π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!! π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3


Health College

π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š.....!! π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆 π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3

 


π“π²π©π’π§π πŸ“²

  πŸ«— π™π™π™π˜Όπ™ π˜Ώπ˜Όπ™‰π™†'π™Š....!!πŸ«—

           π‘©π’Šπ’π’šπ’ 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 π’„π’†πŸ€™πŸ»

π‘ͺ𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣

........Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard Ι—in sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik Ι—in ya dubesa. Komai a gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik Ι—in. “Ranka ya daΙ—e Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu Ζ™amshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so Ι—in ba. Kamarka ma Ι—an manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta”.

        Ƙaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. “Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faΙ—amin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka”.

     Cikin rashin damuwa saurayin ya faΙ—a masa cikakken adireshin gidan su Lulu Ζ™amshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buΙ—e masa fuskarsa Ζ™awace da murmushi......

         *_Manseer M Atik Kumo_* kenan. Ɗa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban Ι—an siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana Ι—aya daga cikin Ζ΄an takarar shugaban Ζ™asa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin Ι—an kasuwa ne da kuΙ—i ke kaΙ—a masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaΙ—ar marasa ji na Ζ΄aΖ΄an manyar Ζ™asar sune Ι“oyayyun limamai. Manemin mata ne Ζ™wararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziΖ™i abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko'ina yake yarda ya nuna halinsa mara Ζ™yau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya Ζ™aryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai....

   Wannan kenan.

     ∆••••••∆ ★ ∆•••••∆

          Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi Ι—in yay horn kamar yanda ta umarcesa. LeΖ™owa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi Ι—in wulaΖ™anci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buΙ—e gate Ι—in. Ko gama parking mai taxi Ι—in baiyi da Ζ™yau ba ta Ι“alle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaΙ—a. Abinda zai baka mamaki ko rawa Ζ™afarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin Ζ™afarta mai shegen tsini. Duk wani ma'aikaci dake gidan da ga kallo Ι—aya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buΙ—aΙ—Ι—en abune ga duk wani ma'aikaci na gidan. Duk tsufarka duk Ζ™anΖ™antarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a Ζ™anΖ™anin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi Ζ™oΖ™arin mata a yanda ta buΖ™ata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daΙ—i kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen Ζ™anin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu'a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu'ar tasu bata amsu baπŸ˜‚ dan gata ta dawo Ι—in a bazata.

         Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki Ι—agowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa. 

    “To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faΙ—a cikin taΙ“e baki. Kamar mai jira a taΙ“ata a fusace ta ce, “Shi Ι—an uban waye a Ζ™asar nan da aka aikashi Ι—akkoni? Miyake taΖ™ama da shi?...”

         Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum Ι—aya da jarida a hannu ya miΖ™a mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.

         “Daddy babu maganar zama a fara faΙ—a min uban waye shi?, dan sai na wulaΖ™anta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faΙ—amin ba ALLAH duk wani ma'aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan...”.

      Sun san zata iya aikatawa, kaΙ—an daga aikinta kuma babu abinda Daddy Ι—in nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ζ³ar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, Ζ™yawun fuskar tasa ne inaga ke ruΙ—arsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!.....” Ta Ζ™arasa maganar a hankali cikin Ζ΄ar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, “Wai miya miki ne? Bai je ya Ι—akkokin ba?”. 

        “Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faΙ—a mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi” yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, “An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy Ι—in nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!”.

      Cikin sauri dattijon ya miΖ™e yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace “Kinga Baby yi haΖ™uri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan Ι—auki matakin dan bazan taΙ“a zama da wanda zai saΙ“a miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai Ι“ata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat Ι—in Daddynta yanzu zan nema Yousef Ι—in ma ya dakatar da shi”.

         Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna Ι—in, sauran yaran duk sai suka shiga taΙ“e baki. Hakama mamansu tsaki ta Ι—an ja a hankali tama miΖ™e tabar falon. Shiko Daddy ko'a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haΖ™uri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine Ζ΄ar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. KaΙ—an tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaΙ—arsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaΖ™in yaΖ™in duniya, sai kuma zuwa can ta Ι—an Ι—ago. “Daddy kar ka kira Uncle Yousuf Ι—in ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja”.

        “Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke”.

    “Thanks you sweet Papa..”

Ta faΙ—a tana Ι—an rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miΖ™e, yatsu biyu ta Ι—aya masa alamar bye ta nufi Ι—akinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta Ι“acema ganinsa. Bata zauna a Ζ™ayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. Ɗaki ne haΙ—aΙ—Ι—en gaske kuma Ζ™ato. Dan bayan Ζ™aton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai Ι—akin ya haΙ—u tare da amsa sunansa Ι—aki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faΙ—a da masifarta ta daka mata tsawa. “Da uwar mi kike a Ι—akin da baki gama min ba har na shigo....?”

        “A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma'aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da Ζ™yau har jikin bangon da kikace”.

    Kakkauran tsaki ta Ζ™ara ja da Ζ™arasa shiga Ι—akin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen Ζ™yau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faΙ—a ta kwanta tana mai wargaza fillos Ι—in da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buΙ—e, a gadarance ta ce, “Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haΙ—amin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza Ζ™azamiya sai wani tsamin zufa kike”........✍️

        *_Humm nama rasa abin cewa nikamπŸ˜ΆπŸ˜’._*

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay atπŸ‘‡


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka ananπŸ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura ananπŸ‘‡

09033181070


Ζ³an Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number Ι—inπŸ‘‡


+22799643131


VIPπŸ”₯πŸ’―

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*πŸ₯°

Zafafa🫢πŸ”₯


*_ALLAH ya gafartama iyayenkuπŸ˜­πŸ™_*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post