💋The father Of Soldiers💋_
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥
Story
&
Written
by
*_Boss Bature_
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
Dedicated to my beloved sisters. 😍
Proud Of My First Novel💋
_Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina,Sannan kar a kuskura a haɗamun document,Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3 yayi mun magana ta whatsapp 08103884440_
Canza ra'ayi yayi"Omar,bana buƙatar using the bluetooth Just komai ya dace ka sanar da ni,"
Murmushi Omar ya ɗan saki don yasan cewa Sgr zai iya,A nan ya shiga kwatanta mashi yadda zai bayyanar da Soyayyarshi,bayan Ya Kammala Sgr yace"thanks,sai nadawo,"yakai ƙarshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar fita ɗakin,Yana jiyo muryar Omar Yana faɗin"Wish u all the best,"
A lokacin Sehrish tana zaune ta tasa abincin da Aunty Azeema ta haɗa mata sai ci take yi,bayan ta kammala ta yagi tissue tana goge bakinta,A dai dai wannan Lokacin taji an turo ƙopar ɗakin,dakatawa tayi tana jiran ganin mai shigowar,Natsuwa tayi tana shaƙar daddaɗan kamshin turaren dake kai ma hancinta ziyara,tunkafin ma Ya shigo ƙamshin jikinshi ya gauraye ɗakin saƙo da lugu,
A hankali ya sako ƙafarshi kafin ya ƙarasa shigowa ciki,Har sai da gabanta ya faɗi rass,Saboda razana da tayi da kyawun da Sgr yayi,Kayan hausawa ba ƙaramin kyau suke yi mashi ba,yadda kasan danshi kamfanin shadda suke ƙerata,cikakkiyar surar jikin nan nashi ta ƙara fito da kyan shaddar,
Tunda ya ɗaura idanuwanshi akanta,gaba ɗaya wankanta ya tafi da imaninshi,natsuwa yayi yana kallonta,from head to toe,Atampar jikinta ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,Ya kasa kawar da idanuwanshi kamar yadda itama take Kallonshi,
Sallama yayi mata cikin sanyin Murya ta amsa mashi,kafin ya ƙarasa shiga ciki,gefen gadon ya zauna dab da ita,tuni kasala ta fara baibaye kowannansu,
Almost 15 mins,tsit kake ji ba wanda yace uffan acikinsu,Ajiyar Zuciya ya ɗan sauke kafin Ya soma magana,
"Ya jikinki?"A hankali tace"da sauki" jinjina kai yayi yana cigaba da kallonta,hakan yasa ta Sunkuyar da kanta tana kallon hannuwanta,
"Reesh,nasan nayi maki laifi wanda yasa kika juyamun baya,But Why can't u forgive me?komai ya wuce mana,Idan har bana ƙaunarki serious bazan kulaki ba,kuma abunda ya faru,duk don saboda ƙaunar da nake yi maki ne,Naji fargabar su rabani dake,I thought yi maki hakan da nayi will be the solution,sai dai nayi mistake na kusantarki a lokacin da nake cikin fushi,wanda duk Iyayenmu ne suka jawo hakan,"ya ɗan dakata da yin maganar Yana mayar da numfashi,jin yayi shiru yasa ta dago,yayin da idanuwansu ke kallon cikin na Juna,
"Ina neman alfarma a wurinki,For the Last time,ki bani dama,zan gyara kuskure na,Zan canza maki kamar yarda kikeso,"
Jikinta ya ɗanyi sanyi da jin kalamansa,Amma still tana kokwanto akanshi,gani take kamar Sgr bazai ta6a sonta don Allah ba,sai don ya mayar da ita abun biyan buƙatarshi kamar yadda ya saba yi mata,Zurfin tunani ta shiga,ba zato ba tsammani,taji ya ruko hannuwanta Acikin nashi,sosai ya ruƙe hannun yana shafa lallausar fatar hannun,a hankali ya fara matsawa yana niyyar rumgumeta....
"Reesh,I've Fallen for you...... "Tunkan yakai ƙarshen Maganar,Rai a matuƙar 6ace Sehrish Ta ƙwace hannunta daga nashi tare da yin wurgi da hannunsa ta dan ja baya,Abunda bai ta6a tsammani ba,Waro idanuwanshi yayi waje yana kallonta,
A fusace take magana"Wlh ba sona kake yi ba don Allah,Ni nasani don kawai biyan buƙatarka yasa kake so naci gaba da kasancewa dakai,idan har dagaske kana sona,Meyasa tuntuni baka sanar dasu cewa kana sona ka maida ni matarka ba,kuma tun farko kayi accepting aurena don kawai naci gaba da yi maka Aiki,Saboda kafi ƙarfin kayi soyayya dani,bankai matsayin da zan zama Matarka..... "Kasa ƙarasa Maganar tayi sakamakon gigitacciyar tsawar da Sgr ya daka mata,A firgice ta zazzare idanuwanta tana kallonshi,tuni idanuwanshi sun Canza launi sosai,Ranshi yayi Mugun 6aci,Zuciyarshi ta hasala,har ya ɗaga yatsu biyar cuf zai wanka mata mari,Ta fashe da matsanancin kuka,Ta dinga ja da baya har ta ƙurewa kan gadon,ta runtse idanuwanta sosai,'
Yarfar da hannun gefe yayi,wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyarshi,tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla,takaicin Duniya ya ishe shi,ƙaramar yarinya kamar wannan ce take gaya mashi Magana,gudun kada ya karya ƙasusuwan jikinta ne Yasa yayi saurin miƙewa da saurin gaske har yana tuntu6e ya fuce daga ɗakin,A makance yake tafiya Allah yaso babu kowa a babban falon,A zafafe ya nufi twin stairs ɗin Ya haye,yana taka staircases ɗin wasu Zafafan hawaye suka wanke mashi fuskarshi masu ɗumin gaske,har wani zazza6i yake ji ajikinshi,Sehrish ta hasala shi sosai,
Yana shiga Bedroom Yasa hannu Ya tu6e rigar jikinshi yayi wurgi da ita ƙasa,A haukace Yakai hannu Ya damƙi bedsheet din gadon Ya yayeshi tare da Jefar dashi gefe guda,Dunƙule hannunshi Yayi da ƙarfin gaske Ya naushi Dressing Mirror ɗinshi,gaba ɗaya madubin ya farfashe ya zube,hatta hannunshi sai da glass din ya faffasashi,jini ya shiga tsastsafowa,raɗaɗin da yake ji a hannunshi bai kai raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi ba,lokacin da Sehrish ke faɗa mashi wannan maganganun,Biji biji ya fara gani acikin idanuwanshi,Jiri ya soma ɗaukarshi,tangal tangal yayi zai faɗi,kaitsaye ya faɗa saman gadonshi,numfashin shi na fita da wani irin huci,ga wani matsanancin ciwon kai daya farmasa,
Wuraren ƙarfe 12 na dare,Omar ya faɗo part ɗinsa,fuskarshi ɗauke da Murmushi,Yazo cike da sa ran sunyi nasara,Tun a palour Yake ƙwala mashi kira"Bro!bro!"shiru ba Amsa,har yayi tunanin ko bai kaiga dawowa bane,Acikin ransa har yana cewa"Yanzu haka yana can manne da ita suna shan Soyayya,"ya ƙarasa zancen zucin yana kokarin juyawa kwatsam Idanuwanshui suka sauka akan Agogon Diamond ɗin Sgr,dake yashe a ƙasan tiles,
Har sai da gabanshi ya faɗi,don yasan cewa ba ƙaramin abu bane zaisa Sgr ya yarda watch dinsa ba,zuƙunnawa Omar yayi tare dakai hannu ya ɗauki wrist watch ɗin,A fili Ya ambaci Sunanshi Rafayet,Da gudun gaske Omar Ya faɗa bedroom ɗinshi,A kwance ya samu Sgr tamkar baya numfashi,hankalinshi yayi Mugun tashi,A sukwane ya haye saman gadon saitin fuskar Sgr,hannu yasa yana shafa fuskarshi"Rafayet meya faru dakai?Meyasa kayi hakan?duk ka hargitsa ɗakin ka fasa glass,"ɗago da kanshi yayi tare da ɗaurashi saman laps ɗinshi,Omar sarkin tausayi tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla,
Muryarshi na kerma yace"Dan Allah Rafayet ka fadamun meya faru da kaine?nashiga damuwa sosai pls....."tuni hawayen fuskarshi sun soma sauka saman fuskar Sgr,
Sai lokacin Sgr Ya yunƙura tare da miƙewa daga zaune,yana faman fitar da huci,
"Omar,Reesh batasona,She hates me completely,i can see dat in her eyes,danasan zata ci mutuncina haka da banje ba,nafi ƙarfin wulaƙancin mace,Saboda Allah ya jarabce ni da son ta shiyasa har take ƙoƙarin gaya mun magana".....Ya ɗan dakata da yin maganar,Omar ya kasa kunne yana sauraronshi,.
"tana tunanin cewa Jikinta nakeso!Me take dashi?Mata nawa ne suka sha kawomin kansu wanda suka fita komai don kawai nayi lalata dasu,Amma banta6a kula ɗaya daga cikinsu ba,sai ita da Allah ya bata dama?
