Hamshakiya chapter 3 by Jiddah S Mapi

Hamshakiya chapter 3 by Jiddah S Mapi

 

Hamshakiya chapter 3 by Jiddah S Mapi

🌸 *HAMSHAƘIYA*🌸

    Na

Jiddah S Mapi

 *Chapter 3*

               ~Amrish ta shiga damuwa akan wannan maganan kullum tunani take tana kuka sa ido akan shige da ficen yaran, bata bari su raɓi kowa sai ita bata barinsu su zauna su kaɗai koda yaushe tana tare dasu, yau ba school tasa kowa a gaba tana yimusu lesson, suna fahimta sosai da sosai, sai dariya suke burinta tasa yaran cikin farin ciki kada suyi kewan iyayensu, a gefen ɗakinsu suke zaune anan take musu lesson ɗin domin ita Allah ya bata ilimi bata samu me tsaya mata tayi karatu bane, aikawa akayi a kirata, a hankali ta mike jikinta a mace tacewa yaran bari taje ta dawo, tana zuwa office taga manyan mutane ciki harda shugaba wacce ta zuba mata ido tana kallonta, ƙarasawa tayi ta zauna a gefe ta gaishesu, Amsawa sukayi ɗayan yace "ke ɗago kai ki kalleni"

a hankali ta ɗago ta kalleshi idanunshi jajaye gashi baƙi dashi, yayi dariyan mugunta yace "kece kika hana a ɗauki yara?"

cikin storo da rawan jiki tace "eh"

daka mata tsawa yayi "zaki buɗe baki kimin magana ne ko saina saɓa miki mara mutunci kawai"


Da karfi tace "eh nice"


"kenan wuyanki ya isa yanka, tunda kika tashi a cikin gidannan kece kike ɗaukan ɗawainiyan kanki?"

girgiza kai tayi cikin tsoro, yace jeki kawomin maza guda biyu yanzu zan nuna miki na fiki taurin kai, gabanta yana faɗuwa tace "kayi hakuri bazan iya ɗaukosu na kawosu da hannuna ba, idan nayi haka bazan taɓa yafewa kaina ba"


kallon juna sukayi su duka uku da suke zaune a wajen, shugaba ta kaɗa kai alaman dama ai na gaya muku tana da taurin kai, murmushi yayi irin na mugaye kafin yace "to ki zaɓi ɗaya, ko ki kawo guda uku ko kuma mu muje mu ɗibo guda goma"

a tsorace tace "zan kawo su"

jikinta yana rawa ta mike, tana jinsu suna cewa "marasa galihu kun samu ma zamu taimaka muku shine zakice bakwaso mu muke ciyar daku mu muke baku sutura kuma ku watsa mana kasa a ido"


fita tayi daga office ɗin har wani jiri yana shirin ɗibanta, kanta taji yayi nauyi ta rasa ta ina zata fara, gaba ɗaya jikinta ya mata nauyi, hawaye ma nema tayi ta rasa, a hankali take takawa har ta isa inda take musu lesson, Na'eem ne ya kalleta yace "Unty Amrish kin tafi kin barmu baki dawo da wuri ba"


Wasu zafafan hawayene suka cika mata idanu, ji tayi kanta yana cigaba da sarawa, a hankali tasa hannu ta share hawayen dake shirin sauka daga idanunta, zama tayi a gefe ta rasa ta inda zata fara, Ahmad ya matso ya rungumeta yace "Unty meya sameki?"

fashewa tayi da kuka me tsuma zuciya, tare sukazo su duka suna share mata hawayen

"ki daina kuka Unty bamaso kina kuka"


share hawaye tayi tace "kun san me?"

girgiza kai sukayi, cikin kunan rai tace "kuyi rige rigen zuwa office na shugaba duk mutane uku da suka riga shiga sune first, wanda basu shiga ba kuma saisu dawo zan kara yi musu wani kunji?"


Da ihu sukace "yes zamuyi"

kallonsu tayi tace "Aisha banda mata maza kawai"

matan suka koma gefe, mazan kuma suka jeru su goma sukayi haɗa kafa waje ɗaya nan ta fara kirga musu 1.2.3 cikin kuka sosai tace "go"

da gudu suka bar wajen suna rige-rigen shiga office ɗin, kifa kanta tayi a kasa ta fara wani irin kuka me tsuma zuciya, da ihu Ahmad yace "wayyo unty bamu ci ba"

hankali a tashe ta ɗago tace "wa suka shiga?"


