YAYA ZANYI IDAN CUTAR HANTA TA KAMANI?

YAYA ZANYI IDAN CUTAR HANTA TA KAMANI?

 

YAYA ZANYI IDAN CUTAR HANTA TA KAMANI?

Ita cutar hanta cutace wacce yawanci bata cika baiyana a jikin mutum ba sai ta hanyar gwaji, mutane da dama na dauke da cutar hanta amma basu sani ba, shiyasa ma'abota kiwon lafiya suke bamu shawari kullum cewa muje muyi gwaji domin sannin lafiyar hantarmu.

Bayan munyi gwaji sa'annan likita ya tabbatar da cutar a jikinka, zakaci gaba da karbar kulawa gami da shawarwari daga wajensa domin kare hantarka daga lalacewa gaba daya wato SCARRING OF THE LIVER (Cirrhosis).

WANNE HANYOYI ZANBI DOMIN BAWA HANTATA KARIYA?

Hanyoyi da zamubi domin kare kan mu daga kamuwa da ciwon hanta sune kamar haka:

1. Mu rage/dakatar da shan giya da sauran abubuwa wanda suke dauke da sinadarai wanda a turance ake kiransu da (chemical's).

2. Muke cin abinci mai amfani a jikimmu, amma karmu yawaita cin abinci da suke gina jiki sosai.

3. Mu gujewa shan duk wani nau'in abubuwa na hayaki kamar su taba da sauran su.

4. Mu kasance masu yawan motsa jiki.

5. Mu rika samawa kan mu lokacin hutu.

6. Mu gujewa shan maganguna da basu da asali da kuma gujewa yawaita shan maganin gargajiya.

Daga karshe Munada maganin ciwon hanta mai kyau na assibiti wanda muke saidawa, idan kana bukata sai a tuntubeni ta wannan numbar: 07034638905.

Mun sani dama shi magani sababi ne, ita lafiya kuma na gurin ubangiji, amma babu shakka idan munbi wadannan hanyoyi zamu samu ingantacciyar lafiyar hantarmu dama jikin mu baki daya.

Muna addu'a marasa lafiya Allah ya basu lafiya masu lafiya kuma Allah ya kara musu lafiya amin.

Mashkur abdullahi Tsafe

Health educator

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post