ππ²π©π’π§π π²
π« ππππΌπ πΏπΌππ'π.....!!π«
π©ππππ π¨ππ πππ πππ€π»
πͺππππππ 4️⃣
........Idanun dattijuwar cike da Ζwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata Ιaga Ζafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma itafa da sauΖi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata Ιaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key Ιin Ιakin ita kaΙai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai Ζamshi amma ta ce mata tana warin zufa. “ALLAH ya shiryeki Ζ΄arnan” ta faΙa cikin tausasawa tana Ιauke Ζ΄ar Ζwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaΖancin da Lulu ke mata tana Ζyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta Ζ΄aΖ΄anta dake Ζauye da Ζ΄an jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, dan in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf Ιin ne ya Ιan fi cin nasararta, dan shi har faΙa yakan Ιan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai Ιin bane ba....
Wannan kenan
∆•••••∆ ★ ∆•••••∆
Da ga airport babban kamfanin JiΖamshi's ya nufa ransa a Ιace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa'ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya Ζara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key Ιin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay Ιan rubutu ya haΙa da key Ιin. A takaice yace, “Ki bashi idan ya dawo”. Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da Ιan taΙe baki...
Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a Ζofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a Ζasan maΖoshi har yanzu zuciyarsa na masa Ζuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika'il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ΖasΖantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da Ζarfin Ζwanjinsa amma ba ΖasΖanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ΖarΖashin takalmin kowa ba. Da'ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata Ζasusuwa ya zubar da ita a airport Ιin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance Ζ΄a mace.....
“Ζan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faΙa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep Ιin maimakon amsa, ya zaro Ιari biyu a cikin aljihunsa ya miΖa masa. Bai jira mai napep Ιin da ke faΙa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..
*_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na Ζasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuΖar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ζa na bakwai a gurin Malam Mika'il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huΙu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuΖar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine Ζwallon Ζafa. Ya iyata matuΖa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire Ιinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga Ζwallo sai ya yanke jiki ya faΙi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al'amarin da asiri, sai dai shi yaΖi Ιaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara Ζwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan Ιan gwada yin Ζwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar Ζasa ma, ya fara neman aiki amma yaΖi samuwa duk da takardunsa sunyi Ζyau matuΖa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an Ιaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaΖanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya Ιaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da Ζwallon Ζafa ya ajiye gefe ya shiga ΖoΖarin sana'a, sai dai anan Ιin ma dai komai yaΖi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ΖanΖanin lokaci al'amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ΖoΖarin kamo can idan nan taΖi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu Ζ΄an uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika'il Idris Mawashi huΙu ne cif, hakama Ζ΄aΖ΄a su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da Ζ΄ammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay atπ
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka ananπ
09018600202
Idan katin waya ne kuma saika tura ananπ
09033181070
Ζ³an Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number Ιinπ
+22799643131
VIPπ₯π―
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*π₯°
Zafafaπ«Άπ₯
*_ALLAH ya gafartama iyayenkuππ_*