MAGARYA
Magarya, wadda ƙananan ƴaƴan itaciya ce, ana samunsu a ko'ina a sassan duniya.
Waɗannan ƴaƴan itaciyar ba kawai tushen ƴaƴan itatuwa ba ce, amma kuma su na da kaddarorin sinadarin magani a tattare da su.
Tare da ɗanɗano mai daɗi, mutane kan yi amfani da Magarya bayan an busar da ita.
Haka nan, bayan ƴaƴan itaciyar ana amfani da ganyen domin maganganu daban-daban.
An san Magarya da sinadarin "antioxidant" kuma ta na iya taimakawa wajen magance damuwa da rashin barci, ta na kuma taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauƙi.
Har ila yau, ƴaƴan itaciyar ta ƙunshi nau'in alkaloids, da saponin, da kuma triterpenoid. Dukkan sinadaran uku su na taimakawa wajen tsaftace jini. Kyakkyawan tsaftataccen jini alama ce da ke nuna cewa duk mahimman gaɓoɓi sun sami isashshen jini mai wadatar iskar oxygen. Wannan ya na sanya ƙara samun kuzari da ingantacciyar lafiy
Akwai nau'in bitamin C a cikin Magarya, wadda ya ke fitar da fata mara kyau da kuma bayar da kariya ga fatar domin lafiyayya ta samu gurbin zama.
Bugu da ƙari, Magarya na da amfani ga tsarin juyawar ƙwaƙwalwa. A al'adance wasu mata kan yi amfani da Magarya domin rage juyayi da damuwa.
An bayyana cewa, Magarya na taimakwa wajen rage ƙiba, kuma ta na zama rigakafi ga kamuwa ga wasu ƙananan cututtuka.
Wane bincike ya kuma nuna cewar, Magarya za ta iya zama babban tushen sinadarin "calcium da phosphorous," wadda ke taimakawa wajen kula da ƙarkon ƙashin jikin ɗan adam. Musamman ga tsofaffi ko mutanen da ke da raunin ƙashi.