"su na'eem ne dasu Aliyu"

wani irin bugawa taji kirjinta yana yi, Innalillahi wa inna ilaihiraji'un shikenan Na'eem ya faɗa hannunsu gashi babu inda zata kai kara a karɓa mata"


kallon yaran tayi tace "ku shiga ɗaki lokacin break ne"

shiga sukayi ita kuma taje bakin Office ɗin ta tsaya jikinta yana ɓari, shugaba ta fito ta tafi ta barsu da yaran a ciki,

jim kaɗan ta jiyo ihun na'eem yana kiran sunanta, hannu ta dunkule tana kuka sosai, kusan 30mins kafin taji yaran sunyi shiru, su kuma mutanen suka fito suna murmushi, kallonta sukayi su duka suka ciro kuɗaɗe masu yawa "gashi ki kaisu hospital a dubasu"

bata karɓi kuɗin ba sai zubewa tayi akan gwiwanta tana cigaba da kuka, watsa mata sukayi kafin suka juya suka tafi.


tashi tayi ta shiga ɗakin jikinta a mugun sanyaye, da kyar take iya ɗaga kafarta, kwance ta gansu basa ko motsi ga jini daya ɓata wajen sosai, ƙarasawa tayi da gudu ta rungumesu tana kuka, babu wanda yake motsi a cikinsu, cikin tashin hankali ta fita da gudu ta kira su zainab dasu umman manal, suna tambaya meya faru hanyan Office kawai take nuna musu, da gudu suka shiga ganin yara kwance a cikin jini suka fara tambaya meya faru? bata iya tace komai ba dan tana gudun abinda zaije ya dawo, ɗagasu sukayi aka kira me adaidaita sahu suka sa yaran a ciki, a tare da ita dasu zainab ɗin suka kaisu asibiti mafi sauki wato general, suna zuwa doctor sukace ba zasu karɓesu ba saida police, zubewa kasa Amrish tayi ta rike ƙafan likitan tace "dan Allah ka taimaka ba dan halinmu ba ka dubasu"

ciro kuɗin data kwaso daga kasa wanda suka watsa mata tayi ta mika mishi "gashi dan Allah shine iya kuɗin dake hannunmu ka taimaka mana mu marayu ne"


karɓan kuɗin yayi ya irga kafin yace "gaskiya wannan kuɗin ba zaiyi komai ba hajiya ku fitamin da wannan yaran anan, kuna ina har kuka bari akayi musu wannan lahanin? yanzu ko kashi bazasu iya rikewa ba"

watsa mata kuɗin yayi tana zaune daram a kasa ta gagara tashi, gaba ɗaya ta kasa motsi, zainab da Umman manal ba abinda suke yi sai kuka, Amrish ta mike batayi magana ba ta ɗau Na'eem zainab ta ɗau Aliyu sai Umman manal ta ɗauki Hafiz, fita sukayi dasu daga asibitin suka kuma kama napep suka shiga, asibiti me ɗan sauki sukace ya kaisu, ya kaisu kofan wani hospital me kyau, fita sukayi suka biyashi kuɗi yace kuɗin yayi kaɗan, saida Amrish ta kara mishi kafin ya karɓa suka shiga ciki.


kati suka yanka na ganin likita, saida suka ɗan jima kafin akace mutum ɗaya ta shiga, Amrish ce ta shiga domin ganin likita, tana zama yace "meya samu yaran?"


Tace "yawo sukaje shine aka dawo mana dasu haka, ka taimaka ka duba mana su dan Allah kada su mutu"

murmushi yayi yana daga zaune akan kujeranshi me jujjuyawa yace "calm down zan dubasu zasu samu lafiya amma ni kuma me zaki bani?"

da mamaki ta kalleshi cikin rashin gane me yake nufi tace "ga kuɗin da yake hannuna kayi hakuri dashi"


dariya yayi ya mike ya matso kusa da ita yana shirin taɓa ta ta buge hannunshi tace "me kake nufi?"


