A dangane da NAMIJI duk wadannan
abubuwan na iya hana sa haihuwa
1)- Karancin kwayayen halitta, Ko sakamakon haka mutum ya tsinci kansa, ko asakamakon yawan masturbation, hatsari, da sauransu.
2)- Rashin kwarin kwayayen halitta
3)- Cuta me karya garkuwar jiki, ko ciwon Asthma.
4)- Ciwon sanyi wato fitar farin ruwa daga gaba, musamman masu saduwa da mata barkatai
5)- Idan golon mutum suka zamto kananu ko daya yafi daya musamman in suna ciwo
6)- Ko wata matsala data shafi mazantakarsa wacce ta zamto ta gado ce: kamar kankantar azzakari ya zamto ba tsayi
7)- Cuttuka irinsu ciwon suga.
A MATA KUMA
1}- Ciwon sanyi dake sa fitar ruwa daga gabansu musamman in anyi sakaci batare da neman magani ba, zuwa PID, UTI da cervical cancer.
2}- Kumburi awani sashi na cikin mahaifa wato (polyp)
3}- K'arin cikin mahaifa (fibroids), mace na iya kaucewa wannan ta hanyar yin aure da wuri. Yan mata musamman ayanzu da yawa na haduwa da wannan larurar tare da ovarian cyst.
4}- Fara sha ko yin allurar magungunan hana daukar ciki kafin haihuwar farko ko kafin fara samun ciki
5}- Idan mace ta taba samun ciki awajen mahaifarta (uterus) memakon cikin mahaifa kamar yadda yake.
6}- Idan mahaifar mace ta samu matsala Kila ko sakamakon operation da aka taba mata abaya.
7}- Cuttuka masu wuyar sha'ani kamar Asthma ko ciwon suga ga mace.
8}- Haihuwarta da wata nakasa wacce bazata iya bari ta sami ciki ba (birth defects).
Wadannan sune mahimman abubuwan daka iya hana shigar ciki, saide kamar yadda nace baza ace gaba daya mace ko namiji baya haihuwa ba sai ansami kamar shekara 5 toh sannan ne lallai za'a fara tunanin haka, sannan atashi tsaye wajen neman mafita idan matsalar wacce za'a iya gyarawa ce
Allah yabamu lafiya
Mashkur Abdullahi Alkali Tsafe
Health educator