Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 107


Health College

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 107

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 107

Abun ya ɗaurewa Jahad kai,irin wannan tambayoyi haka,Anya ba aljanu bane suka shige ta ba,

Babu kowa a babban falon,ko tsoro bata ji haka ta nufi Upstairs,gudu gudu sauri sauri take tattaka staircases ɗin,kaitsaye ta wuce bedroom ɗin Marshal Omar,sallama tayi jin anyi shiru ba'a amsa mata ba,Yasa ta fada cikin falon nashi,babu kowa a falon,da sauri ta nufi bedroom ɗinshi,a bakin kopar ta tsaya tare da Leƙawa cikin ɗakin nashi,A kwance ta same shi yana ta bacci,Ajiyar zuciya ta sauke,Cikin sanɗa ta shiga cikin ɗakin nashi,saɗaf saɗaf ta nufi side drawer dinshi dake a righ hand na gadon,Zuƙunnawa tayi agaban drawer chest din,Ta sanya hannu tana bubbuɗesu a hankali,tare da bincikawa ko zata ga wayar jahad,babu ita aciki,a hasale ta miƙe ta nufi wardrobe din kayan shi,gaba daya duk ta hargitsa kayan amma bata ga wayar ba,tsayawa tayi a tsanake ta shirya mashi kayanshi yadda suke,Bayan ta kammala jiki asanyaye ta nufi hanyar fita daga ɗakin dakatawa ta yi da yin tafiyar,Waiwayowa tayi tana kallon cikon ɗakin,tunani take yi kamar akwai wurin da bata duba ba,can ta tuna da Drawer ɗin dake ɗauke da mirror,da sauri ta juya izuwa gaban mirror ɗin,Janyo gida na farko tayi lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya,ganin Wayar Jahad ajiye aciki,


Saukowa downstairs tayi,a main palour ɗin ta zauna saman Sofa tare da kunna wayar don akashe take,Allah yaso babu password a wayar,


Direct ta shiga Gallery ɗin wayar,videos ta gani tare da hotunan dasu Jahad sukayi tare da juna,A hanzarce ta shiga kunna videos ɗin ta ƙura ido tana kallonsu,

Cikin motar Junaid shi da Jahad suka ɗauki video ɗin da take kallo,da hannu ɗaya yake ɗaukarsu video,yayin da dayan hannu ya rungumo jahad ajikinshi yana dariya,yana fadin"With My Juliet,My wife to be in sha Allah"

Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rass!rass!a zabure ta miƙe tsaye tana kallon yatsun hannun Junaid dake sanye da diamond ring ɗinsa,ya Aza hannu saman sumar kan jahad Sosai Zoben ya fito mai ɗauke da harafin *J* sai ƙyalli yake yi


Abun yayi matukar ɗaure mata kai,a rude tace"Kai!junaid ya fita da zoben shi aranar!Ya akai zoben kuma ya koma ɗakin Aunty azmee?Taya akai hakan ta faru?Ta yaya zoben shi ya koma ɗakin Aunty azmee..?" tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Still bata kawo komai aranta ba,


Jiki na rawa ta nufi bedroom ɗinsu,asaman side drawer ta ɗauki wayarta da ta ajiye,kafin ta ajiye wayar Jahad asaman drawer ɗin,


Gaban mirror ta koma ta zauna saman kujera,Layin Aunty Azeema ta kira,Cikin sa'a wayar ta soma Ringing,'natsuwa tayi tana jiran ta amsa kiran nata,jikinta sae kerma yakeyi,Allah Allah take yi acikin ranta ta samu Aunty azeema ta ɗaga kiran,

Almost 15 missed Calls hajiya Azeema bata ɗaga kiran ba,A ƙarshe dole ta haƙura da kiran nata,ba don taso ba,saboda akwai wani muhimman abu da take so ta tambayeta kuma a wurinta ne kaɗai zata iya samun amsoshin tambayoyin da take dasu,


Ajiye wayar tayi gaban mirror ɗin,Kafin ta miƙe tsaye tare da kai idanuwanta ta kalli wall clock ƙarfe 2 na dare,


Dafe kanta tayi saboda matsanancin ciwon kan da ya farmata lokaci guda,a sakamakon tunanin da take ta yi,Zuciyarta tayi nauyi sosai,ga kokwanton da take yi,ga fargabar da take ji,Abubuwa dak sun tarar mata,


Don bala'e a zaune ta kwana,batare da ta runtsa ba,sai wuraren sallar asuba bacci ya ɗauketa can cikin kunnanta taji ana ambaton Sunanta sehrish sehrish,a firgice ta farka,idanuwanta a zare,

Oummansu ta gani atsaye tana kallonta"Sehrish A zaune kika kwana?meyasa baki tafi ɗakin Auntyn taku ba"?

