Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 9

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 9

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 9

 _BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

         _09_

    Bakunan su dauke da sallama suka shiga babban parlorn Hajiya. Wasu daga cikin iyalin ta sun zo suna zazzaune. 


Amb. Junaid na daga gefen hajiyan a a kasa yana zaune. Ya sanya hannun sa duka biyun yana yiwa kafafun hajiyan tausa.


Amsa sallamar yan parlorn suka yi naki daya. Domin a ranar ne mahaifin su zaa dawo da shi daga kasar south Korea inda aka kaishi don yo masa eani aiki a hakarkarin sa. 


Dukkanin yaran na sa sun hallara da sauran yan uwa da 'ya'yayan su.suna tsammatar dawowar tasu


Hajiyan na zaune ne a babbar kujera me cin mutane uku. 


Sai Babban wansu Alhaji Nuraddeen, 'Ya'yan yan uwa nace da shi, Bappah na kandemi, Sai kanin sa da ke binsa a kusa da shi, Honorable Minister of finance, Alhaji Jalaludden  Muhammad anace da shi Bappahn Hajiya... Sunan kanin hajiyar yachi mai rasuwa. 


Sai ta ukun su wato mabiyar Alhaji Jalaludden... attorney general ce ta kasa, Justice Fateemah suna ce da ita (Gwaggon court)..


Sai Bappah Abdullahi. Wato farfesa/professor Abdullahi suna ce da shi Bappahn Istanbul. Saboda ya zauna a Istanbul.


Daga gefen wasu tumtum da suka sha kawaatuwa da wani irin kyalkyalin beza kuma Dr. Aisha ce a zaune ta mike kafafun ta. Gaban ta da kofin tangaran ne dauke da kunu aciki tana juya shi da sukarin data zuba.


  Baki daya dai yaran hajiyan sun hallara.... 


Su Hajiya hadiza suka karasa shjga cikin parlorn suka zaazauna. Daya bayan daya suka fara gaggaushe da juna..


Amj Junaid na daga gefen Hajiya shi dai yana mai cigaba da matsa mata kafafu.. wasun su sun amsa musu fuskokin su a sake wasu daga ciiki kuma fuskar nan tasu babu yabo babu fallasa.


Alhaju Jalaludden wanda shine babban Yayan su bayan Alhaji Nuraddeen. Mikewa yayi yana gyaran zaman babbar rigar jikin sa.


Amb junajd ya daga idanu ya dube shi alokacin ya kai kansa ga agogo yana son yaga lokaci 


Wata harara mai tattare da tsantsar tsana da kyamata ya zuba wa amb junaid. Ya karasa wajen hajiyar tasu ya zauna daga gefe har yana mirje yatsun amb junaid dake maya tausa abisa sani kuma ya take sun.


"Hajiya ni zan dan fita..."


Hajiya bacci ya fara fusgar ta. Da sauri ta dan bude idanun ta,


"Iyye? Magana ake?"


"Jalaludden ne hajiya..." 


"Ina zakaje kuma?"


"Zan dan futa ne Hajiya na shawo iska....."


"Ba zaka jura su dawo ba?"


"A kofar gidah zan dan huta . Nan din ne acike."


"Toh shikenan Allah yayi albarka."


"Aamin Hajiya."


Mikewa yayi daga zaman da yayi a gefen ta. Ya fuce da sauri. Yana fita.Alhaji Nuraddeen yabu bayan sa.


Professor Abdullahi ya daga idanu ya dube su ya mayar kasa kawai yana jujjuya kai. Kasan makoshi yake furta,


"Allah ya kyauta...."


Amb junaid baki daya jkkin sa sai ya sake masa sanyi. Ya rasa wacce iriyar wutar kiyayyayar ce ke sake ruruwa a zukatan yan uwan na sa dake suke uwa daya uba daya.


"Junaidu kaga yadda nake renovating asibitina kuwa?" Cewar gwaggo indom wato dr Aisha.


Ta karkato masa kan iPad din nata yana kalla... Murmushi yayi sosai. Kafin ya mike ya koma inda take zaune ya saka hanu ya karbu ipad din yana zooming hotunan asibitin farfajiya da cikin sa..