Jinjina kanshi ya ɗanyi kafin yaci gaba da cewa"As a Surgeon General,I stoop too low don kawai inason cigaba da rayuwa da ita,wata ƴar ƙarama da ita,if not love dat's Crazy me zanyi da ita.........."tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,
"Itace mutun na farko da ta fara sani zubar da ruwan hawayena,"
Jikin Omar ba ƙaramin sanyi yayi ba,Hannu Yasa tare da janyoshi jikinshi lallashinshi ya shiga yi,Yana tausarshi,
"Omar,dama kadaina Wahalar da kanka,Na yanke shawarar gobe zan tafi U.s,"
"Dan Allah Rafayet mubi komai a sannu,Ni nasan cewa tana sonka,zata sauko ne,amma tafiya U.s will not be a Solution,"
"Na riga na yanke shawara Omar,i will distance Myself from her,nasan hakan zai sa nasamu kwanciyar hankali in na daina ganinta,So Zan tafi kawai first thing tomorrow Morning",
Shiru Omar yayi,don kuwa yasan Sgr bazai canza ra'ayinshi na tafiya ba,
"Shikenan,bazan hanaka tafiya ba,bari na taimaka maka,Hannunka yana bleeding,"
Girgiza kai yayi"a'a,kabarshi kawai,"yana faɗin hakan ya sauko daga saman gadon Ya nufi toilet ɗinsa Ya shige,
Saukowa Omar yayi daga saman gadon,Ranshi ya 6aci sosai baiji daɗin abunda Sehrish ta yiwa Sgr ba,bai ta6a tunanin zata Iya furta mashi waɗannan kalaman ba,
Gyara mashi Bedroom ɗin ya tsaya yi,Sai da ya kwashe glass ɗin daya zube duka ya kawar da komai,kafin Ya sauko Downstairs Ya nufi Medical Room ɗinsu,P.A box ya ɗauko Kafin Ya koma up part ɗin Sgr,Ya ajiye mashi asaman gadonshi don yayi dressing ɗin hannunshi,
Bayan Omar ya fito a hanzarce ya nufi ɗakin Azmee,A lokacin Sehrish tana ƙumshe cikin bargo,tajiyo bugun ƙopar ɗakin,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,duk a tunaninta Sgr ne ya dawo,gabanta sai faɗuwa yake yi,ƙin buɗe ƙopar tayi Har sai da Omar ya ɗaga Murya tare da cewa"Sister Omar ne,Zo ki buɗe mun ƙopa,"
Cire blanket ɗin tayi cike da fargaba ta ƙarasa gaban door din tasa hannu ta buɗe mashi,tunda take bata ta6a ganin Omar cikin 6acin rai irin na yau ba,jikinshi har wani jijjiga yake yi,sam babu annuri akan fuskarshi,
Muryarta na kerma ta ambaci sunanshi"yay...ya Omar,"
Shiga cikin ɗakin yayi bayan ya sanya hannu ya garƙame kopar,
A fusace Ya damƙi kafaɗunta tare da jijjigata yace"Ke!Ashe baki da hankali bansani ba?Anya kuwa kinsan ciwon kanki?kin bani kunya kin kuma bani mamaki,Ki rasa abun wulakantawa Sai Sgr?tsaran wasanki ne?dan Kin samu Allah ya mallaka maki shi shine har kike kokarin banzatar dashi?Idan saboda laifin da yayi maki ne baya baki hakuri ba!shine bazaki hakura ba!........"fashewa tayi da wani irin matsanancin kuka,
"Don me zaki ce wai jikinki yake so?ke kinsan adadin matan dake bibiyar rayuwarshi don kawai su samu shiga awurinshi koda da sunan lalatane bada aureba,Sai ke don Allah ya jarabceshi da Sonki,ni shaidane Akan Sgr,wlh da ace baisonki bazai ta6a sha'awar ta6a jikinki ba,don yana sonki ne yasa har yake yi maki hakan,shi baturen mutun ne shiyasa yake nuna maki so ta hakan........"dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,zufa duk ta wanke mashi fuskarshi,Sehrish kuwa sai faman shessheƙar kuka take yi,
Sassauto da Muryarshi yayi kafin yaci gaba da cewa"Yanzu hankalinki ya kwanta,kin kaishi ƙarshe,Gobe zai koma U.s,duk don saboda abunda kikayi mashi,Kuma inaso ki sani da zarar ya ɗaga ƙafarshi yabar ƙasar nan,Akwai mata dayawa dake jiranshi,daga Cikinsu akwai Eva his Uncle's Daughter,dawowarshi kawai take jira don a ɗaura masu aure...tun suna yara take sonshi,ba abunda bata mallaka ba da duk wani ɗa Namiji zai buƙata a wurin ƴa mace..,......"
Tunda ya soma maganar tafiyar Sgr U.s da kuma Maganar Eva,hankalin Sehrish yayi mugun tashi,duk tabi ta ruɗe ta susuce,
"Sgr baya kula mace don bashi da ra'ayin yin aure,kuma shi ba ɗan iska bane bai ta6a kusantar zina ba balle har ya aikata ta,baisan menene so ba,baisan kuma ya akeyin shi ba,Amma wannan karon Akanki Yasan menene So,ya kuma san daɗin mace,Kinga kuwa da zarar yabar ƙasar nan Ya koma can,zai amince da Auranta ne,kodan ya nema ma kanshi mafita,ke kuma zakiyi dana sani ne,domin kuwa duk macen data samu miji kamar Sgr tayi watsi dashi wlh sai tayi danasani na har Abada,"
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan tamkar ranta zai fita,Sam ta kasa buɗe baki tayi magana,
"Ya Sauke duk wani girman kai nashi,Ya ajiye matsayinshi duk don saboda ke ɗinnan,Don Ya samu soyayyarki,da kanshi ya nemi da in koya mashi soyayya saboda yana son ya faranta maki,Yana kuma son ki gane cewa ba jikinki yake so ba,Zuciyarki yake so,kuma kinyi kuskure da iliminki da hankalinka,kika bari Mijinki yake kwana da baƙin cikinki acikin zuciyarshi!?"
Rass taji gabanta Ya faɗi,girgiza kai Omar yayi,tare da juyawa rai a6ace ya nufi hanyar fita daga ɗakin har ya ruke handle ɗin ƙopar ya kuma juyowa ya kalleta,
"Ina ƙara tunasar dake,Gobe da Safe zai tafi,shawara ta rage taki,wlh don kina ƴar uwata ne yasa na zauna ina yi maki wannan gargaɗin,Saboda ina sonki dashi,Kuma kema kina sonshi,wannan damarkice ta ƙarshe kiyi tunani kafin nan da safe,nabarki lafiya,"
Yana kai ƙarshen Maganarshi,Ya buɗe kopar ya fuce waje,
Tashin hankali,Wani irin zazza6ine Ya lullu6eta,hawaye ta ko'ina saman fuskarta,wani irin tuƙuƙin baƙin ciki take ji acan ƙasan zuciyarta,sunan Eva ya tsaya mata aranta,saboda ta ta6a jin sunyi magana akanta a lokacin baya shi da Omar,har yake cewa in ma akwai Macen da ya dace ta mallake shi,to itace,
A hankali ta soma ambaton"Innalillahi wa'inna ilahirraji'un,"
Maganganun Oummansu ta shiga tariyowa acikin kanta,daƙyar ta iya lalla6awa ta haye saman gadon ta kwanta,sosai tashiga raira kuka kamar jinjira jikinta sai kerma yake yi,Wani irin kishine ya rufeta,cikin shesshekar kuka take faɗin"Ya Rafayet zai tafi U.s ya barni,zai je ya aureta,"nutsar da fuskarta tayi jikin pillow tana ta raira kuka,
A daren Ranar Mutun biyu basu runtsa ba,Waɗanda zuciyoyinsu ke cikin halin ha'ula'e,kamar yadda Sgr ya kwana kwance saman gadonshi cikin mawuyacin hali,Haka itama Sehrish ta kwana da tunanin abu biyu,kalaman Oummansu da kuma kalaman Marshal Omar sun tsaya mata aranta,shi kanshi Omar ɗin bai samu isasshen bacci ba,saboda damuwar daya shiga duk akan Ɗan Uwanshi,
Wuraren Sallar Asuba Sehrish tana a kwance kamar matacciya,jikinta duk ya saki,ga zazza6in da take fama dashi tare da matsanancin ciwon kai,daƙyar ta samu ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,agaban Sink ta tsaya tana kallon kanta cikin Mirror,fuskarta tayi jaga jaga da hawaye hada majina,jan bakin data shafa duk ya 6ata fuskar,duk ta harmutsa gashin kanta,tasha kuka sosai,lips ɗinta duk sun kumbura,hancinta yayi jawur dashi saboda matsar daya sha,tajima acikin Toilet ɗin kafin ta samu tayi alwala,
Lalla6awa tayi ta fito daga toilet ɗin ta tunkari wardrobe ɗin kayanta,hijab ta ɗauko tare da darduma ta shimfiɗata,daƙyar ta samu ta tattara natsuwarta kafin ta kabbara sallah,bayan ta kammala Sallar ta zauna tare da ɗaga hannuwanta,tana Addu'a hawaye na shararowa akan face ɗinta,jikinta duk yayi sanyi,A saman dardumar bacci ya ɗauketa,
Baccin bai kaiga yin nisa ba aka soma kwankwasa ƙopar ɗakin,kwan kwan,can cikin bacci take jin bugun ƙopar,firgigit ta farka,zufa sharkaf akan fuskarta tamkar an watsa mata ruwa,bakomai bane ya fado mata aranta ba fa ce Maganar Omar na cewa Yau Sgr zai koma U.s,A hargitse ta miƙe tare da nufar ƙopar tasa hannu ta bude,Amrish ce a tsaye jikinta sanye da hijabi,ganin Sehrish cikin damuwa yasa tace"Meya faru ne?baki da lafiya ne?a ruɗe tayi tambayar,
Sehrish bata tsaya jin amsarta ba,duk hankalinta ya tashi,ta gefen Amrish tabi da gudun gaske ta nufi babban falon gidan,babu kowa duk basu tashi daga bacci ba,Upstairs ta haye har tana tuntu6e wurin taka matattakalar,Idanuwanta sun makance tana tsoran ta rasashi,a fujajen ta faɗa part ɗinsa,shigarta falon keda wuya,Sai ga Sgr Ya turo trolley a hannunshi,Ya kammala shirin shi tsaf zai tafi Airport,Jikinshi nasanye cikin jeans da T-shirt,fuskarshi sam babu annuri akanta,ga hannunshi daya jima rauni,
Cikin sanyin Murya ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet,"ɗagowa yayi da idanuwanshi akan fuskarta,ita kanta ta tsorata da ganin launin idanuwanshi,Sun yi jawur dasu gwanin ban tsoro,tsantsar 6acin raine acikinsu,bai amsa kiran sunanshi da tayi ba,tamkar ma baisan da zuwanta ba,janyo trolley ɗinshi yayi kaitsaye ya nufi hanyar fita daga falon inda take a tsaye,tayi tunanin zai kula ta,amma ko kallo bata ishe shi ba,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni hawaye sun wanke fuskarta,Yana ƙoƙarin bi ta gefenta ya wuce,a hanzarce tayi saurin sanya hannu ta ruko damtsen hannunshi,
Muryarta na kerma tace"Ya Rafayet,idan ka tafi ni kuma fa?ya kakeso nayi da rayuwata"?
