Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 123


Health College

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 123

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 123

 ABBAN SOJOJI* 💖

                                 💖💖

                            💖💖💖

                       💖💖💖💖

```The father Of Soldiers```

          *🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Story 

       &  

       Written 

                   by 

      *_Hafsat Bature_*

          ~(Boss Lady)~

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Dedicated to my beloved sisters. 😍   

Proud Of My First Novel💋

_Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina,Sannan kar a kuskura a haɗamun document,Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3 yayi mun magana ta whatsapp 08103884440_

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

Baccine ya fara ɗaukarshi,a hankali ya ƙarasa hawa saman gadon ya kwanta gefenta,duk bata sani ba,saboda baccin da yayi awon gaba da ita,bai jima da kwanciya ba,bacci ya ɗaukeshi,can cikin bacci ta dinga jin numfashinshi asaman neck ɗinta,mutsu mutsu ta soma yi zata buɗe idanuwanta,ta ko'ina taji tamkar an ɗaureta,gaba ɗaya sumar kanshi ta lullu6e idanuwanta,ƙoƙarin raba jikinta ta soma yi da nashi,kiciniyar data rinqayi ne tana kokarin janyeshi,Yasa shi farkawa,shi kanshi baisan ya akai suka haɗe da juna ba,sun manne sosai,gaba ɗaya ta shige ƙirjinshi,hannunshi na dafe da ita,


Fashewa tayi da matsanancin kuka,na takaicin haɗa jiki da sukayi,ga baƙin cikin hannunshi daya sanya abayanta,ta kasa janyewa,saboda nauyi,ta haɗa uban gumi akan fuskarta,


Daƙyar ya iya buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci,ɗago da kanshi yayi,ya kasance tsinin hancinshi na gogar forehead ɗinta,janye hannuwanshi yayi daga saman bayanta,karaf idanuwanshi suka sauka akan surar jikinta,rigar ta cukuikuye ta nannaɗe,Fararen cinyoyinta sun fito waje,daga sama rigar ta zame,har ta sauko under boobs ɗinta,fatar jikinta har wani salƙi take yi saboda kyau,


Kasa janye idanuwanshi yayi daga kan jikinta,Sam bata lura ba,tana ta shessheƙar kuka,hawaye sun wanke fuskar sae kace ta haɗa jiki da wanda ba muharraminta ba,


Lokacin data buɗe idanuwanta sosai,taga yadda ya zuba mata ido batare da ƙyaftawa ba,a hanzarce Ta soma bin jikinta da kallo,ranta yayi mugun 6aci duk a tunaninta shiya yaye mata rigar,don ya biya buƙatarshi,jikinta har kyarma yake yi wurin sanya hannu ta janyo rigar ta mayar da hannunta,taja can ƙasan ya rufe ƙafafun,


Shi dai baice mata komai ba,zuba mata ido kawai yayi yana kallonta,

  Cikin shessheƙar tace"Dama abunda kakeso kenan,ina jinya ma ba zaka ƙyaleni ba,"

  Aruɗe Sgr ke kallonta don bai fahinci inda zancen nata ya dosa ba,wani irin kallon tsana take jifarshi dashi,Saukowa tayi daga saman gadon,da gudu ta fuce daga ɗakin tana kuka,


Runtse idanuwanshi yayi tuni sun cicciko tab da kwalla,ta harzuƙashi sosai ranshi ya 6aci,sai daga baya ya gane me take nufi,hannu yasa ya daki mattress din,Zuciyarshi sai tafarfasa take yi,


Cusa hannunshi yayi acikin sumar kanshi yana cakuɗata,har lokacin bai buɗe idanuwanshi ba,sai faman cizon le6ensa yake yi,har sai da ya fasa shi,


Almost 15 mins,kafin ya sauko daga saman gadon ya nufi hayar fita daga ɗakin,Lokacin daya fita,Bai sameta ba,tuni ta shige bedroom ɗinsu,ta faɗa cikin toilet ta rufo ƙopar,wani irin ƙululun baƙin cikine ya tsaya mata aranta,aduk lokacin da ta tuna cewa Sgr ba sonta yake yi ba,Jikinta yake so,shiyasa har ya gaza hakura ta samu sauƙi yazo yana neman ƙara yi mata illa,hakan yasa ta ƙara jin tsanarshi acikin zuciyarta,a jikin ƙopar ta zuƙunna tana shessheƙar kuka,


Jiki a sanyaye Sgr ya wuce upstairs,kaitsaye yana shiga bedroom ɗinshi,Ya zube ƙasa saman guwowinsa,Ya kwantar da kanshi agefen gadon,Batare daya hau saman gadon ba,wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyarshi,yayi mamakin dabai iya tsawatar mata ba,lokacin da take gaya mashi maganar nan ba,Ƴar ƙaramar yarinya tana shirin Zautar dashi,ta ko'ina ta gama dashi,ta kanainaye dukkan wani sashe na zuciyarshi,


Acikin wannan yanayin Omar ya same shi,yazo tashin shi sallar asuba,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,A sukwane ya tsaya a ƙopar ɗakin yana kallonshi,still Yana zuƙunne saman guiwowinsa,ya kifa kanshi saman gadon daga gefe,sumar kanshi duk ta rufe kanshi,


A hankali Omar ya ƙarasa cikin ɗakin,zugunnawa yayi agefen Sgr,cikin sanyin murya ya ambaci sunanshi"Rafayet,"shiru bai amsa mashi ba,hannu yasa ya ɗan bubbugi shoulder ɗinshi,Sai lokacin Sgr ya amsa mashi"na'am,"

  Xama Omar yayi tare da janyoshi zuwa jikinshi,a saman kafadarshi Sgr ya ɗaura kanshi,

  "Meya faru ne"?

