Daudar Gora Book 2 page 94

Daudar Gora Book 2 page 94

Daudar Gora Book 2 page 94

DAUDAR GORA 

Book 2 

 Page 94

...Cikin kankanin lokaci zancen haihuwar Iffah ya karade kasar ruman baki daya. Tuni farin cikin kowa ya bayyana, tare da addu'oi ga wadan nan jinjiraye da ga bakin al'umma. Yayinda Tajwar Eshaan daya matsa a kai masa su ke can rungume da kayansa tsam-tsam a jiki. Jinsa yake a yau din kamar wani sabon mutum, final shima dai ya zama Abbie. Ga yaran sun dakko kamanninsa sosai musamman ma mace kamar an tsaga kara an karya da shi, gara namijin yafi rinjaya da Iffah shi kuma. Da kansa ya tauna dabino ya basu tare da musu huduba.

   Duk yanda yaso ganin Sohaa din sa hakan bata yuwuba sai bayan la'asar tai barcinta ta huta sannan. Murmushi ta dingayi kanta a sinne saboda irin kallon nan na kasa-kasa da yake faman binta da shi. Duk sai taji kunya ta lullubeta. Har ya karaso gaban gadon bata yarda ta dago din ba sai da ya zauna a kusa da ita ya dago fuskar tata da kansa. Bai tsaya wata wata ba kawai ya manne lips dinsu waje guda. Sai da yayi yanda yake so da ita ya barta dan kansa sannan ya rungumeta yana jero mata dadadan kalamai masu sanyi da ratsa zuciya da bata san yayi nisa a sani ba har irin haka. Jitai kawai idanunta sun cika da kwalla. Dan ita kanta bata san adadin kaunar da takema wannan bawan ALLAH ba zuwa yanzun. Tana jinsa daban a cikin daban a duniyarta. Shi din na musamman ne a gareta fiye da yanda yake jinsa na musamman..

   Lokacin da aka kaima Malikat Bushirat da har yanzu ake nan yanda ake babu abinda ke motsi sai kai da ido Jasrah baiwar ALLAH nata wahala da ita kuka sosai ta fashe da shi. Suko yara karar sun san inda aka kawosu suka wani dage da tsanyara kuka tsiyau- tsiyau kamar yayan magena da yau mukasha bikin sunansu (Na manta ban fada muku ba magena ta haihu yaya hudu kowa sai a kawo kayan barka haihuwar fari ce habu daga kafa😂🚴🥱) kuka sasa suka dingayi har abin ya bama kowa mamaki, ana fita da su sukai shiru kuma kamar basu ba. Koda aka maidasu anan bama Malikat Haseenat da Iffah labari murmushi kawar iffah tar batace komal ba. Garama Malikat Haseenat tsohuwar kwarai ta tofa kadan. 

   A can ko jikin Malikat Bushrat rikicewa yay sosal. Dan har sai da takai an kira Shahan-shan da Malikat Haseenat. Al'amarin kara yau dai bana wasa bane Dan doctors da suka rufu a kanta ma dai sunyi iya kokarinsu amma bata bar jijjigar da ta dingayi ba, daga baya ma sai ga aman jini. Hankalin kowa ya tashi musamman Tajwar Eshaan, dan da kansa ya hau gadon ya rungumeta jikinsa ta dinga bulesa da aman jinin nan. Addu'a ya dinga tofa mata, ganin fa tafiyar mai tsaho ce Malikat Haseenat ta fara maimaita kalmar shahada ko za'a dace Malikat Bushirat din ta karba. Hakan yasa suma sauran jama"ar dake a dakin suka dinga maimaitawa, Jasrah dai kuka take kamar ranta zai fita. Sai dai kuma ita rayuwa duk yanda kaso, bai zama lallai abinda kaso din ya kasance a yanda kaso shi ba. Dan kuwa da Malikat Bushirat ta koma

ga UBANGIJI batare da ta iya neman gafarar koda dan cikinta tilo data jefa kanta a halaka domin haihuwarsa ba. Tayi mutuwa mai ban toro da tashin hankali, dan kuwa maimakon kalmar shahada da suka so ji daga bakinta sunan UWA ne karshen ambation ta cikin wani irin gurnani mai karajin gaske daban tashin hankali. Wannan al'amari ya matukar kidima Shahan- shan. Dan jikinta na gama saki shima ya kife kansa akan fuskarta. Tsahon lokaci bai dago ba har sai da kowa ya fita a dakin Malikat Haseenat tazo tana lallashinsa. Sannan aka samu ya dago idanun nan nasa jazur matuka abin tausayi, sai dai baiyi kuka ba, ya jima yana kallon fuskar mahaifiyar tasa abubuwan data lissafa ta aikata a dawo masa tiryan-tiryan kamar yanzu take yinsu..