Runtse idanuwanshi yayi"ki sakarmun hannuna,tunkafin ranki ya 6aci,"A kausashe yayi maganar,
"Na yarda kayi mun duk wani hukunci da ya dace dani Saboda bani da hankali,amma dan Allah kada ka tafi ka barni,"
Tana kai ƙarshen maganar,ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi ta rungumeshi sosai tare da fashewa da matsanancin kuka,har cikin zuciyarshi yake jin kukan nata,
"Ya rafayet am sorry,bazan ƙara ba,"cikin shessheƙar kuka tayi maganar,lokaci guda kuma ta ɗauke ɗuff,a hankali ya buɗe idanuwanshi tare da sauke su akanta,tayi tighting ɗinshi sosai,kamar ance za'a ƙwace mata shi,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ya shiga saukewa,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,sakin trolley ɗin hannunshi yayi tare da ruƙota,ya ɗago da kanta daga jikinshi,da alama ta sume,fuskar nan tayi jaga jaga da hawaye,ta jigata sosai,jikinta yayi zafi sosai,tsantsar sonta da ƙaunarta ne acikin zuciyarshi,kamar ya haɗiyeta cikin cikinshi haka yake ji,
Gaba ɗaya ya sa6eta saman kafaɗarshi,ya juya da ita zuwa bedroom dinshi,a saman katafaren gadonshi ya sauketa,ya gyara mata kwanciyarta,ya kasance tana fuskantar ceilling,hijabin jikinta ya cire mata,ganin yadda take zufa,a gefe ya ajiye hijabin,ya sauko daga saman gadon ya fita palour,within minute ya dawo hannunshi ɗauke da bottle water mai sanyi,gefen gadon ya zauna bayan ya buɗe murfin ya tarfa ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi asaman fuskarta,nan take taja dogon numfashi haɗi da sauke ajiyar zuciya ajere,tunkafin ta buɗe idanuwanta,ta soma sambatu"ya rafayet kada ka tafi ka barni,bazan iya rayuwa batare dakai ba,'
Ajiye bottle din yayi saman drawer,kafin ya hau saman gadon gaba ɗaya,a dai dai saitin fuskarta yakai tashi fuskar,zuba mata ido yayi yana kallon yadda take ta sambatu
"Reesh!You know you love me, but why kike wahalar dani"?he said calmly,jin muryarshi yasa ta buɗe idanuwanta,sunyi luhu luhu cike tab da ƙwalla,
A hankali take kallonshi,yayin da shima yake kallonta,batare da kyaftawar ido ba,tamkar zasu haɗiyi junansu,saboda tsabar so,
Ganin tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka,yasa shi yin saurin toshe mata bakinta,da tafin hannunshi"its ok,u don't ave to cry,tunda gani a kusa dake,"
Lumshe idanuwanta tayi tare da sake buɗesu akan fuskarshi,zame hannunshi yayi daga kan fuskarta,
"Ya rafayet,Am really sorry,pls don't leave me,i can't survive without you,"
Kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba,
"why reesh?kin tada mun hankalina,ko bacci bana iyayi just because of you,kin fusata ni sosai,kin sanyani zubar da hawayena,'
Girgiza mashi kai tayi"Bazan ƙara ba,"
"Kin yarda cewa inasonki?ba jikinki nakeso ba?kuma kin amince zaki rayu dani a matsayin Mijinki Uban ƴa'ƴanki"?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,
Kafin tace"na aminta dakai,Na yarda da irin son da kake yi mun,kuma ina namen yafiyarka,akan misunderstanding din da muka samu,ban kyauta maka ba,its all my fault,nice ƙarama koba haka ba,kai ɗan uwana,Yayana kuma Mijina,nice a ƙasa dakai,amma ban duba hakan ba......"
Bata kai ƙarshen maganar ba,ya dakatar da ita,ta hanyar sanya yatsanshi ɗaya asaman lips ɗinta,
"Komai ya wuce a wurin,nima ina neman yafiyarki akan laifin da nayi maki,"
Kallonshi kawai take yi,ba ƙaramin mamaki Sgr ya bata,ta ƙara yarda da irin son da yake yi mata,ya canza mata ba kamar da ba,
"Nima komai ya wuce A wurina,amma pls,ka fasa tafiya U.s din,idan ma zaka tafi ƙafata ƙafarka,don bazan bari na rasaka ba,"
Ƙayataccen murmushin gefen fuska Sgr ya sakar mata,gaba ɗaya ya tafi da tunaninta,natsuwa tayi tana kallon kyakkyawan murmushinshi,ƙurawa juna ido sukayi wani irin kallon so suke jefawa junansu,
A wannan yanayin na shauƙi,Marshal Omar ya faɗo bedroom ɗin,Yazo da niyar ya lallashi Sgr akan ya fasa tafiyarshi,tun a palour yaci karo da trolley an ajiyeshi,yana zuwa bakin ƙopar ɗakin,ba zato ba tsammani ya hango romeo da juliet,abun ya bashi mamaki,Yadda ya samesu,manne da juna,sun ƙurawa juna ido,kamar zasu cinye junansu,Ƙayataccen murmushi marshal Omar ya saki,yadda kasan wani zautacce,Su suke yin soyayyar amma yafi su jin daɗinta,a hankali Ya furta Alhamdulillah Ya Allah,Na gode maka daka cikama ɗan uwana burinshi,Nima Ya Allah ka cikamin burina na ganin na mallaki hosana,A matsayin matata,Uwar ƴa'ƴana,Ya Allah ka dawwamar da farin ciki acikin zukatanmu,Ya Allah ka ƙara haɗa kan masoyan nan,ka albarkance da samun zuri'a ɗayyiba,
Bai bari sun ganshi ba,juyawa yayi da sauri yabar part ɗin,A ƙopar palourn Ya tsaya tare da zura hannu cikin aljihun wandonshi,Ya zaro wayarshi,Layin hajiya azeema ya dannawa kira,sae faman sakin murmushi yake yi,kamar wanda Akayiwa Albishir da gidan Aljanna,yafi kowa farin cikin wannan ranar,
A lokacin da kiran Omar ya shiga,Hajiya azeema na kwance bata farka daga baccin asuba ɗin data koma ba,ringing ɗin wayartane Ya tayar da ita,hannu takai saman side drawer ta ɗauki wayar,ganin sunan daya bayyana akan screen ɗin wayarna yasa ta cewa"to fa,Omar ne ke kira tunda safe,to Allah yasa muji alkahiri,
Ta ambaci hakan tare da ɗaga kiran nashi,ta manna wayar a kunnanta,
Gaisawa suka fara yi kafin tace"Ya Andace ko kuwa har yanzu ba canji"?
Muryarshi da alamun farin ciki atattare da ita,Yace"Congratulation Mommy azeema,munyi winning,"tunkafin Ya karasa maganar tace"Alhamdulillah Ya Allah,'ta ambaci hakan yayin da take miƙewa zaune,
"Omar shaƙa mun naji,wlh aƙagare nake,Meya faru,sun shirya,Sehrish ta janye maganar sakin,"
Dariya omar yayi sosai,jin yadda take ta jero mashi tambayoyi,
"Aunty ae yanzu haka daga part dinsa nake,Na same su manne da juna,maganar saki ta ƙare,Zama na har abada,"daga haka Omar ya kwashe duk abunda ya faru tundaga daren jiya har zuwa yau da safe daya same su,Ya sanar da ita,
Saboda tsabar farin ciki,Saukowa tayi daga saman gadon hannunta manne da wayar,Ta shiga yin rawa,tsantsar farin cikine akan fuskarta,
"Mommy,suna buƙatar wasu abubuwa da zasu ƙara danƙon soyayyarsu,amma kafin nan,Yanzu dai suna buƙatar lafiyayyen breakfast,don jiya ɗan uwana baici komai ba,"
Murmushi hajiya azeema tasaki kafin tace"in sha Allah,Yanzu zan tafi kitchen don in shirya masu,"
"Yawwa aunty,mun gode sosai,sai munzo yin godiya nida rafayet,"
"Haba dai,ae duk yiwa kaine,kada ka wani damu kanka,Amma ya tsakaninka da hosana?Ba tada matsala"?