Muryarta da alamun bacci bai isheta ba tace"Oumma,bansan bacci ya ɗauke ni ba,"

"Ki tashi kiyi sallah,Anata kira"ta ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin toilet,


Miƙewa tayi dakyar take iya ɗaga ƙafarta saboda baccin da take ji,zuwa ta fara yi ta hau saman gadonsu ta tayar dasu Hosana suka farka tukunna ta sauko,bayan kowa yayi al'wala,Abu ta shimfiɗa masu Sallaya suka kabbara Sallah,a tsanake suke yin sallar,Bayan sun kammala sallar ne sun zauna kowa ya ɗaga hannunshi suna addu'a,Sehrish ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa"Oumma,Jahad Hosana,dan Allah ku tayani da addu'a,Akan abunda nake yi,"


"Kada ki damu indai addu'a ce kin samu rishi,"acewar Oummansu,hosana tace"A nawa"?

Harara Sehrish ta wurga mata batare da ta tanka mata ba,


Suna cikin yin addu'ar nan,Wayar Sehrish dake ajiye gaban mirror ta soma ruri,A zabure ta miƙe tare da nufar wayarta,

"Kira kuma tunda Asuba?Wanene ke kiranki"?tsayawa tayi cak jin abunda oummansu tace,juyawa ta ɗan yi tare da kallonta,ɗan murmushi ta  sakar mata"ummm dama Ina tunani ko Aunty Azeema ce ke kira ne"

"Okey,ki amsa kiran"da sauri Sehrish ta ƙarasa gaban dressing mirror ta dauki wayar tare da duba screen ɗin,Wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ganin kiran Aunty Azeema,


Juyawa ta ɗan yi kamar mara gaskiya ta saci kallon Oummansu dake zaune saman darduma,Hosana harta fara hammar bacci sai cewa takeyi"Wai Oumma addu'ar bata isa haka ba?Dan allah mu koma mu kwanta,murmushi abu tayi tare da kallonta,

"kije ki kwanta mana,Wani ya ruƙe maki ƙafafunki,ibadarma baki iya yi da abinci ne duk mun yawanshi sai kin tada shi....."jahad ce tayi maganar tana harararta,

Ganin hankalinsu ya koma kan Hosana yasa ta lalla6a ta fuce daga cikin ɗakin,Gudu gudu sauri sauri take tafiya,kaitsaye ta nufi hanyar nan da zata sadaka da wajen gidan,fitowa tayi ta nufi garden don batason kowa yaji ta,


A gefen wata bishiya ta tsaya,tare da duba Screen ɗin wayar missed call har 3 Aunty azeema tayi mata,Danna mata kira Sehrish tayi cikin sa'a Auny Azeema ta ɗaga kiran,


A hanzarce Sehrish ta kara wayar a kunnanta,tun kafin tayi magana Aunty Azeema tace"Sehrish lafiya kuwa?kin tashi hankalina,kawai ina farkawa yin sallar asuba sai naga missed calls ɗinki"


Muryar ta har shaƙewa takeyi saboda tsabar saurin tayi magana"Aunty azeema,babu abunda ke faruwa,lafiya lou nake,Dan Allah wasu tambayoyi ne nakeso nayi maki,Wani Assignment ne aka bamu a school,"


"Okey,Allah yasa nasani"

"Aunty azeema,Malamar da ta bamu assignment ɗin tana buƙatar muyi bincike akan wani accident daya faru ne,Sai mu sanar da ita amsar da muka samo,"


Natsuwa hajiya Azeema tayi tana sauraronta,

"Saurayi ne da budurwa,suka shirya zuwa shan ice cream,to akan hanyar zuwansu,sai suka dakata agefen titi,ita budurwar ta tsallaka titin zata siya musu ice cream,ta bar saurayinta acikin motar,kwatsam sai ga wata truck ƙatuwa tabi ta kan motarsu,nan take kuma sai wuta ta kama ci da motar,kafin ƴan kwana kwana su ƙaraso wurin,Wutar taci ta cinye,ba'a samu komai ba daga sassan jikin saurayin,


Katseta Aunty azeema tayi"ita malamar taku me takeso ku gano mata ne,"


"Bari na kai maki ƙarshen labarin,shi saurayin ya zama toka,sai ƙarahunan motar aka samu,to abun mamaki kawai sai kuma ga Zobenshi na Diamond an tsince shi a hannun wani dattijo,zoben bai yi komai ba,sai ƙyalli yake yi kamar sabo,to shine take son kowa yayi nazarin labarin ya fada mata abunda yake hasashe"