   Masarautar gaba daya ta gama rikicewa. Dan mutuwar nan kam ta daki kowa musamman da Malikat Bushirat ta zama tamkar wata tauraruwa a zamaninta a cikin gidan. Sai dai yanda mutuwarta tayi dai-dai da mutuwar kaf mutanen nan an kabilar uwa abin ya bama kowa mamaki. Dan kamar wadanda aka shayar guba kawai aka samesu duk a mace su kusan goma sha uku. Dama wasu sun dan mummutu daddaya. A yanzu dai kam Uwa kawai ta rage a raye.Itama din dai sai a hankali dan duk ta kara wani irin yamushewa na tashin hankalin faduwa kasa da tai.Wai yau itace mai zaman kurkuku a cikin masarautar ruman kuma da ranta da lafiyarta tsahon watanni shida. Ai ko'a iya haka aka tsaya ta gama kunyata a wanna duniya.

   Jasrah ce ta mata wanka tana kuka abin tausayi ita da yayarsu Badiha. Bayan an mata sutura aka fiddota Tajwar Eshaan ya jagoranci sallatarta tare da mikata gidanta na gaskiya aka barta da halinta kuma. Dan ya rage ita da UBANGIJINTA. A yanzu kam. Wannan itace ranar da ya kama kowa ya kasance yana gudu a rayuwarsa. Dan ko kaki ko kaso sai tazo. Ko kai mutumin kirki ne kona banza ne ma dai sai tazo. Ko shekara dubu bisa dubu zakayi a duniyar sai tazo. Koka shirya ko baka shirya ba sai tazo. Yau dai gashi Malikat Bushirat ta tafi tafiya ta har abada. An shafeta an shafe babinta dama iyakarta kenan akan duk wani abin kirki ko barna da zaka shuka a duniyar...

    Tajwar Eshaan bai samu hawayen dake rike da makoshinsa sun zubo ba sai da yaje ya rungumi yayansa da matarsa sannan. Kuka yayi sosai Iffah na tayasa. Sai da sukayi mai isarsu abin tausayi. Ranar ma har zazzabi yayi dole Iffah ta kwana tare da shi da yan yaransu da sukaci sunan Ajwaad da Ajwaa (Dan su bawani al'adar suna a sati daya suke ba ba irin yan 9ja bane 😝). An dai yankama yara raguna da shanu akai sadaka a washe gari tunda ranar mutuwar Malikat Bushirat ta hana. Gida kam ya cika makil, yan gaisuwa da taya murnar haihuwa ta ko ina ketowa suke. Su Mamy (Daneen Ammarah) sun zo suka kwana itama da cikinta dan watanni biyar da wasu kwanaki. Da alama dai zancen Babiy ya tabbata. Ita da Ummu idan ka gansu abin sha'awa kamar yaya da kanwa. Sai ma shirye-shiryen bikin Hanash da sukeyi dan shikam ya koma dan dakin Mamy, Iffah dai na nan yar gaban goshin Ummun ta kuma autarta. Dan duk kurarta idan ta yaya Ummu dai, itace abokiyar shawararta itace abokiyar sirrinta. Sai an gama Mammy kanji da Baby. Iyakarsu dariya idan na dariyane. Idan na fatan alkaicine kuma suyi addu'a. Iyyani da kaka kuwa ai dama tuni sun dawo cikin masarautar. Ko yaushe zaka sami lyyani tare da Malikat Haseenat ne da kanwarta Yamma. Tsaffin sun matukar hade kansu sun zama iyayen kowa. Hakama Kaka da su Sayeed Fayzul-haq sun zama aminan juna dattijan kwarai kuma a masarautar kuma iyayen kowa har shi kansa Shahan-shan din..


BAYAN WATTANI UKU DA HAIHUWAR IFFAH DA MUTUWAR MALIKAT BUSHIRAT (BIKIN AL'ADA) Kamar kowacce shekara a wanna karon ma tarin al'ummar kasar ruman da kewaye sun cika birnin Dahab da akafi sani da DAULAR RUMAN tako ina domin gudanar da bikin wasan al'ada. Kowa ka kalla a wannan karon yasan wasan ha musamman ne sanian ana gudanar da shine cikin tsafta da nutsuwa. Duk wani wasan ganganci da za'a iya rasa rayuka an kafa masa doka, hakama matakan tsaro tako ina an baza domin kare kowa da kowa. Duk wani boka ko dan bori ko malamin tsubbun an hanasu yin kowane motsi a yanzu. Dama yanzu kam dokane, in har aka kamaka to hukuncin kisa kawai ake yanke maka.