Omar yace"Nikaɗai zan iya da hosana,Bata da matsala,"
Jinjina kai tayi"shikenan omar,duk da haka zan dage damtse wurin ganin na koya mata abubuwan da suka dace,"
"Thank so much auntynmu,mai son ganin farin cikinmu,"
Murmushi ta saki"yanzu bari naje na shirya masu breakfast din"
Daga haka su kayi sallama dashi,Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta ɗauke da murmushi ta ajiya wayar sama drawer,
A hanzarce ta nufi hanyar fita daga ɗakin,tana kokarin buɗe ƙopar ɗakin,Amrish ta turo ƙopar,jikinta sanye da jallabiya black colour ta yafa mayafi akanta,
"Amrish har kin shirya kenan"?
Ɗaga mata kai tayi"eh mommy,"
'Meya faru naga fuskarki kamar da alamun damuwa attare da ita,"
Cike da damuwa amrish tace"ɗazu da zan shiga ɗaki,naci karo da sehrish,fuskarta sharkaf da hawaye,wlh na shiga damu sosai,bansan inda ta dosa ba,har tambayarta nayi ko bata da lafiya,Amma bata tanka mun ba,sai dai kawai naga ta watsa da gudu..."
Hannu hajiya azeema tasanya tare da shafa gefen fuskarta"Calm down ur mind,A halin Yanzu sehrish tafi ki ƙoshin Lafiya,tana cikin farin ciki,babu abunda ke damunta,don haka kema ki kwantar da hankalinki,"
Ajiyar zuciya amrish ta sauke,haɗi da yin murmushi,
"Muje waje,bari nayiwa wani magana acikinsu sai ya kaiki gidan,"
Ta ƙarasa yin maganar,tare da yin gaba,Amrish tabi bayanta,
Suna saukowa Babban Falon,Sai ga kanal Yusif ya fito daga part ɗinsu sai faman sauri yake yi,jikinshi sanye cikin shadda brown colour,wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi,
"Yawwa yusif"hajiya azeema ce ta kwala mashi kira,A hanzarce ya juyo 6angaren da suke,ganin hajiya azeema yasa shi sakin murmushi,da sauri ya tunkari wurinta,yana ƙarasawa ya soma gaisar da ita"Ina kwana Auntynmu,An tashi Lafiya,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Lafiyalou,Alhamdulilla,Ina zaka je naga kana ta faman zumbula sauri,"
"Inaso zanje dubo jikin abokina ne,An farmakesu ne wurin aiki da aka turasu,yanzu haka yana asibitin yaya rafayet,acan aka kwantar dashi,
"Allah sarki,bawan Allah,Allah ya bashi Lafiya,"acewar hajiya azeema,
Kallon Amrish yayi,ta sunnar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta,
"Wannan fa,ina zuwa"?
Da sauri tace"Ina kwana yaya yusif,"
"Lafiya lou,"cike da jin kunyarshi amrish ta amsa mashi,
"Tana so zataje kwaso kayanta ne a gidansu,ni nace ta shirya zanyiwa wani magana yakaita gidan,"
"Ba damuwa,Zan sauketa,in yaso saina wuce asibitin,kafin ta kammala kwasar kayan,sai na dawo na ɗauketa,"
Wani irin farin cikine ya lullu6e amrish,
Godiya hajiya azeema tayi mashi"nagode ssai,Sai kun dawo,"
Gaba yayi amrish tabi bayanshi,bayan sun fita,Yace ta tsaya ya dauko motarshi,Jim kaɗan sai gashi yayi driving ɗin motar,har zuwa inda take a tsaye,buɗe motar amrish tayi kafin ta shiga daga ciki,yana a diver seat tana a gefen shi,karya kwana yayi,kafin ya fisgi motar da gudun gaske ya fuce dasu,
Lokacin da suka hau titin a tsanake yake yin driving ɗin,har suka isa unguwarsu,adai dai ƙopar gidansu Amrish yayi parking ɗin motar,juyawa ya ɗanyi gefen da take ya saci kallonta,tare da cewa
"Zan dawo na ɗauke ki,nan da 30 minutes,ina fata bazaki gaji da jirana ba,"
Murmushi ta ɗan saki tare da kallonshi,suka haɗa idonsu dashi,tayi mamakin irin sanyin kyan dake gareshi,mai matuƙar jan hankali,musamman kwantaccen sajen gefen fuskarshi,
"Nagode sosai,Ya yusif,sai ka dawo,a gaishe mun da mara lafiyan,"
Mayar mata da martanin murmushi yayi"ki kulamun da kanki,"
"Kaima haka,"tana ambaton hakan ta buɗe motar ta fuce,
A buɗe ta samu ƙopar dake jikin gate ɗin gidan,hannu tasa ta tura ƙopar ta shiga daga ciki bakinta ɗauke da sallama,murmushi ta saki lokacin da tayi arba da baba mai gadi,zaune saman tabarma,Ga tray agabanshi mai ɗauke da soyayyun kaji,Ga kayan marmari,Ga kuma lemu acikin cup hada kankara acikinsa,duniya tayi kyau,
"Assalamu akaikum,"jin muryarta yasa baba mai gadi yin hanzarin kai idanuwanshi kanta,washe baki ya soma yi,ya miƙe ya nufeta"Allah sarki Amrishi,yau kece da kanki,ashe ba rabon in rigaki zuwa,don yanzun nan nake cewa da zarar na kammala yin karin kumallona,naba furannin can ruwa,Zan shirya inzo har gidanku in duba ki,"
Zuƙunnawa amrish tayi tare da gaisar dashi,ba ƙaramin daɗi yaji ba,shi kanshi ya lura da irin sauyawar da tayi,don da lokacin bayane ko kallo bai ishe taba,balle har ta gaishe dashi,"
Bayan sun kammala gaisawa,tace"dama,nazo kwasar kayan sawata ne,"
"Oh to,bari na ɗauko maki key ɗin,"yakai ƙarshen maganar,tare da juyawa ya nufi cikin ɗakinsa,jim kaɗan ya dawo hannunshi,ruke da key ya miƙa mata,tasa hannu buyi ta kar6a kafin ta wuce cikin gidan,
Komawa baba mai gadi yayi saman tabarmar ya zauna,sae faman washe baki yake yi,duk murnar ganin amrish,A fili yace"Mutanan kirki,gashi har zun canza yarinyar nan,Kai Allah dai ya saka masu da mafificin Alkhairinsa,nima ata dalilin Yaron nan da muka taimaka,Sunyi mun alheri,mahaifinsu ya dunƙulo kuɗi har dubu ɗari shida ya damƙa mun,gashi yanzu inata Cin kaji,"sai faman sambatu yake yi,
Amrish kuwa bayan ta shiga gidan,bedroom ɗinta ta shige,ta kwashi kayanta acikin trolley,hada agogon diamond ɗin junaid ta haɗo don ta mayar mashi da abunshi,a falo ta zauna tana jiran dawowar kanal Yusif,har kitchen ta shiga ta dafa indomie ta zubota acikin plate ta zauna saman Sofa,tana ci tana tunanin Kanal Yusuf,
*Boss Bature*
Bayan tafiyar Amrish da kanal Yusif,juyawa hajiya azeema tayi izuwa kitchen,Anan ta samu abu tare da Mommy da saude suna girke girken breakfast ɗin gidan,gaisawa suka fara yi,kafin ta shiga shirya masu lafiyayyen abinci,mutun biyu ta shirya mawa,Na Omar da kuma Na Sgr,Har ɗaki taje ta kira hosana don takai mashi abinci,a lokacin suna kwance saman gadonsu,ita da jahad,Hajiya azeema tazo mata da maganar,hada bata shawarar tayi mashi kwalliya,ta sanya kaya masu kyau,dama kamar jira take yi,cike da zumuɗi ta sauko daga saman gadon ta faɗa toilet don tayi wanka,komawa kitchen hajiya azeema tayi ta ɗauki na Sgr da sehrish Ta nufi Uptairs dashi,
Lokacin da hosana ta fito daga toilet,ɗaure da towel a chest ɗinta,Jahad na zaune saman gadon ta manna wayarta akan kunnata,Da alama da junaid suke waya,akan idonta hosana,Ta zauna gaban mirror tana kwalliya,kamar aljana haka ta koma,amma tayi kyau ba laifi,matsalarta bata iya shafa janbaki ba,dam6arashi takeyi,bayan ta kammala kwalliyar,Ta shirya kanta cikin riga da skirt na lace milk colour,ganin tana ta kiciniyar ɗaura ɗan kwali ta kasa,hakan yasa jahad tayi rejecting ɗin wayar,ta sauko daga saman gadon ta nufeta,Da taimakon jahad, Hosana ta ɗaura kallabin,ta kuma gyara mata makeup ɗinta,asaman kafaɗarta ta yafa mayafinta,juyowa tayi tare da kallon Jahad tace"idan naje kai mashi abincin ya zance mashi"?
