Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 4

Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 4

 

Bakon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 4

_*BAKON MUNAFIKI!!!*_

_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_

                _👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

  _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

       __AREWABOOKS:MSSXOXO_

     _WATTPAD:MISSXOXO00_




            _FREE PAGE: 004_


_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


____

   ASOKORO



  Sannu a hankali motocin suka dauke su zuwa hamshakiyar unguwar ta asokoro da ke birnin Abuja. Tsayawa bayyana tsaruwar unguwar da ke lullube da bishiyu ma bata lokaci ne.


Abu daya zuwa biyu zan iya fayyace muku kamar dankareren gidan Alhaji Abubakhar daya sha kudi ya koshi.


Dauke gidan yake da fenti kalar sararin samaniya. Sai shekin kalar toka ne ke walwali ajikin sa. Ga wasu bishiyu da wani jijjigaggen gate.


Motocin su suka kutsa cikin gidan dake dauke da babbar harabar farfajiya da zaa iya faka motoci da yawa.


Sai kukan tsintsaye ne ke tashi daga garden din da ke gefen wata kofa acikin gidan ta baya.


Ma'aikatan gidan suka tashi da sauri don temakawa bakin da suka ga suna ta fitowa daga cikin motocin. 


Amaal na fitowa daga mota ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sakamakon gajiya dake dawainiya da ita ga wani bacci dankararre dake kokarin rufe mata idanu.


Dakyar ta iya jan kafafun ta tabi bayan ayarin na su da suka shiga cikin gidan bakunan su dauke da sallama.


Alhaji Abubakhar ne agaba sai Hisham dake biye masa abaya. Sai tawagar su amaal dake bayan su. 



    Daga sama ta sakko. Kana kallon ta sau daya kasan matar gidan ce. Duba da tsananin kama da suke yi da Hisham din. Sai dai Hisham din ya debo tsawon mahaifin na sa Alhaji Abubakhar. Amma komai na mahaifiyar sa ya dauka harta murmushin da take yi.  


Sanye take cikin wadatacciyar doguwar riga ta atamfa. Samfarjn style din T-bubu. Ta yane kanta da babban mayafi. 


"Bismillan ku lale marhaba... Ku zazzauna dan Allah..Hisham basu nan su zauna mana ka koma can."


Amsawa suka shiga yi baki dayan su . Nan suka sake sabuwar gaisuwa daya bayan daya bayan sun zazzauna akan kujerun parlorn. Dake parlorn babban ne dake shake da setin kujeru uku kowanne kuma Turkish Royal. Da suka tsaru karshen haduwa. 


Tashi tayi ta nufi wata kofa wadda itace zata sadaaka da kitchen. Tana kiran,


"Hadiza kuzo ke da su Laure."


"Toh Hajiya."


Cikin mintuna kalilan sai ga maaikatan sun fara ajiye tirarrukan abinci da abin sha. 


"Ga bandaku na uku anan akwai biyu a sama. Ga wajen sallah can da hijabai."


Suka shiga yi mata godiya. Amb junaid na daga zaune bayan ya sha ruwan robar da ke hannun sa ya ajiye yace,


"Sannu da kokari... Mun tashe ku a tsaye. Allah ya saka da alkhairi."


"Bakomai...Mune da godiya. Allah yabar zumunci."


"Allahumma Aaameen." Yan parlorn baki daya suka hada baki wajen amsa ta


Mai gidan ta. Alhaji Abubakhar ya ce da ita,


"Yau buri na ya cika, babban bakon mu da nake burin kasancewar ziyarar sa agidah na yazo . Takanas da kansa da iyalan sa. Gaskia nayi matukar farin ciki. Shine Ambassador Junaid da nake gaya miki yana Madina shi da iyalan sa baki daya... Tun lokacin da aka bashi mukamin har ya zuwa ajiyewar aikin sa bayan shekaru hudu ne yanzu nake ji ko yallabai?"


"Eh shekaru hudu ne ranka ya dade" Amb. Junajd ya amsa shi.


