💖💖 *NIHAAD* 💖💖
By Khaleesat Haiydar📖✍🏻
All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar hankali da arziki me amfani, Allah ya saka maki da gidan Aljanna, 👏🏻 my special greetings to my own Barrister KH, Allah ya jibanci lamarinka, ya kara bude hanyoyin arzikin da xa ayi ma addini hidima💖 and My lovely aunt Rukayya Allah ya raya su Lil Khaleesat ya kara maki kwanciyar hankali.. And then my fans, i am who i am as a result of u guys, i love you all for the support always, Allah ya baku farin cikin duniya da na kiyama.... As usual support ur writer and may God bless u.
Tun da ta ji furucin wan Abbanta na karshe ta sakar masu kuka me karfin gaske, ta kalli Mahaifiyarta dake goge hawayen dake sauka idonta, babu alamar dai xata ce komai, Ta kalli Abba da fuskarsa ke hade tamkar hadari, shi ma bata samu courage din ce masa komai ba, yayyinta maza biyu dake parlon babu wanda yace komai cikinsu, ta dinga kuka da shesheka ta kalli Umma warce tayi tagumi, kallon Kakarta dake girgiza kafa tayi cikin rawan murya ta kamo hannunta tace "Don girman Allah kice su yi hakuri sharrin shaidan ne, don Allah kice su yafe min, ni ban san wanda yayi min haka ba..." Kakar ta warce hannunta tace "Ja can, Ke har kinsan sharrin shaidan alhalin kece shaidaniyar Nihad, ai kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu kunyata ki, ki ce lalle ke sai kin xama mutuniyar banxa abinda kaf xuri'a babu? Me yake burgeki da rayuwar 'ya yan iska har wannan abu ya same ki haka?" Kuka kakar ta saki tace "Allah mun gode maka, ka haifi ɗa ne kawai baka haifi halinsa ba, yanxu meye wannan kika mana Nihad" Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta fice daga parlon, direct dakinta ta nufa don tasan ko me xata ce a parlon nan babu wanda xae saurareta, tunda har Umma ma ta ki cewa komai to babu wanda xai ce komai, bayan ta shiga daki ta sa makulli ta fada kan gado tana rusa kuka kamar ranta xai fita, is this actually happening to her? yanda ta ga rana haka ta ga dare, gashi ta kasa sallah ko da raka'a daya ne, gaba daya ta fice hayyacinta, she wish all this is nothing but a dream, she wish xata farka taga mummunan mafarki kawai take, da asuba aka murda kofar dakin ta daga idonta da suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi ta bude, har aka gaji da Knocking aka bar wajen. Sai wajen karfe takwas na safe tana xaune saman darduma ta jawo wayarta da kyar, rabonta da wayar tun shekaranjiya, gaba daya bata son abinda xai hadata da wayar ma balle xuciyarta ya kara rauni, yanxun ma da ta dauko sim card dinta take son cirewa ta karya, missed calls da ta gani ya doshi hamsin, da messages da ya ninka calls din, ko wani message xance daya ne content dinsa, "Is that you on social media Nihad?" "Nihad what came over u?" "Nihad what is happening?" "Nihad something is wrong somewhere, ur Video is all over the internet" Fita tayi daga Inbox din hawaye me xafi na sauka idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da videos... Kashe wayar tayi ta ciro sim card din ta karya kamar yanda tayi niyya sannan ta jefar da wayar saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, wayyo ina ka xata farka taga mafarki kawai take da gaske, tun shekaranjiya take wish din nan, amma taki farkawa wanda hakan ke kara tabbatar mata da gaske ne duk abinda ke faruwa, babu wani xancen mafarki, Knocking din kofa aka yi, ta kalli kofar sai kuma ta mike a hankali ta nufi kofar ta bude, Umma ta gani tsaye, nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Umma ta shigo dakin ta kulle kofar, Nihad ta bi ta da kallo har ta xauna gefen gado, Nihad ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace "Umma don girman Allah ku rufa min asiri kar ayi min haka, wllh xan iya mutuwa, talk to Abba plss" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "It's too late Nihad, tun da har Alhaji Abubakar ne ya yanke hukuncin nan kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasa, ke dai naki addu'a, mu ma kuma muna nan muna taya ki da shi, it's okay to make mistakes as long as we learn from them, so ki kwantar da hankalinki everything will be alright, kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya shiryesa" Ta rushe da wani kuka cikin tashin hankali take cewa "Na shiga uku Umma, yanxu baxa ki iya ce ma Abba komai ba? auren dole fa xa su min, Umma ya xan yi da raina idan hakan ya faru, na shiga uku na..." Mikewa Umma tayi ta nufi kofa ta fita ta kulle. Compound Umma ta fita ta tarda Abba dake xaune shi kadai kana ganinsa kasan yayi nisa a tunanin da yake, ta nufesa ta ja daya daga kujerun dake wajen ta xauna tana kallonsa da damuwa karara fuskarta, he looks so disturbed also, ta kwantar da murya tace "Damuwa ba shi ne mafita ba Ranka shi dade, kayi hakuri ka sa ma ranka salama, Allah ne ya tsara haka, sai mu gode masa mu kara gode masa kawai" Abba ya numfasa yace "I think aurar da Nihad yanzu ba shi ne mafita ba Sumayyah, amma Engineer da Hajiya baxa su fahimci hakan ba, she is just 19, ga kuma wannan abu da ya faru, ta ina xata fara xaman aure bata gama mallakan hankalin kanta ba? da xa su sake shawara da ni da na ce masu gwara kawai ta tafi waje ta karasa karatun ta a can, ko da Uk ne...." Umma dake ta kallonsa tace "Wannan gaskiya ne, aurar da Nihad is not a way out, amma ni dai shawarata kar ka tofa naka a issue din nan Yallabai, duk yanda Yaya yayi da Nihad dai dai ne don 'er sa ce, kuma ran Hajiya xae 6aci idan ka bijiro da wannan batun na taje waje tayi karatu, gani kawai xa su yi kana ma goyon bayanta ne, naka kawai ido sannan kayi mata fatan alkhairi duk yanda suka yi da ita er su ce, kuma baxa su yi abinda xai cuceta ba, tunda suka ce aure mu xuba masu ido duk yanda suka yi dai dai ne, shawara ta biyu kuma kada ka kuskura Yaya yace xai hada Nihad da daya daga 'ya yansa balle ma bana tunanin xa ayi hakan kawai in case xa a bijiro da wannan gaskiya ka nuna a'a, don in har aka yi hakan zumunci xae tarwatse kasan su waye 'ya yan nasa da iyayensu, yara ne masu ji da kansu wa enda ba sa rayuwa a kasar, don haka kar ka soma yarda... don walakantattciya xasu mayar mana da er mu, ni yallabai yanda video din nan nata ya tafi viral gwara kawai a samo wani da ba kowa ba, bawan Allah wanda ba ma shi da abun duniya, shi kadai xai iya aurenta ya rufa mata asiri su xauna lafiya ba tare da ya goranta mata wataran ba, bai kuma walakanta mana ita ba, kyau ace ma a karkara yake rayuwarsa yallabai" Abba ya daga kai yana mata wani kallo babu ko kiftawa, tace "Atoh Allah ya baka hakuri, ka samo wani d'an senator ko Attajiri ka hadasu kawai, hakan ma dai dai ne...." Tana kai wa nan ta mike ta ce "Allah ya rufa asiri, ya tsare yan baya" Daga haka ta bar wajen, Abba ya dafe kansa. Umma ta saka Abba tunani iri iri bayan ta bar sa a wajen, ta wani bangaren she is damn right, abinda ta fada gaskiya ne, babu wanda xai yi ma tayin Nihad ya amsa da farin ciki ko dadin rai, Nihad is nothing but a disappointment to him, bai taba xaton hakan daga gareta ba kuma yayi da ya sanin fifitata da yayi cikin duk 'ya yansa, yayi da ya sanin nuna mata so karara da yayi kan sauran 'ya yan sa, amma Alhmdlh tunda abinda tayi ya tsaya iya haka, shawaran da Umma ta basa kuma shi xai yi amfani da... Mai gadi ne ya bude gate jin ana horn, Abba ya bi motar da ta shigo compound din da ido har yayi parking, yana xaune aka samesa cikin ladabi ya mika masa ledan dake hannunsa yace "Ga aiken Alhaji" mikewa Abba yayi yace "Mu je can parlor daga nan ka kwashi takalman da xa ayi min polish ka ba mai gadi" Abba na gaba yana biye da shi a baya har suka shiga cikin babban parlon gidan, sannan main parlor din Abba, Abba ya xauna yace "Ka ɗan jira xan yi waya, xan sake aikenka ne" Mai gadi ne xaune a position dinsa tare da driver, mai gadin yayi kasa da murya yace "Ka ko ji