Hamshakiya chapter 1 by Jiddah S Mapi

Hamshakiya chapter 1 by Jiddah S Mapi

 

Hamshakiya chapter 1 by Jiddah S Mapi

*🌸HAMSHAƘIYA*🌸

 Na 

_jiddah S Mapi_

*Chapter 1*

                ~Amrish ki ajiyeta kawai ba zatayi shiru ba, kinsan wannan yarinyar da kukan tsiya dan Allah ki huta kema, yau kin gaji kinyi aiki sosai,  ki kyaleta kawai"

wata mata ce zaune a gefen katifa tana naɗe kaya tana sawa cikin akwatin karfe dake gefenta, gefe guda kuma wata karamar yarinya ce wacce ba zata wuce shekara ɗaya ba take aikin kuka kamar zata shiɗe, wacce aka kira da Amrish itace ta juyo tana murmushi cikin zazzaƙar murya tace "umman manal ai zatayi shiru, ban gaji ba nikam"

kyakkyawar budurwa ce ƴar shekara 17, idan ka ganta zaka rantse batajin hausa sai larabci, kama take da larabawa sosai, farace sol gata da tsayi, batada rama kuma batada kiɓa sosai, idanunta wani kala ne kamar brown brown haka, fatar jikinta kamar ka taɓa jini ya fito tsabar kyau da laushi, fararen hakoranta wanda idan tayi murmushi suke bayyana ba karamin kyau suke kara mata ba, musamman idan gefen kumatunta ya lotsa nan zakaga asalin kyaunta ya kuma bayyana kamar ƴar tsanar roba, gaban goshinta gashine kwance luf-luf gashi baƙi ƙirin, eyelashes nata me tsayi ne gashin giranta kuma har suna haɗuwa don yawa da laushi, tsayawa kwatancen wannan halittan ɓata lokaci ne, saide muce tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan halitta.


saida tasa yarinyar tayi shiru ta hanyar lallashi da yi mata wasa kafin ta kwantar da ita, bayan tayi bacci, kallon wacce take gefenta tayi ganin tayi birgima ta matsa daga inda take, yasa ta gyara mata kwanciyar ta lulluɓata, mutane sun kai goma a ɗakin ciki akwai ƴammata wasu kuma kananan yara wasu kuma manyan mata wanda ba zasu wuce su uku bane, Amrish kamar kullum saida ta tabbatar kowa yayi bacci cikin yaran kafin ta raɓa gefe ta kwanta akan tabarma tayi pillow da hannunta kafin ta lulluɓa jikinta da hijabinta wanda bashi da wani tsayi, lumshe ido tayi kamar me bacci, saide baccin yaki zuwa hawaye masu ɗumi suka fara sauka daga idanunta zuwa kyakkyawan kumatunta, tunani ta fara, haka zamuci gaba da rayuwa a cikin wannan gidan? hakika girma a gidan marayu babu daɗi, ababen tausayi kala-kala wasu yaran babu iyaye, wasu kuma an haifesu cikin shege an jefar dasu babu yadda aka iya haka za'a kawosu suzo suna rayuwa a gidan marayu, gidan marayun da babu galihu babu kwanciyar hankali, sai tashin hankali da rashin samun abinci ingantacce.


shesheƙan kuka ta fara a hankali ta yadda babu wanda zai jiyota, umman manal dake kwance a kan katifa tace "Amrish nasan kuka kike ba bacci ba, sai yaushe ne zaki daina kuka akan rayuwar da kika tsinci kanki? haka Allah ya tsara mana nima anan na girma har nayi aure, saide banyi sa'an aure ba saboda mijina yaga banda gata a gidan marayu na taso ya rinƙa azabtar dani, amma na hakura har Allah ya rabani dashi, gashi na dawo ina cigaba da zama tare daku, kiyi hakuri Allah yana tare damu kinji?"

cikin son nuna kamar ba kuka take ba tace "bafa kuka nake ba kawai so nake baccin ya ɗauke ni"

murmushi kawai matar tayi don tasan halin Amrish akwai kawaici.



