban taba tunanin zai canju daga kaddarata ba kuma ALLAH ya share naku hawayen. ALLAH ka hana shaidan shiga tsakaninmu. Nayi alkawarin in har inada rabon sake haihuwa a duniya zan malakama Jumaymah (Ummu) yayan nan har abada".

   Cikin rada-rada a kunenta ya furta, "Insha ALLAHU a yau din nan zan dasa kwam Arfa da Fariha gimbiyata." cike da jin kunyar furicin nasa ta wani kankamesa da boye kanta a jikinsa. Wani irin rungumeta tsam-tsam Baby ya sakeyi shima yana dariya, tare da bata sumbata tako ina a jikinta harya sauke akan lips dinta, Jin tsaiwar na neman gagararsu ya dauke abarsa tsamm suka shige daga ciki, dama dai ga Daneen Ammarah yar dum-dum kai kace bata wuce talatin a duniya ba. Jin an rufo kofa harda murza key nayi baya dan wanna fagen na manya-manya ne ba gain kanana irimmu ba 🥱😉😂🚴


 BAYAN WATANNI SHIDA DA FARUWAR YAKI TSAKANIN SU SHAHAN-SHAN DA SU UWA

Kai kawo yaketa famanyi a cikin bedroom din nashi bakinsa dauke da addu'a. Duk ko yanda waya ta motsa sai ya daga da tsammanin su Malikat Haseenat ne. Babu abinda yafi burin ji a wannan gabar kamar ace ALLAH ya sauki Sohaa dinsa dake nakuda tun a daren jiya lafiya. Duk yanda yake da tarin ayyuka a fada ya kasa fita. Su Sayeed Fayzul-haq ma sun hakura da fitowar tasa yau tun sanda labarin nakudar Iffah'r daya iso kunensu. Sai kowa ya koma fatan saukarta lafiya.

    Daga wayar da tai dai-dal da bugawar agogo karfe sha biyu dai-dai na raar litinin din ya wani irin sauke ajiyar zuciya da zama cikin kujerarsa a hankali. Murmushi ne mai sanyi ya subuce ma kyakykyawar fuskarsa. A hankali ya motsa lips dinsa ya ambaci "Alhmdullah"., Sai kuma hawaye suka dan ciko idanunsa. Shi Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ne yau ALLAH ya azurta da kyautar yayan har guda biyu mace da namiji daga jikin yar uwarsa kuma matarsa, farin cikinsa Fhareedah bint Zayyan. A take bakin ciki da kuncin dake tare da zuciyarsa a cikin watanni shidan nan yaji ya wani fada masa daga makoshi zuwa cikin ciki. Babban yatsarsa ya kai a idanun nasa a hankali ya dauke hawayen da sake furta. "Abbie an haifo maka jikoki har guda biyu a rana daya, lokaci daya da ga tilon danka. Insha ALLAHU za'a sake haifo maka wasu biyun kamar haka har sau hudu Abbie na. ALLAH ya gafarta maka, ALLAH ya yafe maka kurakuranka kai da Jaddi da ma duk zuri'ata data musulmi baki daya. Kai da Jaddi da Jaddah ne abin AL'FAHARINA ABBIE NA"……✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post