Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 5

Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 5

Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 5

 _*BAKON MUNAFIKI!!!*_

_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_

                _πŸ‘ΊπŸ‘πŸ‘©‍πŸ‘©‍πŸ‘¦‍πŸ‘¦__ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_  _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_


       __AREWABOOKS:MSSXOXO_

     _WATTPAD:MISSXOXO00_


     _005_

  _SHAFIN KARSHE NA KYAUTA/LAST FREE PAGE_

_

   °°°Hisham ya daga kai da sauri ya kalleta, Itama wannan karon shi din take kalla. Ba wanda ya janye idanun sa. Mamaki take ashe ba balarabe bane. Yayin da shi dinma hakan take a tasa zuciyar. Yana mamakin dama ba balarabiya bace?


"Gata nan kaman Hisham itama ita kadai ce awajen mahaifiyar ta."


"Allah sarki .. Allah ya raya mana su baki daya ya musu albarka."


"Allahumma Aameen." Cewar amb. Junajd ya sake muskutawa ya gyara zaman sa. Kafin ya cigaba da cewa,


"Ga Hadiza fa ... Ko ka sheda ta?"


"Kwarai kuwa nasan hadiza ba kanwar su labbo ba?"


"Tabbas itace.... Lalle baka da mantuwa, To ga yaranta nan Abubakhar daya ci sunan marigayi yaya?"


'kwarai Yaya. Allah ya gafarta masa."


"Amin Amin, Muna ce da shi sadeeq, Daga shi sai mai bjye masa wancen safwan, Sai Na'eelah da najwa ga sunan a jere."


"Sai kuma Hindu da baka fada ba. Saboda ita agola ce? Wallahi Alhaji ka sauya halin ka. A wajen bare ma sai an raba hali. Hindu dai ko ban aure ka ba ai idan da kara kai ma yar kace. Tunda ni da kai a duk tsatso daya muka fito. Wannan 'ya tace itama Hindu amman ba shine uban ta ba kamar yadda bai lissafo da ita ba. Mahaifin ta dan uwa ne agare mu ni da shi. Mahaifin ta shine babban cousin a family din kandemi" Cewar hadiza matar sa ta fari. 


Tamkar kasa ta tsage ya fada haka yake ji... Kunya duk ta dabaibaye shi. Gashi ita datai maganar ko a jikin ta tacigaba da danna wayar hannun ta.


Parlorn yayi tsit kamar ruwa ya cinye su. Chan dai Alhaji Abubakhar yayi breaking silence din yace,


"Su kuma wadannan yan biyun fa ga sunan kamar su daya baa gane su.?"


Amb junaid ya juya ya jalle su yana murmushi. Kafin ya saka yatsa yayi nuni da haj jameelah yace,


"Ga kuma jameela. Itace mai daki na ta biyu bayan hadiza. Kamar yadda na gaya maka dazu. Amaal ce kawai Allah ya albarkance ta da ita... Itama sai bayan shekaru.."


"Haka... Allah ya raya su duka Amin."


"Amin amin... Sai mai dakina ta karshe... Ruwaida.. Gata nan. Itace mahaifiyar yan biyun da kake magana yanzu. Su kadai ne yaranta."


"Ma shaa ALLAHU... Allah yayi musu albarka ya raya su duka Amin.."


"Allahumma Ameen."


Ya sake daga robar ruwa ya kafa a baki ya sha bayan ya sauke dankarereriyar ajiyar zuciya yace,


"Hadiza, Jamila, Ruwaida...." Ya kira sunayen matan nasa daya bayan daya..


Dukkanin sh suka juya suna kallon sa. Suka kuma kasa kunne don jin abunda zai ce,


Ya saka yatsa yayi nuni da Alhaji Abubakhar yace,


"Wannan shine babban aboki na da nake gaya muku. Kai ya wuce aboki ma ya zama amini. Ya kere wasu da suke ganin su yan uwan na ne na jini. Ya mun abunda a duniya  bazan taba mantawa da da tarin allhairinnsa agare ni ba."


"Kabar maganar nan Junaid... Haba mana kamar wasu yara sakarkaru."