Abun mamaki tana kai ƙarshen labarin sai taji Aunty azeema na dariya,bubbuga ƙafa Sehrish tayi kamar tana agabanta"Wayyo Allah mommy azeema,meyasa kike dariya,dan Allah ki taimaka ki bani amsar tambayata,"


Tsagaitawa tayi da yin dariyar,sannan tace"Abun mamaki abun Al'ajabi,kawai sai aka tsinci zoben diamond ɗin saurayin a hannun wani,bayan shi mamallakin Zoben ya ƙone ƙurmus,Gaskiya Sehrish ta baku Assignment me wuya,Amma fa ni abunda nake tunani,in har babban Diamond ne kamar irin wanda na ta6a siya ma Junaid,nasan kin ta6a ganinshi a hannunshi mai harafin J,"


Muryarta har kerma takeyi wurin amsa mata"eh naganshi ahannunshi"

"Yawwa,so kin ga kalar wannan Diamond ɗin,In har wuta ta ta6a shi baiyin komai,Sai dai akwai wani abunda yake yi idan wutar ta haura mintuna tana ci ajikinshi,Stone ɗin jikinshi zaiyi duhu sosai,kuma ba hakan yana nufin ya mutu bane,Lafiyarshi ƙalau Amma fa wannan duhun da dutsen jikinshi yayi,A nigeria basu da chemical ɗin da zasu gogeshi,Sae dai anan dubai Companyn da nake siyayyar Diamonds ɗin a wurinsu ne kaɗai zasu iya goge wannan baƙin ya dawo yana ƙyalli"


"Amma Aunty Azeema me kike tunani game da Zoben da aka tsinta hannun wani dattijon?Wanda kuma ba'a gabanshi hatsarin ya faru ba,kuma shi saurayin da zoben ya shiga cikin motar Har ya haɗu da hatsarin"ta ƙarasa maganar tana jiran amsarta,don a ƙagare take,


Shiru Aunty azeema ta ɗanyi na wani lokaci da alama nazarin wani abu takeyi,

"Naji kinyi shiru mommy,"

Sai lokacin ta ɗaura da maganarta"Gaskiya abu biyu ne nake tunani,Shi wannan dattijon suspect ne,Amma kuma in har dagaske shi matashin da zoben ya shiga cikin motar,dole abu biyu ne zai kasance!Kodai Shi saurayin ne yayi wurgi da zoben ya faɗo daga cikin motar ko kuma mamallakin Zoben Yana raye!!Yayi escape daga cikin motar shiyasa har aka samu Zobenshi kuma lafiyarshi ƙalau zoben babu alamun wuta ta ta6a shi,kinga kuwa Shima mai zoben bai mutu ba a hasashe na kenan,

Gaban sehrish ne yayi wani irin mugun bugu,Hankalinta yayi matuƙar tashi,idanuwanta azazzare,jikinta har kerma yakeyi,

.."amma Aunty azeema,meyasa kike tunanin cewa mamallakin Zoben yana raye,"

"Wlh sehrish ni ko a school ban ta6a cin karo da question mai sarƙaƙiya ba irin wannan tambayar da kikayi mun,Gaskiya nidai nafi kyautata Zaton Shi Mamallakin Zoben ya ku6uta daga cikin motar,Ai kince ita budurwar ta tsallaka titi ne,taje siya masu ice cream.

Katse mata hanzarinta sehrish tayi"Amma fa Aunty,ita budurwar koda ta tsallaka titi,Shi saurayin sai da ya kira sunanta,ta juya har yana ɗaga mata hannu ta cikin motar,"

"Kinsan tazarar minti nawa ita budurwar ta ɗauka lokacin da mai ice cream ɗin yake zuba mata ice cream ɗin?

Girgiza kai sehrish tayi kamar tana agabanta haka take gani"A'a bansani ba gaskiya,"

"Idan har aka samu tazara koda na minti biyar ne,ita budurwar ta kawar da idonta daga kanshi,ta mayar da hankalinta wurin mai siyar da ice cream din,A wannan interval ɗin zai iya yiyuwa Ya ku6uta daga cikin motar,ko kuma an ɗaukeshi,Ni daga jin wannan labarin ma wlh duk shiri ne aka tsara don a caza maku brain ɗinku,kin sani sai surutu nakeyi ko breakfast banyi ba,"ta ƙarasa maganar da zolaya,

Dariya Sehrish tayi tare da cewa"Am sorry Auntyna,thank u so much Aunty Azeemana,Kin taimake ni sosai,Yanzu na samu amsar da nakeso,"

"Kada ki damu Daughter,duk lokacin da wani abu ya shige maki,ki sanar dani kawai a shirye nake dana baki shawara"

Murmushi sehrish ta saki,har sunyi sallama zata kashe wayar da sauri hajiya azeema ta dakatar da ita "Wait!kince saurayin ya zama toka ko"?

