Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 1 complete

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 1 complete

 

Kurkukun Kaddara ( The Destined Prison) chapter 1 complete

*💋𝑇𝐻𝐸 𝐷𝐸𝑆𝑇𝐼𝑁𝐸𝐷 𝑃𝑅𝐼𝑆𝑂𝑁💋*

_𝐾𝑢𝑟𝑘𝑢𝑘𝑢𝑛 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎_

𝑆oul 𝑆𝑎𝑐𝑟𝑖𝑓𝑖𝑐𝑒,𝐹𝑒𝑎𝑟𝑓𝑢𝑙 & 𝑆𝑦𝑚𝑝𝑎𝑡𝒉𝑒𝑡𝑖𝑐,𝐵𝑒𝑡𝑟𝑎𝑦𝑎𝑙 & 𝐶𝑟𝑢𝑒𝑙𝑡𝑦,💔💔💔

*𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 & 𝑊𝑟𝑖𝑡𝑡𝑒𝑛*

         *𝐵𝑦*

   *𝐵𝑜𝑠𝑠 𝐵𝑎𝑡𝑢𝑟𝑒*

_the W𝑟𝑖𝑡𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝐴𝑏𝑏𝑎𝑛 𝑆𝑜𝑗𝑜𝑗𝑖,𝐴𝑛𝑑 𝑛𝑜𝑤 _the destined prison_

_Kamar Yadda na fara littafin nan ina rokon Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon Kammala shi lafiya,Alfarmar Annabi muhammad(SAW)Allah ya bani ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa,Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abunda bazai amfani al'ummar annabi ba✍️_


Gargarɗi


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book dinnan ba ta kowace siga,ko akaranta mun shi a youtube,batare da an nemi izni awurina ba,ko a haɗamun document,Idan kunne yaji jiki ya tsira,ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina👌_



*full Episode 1*





Sannu A hankali agogon bangon ke harbawa,yana bada sauti tik!tik!!tik!!sakamakon dare daya tsala dan time din karfe ɗaya da rabi na dare,wayar dake ajiye saman bedside drawer ƙirar Samsung galaxy ta soma ruri da ƙarfi gaske,A lokacin Yayi nisa acikin baccin nashi,kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa,A kira na huɗu ne,Sautin Ya daki dodon kunnanshi,A firgice ya farka Yana faman ambaton sunan Allah,jikinshi na sanye da Singlet da gajeran wando fari,a ƙalla yakai shekara 40 a duniya,A launin fata kuwa,Wankan tarwaɗa ne,daƙyar yake iya ware manyan idanuwanshi akan katafaren Gadonshi,kafin a hankali ya mayar da ƙwayar idonshi kan agogon bangon dake ɗakin,tafin hannunshi yakai tare da shafa fuskarshi,cikin sanyin Murya ya ambaci sunanta"Angel"kafin ya zame hannunshi daga kan fuskarshi,Wani kiran Ya sake shigowa wayarshi,a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar,cike da mamakin wanene Yake kiranshi a irin wannan lokaci?Anya kuwa Lafiya?


Lokacin daya kalli screen ɗin wayar Sunan Aminina ne Ya bayana,ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da ɗaga kiran Ya manna wayar a kunnanshi,tunkafin Yayi sallama,kunnuwanshi suka jiyo mashi sautin harbin bindugu,A gigice Ya furta"Aminina"

  tun kafin Ya ƙarasa rufe bakinshi,Muryar Aminin nashi Ta katse mashi hanzarinshi a ruɗe yake faɗin",Na bani na lalace,Shikenan tawa ta ƙare"

 A firgice Ya dakatar dashi"ka natsu kayi mun bayanin meya ke faruwane?

  "sun kamani inayi masu leƙen asiri,Yanzu haka sun biyo motata,Nasan kashe ni xasuyi,Kaima kuma bazasu ƙyale ka ba,bazanso kayi irin mutuwar wulakancin da zanyi ba,dan Allah na rokeka,ka gudu kaida Angel,bana fatan laifina ya shafeka Abokina,Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu,Yana acikin memory ɗina,ita kaɗaice hujjar da asirinsu zai tonu............."bai kai ƙarshen maganar ba,Ɗuff Yaji kiran ya katse,


