Shin Menene Ovulation?
Health College

Shin Menene Ovulation?

 

Shin Menene Ovulation?

OVULATION

Yana da matukar kyau da kuma muhimmanci ace mace ta rike ranakun zuwan hailarta kamar dai yadda wasu likitoci suka yi bayani.

A wasu lokutan matsalar rashin haihuwa ga wadanda suka yi aure hakan ya na samo asali ne daga rashin fahimta akan al’amura da suka sha bamban, da kuma suka shafi yadda halin da jikin mace yake, wannan kuma har da Ovulation, wato lokacin da kwan haihuwar mace yake kyankyashewa.

Ovulation shine wani lokaci da mace ke fafe kwan haihuwarta Wanda da zaran ta fafe ta kusancu miji to shikenan sai ciki da ikon Allah

Dukka duka 48hrs ne kachal idan ya wuce sai wani watan amma wasu lokutan bisa ga hikimar Allah kwan yakan kwana biyu yana jiran abokin tafiyarsa wato kwan namiji. akwai ciwon mara slightly painless contraction ba menses kikeyi ba menstral pains ne, ciwon daga hagu ko dama, wani lokaci idan kinji duka side biyu.

Lokacin ovulation lalle idan kina da kula zaki gane. Yakamata mu dinga kula domin akwai wani irin painless contraction da zakiji. Mun san  fallopian tubes dinmu guda biyu hagu daya a dama. So duk wata daga gefe daya ne kwan zai fito.

Ga kadan daga cikin alamomin ovulation: 

1- farko shine painless contraction zakiji wani irin ciwo a hagu ko dama.

2- zaki dinga jin menstrual pains slightly amma ba menses kikeyiba

3- Areola wato black point na nononki zai kara baki kuma nipple wato kan nononki zai mike yayi erect kuma akwai zafi kadan kadan musamman idan ana tabawa.

4- Vaginal fluid. Majina mai tsananin danko Wanda take zama kaman spring zai dinga fito miki a gabanki.

 5- Matsananciyar shaawar namiji zai kama mace a wannan lokocin.

6- Temperature na jikin mace zai karu, jikin ta yana daukan zafi, kuma ba zazzabin rashin lafiya bane.

Lokacin ovulation wani lokaci ne na musamman da ya kamata mu kiyaye idan kuma kayi rashin saar mai gida baya gari kokuma ba kwananki ba bane to lalle kinyi missing sai kuma wani watan.

 Sai dai yana d matukar wahala gane wannan lokacin musamman ga wacce take da irregula period.

Wannan lokacin kowace mace da irin nata wacce take da irregula period baza ta taba ganewa ba.

Saboda Haka a dage matuka idan aka dage zaa samu abinda akeso.

Idan kuma nema kike yi sai ki dage shima da neman wannan muhimman lokaci wanda idan kika bari ya wuce sai kuma wani watan.

 Shiya yasa zakuji hausawa suna cewa daga sau daya inji mai kunika.

Idan kina gudun ciki tun daga 8days din gama period har zuwa 15 days sai a dau hutu na kusanci da mai gidan idan ba

Duk cikin method na Family planning shine mafi sauki but sai an daure shine ake kira da " Billing method" kokuma "Calender method".

Akoi rubutun da mukai dalla dalla akan calendar method za mu kawo muku domin koya ta gane nata lokocin.

Lafiya Uwar Jiki

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post