Shiru bai amsa mashi ba,

  "Plss tell me what's wrong with u?Meya hanaka bacci?meyasa kayi kneeling?

  Dogon numfashi yaja kafin yace"Omar,she's trying to kill me,bansan me na mata ba,ta tsani koda kallo na,Why zata yi mun haka?sai da ta bari ta saba mun da kanta sannan zatayi mun Illa"

  Tsananin tausayinshi ne ya kama Omar,don ba ƙaramin jiki yake ji ba,tun daga kan yarda yake magana,nunfashinshi na fita da huci....'

  "Pls rafayet,just be strong,har yanzu fa ita matarka ce,Mallakinka,so bai kamata kana sanya damuwa ba akanta,"

  "Omar,ba zaka gane bane....'

Shafa Sumar kanshi Omar yayi"Ka kwantar da hankalinka,zanyi magana da ita,"

  Daƙyar ya samu ya lalla6a Sgr,ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya dawo ya shirya cikin jallabiya,jikinshi duk ba daɗi,tare da Omar suka tafi masallaci,


Bata fito daga cikin toilet din ba,Sai da tayi alwala,tukunna ta fito tana faman ɗan gyasa ƙafa,Still bata daina zubar da hawayenta ba,

  "Sehrish!"oummansu ce ta ambaci sunanta,firgit tayi tare dakai idanuwanta kan oummansu tana kallonta,zaune take saman gadon bata jima da farkawa ba,

  "Lafiyarki kuwa?yaushe kika shigo ɗakin?a ina kika kwana ne"?

  Cikin sanyin murya tace"daga ɗakin aunty azmee nake,acan na kwana,"

  "Ya jikin naki"?tayi tambayar a yayinda take saukowa daga saman gadon,Ta nufi inda sehrish take a tsaye,"da sauƙi Oumma,"rungumota abu tayi ajikinta,

  "Allah ya baki lafiya rishi ɗina,na damu sosai akan halin da kike ciki,"

  Sosai sehrish ta ƙankameta"Oumma,dan Allah ki tayani da addu'a,Akan Allah ya yaye mun damuwata,"

  "Wata irin damuwace wannan?ko zan iya sani"?shiru tayi tana tunanun amsar da zata bata,

  Jin haka yasa abu ta gane cewa bataso ta faɗa mata ne,

  "Shikenan,Zan tayaki da addu'a,kema kuma ki dage da yin addu'ar,"ta ƙarasa maganar tare da sanya hannu ta raba sehrish daga jikinta,suka dan zauna gefen gadon,

  Zuba mata ido abu tayi tana kallonta,maganar da abusufyan ya sanar da ita take tariyowa acikin kanta na cewa Sehrish tana da aure,taso suyi maganar da ita,Amma ta kasa,ta zuba mata idone har zuwa lokacin da Sehrish ɗin taso ta sani,don ta lura 6oye mata take yi,

  "Kinsan wani abu"?

Girgiza kai sehrish tayi"A'a"

Murmushi abu ta ɗan saki kafin tace"Lokacin da mahaifinku ya nuna yana sona nayi matuƙar yin mamaki sosai,Saboda ni bakowa bace,mata dayawa suna sonshi,Suna rubibinshi kamar suyi hauka,Kuma abunda zai baki mamaki waɗannan matan dake sonshi,Sunfi ni komai,gasu ƴa'ƴanmasu kuɗi ni kuma ƴar maigadi,Amma a haka Ya nace ya like yace dole saini,Ni kuma saboda kafiyata da taurin kai irin nawa,Sai zuciyata ta dinga saƙa mun cewa yana mu'amala da mata don kawai ina ganinshi atare dasu shiyasa na fara zarginshi,ashe bansani ba nayi kuskure,sau dayawa muna samun dama a rayuwarmu sai muyi watsi da ita,kuma sai daga baya muzo muna danasani,Na yanke ma mahaifinku hukunci batare dana tabbatar da abunda nake zargi akanshi ba,wanda silar hakan na jefa rayuwata cikin haɗari........"dakatawa abu tayi tuni hawaye sun soma sauka daga kan fuskarta,Sehrish kuwa tunda Oummansu ta soma maganar nan,ta natsu tana sauraronta,

  "Ba'ason yankewa mutun hukunci cikin sauri,batare da an tabbatar da abunda ake zargi akanshi ba,Akwai buƙatar yin bincike sosai,hanyoyi dayawa da zaka iya jaraba mutun kafin ka yanke mashi hukunci,Wanda ni banyi tunanin yin hakan ba,A wannan lokacin,kawai idona ya rufe saboda kishi,nayi wasa da damar da nake da ita,Sai gashi nazo ina danasani mara amfani....."kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,Jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,Sai ta dinga jin maganar oummansu tamkar da ita take yinta,wasu siraran hawayene suka soma sauka akan fuskarta,

  "Ita dama sau ɗaya take zuwa ma mutun,da ace a wannan lokacin nayi amfani da damar da nake da ita,da ban jefa rayuwata cikin hatsari ba,da kuma rayuwar ƴa'ƴana,sai gashi ata dalilin hakan Har gidan mahaukata aka kaini,ni nasan bankyauta ma rayuwata ba,Mutanan da su kayi mun halacci na butulce masu,mutumin dayasoni ya qaunace ni,duk da matsayina na ƴar maigadi,hakan baisa ya ƙyamace ni ba,wlh danasani bata da amfani......"