"Hakane,"ta amsa mata,

"Taya za'ace ko ƙashin jikinshi ba'a samu ba?wutar tayi more than one hour ne tana ci?ba kince an kira motar kwana kwana ba,"

"A'a banda masaniya akan wannan amma zan tambaya,"

"Okey,akwai wani incident daya ta6a faruwa, makamancin labarin da kika bani,almost 30 mins wutar naci A motarsu,ba'a kashe wutar ba,saboda babu wasu a kusa,Ko daga baya da mutane suka zo aka kashe wutar an samu wasu konannun 6angarori na jikinsu,duk da zai iya faruwa dagaske ae yasha faruwa ma,mutun ya ƙone ƙurmus sai tokarshi,ko indiyawa ma ai suke ƙona gawarsu su kuma ƙulle tokar in zasuyi jana'iza Amman kinga ai wutan tana daukar lokaci tana kona gawar,Amma nidai gaskiya a labarinki Ban yadda cewa Wannan mamallakin Zoben ya mutu ba!!Amsar da zaki ba malamar ku kenan!Ki sanar da ita duk wani bayani da nayi maki,Nasan zata baki mark sosai,"


Jiki asanyaye sehrish tace"in sha Allah Aunty azeema,Zan rubuta duk wani bayani da kika yi mun nagode sosai,"


Daga haka su kayi sallama,kamar jira takeyi ta katse kiran,jiki a mace ta zauna gefen bishir,Ta gaza yadda da abubuwan da kunnuwanta suka jiye mata,Dama kuma it will be very hard farat ɗaya ta fara suspecting ɗin Azmee,Bakomai yafi tsaya mata arai ba,fa ce waɗannan tambayoyin masu matuƙar wuyar amsuwa Junaid yana raye ko ya mutu?taya akai zoben Junaid yaje ɗakin Aunty Azmee?kodai zoben aljani ne yana da fiffike harya tashi sama ya fito daga cikin motar da fika fikinshi yazo ɗakin Aunty azmee?Sai lokacin ta soma tunanin wai ma wacece Aunty azmeen nan?tunda suke atare da ita,bata ta6a bata labarin danginta ba,kwata kwata bataso a tambayeta dangane da danginta,Sannan kuma tunda take da Aunty Azmee bata ta6a cewa zata je gano gida ba,Uwa uba kuma Aunty azmee bata ta6a gajiyawa dayi masu aiki ba,A ƙalla idan zata lissafa shekarun Junaid da akace ta shayar dashi tun yana jinjiri,Azmee tayi more than 20 years a gidan,


Zurfin tunani ta shiga yi,maganganun ya sayyadi ne suka shiga dawo mata acikin kanta,inda yake cewa kaf family dinsu a tafin hannunsu suke,Duk wani motsi nasu akan idanuwansu suke,Kenan Suna da ɗan leƙen asiri acikin gidan?Dolen doliya akwai wanda ke shirya wata maƙarƙashiya acikin gidan,Tunawa tayi da wannan malamin makarantar nasu Ya Mu'allim da ya ta6a bata ruwan addu'a ta sha saboda yawan bacci da take a aji,lokacinne kuma ta Manta dasu Hosana kwata kwata,Tabbas Akwai abunda akayi mata,still Sehrish bata fara zargin kowa ba kuma har lokacin bata sanyawa ranta cewa Aunty Azmee tana da sa hannu a Mutuwar Junaid ba,Tama fi zargin Haroon don yasha sanar da ita cewa Zai kashe farin cikin gidan,Duk da tana doubting akan kalamanshi,Saboda shi ɗan giya ne yawancin kalamansu suna faɗi ne ba don su aiwatar ba,koba don haka ba,tana ji aranta cewa Haroon bazai iya kashe junaid ba,


Sehrish bata bar wurin bishiyar nan ba,Har sai da ƙarfe 10 ta buga,kamar wadda tasha ƙwaya haka take tafiya,Ga wani matsanancin ciwon kai da ya rufar mata,Ta caza ƙwaƙwalwarta sosai,


Lokacin da ta shigo cikin gidan,ta ƙopar da ta fita,kaitsaye bedroom ɗinsu ta wuce,Tura ƙopar ɗakin tayi ta shiga,Oummansu ta samu zaune gefen gado tana shan Coffee,


Jin motsin shigowar sehrish ne yasa ta ɗago da idonta tana kallonta,

"Ina kika je ne?har muka kammala yin breakfast baki dawo gida ba,"

Daƙyar ta iya buɗe baki tace"na shiga garden ne shan iska,"gudun karta ƙara tambayarta yasa tayi saurin cewa"Oumma,Coffee kike sha"