"Ohhh Baby girl haka kawai zan taimaka miki ba tareda nima kin taimaka min ba? sau ɗaya kawai zamuyi saina dubasu idan kuma baki amince ba saiku barmin hospital"

a firgice ta ɗago dara daran idanunta wanda suka sauya kala daga fari tass izuwa jawur ta kalleshi, durkusawa tayi kasa ta haɗa hannayenta biyu tace "dan Allah dan Annabi ka taimaka mana"

komawa yayi ya zauna "idan kin shirya sai kizo"


turo kofan akayi da karfi, ganin zainab ce ta mike da gudu taje ta rungumeta tana kuka tace "zainab ki tayani rokonshi"

janyeta zainab tayi daga jikinta tace "kije waje Amrish"

cikin kuka tace "me zakiyi?"


"kije waje kawai nace"

a hankali ta juya ta fita zuwa waje, zainab hijabin jikinta ta cire sannan ta fara cire riganta, matsowa tayi kusa dashi, saida ta kwaɓe ta zama ba komai ta kwanta a kasa tana kuka tace "kazo kayi amma kasa a dubasu first"

cikin jin daɗi ya kira waya yace a dubasu, matsowa yayi kusa da ita ya fara taɓa ta, wasu irin zafafan hawaye ne suke bin gefen fuskarta tana jin yadda yake taɓa jikinta, kashe wutan office ɗin yayi daga nan ya fara shiga jikinta, wani irin azaban zafi takeji saide batace komai ba, saida ya shiga jikinta ya rinƙa yin yadda yaso da ita, ya kai 20mins yana abu ɗaya kafin ya mike yace "good girl you're so sweet"

lumshe idanu tayi tanajin raɗaɗi haka har ta maida kayan jikinta, a hankali ta tashi ta fita daga office ɗin.


an bawa su Na'eem gado su Amrish ne a kansu bata wani kula da zainab ba hankalinta akan su Na'eem ɗin, Umman manal tana gefe tana bawa Aliyu ruwa, saide yaki karba sai shure-shure kawai yake, ganin ya sanƙare yana kiran Unty Amrish tayi ihu ta kira Amrish da gudu tazo tana kiran sunanshi "Aliyu?"

hannunta ya riko yana ɓarin jiki har ranshi ya fita, time ɗin zainab ta turo kofa ta shigo da kyar take takawa tana cije baki, jin suna kuka likita ya duba yace "ya mutu"


Kuka sukayi, Na'eem ma bai jima ba ya rasu, mutum ɗaya ne ya rage shine Hafiz Shima rai a hannun Allah, a hospital ɗin akaje wajen binne gawa aka binne su, Hafiz kuma suna bashi allurai har yayi bacci.


suna zaune su duka sunyi shiru babu me magana cikinsu, Amrish ce ta lura da yanayin Zainab tace "kina lafiya kuwa? me kika gaya mishi har ya yadda ya duba yaran?"


kallon Amrish tayi idanunta pal hawaye cikin muryan kuka tace "amfani yayi dani"


"what!!!?"

suka faɗa a tare, cikin kuka tace "kwarai nayi haka ne domin na taimaki rayuwan su Na'eem gashi kuma sun mutu"

kwantar da kanta tayi a jikin Amrish tana kuka me tsuma zuciya, da karfi Amrish tace "meyasa kika yadda dashi? nice ya kamata nayi wannan sadaukarwar ba ke ba zainab meyasa?"


umman manal ba abinda take iya faɗa sai kuka, haka har aka sallami Hafiz ba laifi jikin yayi sauki, su sukayi jinyan zainab har ta warke suka koma gida.


Amrish tana jin tambayoyin da yaran suke aika mata ta kasa amsa koda ɗaya ne, suna tambaya ina Na'eem da Aliyu tace "sun koma gidansu na asali"

basu fahimta ba sukace "muma yaushe zamu koma?"

cikin hawaye tace "sai ranan da Allah ya kiraku"


daɗi sukaje dan ance zasu koma asalin gidansu, raɓewa tayi a gefe tana kuka harda toshe bakinta dan bataso kowa yasan tana kuka.

_*littafina na kuɗi ne ki biya kafin ki karanta ₦400 ne kacal 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, turo evidence of payment ta nan 08144818849, masu kati kuma zaku iya turo mtn ta numbern dana ajiye*_

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post