  Cikin shessheƙar kuka Sehrish tace"dan Allah Oumma kidaina tuna abunda ya wuce,banason ina ganin hawayenki,"

  Girgiza kai abu ta ɗanyi kafin tace"indaina tuna abunda ya wuce?baƙya tunanin wannan zai zama darasi ga ƴan baya?waɗanda Allah yaba ma dama irin tawa suke ƙoƙarin yin watsi da ita....."

  Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,gani take kamar oummansu tana yi mata gargaɗine a fakaice,duk da tasan batasan abunda ke wakana ba,Amma tasha jinin jikinta,

  "Don me ake bamu tarihin Annabawa da waɗanda suka zo kafin mu?Ba don muji daɗinshi ba kawai face don muyi koyi da kyawawan dabi'unsu da halayansu,mu kuma ɗauki darussan rayuwa acikinsu,"

  Ajiyar zuciya sehrish ta sauke,tare da sanya tafin hannunta asaman fuskar oummansu tana share mata hawayenta,

  "Hakane oumma,kin faɗi gaskiya,"

Murmushi abu tayi"banaso kuma kuyi irin kuskuren da nayi,shiyasanya nake faɗa maki wannan,"ta ƙarasa maganar tare da wuce wa ta gefen Sehrish ta nufi toilet tana faɗin"Ki tada su hosana da jahad,su tashi suyi sallah,"

  "To oumma,"abu na shiga toilet,hakanan tadinga jin gabanta na faɗuwa,kalaman oummasu sunyi matuƙar ta6a mata zuciyarta,hankalinta ya tashi ba kaɗan ba,kokwanto ta shiga yi Akan Sgr,Gaba ɗaya ta rikita kwakwalwarta,tayi zurfi acikin tunaninta Muryar Jahad ta katse ta"My Own sis!"firgit tayi tare da juyawa tana kallon Jahad,dake ƙoƙarin miƙewa zaune,

  "Lafiya naganki zaune kamar kina acikin damuwa"?

  Da sauri tace"babu komai,Oummace tace na tashe ku daga bacci lokacin sallah yayi,"

  "Ya jikin naki"?

"Jiki Alhamdulillah,"

Murmushi jahad ta ɗan saki tana satar kallonta,

  "Na nemeki banganki ba,"

"Ina ɗakin aunty azmee ne,"

  Jinjina kai jahad ta ɗanyi"dama saida raina ya bani cewa kina acan,naso nazo,amma dare yayi sosai ga bacci daya fi ƙarfina,"

  Kafin sehrish tace wani abun,Oummansu ta fito daga cikin toilet,fuskarta da hannunta duk lemar ruwan alwalan da tayi,


"Xaman me kuke yi ne"?tayi tambayar tana kallonsu,miƙewa sehrish tayi,Jahad kuma ta sanya hannu tare da janye bargon jikin hosana,kafin ta ɗan bubbuga hannunta"Get up hosana,Time ɗin sallah yayi,wai bazaki tashi ba "


Rai a6ace hosana ta buɗe idanuwanta a ƙule take kallon Jahad,kamar ta shaqota,

  "Oummace tace atasheki,"

Zumburo baki tayi batare data ce komai ba,ta tsani atada ta daga bacci,


Batare da 6ata Lokaci ba,kowannasu yayi alwala,suka zumbula hijabai ajikinsu tare da kabbara sallah,


*Boss Bature*


Bayan dawowarsu daga masallaci,abusufyan tare da dr harris suka nufi ɗakinshi,kamar yadda ya nemi yin magana dashi,daga gefen gadon suka zaune suna fuskantar juna,

  "Naji kace kana son magana dani,menene"?

  Murmushi abusufyan ya saki batare dayace komai ba,.  

  Harris yace"Hmmm na ganoka,halan kana son yi mun magana akan zainabu abu ne?Ae gwaggo ta faɗamun cewa zaka mayar da matarka,nace ashe da rabon gaurancin abusufyan ya ƙare......"cike da zolaya yayi maganar,

  Dariya abusufyan yayi"hmmm,ae gwaggo ta sanar dani cewa,kaima zaka angwance da saudatu,wlh naji daɗi sosai yarinyar akwai hankali,"

   "Ni fa da farko nayi tunanin gwaggo zata hanani auranta,kasan basu jituwa ita da saudat,yadda kasan Tom and jerry haka suke acikin gida"harris ne yayi maganar yana dariya,

Abusufyan yace"Allah sarki gwaggo,inata so in tambayeka game da rashin lafiyarta,Ana samun cigaba ko kuwa har yanzu sai a hankali,Duk da naga lafiyalou muke magana da ita....  "

Tunkafin yakai ƙarshen maganarshi Harris yace"Gwaggo fa ta samu lafiya,.

  Cike da mamaki abusufyan yace"Kai haba"?

  "Wlh kuwa,Lafiyarta qalou,garass take kallon kowa,Babu wani ta6in hankali atare da ita,Ae gwaggonku Allah ya bata Lafiya,ita da kanta take faɗamun cewa taji sauƙi,tana cikin hankalinta,"

  Wani irin farin cikine Ya lullu6e Abusufyan,har baisan lokacin daya mike cike da zumuɗi ba,yana kokarin kama hanyar barin dakin don yaje ɗakin gwaggonsu,

  Ruko jallabiyar jikinshi Harris yayi"ina zuwa?ba kace zamuyi magana ba"?