"Azmee ce ta kawo mun shi yanzun nan,"

Murmushin yaƙe sehrish ta dan saki tare da samun wuri gefen oummansu ta zauna,

"Ba zaki ci abinci bane"?cike da kulawa tayi mata maganar,

"A'a,na ƙoshi bana jin yunwa sai zuwa anjima zanci,"

Miƙa mata cup ɗin hannunta tayi"kar6i kisha,"batayi mata musu ba tasa hannu ta kar6i Cup din takai bakinta tana sha,kur6a uku tayi ta dakata da shan Coffee ɗin tare da kallon Oummansu,

Ganin tana kallonta yasa tace"Lafiya,kike kallona?"

Murmushi sehrish ta dan yi "babu komai oumma,kawai inaso na tambayeki wani abu ne,"

"Ina sauraronki"

"Amm oumma,jiya naga kin ɗan razana da kika ga Azmee,kinsanta ne?

"Kamar nasanta amma bazan iya tunawa ba,"

"Dan Allah Oumma kiyi ƙoƙari ki tuna,"

"Shikenan,idan na tuna zan sanar dake,"

Ba ƙaramin daɗi taji ba,Miƙewa tayi da sauri ta nufi toilet,Shaf shaf tayi wanka,lokacin da ta fito bata samu Oumman tasu da ta batari a azaune ba,babu kowa a ɗakin,


Tunani ta shiga yi ko Sgr Yana acikin gidan?tanaso taje ta duba lafiyarshi amma tana fargabar a wani hali zata same shi,dan kwanakin nan sam baya buƙatar kowa atare dashi,


Wani haɗaɗɗen lace ta ɗauko Ash colour sai ƙyalli yakeyi,riga da skirt ne,Sanya kayan tayi a jikinta,sunyi mata cuf cuf sun bi shape ɗin jikinta,Ɗinkin ya fito da ita sosai,kashe ɗaurin kallabi tayi,bayan ta ɗaure gashin kanta da ribbom,Gaban mirror ta koma ta zauna ta fara yin make up,murza wanccan shafa wancan manna wancan,kamar Aljana haka ta koma tayi kyau Over,


Wayarta ta ɗauka,ranta ne ya bata cewar ta tura mashi text message,may be ya bata amsa,

_Hi,Gm Ya Rafayet ina fata ka tashi cikin ƙoshin lafiya,bansani ba ko yau kana buƙatar wani abu in kawo maka_

Almost 5 mins da tura mashi saƙon saiga reply ya maido mata"I need coffee,"

Murmushi ta saki kamar bata da damuwa acikin ranta,Ajiye wayar tayi agaban mirror ɗin,ta fito daga cikin ɗakin,kaitsaye ta nufi kitchen,A babban falo ta samu mutanen gidan suna fira abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,ga Oummansu ga Alex gasu fawan ga kuma su Jahad,tare da Abusufyan,"mutun uku ne kaɗai basu Hallara ba,Sgr Omar da Abbansu junaid,


Basu jiyo takun takalminta ba,saɗaf saɗaf ta shiga kitchen,har sai da gabanta ya faɗi lokacin da ta ga azmee a cikin kitchen ɗin,Batayi tsammanin akwai mutun aciki ba,

"Kin tsorata ni,"Azmee ce tayi maganar,A yayin da take tsaye gaban sink tana wanke kwanukan da sukayi amfani dasu,

Murmushin yaƙe sehrish ta sakar mata

'Afuwan Aunty azmee,nikaina saida na tsorata dana gan ki,Banyi tunanin akwae mutun ba,Shiyasa banyi sallama ba,"

"Irin wannan kyau haka Sehrish?lace ɗin nan ba ƙaramin kyau yayi maki ba,"tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,

Murmushi sehrish ta kuma saki"babban yaya zan kaiwa coffee,'

"Allah sarki,kwana biyu na lura yana cikin matsananciyar damuwa shi da Omar,musamman Abba Allah ya kawo masu mafita,Allah ya bayyanar da Junaid,"damuwace ƙarara akan fuskar azmee da tayi maganar,

"Nima na damu akan rashin Junaid aunty azmee,kowa ya shiga damuwa sosai,bawan Allah,junaid da baison komai ba sai kyautatawa,Amma dan rashin imani da tausayi aka samu wasu mugayen suka ɗauke shi,in sha Allah Nan bada jimawa ba asirinsu zai tonu,Sai sun gane kuskurensu,kuma sai sunyi danasanin abunda suka aikata"da biyu sehrish tayi maganar,don taga react ɗin da Azmee zatayi,