A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar Wayar ta katse,Sake kiran layin nashi yayi,cikin sa'a aka ɗaga kiran,abunda bai ta6a tsammani ba,Sautin kururuwa yaji acikin kunnanshi,mai matuƙar razanarwa,wata kausasshiyar murya yajiyo Tana magana ta cikin wayar"idan kana son sanin meke faruwa,ka kalli screen din wayarka,"jiki na rawa Ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video call,


Saboda tsabar Firgita,A ruɗe ya diro daga saman gadon,Idanuwanshi sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon zata faɗo kasa, Bakomai ne yasa shi firgita ba,face Motar Amininsa dake Ci da wuta,Akan idonshi suka zazzaga ma motar fetur,Yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar,Wuta sai cin naman jikinshi take yi,Wata irin zufa ce ta wanke mashi fuskarshi,A kiɗime Ya shiga furta"No!No!"duk ya firgice,rejecting call din sukayi,


Wani irin matsanancin ciwon kaine ya farmasa,ba arziƙi Ya zube gefen gadon a zauna,Yayin da jikinshi ke kyarma sosai,Kusan minti goma shabiyar baya acikin hayyacinsa,Ya rasa ma me yake  yi mashi daɗi duniyar nan,


Yana cikin wannan Halin ha'ula'in,Muryar amininsa Ta soma dawo mashi acikin kunnanshi"Ka gudu kaida Angel banaso laifina ya shafe ku,"tabbas kuwa zasu dawo kanshi ne,domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa,bakomai yafi ji mawa ba face ƴarsa ɗaya tilo daya Mallaka wato ANGEL,


A matuƙar ruɗe ya miƙe,Ko jallabiya bai zura ajikinshi ba,Iya key ɗin motarshi ya ɗauko,saboda tsabar ruɗi Wardrobe ya dosa zai buɗe A matsayin kopar dakin,Har saida kanshi ya bugu tukunna ya ankare,Ya nufi ainihin ƙopar,da sauri sauri Ya fito daga bedroom ɗinshi dake a downstairs Ya nufi cikin babban falon,kaitsaye Upstairs Ya haye,a kiɗime yake tattaka staircases din benen,Bai nufi ko'ina ba sai ɗakin Angel,Bugu ɗaya yayi ma ƙopar ta buɗe,Ko'ina duhu,Kunna hasken ɗakin yayi,nan take haske ya gauraye ko'ina,Wurga kwayar idonshi yayi kan angel dake ƙunshe cikin lallausan bargo,a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin,tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira"Angel!Angle!My daughter!azeezaty!Babu alamun zata farka,A hautsine Ya cakumeta,Ya sungumeta saman kafaɗarshi,Da sauri Ya fito daga bedroom din nata,Ya sauko downstairs,Kaitsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke,ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar range rover,back seat ya buɗe ya kwantar da Angel,tukunna Ya buɗe diver seat ya shige ciki,a gaggauce yayi ma motar key,adai dai bakin gate ya tsayar da motar,A hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin,kafin ya koma Cikin motar  Ya fusgeta da gudun gaske,Fitar motarshi keda wuya,Wasu danƙara danƙaran motoci gudan shida suka nufo shantalelen titin da zai sadaka daga gidanshi,da alama sun hango motarshi hakan yasa suka bi bayan motarshi da wani irin matsiyacin gudu,Hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,Saboda Ya hangi Motocin dake biye da motarshi ta Cikin Mirror ɗin motar,hakan yasa shi ƙara gudun motar,la66ansa na kyarma yake ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,Shi kanshi baisan inda zai dosa ba,Driving kawai yake yi a makance,shessheƙar kukan angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi,da alama ta farka,sakamakon gudun ceton ran da yake yi dasu,Yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar,har hancinta Ya fashe jini ya soma zuba,

  A ruɗe take furta"daddy...what's happening,where are u we going in this darkness night...."ƙaramar yarinyace da bazata wuce 11years aduniya ba,maganarta ma daƙyar take fita saboda Halin da take ciki

  Hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,yana mai danasanin yin Aikin Jarida fiye da tunanin me tunanin,saboda shine silar shigarshi cikin wannan tashin hankali,

  "Angel Am really sorry......na cuci rayuwarki,A yau daddynki bazai iya cetonki ba,Angel bazan jure rashinki ba,bazanso laifina ya shafe ki ba...."yana magana yana kuka,tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding,jini duk ya 6ata fuskarta,cikin shessheƙar kuka ta kuma cewa"Dad...My nose is bleeding,Zan mutu,gaba ɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi Yaji daɗi,Baisan amsar da zai bata ba,Iya sorry kawai yake iya furta mata,