"Kyale ni sai na fada... Amini na ne... Alhaji Abubakhar mai murmushin kudi'. Ko a wani hali kuka tsinci kanku a duniya da rai na ko bayan rai na, Ku kuma  godewa Allah daya azurta ku da shi. Ku kira shi a ko'ina ne zai zo yayi bakin kokarin sa. Mutumi ne da yake adali, Mai dattako, cikar kamala, alheri, Mutunci, gaskiya, Amana da rikon ta, tausayi, kawaici, kauda kai, hakuri, da Imani ga biyayya, ga ladabi ga kamewa, ga temako... Alhaji Abubakhar mutumi ne da baya gajiyawa wanda yasan halacci ba kuma ya mantawa da alkhairi komai tarin sharrin da ka bishi da shi, Yayi da jikin sa yayi da aljihun sa ...zuwan mu zuwa Nigeria ko ince dawowar mu da dik wani zuwa hutu da duk wata tafiya Dr abubakhr ya dauke mun ita ni da iyali na da ahali na gaba daya free of charge muke shiga kasashe...Allah ya saka masa da alkhairi ya biya masa dukkanin wasu bukatn sa Amin... Ga matar sa nan kuna gani sunan ta Aisha.. Ga kuma dan su da Allah ya azurta su da shi Hisham shine matukin jirgin daya kawo mu man... Bugu da kari ma jirgin mahaifin sa ne gashi a zaune na Dr abubakhr ne.. 


"Duk wani Hisham da kuka gani na gidan mai hotel da sauran su duk na de abubakhar  ne yayi masa laqabi da sunan dan sa Hisham, kamar su: Hisham airlines,Hisham travel and tours, Hisham palace,  Hisham showroom, Hisham plaza, Hisham oil and gas ltd, Al'Hisham international university., Hisham mart, Hisham luxury. Wadannan kadan kenan daga mallakin tarin kadarorin abubakhr. Babban oil mogul ne na kasar nan. Duk samda zamuzo Nigeria idan kukaga nasa an fita da motoci an musu full tanks to shine yasa lalle na'aika a dibamun mai kyauta... Kadan kenan daga cikin temammakin da yake yi ko ince ya saba yi ya ke kuma kan yi...Na roke ku da duk wanda yayi sallah ko yake addua ya dinga kamo sunan bawan Allah nan yana masa addua. Yana kuma rokon Allah daya kara kareshi ya azurta shi ya biya masa dukkanin bukatunnsa ya kuma yaye masa damuwar sa da lefukan sa. Allah ya saka masa da alkhairi ya jikan mabaifa."


Baki daya parlorn suka shiga amsa addu'oin amb junaid.


Haka dai suka karasa yar hirar dasike yi. Kafin akai su babban masaukin baki da aka tanadar acikin gidan dake dauke da komai na more rayuwar yau da kullum. Komai yaji babuce kawai babu agidan nan.


Amaal waje daya suke da mahaifiyar ta, daki ne yana kallon daki. Bayan tayi wanka a bandakin dake cikin dakinn ta zura babban hijabin dake ajiye akan sallaya ta zura kayan bacci aciki.


"Hayateey bara naje wajen Abbiey."


"Toh."


Fita tayi daga dakin ta nufi dakin da taga an shigar da akwatin mahaifin nata aciki.


Kwankwasa kofar tayi tana daga tsaye a bakin kofar ta waje,


"Shigo..." Ya amsa ta daga cikin dakin


Ta murda kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama.


Yana daga zaune akan wata kujera. Gaban sa kuma laptop ce yana aiki acikin ta. Daga kai yayi ya kalleta yana murmushi


"Hajiyata"


"Naam Abbiey... Barkan ka da dare"


"Barkan mu dai uwata ta kai na

"


Karasa shiga tayi. Ta zube daga dan nesa da shi tana mai aika gaisuwar ta agare shi chike da biyayya,


" Abbiey  barka da dare,"


"Me sunan yan gayu... Uwata tafi ta kowa."


Nan ma murmushin tayi. Tana mai hada yatsunta wajen lankwasa su cike da maduakakiyar kunya.


"Menene uwata ?"


Nan ma.shirun tayi tana murmushi.


Ya ajiye wayar sa da ke hannun sa yana nazartar ta sosai,


"Ina jin ki..."


"Abbiey dama... Dama ... "


"Ina jin ki Hajiya ta"


,"Dama zuwa nayi wajen ka na nemi gafara abisa lefin da nayi maka ,"


Ya danyi tattausan murmushi kawai yana girgiza kai,


"Uwata ai bata lefi...... Tashi kije na yafe miki duniya da lahira duk kuwa da ban rike ki da komai ba. Da lefin da kikai da lefukan baya da ki kai dama wadanda zaki agaba. Duka na yafe miki. Allah ya miki albarka..."


Murda kofar dakin akayi aka shigo. Hajiya hadiza ce. Tana tafe da kayanta samfarin riga da skirt da daurin ture kaga tsiya


Ta dubi Amaal shekeke tana yamutsa fuska,


"Hmm an turo ki ki kasa ki tsare kenan , Kai gaskia baki saar gyatuma ba. To kije ki gaya mata idan ta isa tazo nan ba wai ta turo ki ba. ... Tashi ki fita kema chan daya munafuka,"


"Meye haka hadiza?" Cewar amb. J.  yana binta da kallon bata kyauta da abunda tayi ba.