abinda ke faruwa kuwa??" Drivern yace "Me ke faruwa?" Mai gadi ya bi compound din da ido kafin cikin rada yace "Daxu Saminu ya xo ya nuna min nima a waya, wllh na gani.." Driver yace "Me ka ga?" Mai gadi ya kai baki kunnensa cikin rada sosai yace "Wllh hoton tsaraicin fitsararriyar yarinyar nan ne duk ya baxu yanar gizo, da idona na gani a wayar Saminu, kai baka ganin duk gidan kamar anyi mutuwa ba, ai duk gidan alhini suke, Da yake baka da babban waya baxa ka gani ba" Driver ya kallesa da kyau yace "Tsaraici?" Mai gadi ya kwashe da dariya yace "Yo tsaraici mana, yar kamfai da rigar mama kawai ne a jikinta kuma hoto me motsi aka mata, duk halittar jikinta babu wanda bai fito ba malam, abun dai ba a cewa komai, ni Alhaji ne ma ke ban tausayi don ya shiga damuwa sosai" Yana kallon mai gadin yace "Kai a ina ka gani??" Mai gadi yace "Toh jira ka ga ikon Allah" yana fadin haka ya nufi boys quarters da sauri, ba a dau lkci ba sai gashi ya dawo rike da wayar saminu, ya mika masa, amsa yayi ya danna play a video din, ko second goma bai yi da kallon ba ya ajiye wayar gefensa yana kallon Mai gadin, Mai gadin ya kwashe da dariya yace "Toh dada, muma duk haka muka gani, Allah kadai yasan iyakar inda abun nan yaje, shi ma a wani gruf ya gani wai, har fesbook yace min ya gani, kaga daga yanxu sai dai ta daga ma wasu kai ba mu ba kuma" Dariya mai gadin ya kyalkyale da, Driver ya mike yace "Ga takalma in ji Alhaji a ba shoe shiner" Daga haka ya tafi boys quarters. Nihad na kwance edge din gadonta ta kafa ma agogon dake manne bangon dakinta ido, xuwa yanxu kam ta hakura da kukan da take, but she is so weak, har ta mance rabonta da wani abinci, babu wanda ke bin ta kanta a gidan banda Umma dake shigowa dakin nata lkci lkci, she still don't have the courage to go to her mother, Bude kofar dakin aka yi ta daga kai da sauri, Husnah ce ta shigo dakin da sallama fuskarta dauke da damuwa, ta karasa kusa da ita ta xauna gefen ta amma ta kasa cewa komai, Nihad din ma dai bata ce mata komai ba, Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Kar ki sa ma kanki wani ciwon kawata, duk abinda ya faru da mutum a rayuwa dama Allah ya tsara hakan, kiyi hakuri da kaddaranki, kiyi hakuri kiyi accepting with good faith" Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad, Husnah da ita ma har hawayen ya cika idonta tace "Pls have faith don Allah Nihad, koma waye yayi maki wannan abun Allah baxai bar sa haka ba, tun a duniya Allah xai bi maki hakkinki, ya saka maki" Nihad ta mike xaune ta fashe da kuka tace "Ji nake kamar in kashe kaina Husnah" Husnah ta rufe bakinta da sauri tace "Kiyi istigifari, who are u not to be tested by Allah?? Kar ki kuma fadin hakan, kowa da irin tasa kaddaran a rayuwa, ki dau naki with good faith nace maki, in sha Allah xaki cinye wannan jarabawan, muna nan muna maki addu'a, Allah ya rufe abun cikin gaggawa a daina yawo da shi a media" Nihad ta share idonta a hankali tace "How will i mend this damage?" Husnah tace "Allah will, ke dai ki ci gaba da addu'a, wllh kawata tunda naga abun nan Allah ya sani baccin kirki for the pass 3 days ban yi ba, amma koma waye yayi mana haka xai ga sakkaya daga wajen Allah, sai Allah ya saka mana" Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace "Kuma fa wai aure Uncle dina da Inna suka ce xa ayi min" Husnah ta xaro ido tace "What?? Aure?? Which of ur uncle are u talking about? Abbansu Hamid??" Nihad ta gyada mata kai, Husnah ta rike ha6a tace "But sorry to say Nihad yanxu duk rashin jin da su Zeenat da Pinky ke yi bai gani ba sai naki? Duk runz din da suke yi babu wanda ya hango nasu sai naki? Lallai kam ance laifi tudu ne, Kawai sbda wani axxalumin yaje yayi posting dinki halve naked shine xa ace xa a maki aure? Wa enda ma aka saki hotunansu fully naked ba ace xa a masu aure ba sai ke da naki nafila ne, Tabdi... to wai wa suka ce xa su aura maki?" Nihad tace "I