Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 15

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 15

 

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 15

_BM_

_NA:_

_NANA HAFSATU_

_PAGE: 15_

_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


  

  Kirjin sa dankare da madaukakiyar damuwa marar misaltuwa... Cikin tsantsar tashin hankali ya sake cewa,


"Yaya wallahi bansan lefin da nayi maka ba kake mun haka..."


Alhaji jalaludden ya nata kokarin kwace rikon da su Kawu Adamu suka masa yace,


"Har kana da bakin tambaya? Wallahi junaidu na tsane ka, Na tsani na bude idanu na na ganka... Rayuwa tare da kai a kandemi estate ba zata taba mum dadi ba wallahi.."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Yaya ka tsane ni fa kache.?"


"Kwarai na tsane ka.... Samuwar farin ciki na bai wuce na bude idanu naga kai da iyalin ka kunbar kandemi estate ba."


Amb Junaid ya shiga jujjuya kansa, zafafan hawayen da yake ta makalesu suka shiga kwarara daga idanun sa. 


Kwakwalwar sa ta shiga tariyo masa dukkanin saqonnin da ake turo masa ta nambobi masu tarin yawa da dimbin barazanar da ake masa shi da iyalin sa.


Ya tuno shekarun baya ma da aka dauke yaran sa an kai su makaranta suna kanana... Shi yasa har girman su idan zasu fita sai zuciyar sa ta masa zugi. Kada tarihi ya maimaita kansa, Dan ma dai Allah ya takaita wahala da karfin addu'oi yaran suka kubuta bayan awa sha takwas da dauke su..


Sam baya jin dadin yadda zuciyar sa ke tabbatar masa da Yaya jalaludden shine ke tura masa dukkanin saqonnin barazana da sauran dukkanin abubuwan da ke faruwa... Yaya jalaludden shine BAKON MUNAFIKIn da ke raba kawunan zumunci...


Kafadar sa yaji an dafa, Yaya Nuraddeen ne babban wansu. 


"Yaya"


"Na'am junaidu..."


"Yaya kabi bayan sa kenan?" Jalaludden ya fada yana sake harzuka.


"Banbi bayan kowa ba jalaludden, Amma a zahirin gaskia kai ne mai laifi?"


"Ni ne me laifi? Wato dukkanin abubuwan da yake shi baa gani kenan sai nawa? Duk tarin shekarun nan dama baka fadar lefin junaidu. Da an fara magana zaka ce kai de babu ruwan ka. Idan tsoron sa kake ni bana tsoron sa. "


Alhaji Nuraddeen ya girgiza kai kawai hadi da sakin murmushin da yafu kuka kuna zuciya yace,


"Dan girman Allah jalaludden ka rage mita da saurin hawa doron zuciya. Baka jira ka karasa jin abunda zan fada ba ka fara fadan wasu maganganu. kuma.shikenan duk wanda yayi ba daidai ba ba zan fada ba sai nayi shiru?"


"Amma dai Yaya"


"Dakata jalaludden inde ka amince gaba na ke da kai ka bar ni na karasa abunda zan fada. Idan kuma kai ka dawo yayan nawa to cigaba Ina sauraron ka."


Alhaji jalaludden yayi shiru bai sake cewa komai ba sai faman dai cika da yake yana batsewa fuskar nan tasa a kumbure ba fara'a. Yanayi yana wullawa amb junaid harara.


Kawu Adamu dai yana rike da kafadun jalaludden yaki cika shi don yana cire rikon da yayi masa to fa zai hau amb Junaid ne da duka. Don baki daya tamkar baya hayyacin sa,


"Yaya dan Allah menene lefi na?" Amb Junaid ya sake tanbayar Yaya Nuraddeen yana girgiza kansa cike da tashin hankali 


"Au tambayar lefukan ka ke? Kunji munafuki algungumi ko?" Jalaludden ya fada yana kwafa


"Junaid je ka dan Allah. Tafi sashen ka sai da safen mu."


"Yaya meyasa zan tafi? Wallahi bansan lefin da nayiwa Yaya jalaludden ba."


"Inde na isa da kai kai ma kana kuma ganin girma na to ka bar nan yanzu."


"Shikenan... Sai da safen ku."


Fita yayi gaban sa yanata masa zugi da radadi. Ya rasa wacce iriyar  kiyayya dan uwan nasa yake masa. Meya tare mesa? Bayan ko acigaba na rayuwa ya fishi? To haushin sa na me yake ji? 


Bangaren hajjyan su yaje ya gayshe da ita. Ta tambayi ya jikin mai gidan na ta ya amsa ta da Alhamdulillah jikin sa yana sauki yana samun lafiya. 


Ya dan zauna suna ta yar hira da ita yana matsa mata kafafu . Har bacci ya fara daukar ta tache masa ya tafi ya kwanta shima yayi mata sai da safe ya nufi bangagren sa.


Kansa har wani sara masa yake yi saboda tsananin yadda yake masa nauyi kan. Wata jijiya ta fito radau a gaban goshin sa tanata harbawa. 


Yana shiga ya zauna akan kujera yana sauke ajiyar zuciya. Ya sanya hannun sa daya ya dafe goshin sa. 


