Tarihin Tsamiya da amfaninta ga Lafiya.

Tarihin Tsamiya da amfaninta ga Lafiya.

 

Tarihin Tsamiya da amfaninta ga Lafiya.

Tsamiya

Tsamiya, bishiya ce mai amfani sosai. Bincike ya tabbatar da cewa, dukkanin jikin bishiyar tsamiya ya na da amfani (Masset, Candia da Ocheng, 2015; Gilma da Watson, 1994; Muzaffar da Kumar, 2017), wadda ka iya zama amfanin abinci, magani, kayan aiki kamar katako ko makamashin wuta.

ASALI

Bishiyar tsamiya ƴar asalin Yammacin Afirka ce (Muzzafar da Kumar, 2017; Massete, Canadia da Ocheng, 2015).

SUNA

Asalin sunan tsamiya a kimiyyance shi ne Tamarindus Indica L. A Turance kuma sunanta Tamarind. Larabawa kuma na kiranta da Tamri hindi (تَمرِ هِندِى).

RAYUWA

Tsamiya, bishiya ce wacce take iya rayuwa a cikin zafin hamada mai tsanani, matsakaici da ma guraren da ba su da zafin. Guri guda da tsamiya, ba ta iya rayuwa a gurin shi ne guri mai gishiri. Wannan dalilin ne ya saka bata iya rayuwa a bakin teku. Saboda haka ta zamo bishiyar daji. Amma duk da haka akwai ƙasashen da ake yin gonarta a reneta.

Sassan Jikin Tsamiya

Saiwa: Ana amfani da saiwar tsamiya wajen haɗa magungunan gargajiya.

Gangar Jiki: Shi ne abin da ya fito daga ƙasa har zuwa rassa, abin da za a iya kira itace ko icen tsamiya. Ana amfani da shi wajen yin katako domin gini. Rassan kuma ana rufin ɗaki da su. An tabbatar da cewa, gara bata kama katakon da aka yi daga itacen tsamiya. Sannan kuma ana yin makamashin wuta da itacen tsamiya, kai tsaye ko kuma ta hanyar yin gawayinsa, kuma an yarda cewa itacen tsamiya ko gawayinta ya na jimawa yana ci.

Ganye: Ana amfani da ganyen tsamiya a matsayin abincin dabbobi. Sannan kuma ana haɗa magani da ganyen tsamiya a kimiyyance da kuma gargajiyance.

Ƴaƴan Tsamiya: Shi ne sashe mafi muhimmanci a jikin tsamiya. Domin a same shi ake shuka ta. Dukkan amfaninkan tsamiya da kuma sinadaran da ake samu a jikin tsamiya da za a zayyano a ƙasa a kansu za a yi magana.

Ƴaƴan Tsamiya

Kwanson Ƴaƴan Tsamiya: Ana amfani da shi wajen haɗa magani.

Ƙwallon Tsamiya: A cikin ƴaƴan tsamiya idan aka cire kwanson, aka fito da asalin ƴaƴan, su ma a cikinsu akwai ƙwallon; wato irin tsamiyar kenan. Da shi ake sake samar da wata tsamiyar.

Sannan kuma a kimiyyance ana yin roba da su sannan kuma akwai wani sinadari da ake kira fektin (Pectin) wanda ake saka shi a cikin magani domin ya bai wa magani kariya daga lalacewa.

Ƙwallon Tsamiya (Iri)

Fure: Ana kiwon zuma da furen tsamiya saboda ta na matuƙar son ƙamshin. Sannan kuma dai ana haɗa magani da shi.

Tsoka: Tsokar ƴaƴan tsamiya ana amfani da ita a gargajiyance wajen fitar da tsatsa daga jikin abubuwan da suka haɗa da zinare, azurfa, tagulla da sauransu.

Kiwon Lafiya

Amfanin tsamiya a ɓangaren abin da ya shafi kiwon lafiya ya haɗa da:

-Narkar da abinci.

-Saka jiki hutu.

-Ƙarin jini.

-Saukar da gudan jini, kasantuwar ta na ɗauke da sinadarin fotashiyom. Wannan sinadari kuma zai taimaka wa masu hawan jini wajen rage wa jinin gudu har ya hana shi hawa. Sannan kuma wadda ba shi da wannan larura to zai samu kariya daga hawan jini.

-Taimaka wa jijiya ta yi aiki. Sinadarin siyamin (Thiamin) da yake a cikin tsamiya shi yake taimaka wa jijiya ta yi aikin da ya dace a cikin jikin ɗan’adam.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post