  "Ba zaka gane ba,inaso naganta ne,ka taso mu tafi acan sai muyi maganar atare,"


Fuskar harris ɗauke da murmushi ya mike suka fita ɗakin a tare,


A ƙopar ɗakin gwaggon katsina suka tsaya,abusufyan ne ya kwankwasa ƙopar dakin,kusan sau uku yana kwankwasawa, kafin suka ji tace"Wanene"

  Har suna haɗa baki wurin cewa"Mune,"


Buɗe ƙopar ɗakin gwaggon katsina tayi,jikinta na sanye da riga da zane na jar atampa,ta kifa ɗaurin ɗan kwali akanta,koda tayi arba da abusufyan sai tasaki murmushi,


   Cike da tsantsar farin ciki Abusufyan yace"Gwaggo wai dagaske kin samu lafiya"?


Kallon Harris tayi"bana ce kada ka sanar dakowa ba"?jin haka yasa abusufyan ya rungumeta yana dariya,

  "Alhamdullillah Ya Allah,I can't hide my happiness gwaggo,"

  Shafa bayanshi tayi"Abusufyan ɗina,kaga yadda Allah ke ikonsa ko?Rana ɗaya kawai na farka batare da haukan nan da nake fama dashi ba,Allah ya yaye mun,"idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,janye jikinshi yayi daga nata,

  Ruƙo hannunta yayi suka shiga daga cikin ɗakin,harris yabi bayansu sai faman sakin murmushi yake yi,saman kujera Harris ya zauna,Abusufyan da gwaggo suka zauna gefen gadon,har lokacin hannunshi na rike dana gwaggo,salati suka fara yiwa Annabi muhammad(S.A.W),kafin daga bisani,Gwaggo tace"Allah yasa inji wani cikinku ya faɗi ma wani cewa naji sauki,Yasin saiyaji ajikinshi,"


Fashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu,harris yace"Saboda me bakiso asani mommyna?wannan fa abun farin cikine,"

  Girgiza kai tayi"A'a,banaso na canza daga yadda nake,inajin daɗin barkwancin da nake yi,Ina sanya mutane nishaɗi,Nima kuma ina samun nishaɗi,koda ace zasu sani ba yanzu ba,Ku bari sai bayan an ɗaura auran kowannanku,"

  Abusufyan yace"Duk yadda kikeso haka za'ayi gwaggonmu,babu wanda zaiji wannan maganar,amma fa zan sanarwa abu,don kuwa tana son yin magana dake sosai,"

  Ƙayataccen murmushi gwaggwon katsina ta saki"Shikenan,ka sanar da ita,Don nima inason magana da abu sosai amma bayan ita,banaso kowa ya sani,"

  Bayan sun ɗanyi shiru na wani lokaci,kowa fuskarshi ɗauke da tsantsar farin ciki,


"Gwaggo,dama akwai maganar da nakeson nayi dake,dana yanke shawarar inyi maganar da harris,amma tunda naga kinji sauki zaifi kyau muyi maganar nan atare,"a tsanake yayi maganar,.  .

   Mayar da hankali tayi akanshi"Ina sauraronka,

   "Dama game da gidan nan ne dake a kano nasarawa g.r.a,nayi laifi ban sanar dake ba,tunda na amshi key din a wurin harris,lokacin da muka je kano,neman abu,mun zauna a gidan,Da zamu dawo kuma sai na mallaka ma Malam nura shi,da niyar idan nadawo muka haɗu zamuyi magana inyaso ko siyarmun da gidanne sai ayi,tunda ba mallakina bane,Gadon Harris ne......."

  Tunkan ya kai ƙarshen maganar dr harris yace"Da ace nasan wannan maganar zakayi wlh da ban 6ata Lokacina wurin sauraronta ba,Haba abusufyan menene aciki don kayi kyauta da gidanmu,Mutanan daka ba wannan gidan sunyi mana halaccin da bazamu ta6a mantawa ba,sun taimaki rayuwar ƴa'ƴanmu,kuma sune silar da aka agano inda Zainab take,Ni inaga kamar kanason nuna banbancine atsakanina dakai........"ranshi a6ace yake maganar,


Murmushi kawai abusufyan yayi yayin da yake kallonshi,Ya harzuka sosai,dama saida ranshi ya bashi cewar hakan zata biyo baya,

   "Allah ya huci zuciyarka,ɗan uwana nakaina,Nima badon naso nayi maganar ba,Sai don in sauke nauyin dake akaina,don nasan cewa gidan ba gadona bane,Naka ne,kuma nayi kyauta dashi,batare dana nemi iznin ɗaya daga cikinku ba"

   "Abusufyan kenan,Ni dariya ma ka bani,musamman daka ce inyaso ko kuɗine ayi mashi ka biya,Nace sannu ko"?gwaggoce tayi maganar tana hararanshi,

  Sunnar dakai ƙasa yayi yana dariya,cike da jin kunyarta,

  Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"Akwai takardun gonakina dake a wurin dankama,guda uku,Na Mallaka masu ita,idan mun koma za'a ɗauki takardun nan a damƙa masu a hannu"


Tunda ta soma magana,Abusfyan ke kallonta,Tsabar farin ciki bakinshi yaƙi rufuwa don murna,