Har yanzu motocin nan na biye da motarsu,lokacin daya fara jin saukar Alburushin bindiga a bayan motarshi,A gigice Ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji,me duhun gaske,shi kanshi baisan ina zai dosa ba,Ga manya manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar,A ruɗe Yayi parking ɗin motar Ya zagaya ta back seat din motar jiki na kerma Ya zura hannu ya ɗauko angel,daga ita sai rigar bacci ajikinta,Sumar kanta duk ta rufe fuskarta,da gudun gaske yayi cikin dajin da ita Yayin da take sa6e asaman kafaɗarshi,Hasken motarshi ne daya bari a kunne yake haskaka mashi gabanshi,yana Cikin gudun nan Batare daya ankara ba,ya ɗaura kafarshi saman wani ƙarfe mai tsatsa,wanda ke a tsire cikin ƙasa,kaifinshi tamkar na Wuƙa,zuruf Ƙarfen Ya shiga ta cikin tafin ƙafarshi Ya 6ulo ta sama,wani irin raɗaɗin azaba ne yakai mashi ziyara,tsigar jikinshi duk ta tashi,tuni jini ya wanke ƙafarshi,Sam ya kasa Motsawa daga tsayen da yake A hankali Ya shiga furta"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,cikin kyarma Yake ambaton hakan,Muryar angel ce ta katse shi"Dad let's go Home,nan fa daji ne,akwai kura da Zagi zasu Cinyemun,daddy kodai mafarki muke yi ne"?tayi tambayar still tana shessheƙar kuka,


Cikin sanyin Murya ya bata amsa"Mafarkine angel,ba gaskiya bane"hannayenta ta sanya tare da zagayo dasu ta wuyanshi,Ta manna mashi kiss a gefen fuskarshi,

  "Daddy,to mu tashi daga mafarkin,Angel tsoro take ji"tamkar ya fashe mata da kuka haka Yake ji,


A tsiyace Suka kwararo da gudu Cikin dajin daya shigo da motarshi,Aiko da Jin sautin shigowarsu,baisan Lokacin daya Fisgi ƙafarshi ba,Ya ɗago da ita daga Jikin ƙarfan,jini ya dinga kwaranya,A haka yadinga Jan ƙafar harya karaso dai dai Wani uban rami mai zurfi wanda kasanshi tafkeken ruwane ke gudana,Tsayawa yayi zuciyarshi na raya mashi cewar Ya jefar da angel cikin ruwan,Ya ƙwammace Ta mutu acikin ruwan data yi mutuwar wulakanta a hannun mutanan da suka biyosu,don babu ɗigon imani akansu,In suka kama mutun fetur suke xazzaga mashi su ƙonashi har Lahira,Yayi zurfi acikin tunanin Angel sai kuka takeyi,Sautin motocin miyagun da suka biyoshine yasa shi dawowa cikin hayyacinshi,Allah sarki,Yana ji yana gani,Haka Ya ɗaga Angel sama Yayi wurgi da ita,tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan me zurfin gaske yana Jiyo sautin kururuwarta,



Ba ƙaramin tashin hankali bane zaisa Uba Yayi silar mutuwar ɗiyarshi,


Saboda tsabar kuka Jikinshi har jijjiga yakeyi,Duk yaji ya tsani kanshi,Don tuni ya fidda rai da rayuwa acikin duniyar nan,domin kuwa angel Tamkar numfashi take agareshi,jiki a mace ya zube saman guiwowinsa agaban ramin,Wani irin jiri ne ya soma kwasarshi,Nan take ya yanke jiki Ya faɗi a mace,




Adai dai Lokacin suka ƙaraso da motocinsu,bayan sunyi parking sun kewaye shi,Wasu gabza gabzan samari ne suka fito,ƙirar samudawa,Baƙake wulik babu ɗigon Imani akan fuskokinsu,sunyi shigar bakaken kaya da alama Bodyguards ne,Atare suka buɗewa Ubayen gidan nasu murfin motocin don su fito,


Abun ban mamaki,Manyan mutanane Dattawa,Suna sanye Cikin shiga ta mutunci wato shigar hausawa,Shadda Hada malun malun kai kace mutanan arziƙi ne,


Koda fitowarsu,basu daura idonsu akan komai ba sai akan Gawar Taj dake yashe cikin ciyayi,