don't even know, but i am thinking of running away" Husnah tace "Nima nayi wannan tunanin, kada ki wani tsaya a cuceki a...." Bude kofa aka yi duk suka yi shiru suka juya suna kallon kofar, Yaya Farooq ne ya shigo dakin, Nihad sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don bata mance dukan tsiyan da yayi mata shekaranjiya ba, banda ma Umma ta masa jan ido ta kwaceta a hannunsa, Ya wani murtuke fuska yana kallon Husnah cikin daga murya yace "Ke, Uban wa ya baki permission din shigowa gidan nan, ta ina ma kika shigo don uwarki??" Husnah ta mike tana sissinne kai jikinta na 6ari, Ita dai Nihad banda faduwa babu abinda gabanta yake har ta fara kallon bandaki ko can xata shige ta kulle, Ya daka ma Husnah wani raxanannen tsawa yace "Xo ki fita kar in karya ki in karya banza" Jakarta ta dauka ta nufi kofa da sauri har tana tuntube, Tana fita ya doka ma Nihad wata harara yace "Kin ga result din bin ire iren kawayen nan ai..." Cikin rawar murya tace "Yaya ita Husnah ai babu ruwan..." Haureta ya kai kafa xai yi ta kauce, ta fashe da matsanancin kuka dai dai shigowar Umma, Umma na ganinsa, tana tafe hannu tace "Wato duk warning din da na maka bai isheka ba ko Farooq? Duk jan kunnen da nayi maka kar ka sake dawowa hanyar dakin nan watsi kayi da shi sbda ban isa ba ko?? To uban naku ma da ya ga abun nan ko nunata da yatsa bai yi ba balle ya kai mata hannu, kai ko zagi bai hadasa da ita ba, to wai shin ma ina ruwanka farooq? Meye naka? To wllh ka shiga hankalinka ka fita harkarta a gidan nan, ka shiga hankalinka nace, Shi Usman da yake ba mahaukaci bane ai nasiha kadai ya hadasa da ita, tun daga sannan ma a ina ta sake saka sa a ido, abun nan dai naga ba yaki bane, kai iskancin da kake sani ake yi balle a tsawatar maka?? To ahir dinka farooq kar ka kuskura in nuna maka bacin rai na wllh" Ita dai Nihad shessheka kawai take, shi kam banda kallon mahaifiyarsa babu abinda yake, ji yake kamar ya karya Nihad ko xai ji sauki a ransa, juyawa yayi ya fice daga dakin kamar xai tashi sama, Umma ta bi sa da harara, sai kuma ta ja tsaki tace "Rabu da shi, ba kanki farau ba ai" Daga haka ita ma ta fice daga dakin. Bayan magrib Nihad ta dake ta fita dakinta for the first time tun da gari ya waye, part din mum dinta ta nufa, duk gaba daya jikinta a sanyaye yake, ta bude kofar parlon a hankali Mumy na xaune parlon da sisters dinta biyu, tun jiya suke gidan amma ko bin ta kanta su ma basa yi, abun duniya duk ya ishesu barin da suka ga damuwar da yayarsu ta shiga, Nihad dai tunda Umma ta kwace ta a hannun Aunty Jamila rabonta da su sai kuma yanxu, banda faduwa babu abinda xuciyarta ke yi, Mumy ta nuna mata kofa alamar ta fita, kuka ta sakar mata ta xube nan bakin kofar cikin rawan murya tace "Don Allah Mumy kiyi hakuri ki yafe min, wllh i don't know how all this happen, i don't know who did this to me, mumy ba halina bane don Allah ki saurareni" Mumy tace "Fita nace Nihad" Kallon Aunties dinta tayi tana girgiza kai wasu sabbin hawayen na sauko mata tace "Aunty Jamila don Allah ku ce Mumy ta yafe min" Ganin Mumy ta mike, ta tashi da sauri ta fice daga parlon xuciyarta na bugawa, kuka take sosai bata da option ta nufi dakin yayanta farooq, bata tadda shi a dakin ba ta rakube jikin kofa tana shessheka, ba a dau lkci ba ya shigo dakin daga masallaci, yana kokarin kulle kofar ya ganta, kan yace komai ta hade hannunta with tears tace "Ya farooq don Allah ka saurareni, only u will understand and listen to me, wllh i knew nothing about that video, ban san wa yayi min ba, ban san yaushe aka min ba, ban kuma san wanda ya fitar ba" Kuka take sosai, ya daure fuska yace "Shaye shaye kika fara da har baki san when and where aka maki video din ba Nihad??" tace "Believe me yaya Farooq, wllh ban sani ba, yanda ku ka gansa haka nima na gansa" Yace "Na rabaki da bin kawaye barkatai Nihad, na rabaki da yawace yawace da xuwa parties, har night