Tana kai ƙarshen maganarta,Dr harris yace"Nima kuma,Na ɗauki nauyin karatun ɗansu sadeeq,tun daga secondry har ya kammala Jami'a,a duk inda yakeso koda ba'a nan kasar ba,sannan mahaifiyar yaron,zan bata miliyan biyar,taja jari dasu,"


Daɗi kamar zai kashe abusufyan,baisan lokacin daya rungume gwaggo ba"nagode sosai da irin ƙaunar da kuke nuna mun da kuma jinina,Allah yabar zumunci atsakaninmu daga nan har gidan Aljanna....."sosai abusufyan ya shiga yi masu godiya,duk da sun hanashi,sun jima a ɗakin gwaggon katsina suna fira,har sai da gwaggo ta shigo ta sanar dasu cewa an shirya masu breakfast tukunna,Suka baro ɗakin a tare da gwaggo


*Hafsat*


Tunkafin ta fito daga cikin toilet tajiyo muryoyinsu Khadija da Nafisat suna fira,la6ewa abakin ƙopar toilet ɗin tayi tana sauraronsu,

  "Nifa abunda yafi bani mamaki,Dana ji Ammi tace,Itace wadda Hamma  rafayet zai aura,abun ya girgizani,Nace ashe yana kula mata"?khadija ce tayi maganar,

  Nafisat tace"Ae bake kaɗaiba,nikaina abun ya bani mamaki,Mutumin nan fa lokacin dayazo damaturu,duk kyawun ƴan matan family ɗinmu,ko kallo wannan basu ishe shi ba,balle aje ga magana,Gaskiya yarinyar nan Allah ya bata,Ƴar baiwace ita,jinin nasarace,Wlh da ace nice ita,Yadda yake da farin jinin nan,Sau da ƙafa zanbi shi,ko musu bazan yi mashi ba,"

  Hafsat dake yi masu la6e,sae faman tiƙar dariya take yi,

  "kinga kullum sainaje gaishe shi,ko Allah zaisa mu haɗa ido dashi in samu shiga,Amma ɗan ta halikin nan gaisuwarma daƙyar yake amsa mun,"acewar khadija,cike da takaici tayi maganar,

  Nafisat tace"Yo ba dole yayi rowar muryarshi ba,in yana magana yadda kikasan ana busa sarewa don daɗinta...  "


Surutunne ya ishi hafsat,Hannu tasa ta buɗe kopar ta fito,Suna ganinta da sauri suka rufe bakunansu,Gaba ɗaya suna xaune saman gadon,sun lankwashe kafafuwasu,Zaman cin tuwo sukayi,

Girgiza kai hafsat tayi"Allah ya shiryeku,Shiyasa dayawa mata suke rasa mijin aure,Saboda Ruwan ido,Yanzu duk kyawun Hamma adam da Osman baiyi maku ba,saboda haɗama ko"?

  Ƙumshe dariya sukayi,batare da Sun tanka mata ba,

    Jin ringing ɗin wayarta ne yasa tayi sauri juyawa ta nufi mirror hannu tasa ta ɗauki wayar,My daddy,Shine sunan daya bayyana akan screen ɗin wayar,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta,

   "Assalamu alaikum,Daddy,"

On the other hand Ishaq yace"Wa'alaiki salam daughter,Ya kike Ya hutu"?

  "Lafiya lau Alhamdullilah,"tayi maganar,a yayin da take zama saman kujerar dake gaban madubin,

   "Shiru baki dawo ba,ko kin manta da aikin ki ne"?

  "A'a daddy Gobe insha Allah xan dawo,naji daɗin zaman gidanne cikin ƴan uwana,"

  "Kada ki damu,yanzu dai goben ki dawo gida,tunda nan bada jimawa ba,zamuzo bikinsu Omar tare,Hada ma Auntynki "

  Murmushi hafsat ta saki"Shikenan zan dawo goben"

  "In kuma kina da wanda kikeso,ki fadamun kinga sai a haɗa auranki danasu Jahad,ayi a wuce wurin,"

    Aɗan shagwa6e tace"Ae bani da saurayi yanzu,nadaina kula kowa "_

Ishaq yace"Zanyiwa daddy magana,Ya sama maki Miji,sai a haɗa auranku,"

   Bubbuga ƙafafunta tayi kamar tana agabanshi"ni banason auran haɗi Allah,nafison in auri wanda ke sona nima nakeson shi,"

  "Allah ya baki Miji na gari daughter,I will keep praying for u,"

  "Ameen daddyna nakaina,"

  Shiru suka ɗanyi na wani lokaci,Kafin yace"Ya jikin Mommyn naki"?

  "Da sauƙi,Ae jiya munyi waya da ita,ta kirani da layin ɗaya daga cikin likitocin dake kula da ita,tama faɗamun cikin satin nan za'a sallameta,"

  "Jiki yayi kyau kenan,To Allah ya ƙara mata Lafiya,".  

  "Ameen daddy,mungode ssai,Allah ya saka da alheri,"

  Sun jima suna waya,kafin su kayi sallama,Ta kira Layin Hayaam......'

  Tana fara ringing Hayaam ta ɗaga kiran,bayan sun gaisa Hafsat tace"Aunty hayaam,tunda safe nake ta kiran Layinki tana ta ringing baki ɗaga ba,"


"Na sanya wayar silent ne,dayake naje makaranta ne,"

  "Dama inaso na sanar dake cewa,Mommy na nan zata dawo gida,An kusa sallamarta,"

  Muryar hayaam da alamun farin ciki tattare da ita tace"Alhamdulullah,Amma naji daɗi sosai,nayi farin ciki,Ya mutanan gidan?

  "Suna nan cikin ƙoshin Lafiya,Ae zakuzo bikinsu yaya Omar ko,"_

  Shiru hayaam ta ɗanyi kafin tace"Anya!"