"Am naji kince zaki kaiwa Sgr coffee ko?Yakamata ki hanzarta kai mashi,idan kin dawo inaso muyi gurasa atare,nasan mutanan gidan nan zasu ji daɗi sosai idan akayi gurasa,Don An jima ba'ayi masu ita ba kuma suna so,"

Cike da mamaki sehrish ke kallonta,Maimakon ta bata amsa kan maganar da tayi mata,amma sai gashi ta Canza magana,

"Shikenan Aunty Azmee,Bari na kaimashi,"

After some minutes ta fito hannunta ruƙe da Cofeen,


Sai da ta fara tsayawa ta gaisar da mutanen falon kowa nata yabon wankanta,kafin ta wuce upstairs,

Lokacin da ta shiga bedroom ɗinshi,a kwance ta same shi saman katafaren gadonshi kamar mai yin bacci alhalin nan kuwa idonshi biyu yadai lumshe idanuwanshi ne,


Ƙarasa shiga ciki tayi ta ajiye mashi cup din asaman table,Sannan anatse ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet,ina kwana,"


Banza yayi bai amsa mata ba,tunani ta shiga yi kodai bacci yake yi ne?

"Babban yaya,"ta ƙara kiran sunanshi nan ma yayi mata shiru,sai da ya mula yasha iska kafin ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da kallon wurin da take a tsaye,duƙar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta,

Da wannan sexy voice ɗin tashi ya furta"Au is that how i taught u to greet me"

gabanta ne ya ɗan faɗi tunawa da irin gaisuwar da yakeso ta dinga yi mashi,tabɗijancan,wani irin kunyarshi take ji,

"Am waiting within 3 mins"ya ƙarasa maganar tare da mayar da idanuwanshi ya rufesu,


Da sauri ta cire takalmanta kafin ta hau saman gadon,Sai da taje saitin inda yake kwance sannan ta tsaya tana tunanin taya Zata fara,ga lokaci na tafiya,don ma Allah Yasa ya rufe blue eyes ɗinshi,

daidai lokacin da minti uku suka cika Cuf,a hanzarce ta ɗan ranƙwafa gefen fuskarshi,lips ɗinta na kerma ta manna mashi kiss,har sai da taji ajiyar zuciyarshi alamar yayi receiving ɗinshi,other side ɗinma ta Manna mashi kiss,Saura na baki,

Zuba ma Sexy lips ɗinshi ido tayi tana kallonsu gwanin ban sha'awa yadda kasan na jinjiri haka suke,saboda kyau da softnesss dinsu,

Ganin yana ƙoƙarin buɗe idanuwanshi ne yasa tayi saurin hada mouth ɗinsu wuri ɗaya,sam bai ta6a tsammanin zata iya yi mashi kiss ba,sosai take shan lips ɗinshi tun daga kan lower lip dinshi zuwa upper,baisan lokacin da ya ƙara ƙankameta ba ajikinshi,hannayenshi gaba ɗaya suna asaman Ass ɗinta,yayin da ita kuma hands ɗinta ke tallabe cikin sumar kanshi,gaba daya suka harɗe wuri guda kamar tip da tyre,da niyyar gaisuwa tayi mashi hakan kamar yarda ya umarce ta sai gashi ta zarce da sarrafashi,ƙaramar yarinya na neman Zautar dashi,sai da yayi dagaske sannan ya samu yayi control ɗin kanshi,a lokacin harya zuge zip ɗin rigarta,kwantar da fuskarshi ya yi asaman boobs ɗinta,hancinshi na gogarsu haka la66ansa,tana jin saukar numfashinshi dake fita da zafi zafi,jurewa kawai yake yi,Shi kaɗai yasan halin da yake shiga a duk time din da ya kasance tare da ita,

Zagayo da hannunta tayi ta cikin sumar kanshi tana shafa mashi ita,nan fa ya ƙara narkewa a jikinta kamar jinjiri ajikin Babarsa,

Bakomai ya faɗo mata aranta ba fa ce abunda Aunty azeema ta sanar da ita,Wato ta ɗaukeshi kamar jinjirin da aka bata rainonshi,komai ta koya mashi zai ɗauka ne harya fara kwatanta yi mata,

Moving lips ɗinta tayi izuwa saitin kunnashi,Calmly ta furta sunanshi"Ya rafayet,"

Ƙasa ƙasa taji ya amsa mata"yeah,"

"Have you ever been in love"?ita kanta batasan ta furta mashi hakan ba,

"I don't know anything about love,I only know how to hold a gun"

Sam batayi expecting ɗin zai bata amsa ba,

Murmushi tayi sosai,kafin ta kuma cewa"Coffee ɗinka fa?Zai huce,"

