Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 3


Health College

Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 3

 

Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 3

_*BAKON MUNAFIKI!!!*_

_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_

                _👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

  _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

       __AREWABOOKS:MSSXOXO_

     _WATTPAD:MISSXOXO00_

            FREE PAGE: 003

 ______________

   *Yana* karasa fadar abunda zai fada ya juya don tafiya wajen tukawar ya zauna bayan ya bawa abokin tukinsa hannu sun gaysa.

"Amaal... Amaal.." mahaifiyar ta dake kusa da ita acikin jirgin ta dan tabo ta.

"Na'am! Hayateey... Magana ki ke?" Ta tambayi mahaifiyar tata tana sosa idon ta daya da yatsanta na dama da ke mata kaikayi.

"Gyara kwanciyar taki zaki, kin bata kwanciya kin fara munshari."

"Wai har bacci ya dauke ni Hayateey?"

"Chab! Muna shigowa kina zama ai kika fara baccin."

"Tun safe nake jinsa naki komawa saboda inason sayo rigunan nan."

"Na gaya miki kar ki sake maimaita abunda kikayi yau ko?"

"Eh Hayateey."

"Yauwa banason neman magana. Kiyi kokari idan Allah ya sauke mu lafiya kije ki roki gafarar mahaifin ki."

"Hayateey. Abbiey yasan da zuwana mart din fa."

"Bata lokacin da kikai achan badan Allah ya temaka pilot din bezo da wuri ba ai da tuni munyi missing flight."

Dan rau rau tayi da idanu, Ta kara saukar da kanta kasa. Ahankali tamkar mai rada tace,

"Garin sauri har wani bakin balarabe na zubarwa milkshake a jikin sa."

"To Allah ya kyauta ya tsare gaba."

"Amin."

"Sai ki dinga lura kina tsayar da hankali waje daya idan kina tafiya. Tafiya ba nutsuwa ai dole haka ta dinga faruwa. Kin dai bashi hakuri ko?"

"In shaa Allah! Eh na bashi." Kasan zuciyar ta ta tuno yadda ya chusa mata tissue papers din a bakin ta. Ko sauraron ta bai ba kuma yayi gaba...

"To Allah ya kiyaye gaba."

"Allahumma Aameen." 

"Kwanta tunda baccin ki ke ji."

"Tohm Hayateey nagode."

Gyara kwanciyar tata tayi ta dau wani abu dake gefen kujerar ta rufe idanun ta da shi. Hadi da jan wni kawataccen abu kaman asaberi ta rufe windown setin ta. Ba dadewa kuwa bacci yayi awon gaba da ita. 

             °°°°°°.        °°°°°.    

   Sun dau awoyi a sama kafin Allah cikin ikon sa da buwayar sa ya sanya jirgin su ya sauke a filin jirgi na tashi da ke babban birnin Abuja Nigeria. 

Haj. Jameela ta saka hannunta akan Amaal tana dan bubbugun bayan Amal din. 

 "Tashi mana..."

"Hayateey bacci nake ji sosai"

"Wane bacci bayan mun sauka. Tashi mana."

Ahankaki tashigaa bude manyan idanunan ta sauke akan mahaifiyar ta dake kokarin mayar da takalman ta sau ciki.

"Amaal."

"Nàm Hayateey."

"Tashi muje."

"Tohm..." Ta sake fada tana murza saman idanun ta.

Cikin saka hannu a baki ta bayan ta saki hamma tache,

"Ina dan kunnen hayatey?"

"Wane dan kunne amaal?"

"Gurasa fa?"

Haj jameelah ta mike tsaye tana murmushi.

"Kinsan na dauka idanun ki biyu ashe magagin baccin nan naki ne." Riko ta tayi bayan ta fadi haka. Yayin da amaal din ke ta tangadin bacci.

Futa sukai can haraba. Tuni sun hallata. Abbiey ne kawai baya waien.

Suna tsattsaye wasu a zazzaune .

Can sai gashi ya taho da wani dattijo zai yi kaman shi.  Sai pilot din jirgin da suka hau.

Suka nufi inda suke suka tsaya. Suka gayshe su cikin girmamawa. Ya nuna matan na sa dake wajen su uku"

"Ga Hajiya Hadiza itace first wife dina."

"Da girman kujerar ki, Ina gaisuwa uwar gidah " Cewar abokin amb junaid. 

Hajiya hadiza ta sake washare hanci da baki yaudin ya tabo inda yake mata kaikayi. Don haka ta sake baje fatar labbanta tana murmishi sosai

"Shine aminin nawa da nake gaya muku Ina da shi."

"Allah sarki."

"Sunan sa Alhaji Abubakhar mai dingishin kudi... Wannan Kuma ....

Ya juya zai dafo kafadar hisham ashe hisham din yabar wajen yana waya. 

Yana dawowar ya gaishe da su yana tsaye waje daya. 

"Yauwa ga yaron namu nan sunan sa,  Hisham. Pilot ne na jirgin sama, Kuma kwararre ne a fannin..."

Amaal ta jiya don ganin waye pilot? Idanuwan ta suka sauka akan number da ke jikin aljihun gaban rigar sa. Kai dama ta baya ta jikin blazer dinsa. 

Dai dai lokacin da shima idanuwan sa suka tasanma ganinta..Tuni kallon na su ya sarqe. Ya narke mata idanuwan sa akanta duk wani motsi da take yana han kan idanuwan sa.

Ya kasa janye idanuwan sa akanta. Ta janye nata da sauri tana kallon gefe.

 Shi kuma gogan tamkar ya samu abun kollo. Tun daga kan yan yatsun kafafuwan ta zuwa goshin ta . Kallonta kawai yake

   "Kai Hisham"

Shiru Hisham bai amsa ba. Ashe ya lula duniyar kallon amaal

"Wai Hisham ba magana nake maka ba ne?"

Da sauri ya juya ya fuskanci mahaifin nasa yana sosa keya ... Harara Alhaji Abubakhar ya dankara masa ya juya kawai wajen Amb. 

"Wallahi da ka dan mun uzuri sai muzo daga baya ."

"Haha ambassador meye haka?"

"Gani nayi muna da yawa"

"Ba wani yawa, Banki kufi haka ba. Har me dakinna na gaya wa tun dazu itama take tanbayata yanzu zasu karaso? Nace zasu zo in shaa Allah "

Hisham ya rufe briefcase din amb junaid . Suka shiga motici suka nufi gidan Alhaji Abubakhar da ke cikin kwaryar Abuja unguwar:

   *ASOKORO...*

*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay at👇

1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post