Murmushi jahad ta saki tare da cewa"bangane me kike nufi ba?ko kina nufin kalaman soyayya,"
"Eh su nake nufi,"
Dariya jahad ta ɗanyi kafin tace"yanzu lokaci ya qure,ki bari idan kika dawo sai in koya maki,"
Girgiza kai hosana tayi"a'a wlh,nidai ki rubutamun ko a paper ne,in naje sai in dinga karanto mashi,"
Fashewa jahad ta kuma yi da dariya,daƙyar ta tsagaita da yin dariyar tace"Its okey,amma karki bari yaga takardar,ki 6oyeta,"ta amsa mata da toh,
A paper jahad ta rubuta mata kalaman soyayyan,sai murna take yi,ninke takardar tayi,a cikin bra ɗinta,ta soke takardar,da gudu ta fuce daga ɗakin,
Murmushi jahad ta saki tana girgiza kai tace"Yau ya omar zaisha kallo,don nasan saiya ganota,"
Toilet ta shiga,after some minutes ta fito ɗaure da towel,jikinta duk lemar ruwa da alama wanka tayi,hannunta na ruƙe da short towel tana goge sumar kanta,
Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,batare da tambayar wanene ba,tace"Come in,"duk a tunaninta oummansu ce,
A hankali ya turo ƙopar ɗakin,jikinshi sanye da Jallabiya,batare da jahad ta juyo ta kalleshi ba,tace"Oumma,kin gamu da hosana kuwa?Yanzun nan ta gama kwalliya wai zataje kaima Ya Omar abinci,ba don na gyara mata janbakin data shafa ba,da shi kanshi ya Omar ɗin sai ya razana.....'sai surutu take yi,
Murmushi kawai junaid ke saki,Ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,sai kallonta yake yi,koda taji oumman tasu bata tanka mata ba,Sam bata kawo komai arantaba,
Cikin sanɗa junaid yake tafiya harya ƙarasa bayan jahad ya tsaya,ƙamshin turarenshi ne ya dakar mata hancinta,lumshe idanuwanta tayi tare da sake buɗesu a hankali tace"hmmmm ina nake jin ƙamshin turare mai daɗi kamar na baby junaid ɗina,
Kwantar da kanshi yayi saman kafaɗarta,aikuwa a firgice ta zabura zata gudu,yayi hanzarin ƙanƙameta sosai,cikin sanyin murya ya furta sunan da yake kiranta dashi"My juliet,its me ur Romeo,"
A ruɗe tace"Junaid kayi hauka ne,Yaushe ka shigo cikin ɗakin?yanzu idan wani ya shigo ya ganmu a haka fa?ko kaya ban sanya ajikina ba,daga ni sai towel,"
A shagwa6e junaid yace"meyasa kikayi rejecting call ɗina,batare da iznina ba?
ɗaure fuskarta ta ɗanyi kafin tace"Am Sorry my romeo bazan ƙara yin hakan ba,but pls ka tafi kada wani ya shigo ya same mu a haka,"
Maimakon ya tafi saiya ƙara ƙanƙameta sosai,yana shaƙar ƙamshin jikinta"Kamar nayi bacci Allah,kina jin abunda nake ji kuwa"?shiru tayi batare da tace mashi komai ba,Gaba ɗaya ya kashe mata jikinta,
Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Babyna,pls ka tafi,idan na kammala shiryawa,zanzo na same ka,'
ashagwa6e junaid yace"i won't go anywhere,an fa biya sadaki,ki bari kawai na taimaka maki ki sanya kayan,tun yanzu mu fara practicing kafin a shafa fatihar auranmu,A sanyamun ke a ɗakina.......'
Baikai ƙarshen maganarshi ba,Oummansu ta turo ƙopar ɗakin da ƙarfi,bakinta ɗauke da sallama,aikuwa a guje daga junaid ɗin har jahad,suka faɗa cikin toilet,tare jan ƙopar suka rufe,Tashin hankali,Tsoro yasa jahad tabi junaid toilet,Komai zai biyo baya,Ga Oumma ta shigo ɗakin..........'
*Boss Bature*
[3/19, 2:58 PM] +234 810 388 4440: Tsayawa abu tayi cike da mamaki take kallon ƙopar toilet din,don taji lokacin da aka banko ƙopar da ƙarfi aka rufeta,bata kawo komai aranta ba,tuni sun kammala breakfast din,jikinta ne baiyi mata daɗi,shine tashigo ɗakin don tayi wanka kota jin daɗin jikin nata,
Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,duk tabi ta ruɗe baiwar Allah,junaid kuwa,koda suka faɗa toilet ɗin,wata irin zufa ce ke kartowa a kan fuskar kowannansu,sun ƙurawa juna ido,
Muryarshi na kerma Yace"Jahad,dan Allah ki taimaka,ki fiddani daga cikin toilet ɗin nan,wlh idan oummanku ta ganmu atare zata sa a fasa bani auranki ne,"
Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Ya kakeso inyi junaid!duk laifinka ne,nayi maka magiya akan ka tafi amma kaƙi tafiya,yanzu duk wanda ya ganmu cikin toilet atare a irin wannan yanayin me kake tunanin zaiyi tsammani"?
Tayi tambayar tana kallonshi,fuskarshi duk a hargitse,sai faman cizon yatsanshi yake yi,
"Jahad na shiga ukuna,Wayyo Allah.....'
Bai kai ƙarshen maganar ba,ta sanya tafin hannunta,ta toshe mashi bakinshi,
Cikin raɗa tace"Kayi shiru,kada agane cewa akwai mutun a toilet ɗin,"
Shiru su kayi,yayin da suka ƙurawa junansu ido,lumshe idanuwanta ta ɗanyi batare data buɗesu ba,ba zato ba tsammani,taji ya faɗa mata,sosai ya qanqameta,hankalinta ya ƙara tashi,aruɗe ta shiga faɗin"junaid wai menene haka?wlh zanyi ihu kowa yaji muna acikin toilet ɗin nan,"
"Jahad tsoro nake ji,dan Allah ki barni a haka,bazan ta6aki ba,"yana magana yana ƙara matseta ajikinshi,tarasa yaya zatayi dashi,ga Oumma acikin ɗakin,
Batayi aune ba,taji yana goga lips ɗinshi saitin nipple dinta,kokarin kamawa yakeyi,A firgice jahad ta soma kiciniyar kwace shi,yaƙi sakinta,Ya ƙanƙameta yana faɗin"Wai menene haka jahad,so kika asirin mun ya tonu,
A ƙule tace"bana son iskanci junaid,bazaka iya hakuri a ɗaura auran ba,"
Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"ae an biya sadaki,tun yanzu mu fara practicing," haushine ya isheta,saboda ƙarya yake yi,ba'a biya sadaki ba,Yana fakewa da hakan don ya samu tadinga yi mashi biyayya,
Gartsa mashi cizo tayi asaman kafaɗarshi,abunka ga shagwa6a66en,Ya fasa ƙara tare da faɗin"Wayyo Allahna,Ta cije ni,"a gigice Jahad ta toshe mashi bakinta,ta janyoshi ta rungume don ta samu yayi shiru,
Abu dake acikin ɗakin,Abun ya ɗaure mata kai,domin kuwa tajiyo muryar mutun acikin toilet ɗin,bakin ƙopar ta nufa,ta ɗan tsaya tare da sanya hannu ta ƙwanƙwasa ƙopar"akwai mutun"
Gabansu ne ya faɗi,tuni ido ya raina fata,
"Junaid mun shiga uku,"tayi maganar,idanuwanta cike ta da kwalla
"Wai bakowa ne"?oumma ta ƙarayin tambayar,junaid yayi shiru ya lafe a ƙirjinta,jikinshi sai kerma yake yi ga tsoro ga iskanci cike dakai,
Muryarshi na kerma yace"Jahad,kice mata kece,"
Jin haka yasa jahad ta ɗanyi gyaran murya,
Ajiyar zuciya abu ta sauke tare da cewa"Lafiya naji kina ihu"?tayi maganar don ta gane wacece,
Ƙasa ƙasa da murya jahad tace"Lafiyalou oumma,na sanya ruwan zafine,ban surka dakyau ba,"
Jinjina kai abu tayi"ki ƙara surkashi mana,"
"To oumma,"
Juyawa abu tayi maimakon ta fita daga ɗakin,Sai ta zauna gefen gadonsu,Tana jiran jahad ta fito itama ta shiga toilet ɗin tayi wanka
Hannu tasa ta 6an6are junaid daga jikinta,hannu yasa tare da dafe cikinshi,ya ɗan ɗago da dara daran idanuwanshi yana kallonta,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,
Kamar wani ɗan iska,Ya kashe mata ido ɗaya,tare da zuro harshen shi yana lasar gefen le6ensa,
Abun ya bata haushi,jarabar junaid tafi ƙarfinta,ita duk a tunaninta yayi hankali tunda an rabashi da sihirin jikinshi ashe dama can tunfil azal,Ɗan iskan kanshi ne,
Harara ta wurga mashi,tare da cewa"Wlh zan fasa auren,"
Bubbuga ƙafarshi ya ɗanyi,Ashagwaye yace"wlh da nayi maki lalata,kinga dole ki amince ayi auran,"
Har sai da gabanta ya faɗi jin abunda yace,hankali atashe take kallonshi"nashiga uku junaid'
Lamarin shi ya fara bata tsoro,ƙura ido tayi tana kallonshi,jiki asanyaye tace"Junaid,kana shaye shaye,"
Girgiza kai yayi"wlh ko taba ban ta6a sha ba,"
Abu dake zaune gefen gadon tana jiran fitowar jahad,kunnuwanta suna jiyo mata ƙusƙus acikin toilet din,
"Jahad,surutun me nake ji acikin toilet ɗin nan,ke da waye"?