  "Dan Allah aunty hayaam kuzo,Gagarumin biki za'ayi,Kuma hada fa Amal ma,Kodan ita yakamata kuzo,tunda ƴar uwarku ce,"

  "Allah ya bamu ikon zuwan,"

  "Ameen,in sha Allah ma zakuzo,"


Sun jima suna waya kafin daga bisani,Sukayi sallama,

  

*Boss Bature*


Wuraren ƙarfe shida na marece,Ya mu'allim yazo gidan domin duba jikin junaid,tun bayan da yayi parking ɗin motarshi,adai dai lokacin Kanal Yusif da Abba suke ƙoƙarin fitowa daga entry din falon,Suka yi arba dashi,Yana sanye cikin shigar nan tashi ta Larabawa,sai ƙamshi ke tashi daga jikinshi,fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,

  Mika mashi hannu abba yayi suka gaisa tare da rungume juna,"Nayi farin ciki sosai da zuwanka,Dama junaid ya addabe ni da tambayarka,Har cewa yake yi shi dai ayi mashi kwatancen gidanka Yaje ku gaisa"yayi maganarne bayan sun raba jikinsu,

  "Allah sarki,junaid Ya jikin nashi,wlh nima nayi kewarshi sosai,Shiyasa na gaza hakura,"Ya kai ƙarshen maganar,tare da miƙawa Kanal yusif hannu suka gaisa"sannu zuwa,ya gida ya aiki,"

  "Alhamdulillah,Yusif Ya mai jiki"!yayi tambayar yana kallonshi,

  Yusif yace"mai jiki da sauƙi,Yana nan yanzu ba inda bai zuwa da ƙafafunshi,don da ace yana da mota da ba abunda xai hana ka ganshi ƙopar gidanka,"

  Dariya suka saki gaba ɗayansu,Abba yace"bismillah mu shiga daga ciki,"


Atare suka nufi falon Ya mu'allim na a tsakiyarsu,lokacin da suka ƙarasa cikin babban falon,mutun uku suka samu zaune suna fira,Major general osman tare da Adam da Najeeb,miƙewa sukayi ganin abbansu,Gaishe dashi suka yi kafin suka miƙa ma Ya mu'allim hannu ɗaya baya ɗaya ya gaisa dasu,daga bisani kowannasu Ya zauna suka ci gaba da firarsu


Hannu abba yasa cikin aljihun wandon jikinshi ya lulubo wayarshi,Mommy ta dannawa kira,tana fara ringin mommy ta ɗaga kiran,

   "Kina ina ne"?

 "Na shiga wurin azeema ne,"

  "Okey,Ya mu'allim ne yazo,muna buƙatar abunsha,"

  Amsa mashi tayi da toh"Gani nan zuwa,"daga haka yayi rejecting kiran,tare da mayar da hankalinshi kan Ya mu'allim

   "Yakamata ka gayyace mu zuwa gidanka,tunda mun zama ɗaya,ko ba haka ba"?yayi tambayar yana kallon su Yusif,

  "Hakane daddy,abunda na lura dashi,baya son sakewa acikin gidan nan,kuma kullum zaizo shikaɗai yake zuwa,banda ya'yanshi,"acewar yusif,

  Murmushi ya mu'allim ya ɗanyi kafin yace"Bani da ya'ya,"

  Abba yace"Karfa kace mun baka da aure"?

  Dariya yayi batare daya ce komai ba,Osman yace"Haba ya za ace baida aure,Yadda yake malamin nan kyau ace yana da mata huɗu cuf,Ya cike sunnah kenan,"

  Sunnar dakai ƙasa ya mu'allim yayi yayin da yake wasa da key ɗin motarshi,

  Abba yace"Kayi shiru bakace komai ba?

  Najeeb yace"duk kunsa yaji kunya,kunsan fa bakowa keso ayi mashi maganar iyali ba,musamman idan ya kasance baidasu,"

  Jin wannan maganar yasa Ya mu'allim ya ɗan ɗago tare da kallon Captain najeeb da yayi maganar,domin kuwa ya canko dai dai,

   "Ae ni tun rana ta farko dana fara ganinshi,raina ya bani cewa,duk irinmu ne,"adam ne yayi maganar,fuskarshi dauke da murmushi,


 Abba yace"wai dagaske ne?kaima irinsu ne"?

  Daƙyar Ya mu'allim ya iya amsa mashi"hakane abba,"

  Tafa hannu abba ya shiga yi yana Faɗin"Subhanallahi!An shiga uku!haba Ya mu'alim,Ni duk a tunani na ka cike sunnah,ashe ko ɗaya baka ajiye ba,"


  Murmushi kawai Ya mu'allim keyi batare daya ce uffan ba,Saboda kunyar abba da yake yi,

  "To dai ga junaid ɗinka nan,In sha Allahu cikin sati mai zuwa zai angwance,"

  Cike da mamaki Ya mu'allim yace"junaid zaiyi aure"?

  Jinjina kai abba yayi"ƙwarai kuwa,Ae bashi kaɗai ba,Suna dayawa,kusan dukansu zan aurar a lokaci ɗaya,Ina fata kaima kafin lokacin zaka fiddo da mata inyi maka aure,"

  Murmushi kawai ya mu'allim yayi,


Fitowa mommy tayi daga cikin kitchen hannunta ɗauke da tray,wanda ta shirya masu abunsha mai sanyi acikin glass cup,hada snacks ta haɗo masu,


Adai dai Lokacin hafsat ta nufe wurinta,jikinta na sanye da arab gown white colour ta yafa mayafi akanta,

  "Mommy,"da sauri takai idanuwanta kan hafsat data ambaci sunanta,

   Fuskarta asake tace"Hafsat,ina zuwa haka"?

  "Ba ko'ina,nagaji da zama cikin ɗakine,Shine nace bari na fito in ɗan zagaye gidan,"

   Kafin mommy ta kuma cewa wani abu,hafsat ta nuna tray ɗin hannunta"Wannan fa"?