party nasan kina xuwa don Sadeeq saw u, na maki magana kika karyatasa kamar bai san me yake ba, u are just different from every other child in this house, just look at the disgrace u have caused to our family, u have tarnished the reputation of our home, how will i face my frnds da suka sanki, my own blood with such act? Oh no, Subhanallah" Ta dinga girgiza masa kai tace "Don Allah ku yi hakuri yaya, i wish my life can end now because of all this, i regret everything" Xaunawa yayi gefen gado ransa a dagule, ita dai ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Yaya farooq i need one favor from u plss" Yace "U don't deserve that favor Nihad" tace "Plss yaya abu na karshe da xa ka iya min a rayuwa shine don Allah kar ka bari Abba su yi min auren dole, wllh xan iya mutuwa kaga har na gaya maka" Yace "What did ur boyfriend say about the video?" A hankali ta sunkuyar da kai tayi shiru, ya hade rai yace "Tambayarki nake" Cikin rawan murya tace "Yayi blocking dina...." Farooq ya gyada kai yace "Good" ta hade hannunta tace "Don Allah yaya, kasan consequences din auren dole kar ku bari ayi min, na yarda a min ko wani hukunci amma banda auren dole, idan ma xa a ce for the rest of my life baxan sake fita waje ba, sannan babu ni babu karatu har abada i agree but kar ayi min auren dole sbda wannan mistake din nawa, ka taimaka kayi ma Abba magana" Umma ce ta shigo dakin duk suka daga kai suna kallonta, tace "So kike ki kara tunxura Abbanki Nihad? Duk shirun da yayi maki bai isheki ba sai kin tunxurasa, Ba na baki shawaran kar ki ce komai a kan batun auren nan ba, so kike ki fusatar da Abbanki yayi maki abinda bai ta6a maki ba?" Faruq yace "Noo wannan ba magana bace Umma, we don't even know da wanda xa a hadata, ko ma me tayi ai da gatanta and she still have her right, su gani suke auren shine way out, whereas it's not" Umma tace "Toh tunda kai ka haifesu ai sai ka gaya masu way out" Ya girgiza kai yace "Umma idan ma auren ne ba sai a bari komai ya lafa ba, ta yaya abu na xafi xafi a shigo da maganar aure, waye xai aureta? Noo bata yi deserving wannan auren ba gaskiya" Umma tace "Ko ma wa xai aureta wannan ba damuwarka bane sai ka xuba ma iyayenka ido, su ai sun san abinda ya kamata, ko so kake ka nuna masu goyan bayan abinda tayi kake?" Ya dinga kallon Ummar tasa, Mikewa yayi ya fice daga dakin, ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo, sai da suka sauka stairs Umma tace "Farooq" ya juyo yana kallonta, tace "Naga kamar so kake ka ja ma kanka bakin jini gun Kakarku da Engineer, sannan nima hakan ya shafeni, kawai so kake ka ja min maganan da ba shi da ranan mutuwa gun tsohuwar nan, don haka kar ka sake tofa komai a kan lamarin nan, ita kanta uwar da ta haifeta taki cewa komai har yanzu, me magana dama daga ni sai kai, kuma a hakan ma haushinmu ake, don Usman ma bai tsoma kansa ba balle a ga nasa, to ba Uba daya ba, ko ciki daya ku ka fito da Nihad ni dai nace ka janye bakinka daga issue din nan domin a samu masalha, daxu Abban naku ma ya kirani wai ya tafi karkara neman wanda xai hadata da, to idan ana son asiri ya rufu ai sai dai hakan dama, to wa xai yarda ya aureta a nan dai cikin gari? don haka nake kara gargadinka, kar ma ka fara cewa a fasa aure" Faruq yace "Karkara kuma?" Umma tace "Ehh nan fa, ko ka ga alamar Nihad xata samu miji cikin gari ba karkaran ba nace, da wannan mummunan abin da ta aikata wa xae yarda nasa ya aureta?" Yace "Ah haba, karkara kuma, noo ba dai karkara ba, waye ya ba Abba wnn muguwar shawaran? Karkara fa kike ce Umma" Strictly Umma tace "Farooq" ya daga kai ya kalleta tace "I am giving u this serious warning, kada ka kuskura ka sake tofa naka a wannan lamarin, kaji abinda nace maka??" Bai ce mata komai ba, tace "To na dai gaya maka" daga haka ta bar wajen ya bi ta da ido.
💖 *Bitter Rivalries*
And i came really prepared...... 🤗
Contact me directly via👇🏻
07087865788✍🏻