_Asuba ta gari_


yara ne kewaye da ita tana shirya su, wannan yana kuka wannan yana cewa ta bashi abincin break, Amrish ta zama busy duk wanda ya matso shi take yiwa shiri, saida ta gama sa musu kayan school kafin ta kalli ɗayan daya zauna a gefe yana kuka cikin muryan lallashi tace "meya faru na'eem nawa?"

maƙe kafaɗa yayi kafin yace "ba untynmu bane tace wai mu babu abinda muka iya sai roko dan jiya na roki pencil a wajen Shub"

shiru tayi kana daga bisani tasa hannu cikin hijabinta ta kwance bakin skirt nata ta ciro naira 20 ta mika mishi "gashi ka siyi pencil ɗin kada ka kuma rokon Shub abu kaji?"

da murna ya karɓa yayi tsalle ya rungume ta "na gode Unty Amrish"

murmushi kawai tayi "nima na gode na'eem"

sasu tayi a gaba su duka suka nufi hanyan school nasu, saida ta kaisu har bakin kofa kafin suka shiga ita kuma ta juya ta fara tafiya zuwa gidansu, gidan da suka tashi a ciki tun tana ƴar jaririya ta tashi ta ganta a wannan gidan marayun, hakan yasa ta ɗau duk wani wanda yake gidan matsayin ɗan uwanta, yara ƙanana kuma ganin kanne take musu, mata manya kuma tana musu ganin iyaye ne.


"to untyn yara har kin kaisu school ɗin?"

jijjiga kai tayi cikin sakin fuska matar tace "to Allah ya biya ki da gidan aljanna"

"ameen unty Khadijah"

shiga ciki tayi ta samu waje ta zauna, kallon abincin dake gaban wata tanaci tayi itama tashi tayi ta ɗiba duk da ba daɗi haka ta tura saboda yunwa takeji, saida ta gama ta ɗibo wankin kayan yaran wanda zasu sa idan sun dawo ta fita zuwa bakin bohold dashi, gaishe da sauran ƴammatan dake wajen tayi kafin ta buga ruwa ta fara wanki, ɗaya daga cikin waɗanda suke zaune tace "Amrish ke kam bakya gajiya da wanke wannan kazantan kayan yaran?"

girgiza kai tayi "a,a ai ba laifinsu bane kayan ne babu da akwai da bazasu bari yayi datti har haka a jikinsu ba"


taɓe baki sukayi kafin kowa yaci gaba da abinda yake gabanshi, wankin dayawa ne tanayi tana shanya har ta gama ta koma ɗaki, nan ta fara shirya dakin saida ya dawo mai kyau kafin ta share, aikawa akayi ana kiranta a hankali tace "tom kice ina zuwa wake kirana?"


"Shugaba ce take kiranki"

"tom Ina zuwa"

fita tayi daga ɗakin ta nufi hanyan office na shugaba, da sallama a bakinta ta karasa, madaidaicin office ne wanda yake da kyau kaɗan, wata mata ce zaune akan kujera me juyawa, matar tana da kiɓa sosai tasa farin shadda da jan mayafi, kallon Amrish tayi tace "zauna anan" tareda nuna mata wajen zama akan kujera, a hankali Amrish ta mike ta zauna, kallonta tayi sosai kafin tace "ina zainab?"

cikin girmamawa tace "tana bacci"

"yawwa naji daɗin haka, dama wata magana nake so nayi dake"


"Tom shugaba ina ji"


saida ta sauke numfashi kafin tace "tsakanina dake ne banaso kowa yaji kinji?"

jijjiga kai tayi.


"yawwa good girl, duk wanda kika ga ya samu cigaba a wannan gidan to ta wannan hanyan yabi"

shiru kawai Amrish tayi kirjinta yana bugawa, gabanta yana faɗuwa.


