Darussan kwamfuta na ƙara farin jini a wajen ɗalibai
Health College

Darussan kwamfuta na ƙara farin jini a wajen ɗalibai

Darussan kwamfuta na ƙara farin jini a wajen ɗalibai
BBC/Getty Image

 Ɗaliban da ke kammala sakandare na zaɓar darussan kwamfuta fiye da kowanne lokaci a baya, a cewar Hukumar kula da Harkokin Shiga Jami'o'i da Kwalejoji ta Ingila (UCAS).

Alƙaluman takardun neman shiga jami'o'i a bana sun nuna yadda matasa 'yan sha-takwas ke ƙara nuna sha'awar karanta fannin kwamfuta "saboda tashen harkokin dijital da fasahar ƙirƙirarriyar basira", kamar yadda babbar jami'ar UCAS Clare Marchant ta bayyana.

Masu neman darussan kwamfuta sun ƙaru zuwa kusan kashi 10% idan an kwatanta da shekara ta 2022.

Sai dai, har yanzu fannonin kwamfuta su ne na bakwai a jerin darussan da suka fi farin jini a fagen karatun ilimi mai zurfi.

Yayin da kusan ɗalibai 95,000 suka nemi kwasa-kwasai a fannin kwamfuta da darussa masu alaƙa da ƙirƙirarriyar basira, kusan ninki biyu na wannan adadi ne suka nemi karanta fannin kasuwanci da gudanarwa wato 'Business and Management'.

Sai ɗalibai sama da 125,000 da suka nemi kwasa-kwasan da suka danganci wasannin kwaikwayo da ƙirƙire-ƙirƙire da zayyane-zayyane.

Darussa masu alaƙa da likitanci da fannin kimiyyar zamantakewa da nazarin halittu da kimiyyar wasanni da injiniyanci da ƙere-ƙere dukkansu sun fi shahara a kan fannin kwamfuta.

Sai dai adadin masu neman karanta kwasa-kwasai masu alaƙa da kwamfuta na ci gaba da ƙaruwa tun daga shekara ta 2019, a cewar UCAS.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post