"To kiga fa.... Sai yanzu Allah yayi ya waiwayo gidah Baki daya da iyalan sa. Bai fara sauka a koina ba sai gidah nan ya amshi tarin gayyatar da nake ta masa. Ina rokon ya zoyarci gidan ya zama bako na."


Amb junaid yayi murmushi kawai yana girgiza kai,


"Baka da dama ranka ya dade"


"Allah yallabai dagaske na ke. Ai kowa ya sani. Naciri babbar tuta. Har garin nukaa zani takanas nayiwa Hajiya godiya."


"Saboda transit din da mukayi anan?"


Suka tafa suna kyalkyalewa da dariya. Ragowar yan parlorn na tayasu. Idan ka cire Amaal da Hisham a gefe da ke wa juna kallon kasan idanu...


"Toh Allah yasa dai su iya cin cimar tamu ta nan ko daddyn Hisham?"


"Chi kai... Ai bamu baro gidah ba. Dukkanin abincin da ake ci a Nigeria munaci acan. " Cewar Hajiya hadiza tana karkada kafa daya kan daya. 


     Haka dai suna yar hirarrakun su jefi jefi, Suka kammala cin abinci tas. Don wanu abun ma ko tabashi basuyi ba. Dubada girke girken da akayi musu suna da yawa . Don haka sai sadaukar da wasu akayi ga mabukata awaje. 


Bayan nan bandakin suka shisshhga suka yi tsarki. Masuyin sallah suka yiyyi. Mazan suka fita sukayi jam'i awaje. Kafin daga baya suka dawo ciki aka cigaba da hira.


"Ni fa nayi mamakin girman Hisham."cewar amb junaid.


Hisham dake gefe ya saka hannun sa a bayan kansa ya shafo keyar sa yana kakaro murmushi..


"Allah Alhaji? Dan dai ka dade baka ganshi bane. Gashi nan ya zama cikakken pilot."


"Kwarai kuwa tunda shine ya dakko mu ai daga can zuwa nan.. Don badan Allah ya temaka ma yayi dan tsaiko ba ai da tuni jirgi ya daga yabar mu. Amaal ta tafi siyan abu a shago lokacin ya kure."


"Ai gwara ku tsautsayi ne. Shi fa saboda tsabar wauta jakar wayoyin sa  data kayan sa ya manta a shagon wani baban abokin aikin sa balarabe. Wai wani abu ya zube a rigar tasa yaje ya canza waye waye duk shirme dai. Nace wannan ai wauta ce. Sai ache saboda jirgin mu ne."


Hisham ya tsrae Amaal da idanu. Kallon su ya sarke tayi saurin janye nata. Shi kuma yaki dauke nasa sai ma sake kafeta da yayi da idanun har ta kasa nutsuwa sosai tanata mutsul mutsul awajen zaman ta. 


"Menene hakane Amaal?" Cewar Hajiya J. mahaifiyar ta.


"Bakomai Hayateey zama na na gyara." Tana daga idanun ta suka hada kallo yayi mata murmushi. Domin sarai ya jiyo abunda ta fada da ma tanbayar da mahaifiyar tata ta mata. 


"To ai tsautsayi ne wannan yana iya jawa kan kowa. Banga lefin sa ba ga mai lefi, wannan yarinyar fa ita da gangan fa tana sani tatafi siyayyar shago itama. "


Alhaji Abubakhar yayi murmushi jin abunda amb junaid ya fada. Ya dan juya ya kalli amaal din,


"Itama yar wajen ka ce?


"Ta karshe ce ma..."


"Auta ce kenan?"


Amb. Junaid ya daga masa kafin yace,


"Eh auta ce..... Sunan Hajiya taci ai."


"Haba?"


"Allah kuwa."


"Ma shaa ALLAHU mai babban suna... Uwata ta kai na. Me ake kiran ki da shi?"


Cikin sanyayyar muryar ta mai sanyin da dadi ga duk wanda ya saurara. Ahankali a kuma nutse cike da tarbiya ga biyayya ga wanda kanta a kasa tace,


"Maryam... Amma Amaal ake kira na da shi ...."


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥



*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k



  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post