"wani Alhaji ne yake neman yara maza domin biyan bukata na rana ɗaya, so yake kullum a rinƙa bashi maza ƙanana yana ɗan biyan buƙata dasu, kuma nasan kin saba da wannan yaran sosai idan kinyi musu wayo zasu yadda da wuri, su kuma matan akwai wata mata da take neman matsayi me girma itama zata zo ranan monday a haɗata da guda biyar, zaki samu arziki wanda baki taɓa zato ba a rayuwarki, zaki zama babbar mace me faɗa aji a cikin garin Abuja, kuma nasan ba zan samu matsala dake ba, saboda kema kin gaji da wannan rayuwa na kunci"


mikewa tayi daga zaunen da take ta kalli matan ido cikin ido tace "kina nufin luwaɗi zaiyi dasu?"

jijjiga kai tayi "yeah that's what I mean"


hawaye ne suka taru a idanun Amrish cikin zafin rai tace "kin taɓa haihuwa?"

da mamaki matan ta kalleta "eh mana yarana uku maza biyu mace ɗaya"


murmushin baƙin ciki tayi "ki bada yaranki maza yayi dasu mana kema ai zai baki kuɗi dayawa"

a zafafe matar ta mike ta wanke fuskar Amrish da mari masu zafi guda biyu kafin tace "kina da hauka ne? yarana zakice in bada su? Idan kika kara wannan banzan magana saina hallaka ki"


dariya Amrish tayi yayinda idanunta yake zubar da hawaye tace "ashe kinsan zafin haihuwa kuma kike cewa akai ƴaƴan wasu, su ɗin ba mutane bane? muma ƴaƴa ne, yaushe zaku gane cewar marayu ma ƴaƴa ne?

bafa mune muka sa kanmu a wannan halin ba, Allah ne ya jarabcemu, a haifeka a gidan arziki ba yin kanka bane, kuma a haifeka a gidan talauci shima ba yin kanka bane, kuma ki sani muddin ina zaune a wannan gidan bazan taɓa bari burinku ya cika ba, waɗannan yaran kannena ne"

fita tayi daga office ɗin tana kuka sosai, abubuwan da suke faruwa sunyi yawa, tana gani suna girmar da ƴaƴa mata su jefasu hanyan karuwanci, da sunga kin girma kin fara zama mace saisu fara baki kulawa ta yadda zasu janyo hankalin maza zuwa wajenki, wasu su zama ƴan lesbian wasu kuma ayi luwaɗi dasu, wasu mazan su zama ƴan shaye-shaye wasu su zama ƴan daba karnukan farautar ƴan siyasa.


yanzu kuma har idanunsu ya koma kan yara ƙanana waɗanda basu san komai ba, ba zata iya gani ana cutar dasu ba, yanzu ace Na'eem dasu Ahmad za'ayi lalata dasu? ai kuwa ranan ko bacci ba zata iya ba, domin hakki ma kawai ba zai barta ba, wani irin mugu ne yake wannan maganan? wani mugun ne zai iya luwaɗi da yara kaman su na'eem? Innalillahi wa inna ilaihiraji'un duniya tazo karshe, ya ubangiji ka karemin kannena a duk inda suke.



"Ke Amrish kina lafiya kuwa?"

firgigit ta juyo tana kallon wacce tayi mata magana, a hankali ta share hawayen kafin tace "Zainab kin tashi?"

"eh na tashi ina kika kai hankalinki ina miki magana tun ɗazu kina tafiya kina kuka?"


"Ba komai ina tuna rayuwar gidan nan ne kawai"


"to ya zamuyi sai hakuri ai"

itama zainab ɗin kyakkyawa ce, saide bata kai Amrish ba domin Amrish duk gidan babu me kamo kafarta a kyau.

tafiya sukayi izuwa ɗakinsu suna shiga ta faɗa kan tabarma ta fara aikin kuka, wannan wani irin masifa ne? idan ta tuno maganan shugaba sai taji kamar kirjinta zai fasa ya fito tsabar zafi.

*Littafin kuɗi ne akan naira 400 kiyi magana ta nan idan kin shirya 08144818849*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post