Wayar sache tayi kara ya dauka ya danna ta a handsfree  ya ajiye ta a kusa da shi. Matar sa jameelah ce ke kiran sa,


"Assalamu alaikum. Nurul qalb..."


Murmushi sosai yayi jin yau ma kuma da wani sunan data kira shi. Kullum cikin kiran sa da sunaye masu matukar dadi da kwantar masa da zuciya.


Take yaji wani kaso na daga cikin bacin ran nasa ya sauka . Ya dan yi gyaran murya don karta gane damuwar da yake ciki yace,


"Waalaykm Salam... Farhatal qalb..."


Dan murmushi tayi mai sauti ta sake lankwashe harshe tace,


"Da fatan Habibi yana cikin koshi lafiya?"


"Alhamdulillah habibty... "


"Ma shaa Allahu... Ka dawo ne?"

Ta tambaye shi kasancewar kwananta ne. 


"Na dawo yanzu ba dadewa kimganni a zaune..."


"Ma shaa Allahu... Toh wanne tea zaa kawo? Chamomile tea?  cinnamon and cardamom tea? Ko tumeric/garlic da milk sai a saka masoro kadan? Wanne ko just the usual coffee? Kana jina kuwa Abbiyeyn su?"


Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannun sa ya shafo kasan keyar sa. Yayin da idanuwan sa yake lumshe su,  dai dai lokacin da Hajiya hadiza ta taho da sand'a tana labewa,


"Ina sauraron ki habibty... Hakika muryar ki na magance mun dimbin  damuwa, magnganun ki na tasiri a zuciya ta... Allah ya miki albarka... Ki kawo tumeric tea din inason nayi bacci dama..."


Hajiya jamila tayi murmushi anata bangaren tana kitchen a tsaye. Sai bulala kamshi take. Sanye cikin laffayar data amshi jikin ta sosai.


Kalar ja. Tasha kwalliyar black. Sai ta daure kanta da danjwali baki ta yafa laffayar akai. Ba kadan ba tayi kyau tamkar a dauke ta kaman yar baby. 


Wayar a kunnen ta. Yayin da hannunta daya take dakko wani flask transparent ne ana ganin komai na cikin sa. Ta dora shi akan wani tray da cups dinsa suma ta dora su a kananaun tray dinsu..


Nan da nan ta fara hadin shayin tumeric/kurkum din . Tache da shi,


"Yanzu zan kammala na zo habibi da'iman, akwai wani abun da kake so bayan tea din?"


"A'a habibty...."


"Ko dan prawn crackers ka temaka kaci kaji?"


"Abunda kikace shi za'ai s...


Bai karasa ba Hajiya hadiza ta shiga tana tafa hannu tana sallallami tamkar wadda akayiwa mutuwa. Taja kwafa tana kada kai,


"Meye hakan ba sallama?"


"Yo ina zakaji sallama ta kana faman soyayya gotai gotai da kai?"


"Ni ba mahaukaci bane hadiza... Idan kinyi sallama zanji. Wayar da baa kunnena take ba ma."


Hajiya jameah da ke jiye dasu tayi hanzarin kashewa . Saboda batasan tashin hankali sai jikin ta yahau bari tana tsaye hannunta sai rawa yake. 


Ya daga wayar zai yi magana yaji tayi ending call din. A fusace ya kallo hadiza yace,


"Kede idan ba tashin hankali kika tasa ba bakya jin dadi hadiza... Ba zaki dena laben nan ba? Wallahil azim a laben nan wataran zaki labewa kan ki Ina rabaki."


Tsaki taja ta kalle shi ta maka masa harara,


"Kai de borin kunya ya isheka, Kanata faman susuta zance. Ni ba wannan ne ya kawo ni ba. Duk da dai na ji zancen da kukeyi.. Allah ya shirya . Da ka aurar da yaran ka da tuni kanada jikoki shine kuke soyewa da matar ka."


"Alhamdulillah kince mata ta. Ba wata daban nake kulawa ba."


"Amman dai kaji kunya... Soyayya da farin gemu."


"Eh naji halal me ai... Matata tace."


"Saboda kana tsoron ta shine ka amince ta dakko dan gidan rukayya? Wato junaidu duk shawarwarin da ake baka ba zaka dauka ba sai da ka amince ta dakko shi? "


Hannun sa ya saka a goshin sa yana dafawa, ciki da kosawa yace,


"Dan Allah hadiza banason tashin hankali wallahi kai na ciwo yake."


"Okay ita da kake kauna ai kace muryar ta na sa maka nutsuwa da kwanciyar hankali ni da ka tsana kuma ciwon kai nake sa ka."


"Ni ba abunda nake nufi ba kenan. Wallahi kai na dama ciwo yake. Kuma kinzo kina kawo wata magana ta daban haba hadiza. "


"Na fuskanci baka son zaman lafiya ba kuma ka kaunata junaidu."


"Kin fara ko hafiza?"


"Ni ce matar ka ko Jamila?"


"Dukan ku mata na ne"


"Ni che ta fari ko ita?"


Ya sauke katuwar zuciya yana junjuya kai,


"Ke che.."


"To banason zaman sa agidan nan ban amince ba don haka da sake ya tattara ya koma inda ya fito....


_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥



*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k



  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post