Tabarmar Ƙashi page 15 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 15 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 15 by H U G U M A

*H U G U M A*


_*TABARMAR ƘASHI*_💔

 

*Arewabooks: huguma*

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 15        Kofar tafkeken gate din kamfanin suka tsaya,kafin sukai ga sanar da isowar CEO OF MT GROUP OF COMPANY har jami'an tsaron dake kai kawo a qofar company din sun ture musu gate din gefe,sannan suka qame dukkaninsu suna sara musu har zuwa sanda suka gama shigewa tsaf,suka maida qofar suka rufe.


          Cikin nutsuwa da sanin doka da order dukkaninsu suka faka a matsayar motoci ta company din,saidai daga gefe guda dake nuna waje ne kebantacce saboda ajiyar ababen hawa na musamman,don akwai qarfen daya raba tsakaninsa da ragowar filin ajiyar motocin.


           Yadda motar ke daukan hankalin kowa haka ta dauki hankalin afifa data taqarqare a dazun tana zubawa sãahar bayanin da yasa takw kallon afifan kamar wata statue


"Wai ta riqe amanar mahmud?,to shi mahmud qanin maama ne ko qanin abba?,yaushe ta karba amanar tasa da har zatayi mata roqon riqewa?,banda afifa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata wannan zancan ta barshi tana kallonshi haka.


            Saida suka gama fakawa sannan ta maida dubanta ga sãahar


"Kinga abinda na gani kuwa?" Ta jefawa sãahar tambayar cikin zallar mamaki,da kuma tafiya da hankalinta da motar tayi.


          Ido kawai sãahar din ta lumshe tare da budesu lokaci guda ba tare data amsawa afifa ba


"Wow....wow.....mybatch vigil abloh fa?,kinsan mutum 150 ne duka duka suka mallaketa a duniya gaba daya?"


"Zan iya tafiya?" Sãahar ta jefeta da wannan tambayar,cikin bawa maganarta rashin muhimmanci,saidai afifan ci gaba tayi da koro mata bayanin zallar tsadar motar da darajarta,sai kawai tasa hannu zata buda motar. 


           Caraf ta riqo tsintsiyar hannunta


"Don Allah ki barni naga wanne me sa'ar ne ya mallaki wannan motar,wanne DON dinne?" Idanu ta kafe afifa dashi tana mamakin qaunar da afifa kewa motar,already tasan halinta,she's a classy ladie,amma me yaja hankalinta haka?. Ido ta zuba mata tana kallon yadda ta natsu tana mata bayani tare da kallon sashen da motar take.


           A qalla an kusa kwashe minti biyar bayan fitowar duk mutanen dake cikin sauran motocin kafin motar ta bude a hankali ya kuma zuro jikinsa zuwa waje,zuwa sannan idanun sãahar nakan wayarta tana dannawar dole,saboda ta cika maqil da takaicin afifa data hanata fita,ga saukar yayyafi da aka fara samu siri siri,wanda ita kuma kwata kwata bata qaunar ruwa ya taba jikinta


           cikin shigar wata lafiyayyar suit ta zallar cashmere wool,charcoal color yake,idanunsa manne da baqin eye glasses,wanda zaiyi wuya ka iya ganin qwayar idanunsa,hannuwansa duka cikin aljihun wandon suit din,yana takawa da sassarfa sosai yana kuma magana a waya ta Bluetooth din kunnensa.


"Tabarakallahu ahsanul khaliqeen,don Allah dago ki tayani ganin wani kyau a nan" afifa ta fada tana tabo hannun sãahar,tana kuma qunshe dariya a cikinta,ya tafi da ita matuqar tafiya,amma tanasl ne itama ta rama ta qunsa mata takaicin yin shuru da tayi sanda taketa babatun mata batun mahmud.


            A maimakon ta kalla inda afifa keson kalla saita kallo afifan


"Na kalli me?,kedai da kika zabawa kanki ganin kyan dan maciji na d'a namiji ai sai nace miki bismillahi,Allah ya bada sa'a" ta fada wani fushi yana motsawa daga qasan zuciyarta,kai afifa ta girgiza


"Ba haka bane sãahar,ban taba ganin irin wannan a zahiri ba Allah i swear,there was no denying that the handsome man was charming,he was elegant in every way Allah,don Allah ki kalla ki gani,zaki tabbatar ba qarya nakeyi ba" haushi ya sake qure sãahar,takaici da bacin rai yasa ta daga kai zuwa sashen da take roqarta ta kalla din,dai dai sanda yake wucesu cikin tarin ma'aikata zuwa main entrance na building din kamfanin.