   A yau kam Iffah taga mutane da yawva da suka kawoma Shahan-shan gaisuwa. Ciki hard Sir Fawzan da tun yay aurensa. Tare na yaren Shahan-shan su Azaan da a yau kam sukaita faman sinne kai na kunyar abinda ya far tsakaninsu da ita a shekarun baya. Ita dai murmushi ma ta dingayi, shi kansa uban gayyar Shahan-shan murmushin yake yi dan kawai ba'a ganin fuskarsa ne. Su Ajwaa da Ajwaad sunsha addu'oi yau a wajen mutane. Duk da ma bawai kowa ake bamasu ba. Yaran sunyi bul-bul abinsu gwanin sha'awa. To mi yafi ransu suna samun kulawa da tattali da soyayyar iyayensu. Dan zuwa yanzu ma dai kam Iffah ta tattara inata-inata ta koma sashen Shahan-shan din gaba daya ita da yaranta. Dan yace shikam babu wani sashen matarsa da ban nasa daban. Idan ka ganta a sashenta sai in tayi bakine ko in wani abun dai tunda babu mai hurumin zuwa sashen Shahan-shan din sai ita. Hatta da amintaccensa ma zuwa yanzu iyakarsa hawa na na uku ne kawai, idan ka gansa a hawan karshen sai kwakwkwaran dalili....

   *Alkawarin ALLAH ya cika akan zartar da hukuncin su Miran Jasim da Miran Arshaan a yau.Dan kuwa wanda ya kashe dole ne a kasheshi. Hatta da malikat Bushirat Tajwar Eshaan ya gama yanke hukunci a yau din zai zartar da hukunci a kanta irin hakan sai ALLAH kuma ya dauki ranta kafin zuwan yau din. Sosai al'amarin ya girgiza kowa matuka, musamman ganin iyalan Miran Jasim kalilan ne a cikinsu suka koka saboda wahalar daya basu a rayuwa. Shi dama Arshaan ba'a ajiye kowa ba. Amma duk da haka Jasrah mai karyayyar zuciya sai da tai kuka. Al'ummar kasa sun taru wajen nema musu afuwar karkashin cigaba da zama a cikin kurkuku tsahon rayuwa. Hakan yasa duk sai jikin Tajwar Eshaan din yay sanyi, dan shima yanajin daci fiye da irin dacin da kowa ke ji kasancewar su kadai ne Uncle's nasa makusanta da mahaifinsa da suka rage a duniya sai mata. Gain dai jama'a sun dage din kuma harda iyalan Sayeed Khairul-Bashar da kansu dana Sayeed Hifzur-rahaman din suma yasa aka maidasu cikin kurkukun a bisa sassaucin daurin rai da rai. To saima dai ta ALLAH dan shi Miran Jasim ma bawani cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Hatta Miran Arshaan din kansa kawai dai a rufe rufau ne.

   Uwa kam da aka fiddo cikin sarka cike da karfin iko kowa ke shelanta a kasheta!! A kasheta!!! A kasheta!!!. Kallonsu kawai take tana kuka da dariya da kiran sunayen gumakansu duk a lokaci daya. A haka aka daureta jikin karfen. Mutane zasu fara jifanta da dutsina aka dakatar da su. Dan wannan aikin ba nasu bane na mai gayya da aikine da kansa tare da matarsa. Bayan lafawar kowa fiye da yanda ake bukata Shahan-shan ya fito hannunsa na dama rike da na Iffah, na haggun rungume da Ajwaa da aka canjama gayu ita da Ajwaad. Da shi kuma ke a hannun Iffah. Masha ALLAH aka shiga ambata, dan a zahirinsa ya tito ga mutanensa babu wani shamaki yana son su gansa ya gansu. Haka itama Iffah duk jilkinta a rufe amma fuskarta a bayyane ga al'ummar kasarta. Bayan sunyi gaisuwa ga al'ummar kasar su da fatan alkairi aka kawo kwari da baka na tsire Uwa da zasuyi. Iyyanni da Malikat Haseenat ne da ke tare da su suka amshi twins, yayinda Tajwar Eshaan ya kamo hanun Iffah a hankali cikin nasa yana kallonta kasa-kasan nan nashi ya tsayar da ita gabansa.Matsawa yay ya jingina jikinsa a nata tare da kamo duka hannayen nata biyu cikin nashi ya saka mata kwarin tare da daga hannayen nasu a tare ya daidaita su sannan ya dardai mashin da zasuyi amfani da shi cikin bakar saitin manya-manyan idanun nan na uwa da ke kwasar dariya da kuka kamar sabon kamu….✍️

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post