ππ²π©π’π§π π²
π« ππππΌπ πΏπΌππ'π.....!!π«
π©ππππ π¨ππ πππ πππ€π»
πͺππππππ 5️⃣
_Free pages end_
.........Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko'ina mulmule yake da suminti. BQ Ιin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki iyayensu mata, baya can Ζarshe sashen mahaifinsu Malam Mika'il Idris Mawashi. Sam baya buΖatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki Ιakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran Ζanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a Ιakinsa. Dan a yanzu haka akwaima Ζanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula Ζ΄ar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faΙan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har Ζwallar Ιacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ΖwaΖwΖwarar sana'a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba Ιaukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taΙe rayuwarsa haka. Duk inda Ιa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko'a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.
Ζakine Ιan babba mai Ιauke da kafet maroon color mai laushi, sai Ζatuwar katifa irin wadda ba'a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an Ιan yi teburin karatu da kujerarsa. Ζakin babu wani tarkace sannan fes yake ga Ζamshi kamar ba Ιakin namiji ba. Uniform Ιin da aka sharΙanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake Ιakin Ζwara Ιaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da Ιaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaΖi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai Ζona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama Ιinkin fidda surar jikinta baΖin ciki yake ji balle wannan da gaba Ιaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai Ζarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al'amurin ma yaΖi barinsa yin barcin da yake buΖatar yin ko zai samu sassaucin baΖin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da Ζyar ya samu barcin ya Ιaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la'asar. tashi yay da Ζyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miΖe ya shiga toilet Ιin Ιakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za'a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan Ζofar gidansu yake, dan baifi gida huΙu ba ne tsakaninsu....
Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon Ιakinsa yanzu ciki ya shiga Ιangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huΙu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a Ζalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na Ιan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya Ιauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau Ιaya ya amsa musu ya nufi Ιakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..
Daga Ιangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a Ζasan carpet Ιin da aka saka a gaba Ιaya falon kalar blue. Basu da kuΙi, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haΖuri sosai, sai dai bata son raini ko kaΙan ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita Ιin jinin zazzagawa ce.
“Ammah barka da yamma”.
Ya faΙa cikin muryarsa mai sauΖin amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya Ιakko wasu da yawa ga mahaifinsu ma.
“Baka da lafiya ne?”.
Gajeren murmushi yayi da Ιan girgiza kansa. “Lafiya lau nake Ammah, na Ιan yi barci ne”.
“Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba..”
Ta Ζarashe faΙa a hankali cikin damuwa. Gaba Ιaya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarΖe ya ce, “Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai”.
Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya Ζarya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko Ζarfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun Ιazun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi. Fitowar Ζannensa biyu Ζ΄ammata Maryam da Asma'u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. Ζ³ammata ne Ζyawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai Ιan turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. Ζauke kanta tai, dan gaba Ιaya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu.
“Yayamu ina yini”
Suka haΙa baki wajen faΙa a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana Ζaunar Ζanensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al'amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a Ιakinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga Ζ΄aΖ΄an gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne..
“Babu wata damuwa ko?”.
Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buΖatu, sai dai sun san koma sun faΙa tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason Ιakinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai Ζarfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma'u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha...........✍️
*_Humm rikitata-rikitata kenan. Masu karatu ina faΙa muku Bama a fara komai na fa, dan ko shimfiΙar labarin bamu kammalaba balle shiga cikinsa. Littafin FURAR DANΖO...!! Labarine da yazo muku da nashi salon na musamman. Babban abinda ke addabar al'ummar mu a wannan lokaci a cikin gidajenmu da ma wajen gidajenmu da rayuwar Ζ΄aΖ΄anmu mata da maza dama na gidan aure duk ya taΙo fiye da inda kuke zato._*
*_Ga dai Uncle Smart a matsayin drivern Lulu Ζamshi, yarinyar Ζ΄ar Ζwalisa mai tsananin wayewar rayuwa. Ζ³ar gata kuma Ζ΄ar hamshaΖan masu kuΙi. Uncle Smart matashin saurayi Ιan talakawa dake cikin jarabawar rayuwa kala-kala. Ya taso cikin gida mai yawan zuri'a da kowa kansa ya sani. Shin ta ina muke tunanin labarin waΙan nan mutane biyu zai kamanceceniya da juna?_*
_Minene abinda Lulu Ζamshi ke Ιoyewa na rayuwarta?_
*Minene ke faruwa a rayuwar Aliyu Hydar (Uncle Smart) da ke taΙe rayuwarsa da ga cigabansa?*
_Baku ba, hatta da ni kaina ina son sani. Dan haka ku garzayo domin kasancewa da ZAFAFA BIYAR Ιin nan naku abin alfaharinku. Ζ³an amanarku, akoda yaushe labaransu masu gamsarwane a gareku._
*_Ki daure a matsayinki na mace mai kima da daraja, musulma da ta san muhimmancin hakki da son cigaban nata kasuwancin ko aiki kizo ki saya domin karanta halak Ιinki, karki bari ki Ιorama kanki nauyin da zaki iya yin kaico da sakacin Ιaukar watarana saboda ruΙi da Ιaukar komai a ba komai ba Ζ΄ar uwata._*
_ALLAH ya Ζarama rayuwa albarka, duk wanda ya tsare domin ALLAH shima ALLAH ya tsare masa kasuwancinsa ko aikinsa. Alkairin ALLAH ya kai gareku a duk inda kuke a duniya masoya. Muna sonku irin trillions Ιin nan. Duk wanda ya somu domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka shi da zuri'arsa baki Ιaya. ALLAH ya gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi baki Ιayaππππ❤️❤️❤️❤️π_.
Garzaya ki biya naki kar a baki labari gasu nan da Ιumi-Ιuminsu sukeπππ.
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay atπ
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka ananπ
09018600202
Idan katin waya ne kuma saika tura ananπ
09033181070
Ζ³an Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number Ιinπ
+22799643131
VIPπ₯π―
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*π₯°
Zafafaπ«Άπ₯
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuππ_*