           Siririn tsaki sãahar taja,ta kuma watsawa afifa harara


"Wai me ya shiga kanki ne yau?,lallai ya zama dole na gayawa su maama suyi gaggawar aurar dake,tunda kin fara sumbatu"


"Ba sumbatu nake ba,don Allah bakiga abinda na gani ba?,haduwa iya haduwa?,he was striking,no one could take their eyes off his good look"


"To ina ruwana?" Ta fada tana jin ta fara hasala,sai afifa ta qwace da dariya,tasan tayi mata abinda tafi tsana a rayuwarta,zancan d'a namiji,kuma har ta zauna tana kodashi haka,duk sa cewa YES wannan din yakai ya wuce ma yadda idanun me kallo zai ganshi,yana da wani irin kyau me sanyi haiba da kuma kwarjini na musamman.


         Kafin afifa ta sake cewa komai sãahar ta buda murfin motar ta fice abinta


"Zan wuce da motar,zan bayar a dawo miki da ita sanda zaku shiga lunch break" gyara yafen laffayarta tayi kawai,ta soma takawa a nutse zuwa ciki ba tare data amsa kota waiwayi afifa ba,yayin da afifan ke binta da kallo,murmushi na fita akan fuskarta. Komai na 'yar uwarta me kyau ne,komai na 'yaruwarta me aji ne,iyakar dukka inda mace takai ga aji da kyau takai,amma abu daya ya tsaida duniyarta cak,saita girgiza kai ta tashi motar bayan taga shigewarta building din.


          Cikin nutsuwa da kamewarta take takawa,a  nutse kuma ba kai tsaye ba tana karantar yanayin kamfanin da kuma inda take takawar,tun daga wajen ta sake karantar girma da tsarin kamfanin,kusan kowa ya duqufa yana aiki sosai,tun lokaci baiyi nisa ba,amma kowa yana mazauninsa ya riqe aikinsa.


"You are highly welcome madam" taji an fada daga gefanta,saita waiwaya a nutse. Matashi ne sanye da shirt da trouser lime green da baqi,yayi maganar cikin zallar girmamawa yana dan rusunawa kadan


"Fourth floor zaki sauka,akwai ma'aikatan dake jiranki a can,zasuyi guiding naki akan komai" ya fada cikin girmamawa,saita jinjina kai ta kuma taka zuwa bakin elevator,ta danna ta shiga,tayi kuma selecting number din floor din da takeson sauka,sannan ta koma daya daga cikin corners din dake cikin elevator din ta goye hannayenta a qirji,idanunta qyar akan numbers din dake jere daga bakin qofar shiga na'urar, zuciyarta na fara ayyana mata ko yaya zamanta cikin wannan babban company zai kasance?.


              A second floor elevator din ya tsaya,da alamar akwai wani dakeson shiga shima,idanunta akan bakin qofar,har zuwa sanda ta bude. Fes ya bayyana daga gaban qofar,fuskarsa na kallon gefansa yana magana da wani cikin nutsuwa da kamewa,duk da cewa baka iya jin abinda yake fada,amma yadda yake maganar cikin izza da kamewa zai gaya maka umarni yake bayarwa.


          Yana gama maganar yayi taku biyu don isa cikin elevator din,karon FARKO idanunsa ya sauka a kanta,kamar yadda itama karon farko nata idanun suka shiga cikin nasa,tsahon tsaiwar da elevator din yayi sai a sannan ta dubi wanda ke bakin qofar da nufin shigowa ciki suyi tarayya na wasu sakannin da zasu kai kowa inda yayi nufin zuwa. Lokaci guda kuma a tare kowa ya janye idanunsa,ta kauda kanta gefe guda tana tsuke fuskarta,ta gane fuskar,fuskar mutumin da a dazu afifa ta cikata da zancansa,saita sake tsuke fuskartata,tana jin qyamatar hada guri dasu,kamar yadda takeji a ranta game da duk wani DA NAMIJI.