"I don't need it now,Am just enjoying being with u"daƙyar yake yin maganar saboda yanayin da yake jin kanshi,sehrish tsantsar farin ciki ne ya lullu6eta,kalamanshi sun ƙayatar da ita,

Wasa wasa bacci yayi awon gaba dashi,dama kwanakin nan bai samu ya runtsa ba,Reesh da babynta,saura babyn baby mai zuwa,


Dayake itama bata samu enough sleep ba adaren jiya,sai gashi ta fara jin baccin,


Wayar Sgr dake ajiye saman side drawer ce ta soma ringing,firgit ta farka,tare da miƙa hannunta tana lalubar wayar,don batason tayi moving din da zaisa ya farka,


Daƙyar ta samu yatsun hannunta suka ruƙo wayar,janyota tayi izuwa saitin fuskarta,Wani kalar suna ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,Can dai na yarensu na sojoji,


Picking Call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta,

Wata kakkausar murya ce ta soma ji acikin kunnanta,

"Sir!kana magana da sergeant Lee ɗaya daga cikin sojojin da ka sanya Su tsare maka grave ɗin younger brother ɗinka Junaid,"

Har saida gaban sehrish ya faɗi rass gashi ta kasa sanar dashi cewa ba Sgr ɗin bane,

"Since yesterday night naso na kira wayarka bansamu halin yin hakan ba!abunda ke faruwa shi ne yau almost 1 week kenan,akwai wani matashin saurayi dake yawan yin zarya a titin nan,kullum yana zuwa ne cikin motarshi ƙirar Venza Ash colour,mun sanya mashi ido sosai,gaskiya Sir we are suspecting him,Zaryarshi tayi yawa,kuma bai tashi zuwa sai wuraren 10 na dare,kuma idan yazo wurin ƙabarin sai yayi parking ɗin motarshi ya fito daga ciki,Yayi ta zagaye wurin da grave ɗin yake,kamar yana neman wani abu......"

Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,batasan lokacin da tayi rejecting kiran ba,jikinta har kerma yake yi,mayar da wayar tayi saman drawer ɗin ta ajiyeta,


Lalla6awa tayi da sauri ta zame jikinta daga nashi,gyara zip ɗin rigarta tayi,kafin ta sauko daga saman gadon,Zuciyarta sai faman harbawa takeyi,tayi danasanin picking call ɗin,da bataji wannan tashin hankalin ba acikin kunnanta,


Fitowa falonshi tayi asaman sofa ta zauna jikinta nata kerma,tsananin tsoro ne ya kamata,tunani ta shiga yi wanene Yake yin zarya a wurin ƙabarin junaid?me yake kai shi?me yake nema a wurin!tuni kanta ya fara yi mata ciwo,dama akwai ciwon kan ya ɗan lafa ne,


Hawaye ne suka soma saukowa akan fuskarta,lamarin ya fara rikitar da ita,daga wannan sai wannan?wai duk waye ke shirya wannan Maƙarƙashiyar ne"?


Miƙewa tayi bayan ta share hawayenta,fitowa tayi daga cikin part ɗinsa ta sauko downstairs kitchen ta koma,A bakin ƙopar shiga kitchen ɗin ta tsaya tare da goya hannayenta akan ƙirjinta tana kallon Azmee dake gasa Gurasa a frying pan,

Gaba ɗaya hankalinta bai atare da ita,

"Sehrish,"Azmee ce ta ambaci sunanta a firgice takai idanuwanta kan Azmeen,

"Tun ɗazu nake ta jiranki baki zo ba,har na fara gasa gurasar,ko zaki taimaka ki yanka mun vegetables din da zanyi amfani dasu?ga kuma ƙuli da za'a daka,"

Tunda ta soma magana sehrish tayi kasaƙe tana kallonta,batare da tace uffan ba,abubuwa dak sun cunkushe mata kwalwarta,ta fara rasa tunaninta,ji take kamar ta tambayeta ya akai Zoben Junaid yaje ɗakinta amma ta kasa yin hakan,

Dafa kafaɗunta Azmee tayi tare da ɗan girgiza jikinta"Wai baki ji ina magana bane"?