"To ai gaskia ne. Naga ba kwanan ta bane. Na wane dalili ne zata turo yar ta kawai don ta zo ta h..."


"Ya isa haka Hadiza. Ba girman ki bane."


"To tashi ta fita. Ko na fadi abunda zai fi karfin sauraron ta wallahi."


Girgiza kai kawai yayi cike da takaicin ta dama kalaman ta marasa kan gado. Ya dubi Amaal dake tsakure duk ta dubibice tanata harde yan yatsunta na hannu yace da ita,


"Je ki ki kwanta uwata... Allah ya tashe mu lafiya. Ya kuma yafe mana baki daya Amin. Ki kwanta ki huta kinji ko?"


"Tohm abbiey."


"Ki saki ranki ki sawa zuciyar ki nutsuwa kinji? "


"Tohm abbiey." Ta bashi amsa tana kokarin murda kofar zata fita 


Ya sake cewa da ita,


"Sai da safe. Baki mun komai ba kinji? Allah ya mana afuwa gaba daya Amin. Kar a manta da adduoin bacci kinji ko?"


"Tohm abbiey in shaa Allah. Sai da safe." Tayi saurin fita ta rufe kofar. Sakamakon wasu zafafan harara da hadiza ke aika mata .


Amaal na fita daga cikin dakin ta sauke ajiyar zuciya. Hadi da saka hannu ta dafe kirjin ta dake bugawa tamkar zai fado a kasa saboda tsananin tashin hankalin data shiga...


Samun kanta tayi da fita ta kofar da zata sadaaka da waje.. saboda gumin tsoron da ke zurara daga idanun ta . Wani kayataccen garden mai dauke da fitilu masu matukar kyau da kayatarwa da ke kallon kofar ta shiga


Tamkar tsakar rana saboda yadda hasken fitilu daban daban suka dallare wajen. Ta sanya hannun ta tana shafa fulawawwakin da ke shuke cikin wani gini me basu ruwa. 


Ta sake sauke zuciya a karo na ba adadi alokacin da ta tuno mugayen kallon da hadiza ta rika jefa mata. Ta samu kanta da girgiza kai kawai can kasan maqoshi don ita ta dauka a zuci ma tayi tace 


"Allah ya kyauta...."


"Amin... Ya kyauta abunda yafu haka ma.."


Da sauri sauran kadan ta saki fitsarin tsoro dubada tasan ita kadai ce awajen gashi dare ne. Uwa uba a zuciya take tunanin tayi maganar kawai taji murya da ta amsata daga bayan ta.


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Ta fada da dan karfin ta." Hadi da sake bude baki zata saki zundumemiyar kara yayi saurin zuwa gaban ta, Hadi da saka tattausan hannun sa ya toshe mata baki...


Ya rankwafa har saitin fuskar ta yana bin zara zaren gashin idanun ta da kallo,


"Calm down...Matsoraciya ce ke dama? Meya kwan kiyi addua sai kara da zaki saki? A daren nan kusan kowa yayi bacci meya fito da ke ma?"


Tanata girgiza masa kai. Sam ya manta ya toshe mata baki da tafun hannun sa. Ya nata mata magana shiru


Data gaji ta saka hakora ta gartsana masa cizo ya saki hannun dakyar yana yarfe shi hade da runtse idanun sa.


"Akan wane dalili zaki cijeni?"


"Bakinta ka rufe mana..."


Ya juya ya dankara mata harara yana mulmula wajen da ta cije shi.


"Lefuka biyu kika mun...." Ya fada yana hura iska awajen data gartsana masa cizo


"Ba abunda na maka.." tafada tana tafiya hanyar fita zata gudu ya sha gaban ta da sauri 

"A Madina kika zuba mun milkshake a jiki na... Yanzu kuma kin cije ni. "

"Duka ba da gangan nayi ba. Allah ya baka hakuri" magana take tana turo baki gaba saboda tsabar shagwaba ta autanci

"Zo ki dressing mun cizon nan da kika mun. Da hakoran ki kaman na vampire "

"Ka samu babba yamaka...ni ba muharramar ka bace." Ta fada tana tuna kashedin da Hayateey ke mata shekarun baya na karta bari namii ya taba ko da hannun ta ne zata haihu

Dariya abun ya bashi gege daya kuma ya yaba da hankalin ta,

"Shekarun ki nawa?"

"I'm clocking sixteen...."

"Sha shida?" Ya sake tanbayar ta cike da madaukakin mamaki. 

"Ashe ke girman finkaso ce da su buredi?"

'tubarkAllah..."

Ta tabe baki Hadi da ketarewa ta bayan sa ta fuce da sauri har tana tuntube tayi cikin masaukin su..