  "Abbane yazo da baƙo,wannan malamin dake duba junaid,shine ya buƙaci in shirya masu drinks,"

  "Bari nakai masu,"

 Ba ƙarami daɗi mommy taji ba,Miƙa mata tray ɗin tayi,ta sanya hannu biyu ta kar6a,kafin ta wuce cikin palourn,Mommy kuma ta juya zuwa ɗakinta,


"Assalamu Alaikum"cikin sanyin murya tayi masu sallamar,gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta,cikin girmamawa ta shiga gaishe dasu,fuska asake suke amsa mata,

  Abba ta fara mika mawa ya ɗauki kofin ɗaya,

  "Ga ya mu'allim nan ki miƙa masa,"juyawa tayi wurin Ya mu'allim ta miƙa mashi cup ɗin,a hankali ya sanya hannunshi ya ɗauki cup ɗin,har zata juya taji yace"kina mace kike shafa turare har haka"?ƙasa ƙasa yayi maganar

  Gabanta ne ya faɗi rass,dama sai da ranta ya bata cewar zaiyi wuya in bai tanka mata ba,saboda tasan halin malaman nan,kuskure kaɗan sai sunyiwa mutun wa'azi akanshi,'ƙasa ƙasa da murya tace"Za'a gyara,'bata jira amsar da zai bata ba,tayi saurin yin gaba wurin Su osman ta miƙa masu,


Murmushi abba ya ɗan saki bayan ya kur6i lemun yace"Nasan bakasanta ba,Jikata ce,sunanta hafsat,"

  Murmushi Ya mu'allim ya ɗan saki kafin yace"Masha Allah,"

  Abba da ɗumi sai cewa yayi"itama bata da aure kamar kai,sai dai bansani ba,ko tana da saurayi,"

 A sukwane hafsat ta juyo tana kallon Abba,hankalinshi kwance yake magana,

     Ƙumshe dariya kanal yusif yayi ganin yadda hafsat ta gumtse fuska,taji ana ƙoƙarin yin tallatarta,da sauri ta juya tabar wurin,sai da tayi nisa,takaici ya isheta,juyowa ta kuma yi don ta kalli Ya mu'allim,karaf suka haɗa ido dashi,watsa mashi harara tayi,duk don saboda yayi complain akan turarenta,abun ya bashi mamaki,hakan da tayi kuma ba ƙaramin burgeshi tayi ba,har yayi tunanin yin magana da abba akanta,idan sun ke6e,


Bayan ya kammala shan lemun,Abba yayi mashi jagora zuwa bedroom ɗin junaid,Lokacin da suka shiga zaune suka same shi,tare da Talal suna kallo acikin laptop ɗinshi,


Cike da zolaya ya mu'allim yace"kaida zan sameka kana karatun qur'ani,sai in sameka kana kallon drama?haka mu kayi dakai"?


Saukowa junaid yayi daga saman gadon ya ƙarasa da sauri ya rungumeshi,ba ƙaramin daɗi Ya mu'allim yaji ba,ganin yadda junaid ya samu lafiya sosai,har ƙiba yayi sa6anin da,

Shafa sumar kanshi yayi"Masha Allah,jiki yayi kyau junaid,Naji daɗi sosai,Allah ya Albarkanci rayuwarka,"Abban ya amsa mashi da Ameen

  Ɗagowa junaid yayi fuskarshi ɗauke da murmushi yace"I really missed u,meyasa bakazo ba,2 days banganka ba,"ya ɗanyi maganar shagwa6e

  Waro ido abbansu yayi ganin junaid na shagwa6a,

  "La haula masalli ila!Junaid me nake gani haka?Dama har yanzu akwai sauran shagwa6ar"?

  Dariya ya mu'allim yayi"A jininshi take,shiya sanya har yanzu bata rabu dashi ba,kuma hada ƙarin autane shi,dole yayi shagwa6a,"

  Abba yace"amma yaci ace ya daina,Nan fa da wani lokaci zai zama ango,"jin wannan maganar yasa junaid,Jin kunya da sauri ya koma saman gadonsu,Ya janyo pillow ya kifa kanshi asama yana dariya,Talal ma dake a gefenshi dariyar yake yi,


 "Yana da kunya sosai,"acewar Ya mu'allim,

 Abba yace"hmmmmm abar kaza cikin gashinta dai,kar atona,"


Dariya sosai su kayi,Sun jima a wurin Junaid sai da aka fara kiran Sallar magrib tukunna,suka fuce atare,


*Sehrish*


A hankali ta turo ƙopar toilet ɗin,jikinta sanye cikin bathrobe fara ƙyal,ta ɗaure igiyar rigar,wani irin ƙamshine ke fita daga jikinta,kamar wadda tayi wanka da ruwan turare,lallausar suman kanta tayi mata rumfa a bayanta,mai yawan gaske,jiƙe take lemar ruwa,tun bayan sallar Azhar,ta dawo ɗakin Azmee,gudun kada hajiya azeema taga tabaro shi,


Gaban mirror ta zauna,zugudum bakomai keyi mata yawo aranta ba,face maganganun da oummansu ta faɗa mata,sun tsaya mata aranta,

  A hankali ta furta"Ya rafayet sona  yake yi,ko jikina yake so?taya za'ae na gane haka?,tana tsoran tayi irin kuskuren da Oummansu tayi,Nayin watsi da damarta,


Hand dryer ta fara ɗaukowa,ta jona ajikin socket,busar da gashin kanta tayi,bayan ta kammala ta kashe ta,jikinta ta soma gyarawa,ko'ina ta shafe shi da mai,


Turo ƙopar ɗakin Hajiya azeema tayi da sallama abakinta ta shigo,Sehrish ta amsa mata,fuskarta adan sake ta amsa mata,

  'Ina yini aunty azeema,"

"Lafiya Lou daughter,Ya jikin naki"?