Ma shaa Allah Allah yasa an fara a sa'a..Allah ya temaka Amin.""Aamin suka hada baki."


Suna dai zazzaune baki daya wasu na magana wasun su na daddanna wayoyin hannun su ya yin da wasu ke kallon shirin da ake haskawa a talabijin na tashar Aljazeera. 


"Zo nan takwara ta ...." Hajiya Maryam ta kira Amaal da ke gefen mahaifiyar ta a zaune.


"Tohm Hajiya.." Ta mike da sauri ta nufi wajen hajiyan ta tsugunna 


Hajiyan ta kamo hannun ta ta rike cikin nata tana mai duban idanun ta,


"Sannu takwara... Je ga daki can zaki ga magogin goro a gefen gado ki dakko mun."


"Tohm Hajiya."


Tashi tayi da sauri ta nufi dakin ta dakko ta kawowa Hajiya. 


"Bari na goga miki."


"Allah yayi albarka..."


"Ina safwanu mai gidan nawa?" Hajiya ta tambaya tana duban inda sauran yaran suke a zazzaune..


Hajiya hadiza ta dashare baki. Da dazu da hajiyan ke yiwa Amaal magana ita kadai sai kumbura fuska take amman da ke hajiyan ta tambayi nata dan yanzu sai washe hakora take kaman gonar auduga..


"Kai tashi Hajiya na kiran ka.."


"Kyale shi idan ya na hutawa... Ga kuma Abubakari, ga Na'eelah nan ga ...."


"Najwa..." Haj Hadiza ta amsa ta tanata murmushi ita ga mai tarin 'ya'ya..


"Ga kuma biyu kyautar Allah ...Ikram da Ikhlas.." Ta saka yatsa tana mai nuni da yan biyun Hajiya Ruwaida 


Hajiya Ruwaida ma sai kuma fuskar ta ta gauraye da farin ciki. 


Duk dai Hajiya ta kamo sunayen su daya bayan daya tana musu wasa. Duk kuwa da dattijuwa ce me kamewa, batada rikicin tsufa sannan bata wasa da jikoki irin wasan nan da yake wuce gona da iri. Tana da matukar kwarjini shi yasa ko jikokin nata suke nutsuwa idan suna tare da ita..


"Ku tashi mu lalleka a gaysa." Cewar amb. Junaid daya mike daga inda yake a zaune.


Ya isa wajen Hajiya ya durkusa cikin girmamawa yace,


"Hajiya bari mu shisshiga  gidajen a gaysa."


"Toh junaidu sai jun dawo. A gayshe su da dakyau."


"In shaa Allah hajjaju."


Yana gaba suna biye da shi a baya suka nufi sashe sashen da ke cikin gidan suna gayshe da su 


Duk inda suka je anyi maraba da ganin su. An kuma kakkarbe su hannu dubu bama biyu ba...


Sai da suka gama gayshe da kowace ahali na zuriyar ardo kandemi da ke cikin kandem estate sannan suka koma sashen Hajiya. 


Yaran Gwaggo indo da basa cikin estate din suma sun kawo ziyara, hakama iyalin Gwaggon court. 


Tuni suka fara hirar yaushe gamo da yaran Amb. Junaid. Gwanin ban sha'awa. Sai hirar zumunci suke.


Alhaji jalaludden na daga kujera ya dawo ya zauna sai muzurai yake yana yamutsa fuska musanmam da yaga Amb Junaid ya zauna a kusa da Hajiya...


"Wai har yanzu abun na su bai kammala ba?" Hajiya ta juya ta dubi jajaludden tana tanbayar sa


"Sun kusa waiwayowa gidah gaba daya Hajiya. Matsala aka samu ne da visa din musty. Amman su nan da sati uku zasu dawo gaba daya. Da sun dawo kuma shikenan ba komawa. "


"To Allah ya kawo su lafiya. "


"Allahumma Aameen Hajiya .."


  Suna dai zazzaune kowanne da abunda yake yi. Zaman jiran dawowar shi da yan rakiyar sa kawai suke ... Mahaifi agare su, wato Grand Kadi/Chief Justice/Alkali      "Alhaji Muhammad Mahmud Kandemi ..."


__

_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post