Aruɗe tace"babu kowa oumma,"jinjina kai abu tayi"kiyi sauri ki fito inaso in shiga,"
Rass taji gabanta ya faɗi,amarairaice ta kalli junaid"Ya zamuyi,"
"Nima kaina bansani ba jahad,pls ki nema mana mafita,"
Shiru su kayi na wani lokaci,can taga yana nannaɗe jallabiyar jikinshi,tayi tunanin wata dabara zaiyi hada saurin cewa"Junaid,ka gano mana mafita ne"
Batare daya kalleta ba,yace"fitsarine ya matse ni.....'
Tunkan yakai ƙarshen maganar,tayi hanzarin buge hannunshi"ashe baka da hankali,agabana zakayi,"
"To sai me,wlh ya matse ni,in ba so kike inyi a wando ba,"zuba mashi ido tayi tana kallon ikon Allah,
Ganin yana kokarin xame short ɗin ya curo abunshi yasa tace"Nashiga uku"!da ƙarfi tayi maganar,Abu dake zaune a ɗakin a firgice ta mike ta nufi toilet ɗin tana faman kwala mata kira"Jahad lafiyarki kuwa?wai me ke farune?tun ɗazu nake ta jin surutu acikin toilet ɗin nan,Zaman me kikeyi ne,Ya isa ace kin fito,"
Hankali atashe Jahad tace"Babu komai oumma,Yanzu zan fito,kan famfo ne ya lalace,ruwa duk ya fallatsarmin,Shiyasa kika ji ina magana,Yanzu zan gyara shi,ba wuya,"
Jinjina kai abu tayi"ok ina jiranki,"komawa tayi gefen gadon ta zauna tana jiran fitowarta,
"Dan Allah junaid,kada kayi fitsarin nan,"a ƙule yace"ji wani ikon Allah,Nace dole saikin kalleni ne,ki juya baya mana,wlh sai nayi,"da sauri ta juya mashi baya,ta kifa kanta da bango,tana jin sautin fitar fitsarinshi,abun ya bata mamaki,kwata kwata junaid baida kunya,bata ta6a tunanin haka yake ba,tabbas zata sha wahala a hannunshi,don ba ƙaramin jarababbe bane,
Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,da sauri abu ta miƙe ta nufi ƙopar tana tambayar wanene,daga waje akace"Mommyn junaid ce,"hannu tasa ta buɗe mata ƙopar fuskarta ɗauke da murmushi,gaisawa suka fara yi kafin mommy tace"bansani ba ko Azeema ta sanar maki game da tafiyarmu dubai,"
Girgiza kai abu tayi'a'a bata sanar dani komai ba,"
Mommy tace"Inaji ta mantane,Dama zamuje haɗo lefen yaran nan ne,shine muka yanke shawarar zuwa can don muyi masu siyayya,amma kafin nan zamu fara zuwa kasuwa mu fara sayen wasu kayan anan,"
Murmushi xainab ta saki"masha Allah,naji daɗi sosai,Allah yakaimu lafiya,"
"Ameen ameen,"har mommy ta juya ta kuma cewa"oh na mata,Ya jikin Sehrish?tun a kitchen naso na tambayeki,Nayi tunanin ma idan nazo nan,zan sameta,"
"A'a,suna a ɗayan ɗakin,Nima yanzu nake tunanin zuwa na duba jikinta,Ya jikin fawan?
Mommy tace"da sauƙi sosai,Yanzu bai cika son fitowa waje ba,kullum yana ƙunshe a ɗakinshi,
A ƙarshe abu tabi mommy suka tafi duba jikin sehrish,dana Fawan,'
Su jahad dake ƙumshe cikin toilet suna jin fitarsu,a hanzarce suka buɗe toilet ɗin,cikin sanɗa junaid ya lalla6a ya fuce daga ɗakin,Cikin sa'a bai ci karo da kowa ba,
Ajiyar zuciya jahad ta sauke,shaf shaf ta ɗauko kaya cikin wardrobe ta zura ajikinta,
*Boss Bature*
*Reeshraf*
Sannu a hankali bacci ya ɗaukesu,rungume da juna,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,a Lokacin da Mommy azeema tazo part din nashi,sallama ta fara yi shiru ba'a amsa mata ba,ranta ya bata cewa ko suna a cikin bedroom ne,Shiga cikin palourn tayi babu kowa,kaitsaye ta nufi wurin sofas ɗin,A saman table ta sauke masu trayn,yanke shawarar zuwa tadasu tayi,can kuma tayi tunanin yiwa omar magana,Ya kira shi a waya,don ya sanar mashi an kawo masu breakfast,
Sun yi nisa acikin baccinsu,wayar Sgr dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,a hankali ya buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci don bai ishe shi ba,akan fuskar sehrish ya saukesu,zuba mata ido yayi yana kallonta,sosai ta shige mashi,ta ƙanƙameshi,sai jan numfashi take yi,lumshe idanuwanshi yayi tare dakai hannu ya shafa sumar kanta,kafin ya manna mata kiss asaman forehead ɗinta,
"I love u.....'ya furta ƙasa ƙasa da muryarshi,har kiran yayi rejecting wani kiran Ya kuma shigowa,Hannu ya miƙa saman drawer ɗin ya ɗauki wayar,tare da duba sunan mai kiran nashi,Omar ne,picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnashi,
"How are u my own bro,"
Muryarshi a kasalance yace"Am ok,ya kake?
"Lafiya lou,jiya banji ya kuka ƙare da mutuniyar taka ba,"
Murmushi sgr ya saki,ɗayan hannunshi na acikin sumar sehrish yana wasa da ita yace"nasan duk kai ka shirya wannan,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka,
Omar yace"ae ba komai,duk yiwa kaine,"
"Tana tare dani,na samu kwanciyar hankali,yanzu haka ma kiran wayarka ne ya tashe ni,"
Cike da zolaya Omar yace"Ya maganar tafiya U.s ɗin?ɗazu nazo part ɗinka,na samu trolley ɗinka ajiye,"
"Ka fara ko"?
Dariya omar yayi"Nifa nayi tunanin yanzu haka jirginka ya sauka los angeles,"
dariya Sgr ya ɗanyi,kafin yace"don't worry ur self,tunda na samu abunda nakeso,Very soon zamu tafi,"
"Kada na takura maka,naga jiya bakaci abincin kirki ba,Ga break fast nan a palour an ajiye maku,kaida Babynka,"
Ƙayataccen murmushi sgr ya saki tare da cewa"thank u Omar,"
"Aunty azeema yakamata kayiwa godiya,duk ita ta shirya wannan,"acewar Omar,
"Okey,zanje na same ta,"ya ambaci hakan yayin da hannunshi ke asaman wuyan sehrish,yana shafa shi,laushin skin ɗinta ba ƙaramin fusgarshi yake yi ba,
"Sai anjima,but karka manta,kuyi feeding ɗin juna,hakan yana ƙara danƙon soyayya,"ya ƙarasa maganar muryarshi da alamun dariya yayi rejecting kiran,"yaji daɗin shawarar Omar sosai,don kuwa yana cikin tsarinshi,
Ajiye wayar yayi saman drawer ɗin,a hankali ya matsar da fuskarshi saitin fuskar sehrish,saitin kunnanta yakai bakinsa,cikin raɗa ya ambaci sunanta"Reesh,can u hear me"?
Shiru bata Motsa ba,hannunshi ya sanya yana ɗan shafa bayanta,yaci gaba da ambaton sunanta cikin raɗa,har sai da Sehrish ta fara mutsu mutsu zata farka,tukunna ya janye kanshi daga saitin nata,
Biji biji ta fara ganinshi lokacin da take ƙoƙarin buɗe idanuwanta,ya tasa ta gaba yana kallonta,lips ɗinta duk sun bushe,still akwai jirwayen hawaye akan fuskarta,
A hankali ta ambaci sunan shi"Ya rafayet,are u with me,"
Shafa gefen fuskarta yayi"My wife,am sorry nayi disturbing dinki ko?na katse maki bacci"?
Lumshe idanuwanta ta ɗanyi sun marairaice,
"I know you're feeling hungry,that's why na tashe ki,"ya ƙarasa maganar,tare da kai hannu ya shafi cikinta,
A hankali ta furta"Ina jin yunwa sosai,amma nafi buƙatar yin wanka,jikina duk babu daɗi,"yadda take magana tana ɗan yamutsa fuskarta,ba ƙaramin yanayi take jefashi ba,daurewa kawai yake yi,
Miƙewa sukayi zaune saman gadon ganin tana ƙoƙarin ɗaukar hijab ɗinta yasa shi yin saurin cewa"Ba anan zaki yi ba"?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,ɗaure fuskarshi ya ɗanyi alamar baiji daɗin maganarba,
"Why ba zaki yi using da toilet ɗina ba,"?
"Idan kanaso,Sai nayi,"
Ta6a bakinshi ya ɗanyi"Sai inaso"?