Da sauri tace"Amm ummm yanka kuli ko zanyi"

Dariya azmee tayi sosai jin abunda tace,

"Kin ta6a ganin inda aka yanka ƙuli ne?Nifa Cabbage dasu tumatur nace ki yanka mun,Shi kulin daka shi za'ayi,already akwai shi,wai ko baki da lafiya ne?naji jikinki da zafi"tayi maganar tare da sanya hannunta agefen wuyan Sehrish,

"Banajin daɗi Aunty azmee,ina buƙatar addu'arki,"tana magana kamar ta fashe da kuka,

Janyota azmee tayi tare da rungumeta ajikinta,

"Allah ya baki lafiya ƙanwata,in dai addu'ace zan cigaba da tayaki,kema kuma ki dage da yin addu'a akan Allah ya yaye maki abunda ke damunki"

Lamo sehrish tayi ajikin azmee har yanzu bata fara zarginta ba,kuma bata kawo komai aranta ba,Tana jinta tamkar mahaifiyarta,Saboda irin kulawar da take bata,

"Aunty azmee na gode sosai,Allah ya barmu tare"

."Ameen ameen,"ta ƙarasa maganar tare da ɗago sehrish daga jikinta,

"Kije ki kwanta kawai kina buƙatar hutu ni zan ƙarasa yin gurasar"

Girgiza kai Sehrish tayi"A'a ae da sauƙi ciwon,Inaso na tayaki aikin,Ae ba wani abu bane me wahala,"

Batare da 6ata lokaci ba,Sehrish ta fiddo kayan da zasu yi amfani dasu,Cabbage ne tare da tomotoes,Albasa da sauransu,


Suna cikin yin aikin Sehrish ta soma ƙoƙarin bugun cikinta,

"Aunty azmee,jiya da kika ga Oummanmu naga kin ɗan razana haka kamar kinsanta,"

"Kallon sani nake yi mata,Amma gaskiya bansanta ba,Zai iya yiwuwa sunyi kama da wata wadda na ta6a sani ne,"

"Okey,amma tunda nake dake Aunty azmee,baki ta6a bani labarin danginki ba,Gashi na kwaɗaitu da son jin Labarinki,inaso wata rana idan kin tashi kai musu ziyara mu tafi tare,"

Shuru Azmee ta ɗan yi har lokacin tana tsaye agaban gas tana gasa gurasar,almost 15 mins bata ce komai ba,har sai da Sehrish ta ambaci sunanta"Aunty azmee,kin yi shiru,"

Murmushi azmee tayi irin na gefen fuskar nan,

"Sehrish tunda nake dake baki ta6a tambayar dangina ba sai yau,shiyasa ban ta6a baki labari ba nima,ina da wani hali ni,in har mutun bai tambayeni abu ba,to kuwa bazai ta6a ji ba abakina,Amma yanzu tunda kin tambaye ni,idan muka samu Free time zan baki tarihin rayuwata,"

Daga haka suka mayar da hankalinsu akan aikin da suke yi,Bayan sun kammala yin gurasar a saman faffaɗan tray Suka jejjerata,uban ƙuli suka barbaza asamanta,sannan suka shanana mai asaman kulin,ko ina yaji,daga sama kuma sukayi mata ado da kayan lambun da sehrish ta yanka,


Fita azmee tayi daga kitchen ɗin tabar Sehrish kamar yadda sukayi ita zata raba masu gurasar,Ba ƙaramin daɗin gurasar nan suka ji ba,musamman matasan gidan har rububi suka dinga yi,kowa sai da ya yaba daɗin da tayi,


Wurarren ƙarfe biyu na rana,bayan ta kammala sallar azhar ta koma kitchen ta shirya ma Sgr tashi gurasar,A saman wani ƙayataccen plate mai faɗi,batasan ko yana ra'ayinta ba,ita dai kawai tayi niyar kai mashi ne,


Tana ƙoƙarin shiga falonshi suka ci karo da juna,ƙiris ya rage plate ɗin hannunta ya 6are da sauri ya tallabo mata shi,tun daga ƙasa ta soma kallonshi,T shirt ce a jikinshi Blue ta fito da hasken shi sosai,Sai trouser ɗinsa black colour,da alama sauri yake yi ya fita,

Zuba ma juna ido sukayi batare da ƙyaftawa ba,

"Ina yini,ka tashi lafiya"?

Lumshe mata eyes ɗinshi yayi alamar yana lafiya batare daya furta mata ba,

..."menene wannan"yayi tambayar yana nuna plate ɗin hannunta,

"Gurasa ce,kai na kawo mawa,"

Yatsina fuskarshi ya ɗan yi,tare da cewa"Sauri nake yi zan fita,"jiki asanyaye ta juya zata koma da ita,

"zonan"ya kirata,da sauri ta juya tana kallonshi,

"Someone called my line,Ke kika ɗaga"?

Zuru tayi mashi da idanuwa gudun kada yayi mata faɗa,

..a ɗan hasale yace"Am asking u!"

A tsorace ta ɗaga mashi kai alamar eh'

"Its okey,juyawa yayi tare da komawa ciki"

Bin bayanshi tayi asaman Sofa ya zauna,Ta ajiye mashi gurasar saman table,cire mashi murfin da ta rufe plate ɗin tayi,


Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post