Ta shedawa Hayateey dinta dukkanin abinda ya faru da take wajen Abbiey dinsu dama lekawarta garden inda Hisham ya sameta

Mahaifiyar tata ta sake jan kunnenta sosai game da ilimin rayuwa. Sun dan jima suna yan hirarrakun su, Kafin daga bisani kuma subi lafiyar gadajen dakunan nasu bayan sunyi tsarki...


   ×

   Kwanakin su biyu a burnin Abuja dakyar amb ya amince suka kwan biyun ma saboda yadda aminin na sa ya dinga rokon sa dan Allah su sake kwana

Ai kwa suna cike kwanaki biyun suka biyi jirgin safe daga babban birnin Nigeria wato Abuja zuwa ga garin NUKAA.. wato NUKAA STATE dake nahiyar kasar Nigeria...

Motoci da masu tsaro ne suka je suka dakko su daga filin jirgi zuwa babbar unguwar datafi kowace unguwa tsadar rayuwa da manyan masu kudi . 

A cikin unguwar katafaren babban gidan. Ko ince girman gidan kusan yankin wani kauyen.. Anan hamshakin gidan yake. 

Gidah ne na yan uwa masu zumunci dai dai misali.. Wanda suka ta-da kai suka koma koshi da kudi... Ana damawa da su a nahiyoyi da ketare. 

Babban gidah ne na yan uwan da suka hada manyan maaikatan gwamnati, manyan yan siyasa, alkalai na kotu, frofesoshi na jami'u, manyan malami na sunna da dai sauran su. 

  Estate daya ce me kama da gari guda ko karamin kauye saboda tsananin girman ta. Kudi yayi kuka agidan nan domun ya hada komai idan aka cire babu da dangin ta.

      ×× A tare motocin da sukayi convoy suka shiga cikin babban jijjigaggen gate din dake dauke da gidaje masu matukar kyau da tsada. Ciki harda islamiya, computer school , gym, garden, swimming pool da dai sauran abubuwan more rayuwa na yau da kullum...kaf birnin NUKAA ko na cikin kauyuka sunsan attajirar zuriyar KANDEM...

    *KANDEM ESTATE......*

    Babban gidah ne na zuri'ar yan uwa da suka kunshi rassa......

     --------

_ANAN NA KAWO SHAFUKAN KYAUTA NA WANNAN LITTAFI MAI SUNA A SAMA.._

_KU ZO A DAMA DAKU CIKIN TAFIYAR ZAFAFA BIYAR AKAN KUDI MAI RAHUSA.. AKWAI DARUSSA SOSAI NA QARUWA ACIKI..._

_LITTAFIN BAKON MUNAFIKI YAZO DA WANI SALO NA DABAN..._

_YA ZATA KAYA NE A KANDEM ESTATE? SHIN WACECE KO WANENE BAKON MUNAFIKIN ACIKI?_

_YA RAYUWAR AMAAL ZATA KASANCE???WACCE CAKWAKIYA CHE ZATA CHUDE TA?_

_AMB JUNAID MAGIDANCI NE MAI MATA UKU DA TARIN YARA CIKI HARDA AGOLA DA YAKE RIKO..._

_TUKUNNA MA ME KANDEM ESTATE DIN TA  KE CIKI NE? GA TARIN ZURI'AH DA SUKA HADU WAJE DAYA? ZUMUNCHIN ZAI TARWATSE NE KO KUWA MATSALOLIN CIKIN SA NE ZASU WARWARE ZUMUNTAR TA SAKE QULLUWA?_

_KADA KU MANTA AMAAL A SHAFUKAN KYAUTA TANA YARINYA YAR SHEKARU SHA SHIDA..YA ZATA KAYA IDAN TA SAKE GIRMA? MENENE ZAI KUNNO KAI KUMA....?

_GEFE DAYA KUMA GA HISHAAM KYAKKYAWAN MATASHIN MATUKIN JIRGI MAI JINI A JIKA, WANDA YA TASO CIKIN DUKIYA YA BAWA KADARORI BAYA..._

_AAYAN, AL-MUSDHAFA, HAMID/HABIBI TALBA ..RIGIJI GABJIN FA KENAN TO SU KUMA WADANNAN DIN SU WAYEπŸ™Š???_

_DANKARI MAKARI...AKWAI KASURGUMAR CHAKWAKIYA MAI LULLUBE DA TARKO NA ZUMUNTA....._


_DUKA DUKA AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WADANDA BAN LISSAFO  BA ZASU ZO MUKU NE CIKIN LITTAFIN NA:_


 _BAKON MUNAFIKI_

    _(BA NA MUTUM DAYA BANE)_..

*_MATSO KIJI_*πŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

Pay atπŸ‘‡

1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka ananπŸ‘‡

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura ananπŸ‘‡

09033181070

VIPπŸ”₯πŸ’―

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*πŸ₯°


Zafafa🫢πŸ”₯

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post