Girgiza kai tayi"Am Sorry,"
Ta ambaci hakan tare da saukowa daga saman gadon ta nufi toilet dinshi,ji yake tamkar yabita yayi mata wankan,amma yana jin shakkar ta6ata yanzu gudun kada a koma yar gidan jiya,ta burkice mashi tace Jikinta yake so,
Shiga toilet ɗin sehrish tayi tare da jan ƙopar ta rufe,saukowa sgr yayi daga saman gadon ya dawo bakin ƙopar toilet ɗin,ya jinginar da kanshi,don ya dinga jin motsinta,
Yana jiyo sautinta tana fadin"Assh..wash,"kamar ya faɗa toilet ɗin ya taimaka mata tayi wankan haka yake ji,
After some muninutes yaji motsinta a bakin ƙopar,komawa yayi gefen gadon ya zauna,yana jiranta,a hankali ta buɗe ƙopar,ta zuro ƙafarta kafin ta ƙarasa fitowa daga ciki,hannunta ruƙe da rigarta,skirt ɗin tajashi har saman ƙirjinta,gashin kanta duk ya rufe mata bayanta da gefen fuskarta,natsuwa yayi yana kallonta batare da ƙiftawa ba,
Tunda ta ɗago suka haɗa ido dashi,tayi saurin kawar da idonta,wani irin nauyinshi taji,
"Zan jiraki a palour,idan kin kammala shiryawa ki same ni acan,"
Amsa mashi da toh,kafin Ya miƙe ya fuce daga ɗaikin,zubawa mirror ɗin ido tayi ganin babu glass ajikinshi,bata kawo komai aranta ba,mayukanshi na jiki masu ƙamshi tashiga shafe jikinta dasu,hada turarenshi ta fesa,bayan ta mayar da rigarta,sai da ta fara ɗaukar hijab dinta ta zurata,tukunna ta fito daga ɗakin,A saman Sofa ta same shi,ya jingina bayanshi jikinta,yayin da idanuwanshi ke a lumshe,a tsanake ta samu wuri gefenshi ta zauna,kafin ta ambaci sunanshi cikin sanyin murya"Yaya rafayet,"
Buɗe idanuwanshi ya ɗanyi a hankali yana kallonta"har kin kammala,"ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Yana ƙoƙarin kai hannu yayi serving dinsu tayi saurin rigashi"Zan zuba mana,"wani irin kallon so suke bin juna dashi,zama su kayi gwanin ban shawa'a tana bashi abaki yana bata,atare suka ciyar da junansu,bayan sun kamala cin abinci,ta faɗa mashi cewa zata je ta canza kayan jikinta,tana ƙoƙarin miƙewa ya ruƙo hannunta,tare da janyota ta faɗo saman laps ɗinshi,matsa hancinshi yayi asaman suman kanta"when are u coming back"?yayi tambayar cikin sanyin murya,kafin ta bashi amsa ya kuma cewa"kona minti ɗaya kikayi nesa dani,zanyi missing ɗinki sosai,'gaba ɗaya ya kashe mata jikinta,sae faman sauke ajiyar zuciya take yi,hannayenta duka biyun suna a dafe dashi,
"Zan dawo da anjima,"
"Promise me,"ya ambaci haka yayin da yake shafa sumar kanta da hannunshi,
"Nayi maka alƙawari,"jinjina kanshi ya ɗanyi,Okey,zan zuba ido naga zuwanki,idan ma baki zo ba,Ni zanzo,don na baki maganinki"ba don yaso ba,ya saketa,ta mike tare da kai hannu ta ɗauki tray ɗin kayan abincin da suka kammala ci,a hankali take tafiya,yayin da ranta ke bata cewa yana kallonta,
Sai da takai bakin ƙopar,ta ɗan dakata dayin tafiyar,juyawa tayi don ta saci kallonshi,karaf suka haɗa ido dashi,murmushi ta sakar mashi,shima ya mayar mata da martanin murmushi na gefen fuska,dimple ɗinshi ya lotsa,juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin,
Tana tafiya tana tunaninshi sai kace ba yansu suka rabu dashi ba,tsananin ƙaunarshi take ji acikin zuciyarta,kitchen ta fara zuwa ta ajiye tray ɗin hannunta,kafin ta koma besdroom ɗinsu,kaitsaye ta faɗa saman gadon,yayin da idanuwanta ke kallon sama,A hankali ta furta"I luv u so much Ya rafayet,Mijina nakaina"
A 6angaren hosana kuwa,Lokacin da taje Kai ma Omar abinci,Cike da zumuɗi ta zabga sallama hannunta ruƙe da tray,sae faman zabga murmushi take yi,kamar wata zautacciya,kamar yadda ta saba shiga ɗakin shi ko sallama babu,a haka ta faɗa ciki sai da tashiga tukunna tayi sallamar daga baya"Assalamu Alaikum"a lokacin yana kwance saman gadonshi,hannunshi ruƙe da wayarshi,ɗagowa yayi tare da kallonta,wani irin kyau yaga tayi mashi,miƙewa yayi daga zaune yana kallonta batare da ƙyaftawar ido ba,gaba ɗaya ta tafi da imaninshi,ganin ya ƙura mata yasa ta ɗan turo baki tare da cewa"Ya omar,wai lafiya kake kallona,"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da cewa"hosana,wa yayi maki kwalliya?
"Ni nayi abunda,"
"Amma dai,ni akayiwa kwalliyar ko"?
Murmushi ta ɗan saki tare da ɗaga mashi gira alamar Eh,
Ba ƙaramin daɗi yaji ba"Ki kaimun abincin falo,Yanzu zo muci tare ,
Da sauri ta juya,tana shiga ta sauke tray ɗin a saman table,jiki na rawa ta zura hannunta cikin bra,ta zaro paper din da jahad ta rubuta mata kalaman soyayya,
Karantawa ta farayi don ta samu ta haddace wasu kafin ya fito,
"Ya Omar,inasonka so irin wanda uwa keyi ma jaririnta,kaine mutun na farko dana ji ya kwanta mun araina,nakeson kasancewa dashi na har abada,A matsayin mijina uban ya'yana,"tana cikin karantawa Tajiyo mutsu mutsun fitowarshi,A ruɗe ta nannaɗe takardar ta turata acikin bra ɗinta,
Ƙarasowa cikin falon yayi,hannu yasa ya ɗauki tray ɗin data ajiye saman table ɗin,Ya sauke shi saman carpet don suji daɗin cin abincin atare,
"Bismillah,"yayi maganar yana nuna mata wuri,da sauri ta zauna tare da lanƙwashe ƙafafunta,kamar yarda shima yayi,da kanshi ya zuba masu abincin Yace mata"mu fara ko'maƙe mashi kafaɗa tayi"Ae ni naci ya omar,kaidai kaci,"gyaɗa kai yayi batare da yayi mata musu ba,Ya soma cin abincin,
Yana kokarin cin abincin karaf suka hada ido da ita,dakatawa ya ɗanyi"Wannan kallon fa"?
Ƙayataccen murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Kai dai kawai kaci gaba da cin abincin ka,"jinjina kanshi ya ɗanyi kafin ya mayar da hankalinshi kan abincin dayake ci,
Tunani ta shiga yi,Ta manta kalaman data haddace,ganin hankalinshi baya akanta,yasa tayi sauri tura hannu ta ɗauko takardar duk ta cukuikuye,jikinta har kerma yake yi wurin karantawa,bayan ta kammala ta ninke ta mayar,
Murmushi ta ɗan saki kafin tace"Ya Omar"ɗagowa yayi tare da kallonta yana jiran jin me zatace
"Kasan yadda nakeson kuwa"?tayi tambayar fuskarta babu alamun wasa,
Girgiza kai Omar yayi"a'a saikin faɗa,"
"Inasonka sosai ya omar,irin son da uwa keyi ma ɗanta,banajin zan iya rayuwa da wani ɗa namiji in bakai ba......'
Saboda tsabar mamaki baisan lokacin daya saki cokalin hannunshi ba,ya fada cikin plate ɗin gabanshi,zuba mata ido yayi yana kallonta,
"Kaine tauraron dake haska zuciyata,dakai nake kwana dakai nake tashi Ya omar,bani da burin daya wuce in mallake ka a matsayin mijina......."