            Sanda taji anyi releasing elevator din ya wuce ba tare da an shigo ba sai taji mamaki kadan ya kamata,ta maida dubanta ga qofar taga taci gaba da hawa zuwa saman,saita yarfar da hannunta tare da tabe bakinta,ita dama hakan takeso,bata buqatar hada numfashi da jinsi irin nasu.


           Fitowarta daga ciki yayi dai dai da matsowar sajjad dake cikin aiki kace kace,amma Dr girema ya tasheshi takanas saboda ya marabci sãahar din,ya kuma tabbatar ya bata duk abinda take da buqata da zai sake jin ta gamsu da aikin da kuma kamfanin gaba daya.


           Kamar wancan data baro a qasa haka shima yayi welcoming nata,sannan cikin sanin kima da darajar dan adam daya sanyata tadanji zuciyarta ta saki kadan yace mata


"If you don't mind......i will show you your office" kai ta jinjina kadan,yayi gaba tana biye dashi,sannan sauran ma'aikatan da suke qarqashin kulawar office dinta.


            Kusan kafin ya fita sai daya gabatar mata da komai da take da buqatar sani,tana zaune saman kujerar da sai da tayi addu'a sannan takai ga zama,ta bada dukka hankalinta ga bayanansa,abinda zai nuna maka zallar seriousness dinta,yanayin yadda kyakkyawar fuskarta ke a tamke ya isheka shiga taitayinka da tabbatar maka ba zata dauki wargi ko wasa ba,har ya kammala,saita dan lumshe kyawawan idanunta kadan sannan ta budesu


"Inason a sanarwa suk department din dake qarqashin wannan office din akwai general meeting a gobe"


"In sha Allah" ya fada sannan sukayi mata sallama suka fita don bata damar duba ayyukan da aka tsaya akai don ta dora.


           A nutse ta fara buda computer din dake gabanta,ta soma aika saqon email zuwa ga sauran department dake cikin kamfanin da sauran dukka board members,tare da introducing kanta,email guda daya daya rage zata turama,wani saqo ya shigo mata ta email,abinda ya janye hankalinta kenan ta shiga Wani aikin daban,sai kuma ta shiga binciken dame dame aka aiwatar cikin office din.


              Cikin qwarewa tare da amfani da zallar basira take sarrafa na'urar,da wani irin qwarin gwiwa da karsashi da batasan ya sauko mata ba. Ta kusan kashe awa biyu cur,kafin ta zame hannunta daga kan computer din,ta kuma maidasu saman fuskarta ta rufe fuskartata da kyau tana fidda numfashi me dumi daga bakinta. Ta fuskanci akwai jan aiki a gabansu,da kuma wasu al'amura na rashin gaskiya masu tarin yawa da aka aiwatar,wadanda sune suka taka rawar gani wajen kawowa company din naqasu da kuma koma baya,ta tura kujerar ta baya tana hade yatsunta da suka gaji guri daya ta lanqwasasu da kyau,dai dai lokacin kiran afifa ya shigo wayarta. 


            Har ta saka hannu zata daga wayar saita fasa,ta jefawa wayar harara kamar itace afifa din,saita miqe bayan ta zare takalman qafarta,ta taka saman lallausan carfet din da zai sadata da qawataccen fridge din dake office din tana sake nazartar office din,komai an shiryashi base on her favourite colors,har ta soma zargin anya ba tare da yaa muhyi aka zuba furniture na office din ba?.


          Komai an tanadeshi,don hatta fridge din cike yake da kalolin drinks,ruwa kawai ta dauko,ta dawo ta zauna saman couch masu laushi da aka shirya daga gaban table dinta bayan ta dauko wayarta.


            Sms guda biyu ne suka shigo kusan lokaci daya,na afifa ne a sama,shi ta fara budewa


_"I hope you are enjoying your work?,god bless you dear,All the best"_. Dole murmushi ya subuce mata,afifa ta wajenta,ayi dadi ayi tsiya,saita maida mata amsa a taqaice


_"All is well bestie,thank you"_. Komawa tayi ta duba saqo na biyu


_"assalam gimbiya,iam wishing you a joyful day,i hope you will remain blessed,fatan nasara,mahmud A gana"_ dogon tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,saita goge saqon kamar yadda ta saba,ta bude gorar ruwan ta zuba a glass cup ta fara sha tana tunanin next abinda zata aiwatar.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post