  "Alhamdulillah,ina samun sauƙi sosai,"

   "Naga gashin kanki,Yayi tsayi sosai,ga yawa,yakamata ku shirya in kaiku wurin Saloon dake da ƴan uwanki,amma fa idan kinji sauki,"_

  "Ae nama ji sauƙi,warwarewa kawai zan ƙarasa yi,"

  Hararar wasa Azeema tayi mata"A haka din,kina ɗan gyasa ƙafa shine kinji sauki?

  Dariya sehrish ta ɗanyi"bari nayi maki make up,"acewar hajiya azeema,

  Ba don taso ba,Saboda yanzu bata buƙatar yin kwalliya,tunda wanda take yi dominshi,Rabuwa zasuyi,

   Within mins hajiya azeema tayi mata make up,fuskar ta fito sosai,jan bakin data shafa mata red ne mai ƙyalli ajikinshi,daga sama ta shafa mata lip gloss,fuskar ta lindu da foundation mai kyan gaske,ga eye brows ɗinta natural amma ta ƙara mata da brown eye pencil,

  "Masha Allah my daughter,Allah yayi maki kyau,ki godewa Allah,Son kowa ƙin wanda Ya rasa,"

  Murmushi sehrish ta ɗan saki,

"Bari na ɗauko maki,kayan da zaki sanya,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi wardrobe ɗin kayanta,

  Can ta hango wata Atampa,Golden glitter,Brown Colour,Riga da skirt ne,ɗinkin ya haɗu over,

  Juyawa tayi tare da kallon Sehrish"Har na hangoki acikin wannan,"

  "Sunyi kyau sosai,Amma dare yayi,koda na sanyasu,zan cirene in na tashi kwanciya,"

  "Duk da haka,ki sanyasu,in yaso daga baya kin cire,"

  Gyaɗa kai tayi"shikenan,"ta ambaci hakan tare da mikewa,taje ta kar6i atampar daga hannunta,

"Bari naje,na kawo maki dinner dinki,"tayi maganar tare da nufar hanyar fita daga dakin,Harta ruƙe handle ɗin kopar ta juyo ta kalli sehrish"Munyi magana da Amrish,tace tana so taje gidansu ta kwaso kayanta,bansani ba kota fada maki"

  "Bata faɗamun ba,"

"Okey,in Allah yakaimu,Zuwa gobe zanyiwa wani magana cikin  matasan gidan nan,yakaita gidan ta dauko kayanta,"

  "Allah yakaimu Lafiya,"

  "Ameen"ta amsa mata tare da juya ta fuce daga ɗakin,


Shaf shaf ta shiga zura kayan ajikinta,sun zauna mata sosai sunbi dirin jikinta,bata ɗaura ɗankwalin ba,don bata iyaba,zama tayi gaban mirror ɗin tana jiran dawowar,Hajiya azeema don ta ɗaura mata shi,


After some minutes hajiya azeema,ta shigo hannunta dauke da tray mai fadi,Asamanshi food stuff ne,Saman table ta sauke tray ɗin,kafin ta nufo Sehrish,

  "Banta6a ganin budurwar da atampa keyi mata kyau ba irinki,yadda kasan donke companyn suka ƙerata,"fashewa sehrish tayi da dariya,don ba ƙaramin nishaɗi ta sanyata ba,


Bayan ta kammala ɗaura mata ɗan kwalin,style me kyau,tace"Aikina ya qare,ga abincinki can kije ki zauna ki ci,"

  "Nagode sosai,"tana kai karshen maganarta,ta fuce daga dakin,


Murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallon kanta ta cikin madubin,miƙewa tayi daga gaban madubin ta dawo gefen gadon ta zauna,sae ƙamshi ke tashi ajikinta,


Tsaf Ya kammala Shiryawa cikin shadda Ash colour,wa'iyazubillah,kyau iya kyau,a tsaye yake gaban mirror yana gyara agogon diamond ɗin hannunshi,


Omar dake zaune gefen gadonshi sai faman sakin murmushi yake yi,yayin da yake kallonshi,

  "Kasan Allah duk macen data mallake ka ba ƙaramar me sa'a bace,cos you're expensive,komai naka Extraordinary ne,wlh mace koda Ilminta koda kyanta koda arzikinta sai da rabonta,"Sai faman zuzutashi Omar yake yi,Shidai baice mashi uffan ba,a hankali yakai hannu tare da ɗaukar turaren nan nashi,Yabi ko'ina na jikinshi ya feshe,

  "just ka bayyana mata irin son da kake yi mata,ka ƙaddara cewa yau zaka fara dating......"

  Slowly ya juya gefe tare da kallon Omar"how can i do that"?

  "Ni zan koya maka,"

Girgiza kai yayi,Omar  kasan ban iya soyayya ba,'

  Matsalarka kenan,tunda baka iyaba ka bari in koya mata,natsuwa sgr yayi yana sauraronshi

  "Kece sanyin idaniyata,bana iya runtsawa in bakya a kusa dani....."

  Kwata kwata Sgr baya fahimtar abunda Omar ke koya mashi,

  "Na lura baka fahimtata,Zamuyi amfani da bluetooth,zaka manna shi a kunnanka,Idan kaje wurinta,zan dinga karanto maka,kai kuma kana faɗa mata,haka yayi"?

  Ɗaga mashi kai yayi"yeah,i can try it,


1 Comments

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

  1. Abban sojoji takun ka

    rshe shafina 124

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post