A sukwane marshal ke kallonta,abun ya ɗaure mashi kai,kamar an sanya mata radio sai zuba take yi,abu kamar na hankali,ganin ta kakare yasa ta ɗan dakata tare dacewa"masoyina meyasa kake kallona?kaci gaba da cin abincinka mana,ni kuma zan cigaba da faranta maka rai"
Shiru yayi yana tunanin taya akai hosana ta iya kalamai masu daɗi na hankali,Sam bai yarda da ita ba,
"Hosana miƙe tsaye,"yayi maganar yana yi mata nuni da hannunshi,miƙewa hosana tayi,tsaf ya shiga kallonta daga saman har kasa,don yana zargin kamar karantowa take yi,ganin baiga komai ba yasa shi cewa tayi tsalle,
Ranta ya 6aci sosai,a kule tace"Ni bazanyi ba,"
Murmushin gefen fuska omar ya saki,
"Shikenan,koma ki zauna,sannan kuma ki cigaba da fadamun daɗaɗan kalaman nan,inajin daɗinsu,"
Murmushi ta saki,cike da zumuɗi ta koma ta zauna,tana kokarin kai hannu ta zaro takardar ya kafe ta da idanuwanshi,duk tabi ta susuce,
Ashagwa6e tace"Ya omar wai menene haka?ka ƙuramun ido,kaci gaba da cin abincinka mana,"
Girgiza kai yayi"a'a,nafi jin daɗin kallonki,yayin da kike faɗamunsu,"da biyu Omar yayi mata haka,
Shuri tayi tana ta faman mazurai,domin kuwa bata iya komai ba,
"Am listening to u,My baby "yayi maganar yana kallonta,
Haushi ya isheta,daƙyar ta cigaba da cewa"yakai bunsurun dake cin ciyawar zuciyata,"
Waro ido waje Omar yayi"Hosana!ni ne bunsurun"?da sauri ta sanya tafin hannu ta toshe bakinta,tana girgiza mashi kanta"wlh Ya Omar su6ul dabaka nayi,ba haka nakeso nace ba,kaine ka tsare ni da idanuwanka,"
Harara ya ɗan jefa mata,Hannu yakai tare da ɗaukar lemu ya tsiyayashi Acikin cup,kafin ya ɗago tayi saurin Zura hannu ta ciro paper ɗin,hannunta nata kerma ta shiga dubata,da sauri ta mayar cikin bra ɗin ta ajiye,tana faman mayar da numfashi kamar wadda tasha gudu,
Ɗagowar da zaiyi A furgice Yace"hosana!kyankyaso....."tana jin haka ta miƙe a ruɗe tana kakka6e jikinta,hada kuka nan take takardar da take ta faman 6oyo ta faɗo ƙasa a cukuikuye,tuntsirewa Omar yayi da dariya,hada dafe cikinshi,ya hasala ta sosai,Ta bubbuga ƙafarta,tare da fashewa da wani sabon kukan da gudu ta nufi hanyar fita daga falon tana kuka,miƙewa yayi da sauri yabi bayanta,har ya samu ya ruƙota tare da jangota jikinshi ya rungumeta,Yana ɗan bubbuga bayanta"Am sorry,banso na 6ata maki rai ba,nasan kinyi ne donki faranta mun raina,"
*Boss Bature*
A 6angaren Amrish kuwa,Har kusan one hour tana zaman jiran Kanal Yousouf,tuni ta jima da kammala Cin abincin,ta mayar da plate ɗin kitchen,A saman doguwar sofa ta kwanta tana jiran zuwanshi,har bacci ya ɗauketa,wuraren ƙarfe ɗaya da rabi,Motar shi ta ƙaraso bakin gate ɗin gidan,Yana yin horn baba mai gadi ya buɗe mashi,A mutunce suka gaisa da junansu,saboda ya ganeshi sosai,kuma yousouf yayi mashi bayanin zuwanshi,Bayan ya buɗe mashi gate ɗin ya wuce da motar cikin gidan,parking ɗinta yayi,kafin Ya fito ya nufi cikin gidan,A ƙopar shiga falon Ya tsaya yana zabga sallama shiru ba'a amsa mashi ba,kusan sau biyar,A karshe ya yanke shawarar shiga ciki,Da sallama abakinshi ya shiga falon,Tunkafin ya ƙarasa ciki ya hango Amrish,kwance tana bacci,gaba daya mayafinta ya zame ƙasa,tsayawa yayi yana kallon kitson kalabar dake akanta,manya manya,tayi mata kyau,baisan ta yarda zai tashe ta,Tunawa da makullin motar hannunshi Yasa shi yin dabarar girgiza key din saitin kunnanta,Sautinne Ya farkar da amrish daga bacci,mutsu mutsu ta fara tana kokarin buɗe idanuwanta,duk bata Lura dashi ba,har ta miƙe tsaye ta Sauko da ƙafafuwanta ƙasa,Ta ɗaga hannayenta tana yin miƙa,Da sauri Yousouf Ya kawar da idanuwanshi,ganin yadda ƙirjinta ya fito sosai,
Sai daga baya ta lura dashi,da sauri Ta ɗauko mayafinta,ta rufe kanta dashi,
"Yaya yousouf,ka dawo,"
Batare daya kalleta ba yace"Am sorry,na barki kina ta jirana,wani uzirine ya ruƙe.ni"
"Babu komai,"ta ambaci hakan tare da mikewa ta ruƙo trolley ɗin kayanta,Gaba yayi tabi bayanshi har suka isa motar,kowa ya shiga ya zauna kafin ya tashi motar,ya nufi hanyar gida dasu,yana driving suna fira da ita,
*Boss Bature*
*Amani*
Tana cikin gyara kitchen tajiyo muryar Jahan daga falo yana kwaɗa sallama,fuskarta ɗauke da murmushi ta tunkari falon,A zaune ta same su saman Sofa,su biyu sun ɗauki wankan suits,ba ƙaramin kyau su kayi ba,dama duk in jahan zai zo zance,Atare da Ayaan suke zuwa,kamar yadda suke twins komai atare suke yinshi,
"Yau kune a gidan namu,"tayi tambayar tare da samun wuri ta zauna tana fuskantarsu,
Haɗa baki su kayi wurin gaisar da ita"Ina yini aunty,mun same ku lafiya"?
"lafiyalou,Ya kuke?ya mutanan gidan naku?Ya jikin junaid da fawan"?
Ayaan yace"Kowa yana cikin ƙoshin lafiya,marasa lafiya kuma jiki yayi kyau,".
"Masha Allah abu yayi kyau,"acewar amani,
"Bari nakawo maku abunsha"da sauri suka haɗa baki wurin cewa"a'a,bama bukatar komai,"
Dariya ta ɗanyi,ba ƙaramin burgeta suke yi ba,har magana ma wani lokacin in zasu yi atare suke yinta,
Ta lura da jahan sai faman waige waige yakeyi,
"Amal ko"?tayi tambayar fuskarta ɗauke da murmushi,
Murmushin gefen fuska Jahan ya saki tare da cewa"eh,tana ina ne?naga banganta ba"
"Bari nakira maka ita,"miƙewa tayi tare da juyawa ta nufi upstairs,
"am so eager to see her,nayi kewarta sosai,"jahan ne yayi maganar yayin da yake zaro wayarshi daga cikin aljihunshi,
Ayaan yace"In ka kwantar da hankalinka,Cikin ƴan kwanakin nan za'a shafa fatihar auranku,idan yaso saika mayar da ita madubi kayi ta kallonta,"
Harararshi jahan yayi "oh kana nufin zan aureta ne,kawai don na ajiyeta,na zuba mata ido ina kallonta?kaima ka sani wlh,"
Dariya ayaan yayi,kafin ya ƙara cewa wani abu,Amal ta sauko jikinta sanye da riga da skirt na material maroon colour,tasha uban makeup,
Da sauri jahan ya sanya tafin hannunshi Ya rufe ma Ayaan fuska,wai don kada ya kalle mashi matarshi,
Buge hannun Ayaan yayi yana fadin"Me yayi zafi?Bari na tashi na baku wuri,idan kun kammala Zancen ka kirani in dawo in ɗaukeka,"yana kai ƙarshen maganar ya miƙe tare da nufar ƙopar fita falon yana dariya,
Ƙarasowa Amal tayi,Tana ƙokarin zama ya nuna mata laps ɗinshi wai tazo ta zauna asama,waro ido waje tayi tana girgiza mashi kai"a'a kunya nake ji idan aunty amani ta gani fa,"
Zare mata ido yayi"Ina wasa dake?zaki zo ki zauna ko sai ranki ya 6aci,"sam babu wasa a fuskarshi,dama haka take fama dashi,baida kunya ko kaɗan,ita kuma kunya gareta sosai,kuma sam bai iya soyayya ba,yafi ƙwarewa a harkar romance,ta ko'ina jahan yafi ƙarfinta,lalla6awa kawai take yi dashi don tana sonshi,
"Ni bazan zauna asaman cinyarka ba,Amma zan zauna a gefenka,in kuma hakan baiyi maka ba,ni zan koma ciki"idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
Sassauta muryashi yayi"its ok,don't cry nima wasa nake maki,zoki zauna,"gefenshi ta zauna ya tsareta da idanuwanshi,sae faman gyara mayafinta take yi,saboda kallon ƙurullan da yake yi mata,.
"Baki yi farin ciki da zuwana bane"cikin sanyin murya yayi mata maganar,
"Yakamata ki saki jiki dani,nan bada jimawa ba,za'a ɗaura mana aure,ko baki sona ne"?
Ƙasa kasa da murya tace"inasonka mana,"
"To meyasa ko kallona bakya yi"?
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta,matsawa yayi tamkar zai shige mata,ruƙo hannayenta yayi cikin nashi,
"Amal,"ta amsa mashi da na'am,
"Yakama ki koyi zama dani,tun yanzu in ba haka ba,zakisha wahalata,Kin cika kunya,ni kuma banason mace me kunya,its better ki cire kunyarki wurin nuna mun soyayya,kinji ko"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Shafa gefen fuskarta yayi"faɗamun idan munyi aure,a first night ɗinmu,me zaki yi mun,"shiru amal tayi tana tunanin amsar da zata bashi,hasalima bata gane me yake nufi ba,
"Kinyi Shiru bakice komai ba"?
Cike da jin kunyarshi tace"Ni bansan me kake nufi ba,"
Dai dai satin kunnanta yakai bakinsa tare da cewa"I mean...idan zamuyi sunnah,"
Still bata gane me yake nufi ba,
"Ya jahan ni ban fahimce kaba,"
Takaicine ya isheshi,a ƙule yace"oh,kina nufin bakisan Komai ba?a haka zamuyi aure?that's impossible,"
Ganin yadda ya 6ata ranshi yasa tace"Am sorry,wlh bansan kan me kake magana ba,"
"Gaskiya idan har kinason mu zauna lafiya dake,to ki koyi yadda zaki farantamun kinji ni ko"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
"Idan na tafi,kice ma Auntynki ta koya maki yadda zaki kwanta da mijinki,ina fata kinji ni"?
Gaba ɗaya ta dabarbace,Amma tabbas bata gane me yake nufi ba,
"Zan faɗa mata,"jinjina kanshi yayi yanzu naji magana......'ya jima a wurin Amal,kafin yayi masu sallama,ya kira ayaan ya ɗaukeshi suka koma gida,