Guntun tsoki ɗaya daga cikinsu Yaja"Mala'ika Ya riga mu ɗaukar ranshi,Ba haka naso ba"


na gefenshi Yace"Banso yayi salihar mutuwa irin wannan ba,amma duk da haka bamu makaro ba,tun anan zamu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun munkar da nakir,"


Tuntsirewa sukayi da wata irin mahaukaciyar Dariya,lokaci guda kuma Suka ɗaure fuskokinsu,


Ɗaya daga cikin alhazawanne Ya juya tare da kallan ɗaya daga Cikin Miyagun da suka zo dasu,Cike da bada Umarni yace"Miƙo mun galon ɗin fetur tare da lighter"a hanzarce wanda yayi ma magana Ya nufi motocinsu,


"Maganin masu kunnan Ƙashi kenan,angaya masu shiga gonarmu abune mai sauƙi,"bai kai ƙarshen maganar ba,Aka miƙo mashi galon din fetur yasa hannu Ya kar6a,cire murfin Yayi tareda zazzage mashi fetur ɗin Ajikin Rigarshi,sharkaf suka wanke shi,

   Dalilin dayasa zamu ƙona shi,saboda gudun mubar wata hujja da zaisa A zargemu,


Basu ƙyasta lighter ɗin ba,har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyastata,ya jefe saman ciyayin dake a kewaye dashi,Da gudu wutar tashiga Cinye ciyayin har ta hau saman jikinshi,


A lokacin sun shige cikin Motocinsu,da gudu suka fisgesu tare da barin Cikin dajin....,.........Cikin ƙanƙanin Lokaci,Wutar tacinyeshi ƙurmus,


The Begining Of The Story,


_Paid Book ne,Amma Ba'a fara payment ba,Sai an kammala free tukunna👌_


_Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i wannan numbobin_


08103884440

08169856268


Mu hadu a Next page😍In jiran ruwan Comment,Ta hakan zangane kunyi farin ciki da dawowata😍


Daga Abu Dharri al-Gifariy Allah ya yarda da shi daga Annabi (SAW) cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa Mai Girma da ɗaukaka ya ce:


“Yaku bayina Lallai ni na haramtawa kaina zalunci, kuma na sanya shi abin haramtawa a tsakanin ku, kar ku zalunci juna. Ya ku bayina, dukkanku ɓattatu ne, sai fa wanda na shiryar dashi, ku nemi shiriya daga gare ni, ni kuma zan shiryar da ku. Ya ku bayina, kowanen ku mayunwaci ne, sai wanda na ciyar dashi, ku nemi ciyarwata ni kuma zan ciyar da ku. Ya ku bayina kowanen ku tsirara yake, sai wanda na azurta shi da yi masa sutura, ku nemi suturata to zan yi maku sutura. Ya ku bayina kukanyi kurakurai dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gaba ɗayan su, ku nemi gafarata ni kuma zan yi muku gafara. Ya ku bayina, baku isa ku cutar dani ba, ballantana kuce zaku cutar da ni. Baku isa ku anfanar dani ba, ballantana kuce za ku anfanar dani. Ya ku bayina, da ace na farkon ku da na ƙarshen ku, da mutanen ku da aljannun ku, su kasance a bisa zuciyar wani mutum ɗaya a cikin ku mafi tsoron Allah, inda zakuyi haka hakan bai ƙara komai acikin mulkina ba. Ya ku bayina, da ace na farkon ku da na ƙarshen ku, mutanen ku da aljannun ku, su kasance a bisa zuciyar mutum ɗaya mafi kowa fajirci, inda zakuyi haka hakan bai rage komai a cikin mulki na ba. Ya ku bayina, da ace na farkon ku da na ƙarshen ku, mutanen ku da aljannun ku, su tsaya a wuri ɗaya, kowanen su ya roƙe ni, in bawa kowane ɗaya abinda ya roƙa, hakan bai rage komai ba na daga abinda ke wurina na mulki na, sai fa gwargwadon abinda allura zata rage idan antsoma shi cikin ruwan teku an zare shi. Ya ku bayina, ayukkan ku dai yana kare ku gare ku, sannan in cika muku ladar ku, wanda duk ya sami alheri to ya godewa Allah, wanda ya sami kansa a mumunar tafarki kar ya zargi kowa sai kansa”.

Muslimu ne ya ruwaito shi

Share Fisabilillah😍

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post