Tabarmar Ƙashi page 25 by H U G U M A

Tabarmar Ƙashi page 25 by H U G U M A

 

Tabarmar Ƙashi page 25 by H U G U M A

*H U G U M A*


*_TABARMAR ƘASHI_*💔


Page 26



         Haka kawai taji gabanta yayi mummunar faduwa,kowanne sashe na jikinta yayi sanyi saboda yadda ya zuba mata mayatattun idanunsa,yana jifanta da kallon tsana. Tayi tunanin zata iya jurewa kallonsa kamar yadda ya ritsata da nasa idanun,amma tun ba'a yi nisan zango ba taji ta gaza dauke nauyin zagayyun idanunsan nan masu tsananin haske,kamar ba idanun namiji ba. Gaba daya sai ta jita kamar wadda aka nannade aka jefa cikin wani keji,kamar an sanya igiya an daureta,ta dinga fatan na'urar ta sauketa da inda ta umarceta tayi ta fice ta bashi guri.


            Saidai kuma suna isa floor din ya matsa gurin madannan ya sake bata direction na dawowa dasu floor din qasa,a sannan ta waiwayo ta sake dubansa da fararen idanunta karo na biyu,still har yanzu ita yake kalla,kallon dake sake bayyana fushin dake kwance a zuciyarsa. Sake janye idanun nata tayi ta maida dubanta wani wajen,gaba daya kallon da yake mata ya wuce qa'idar da jarumtarta zata iya dauka,uwa uba kuma shirin rikicewa takeyi gaba daya,saboda yadda qamshinsa yake sake cika elevator din. Tattara hankalinta tayi tana jiran jin sun isa,ta riga ta gama ayyanawa a ranta suna isa zatayi hanzarin ficewa,don ta fuskanci kamar ya shirya tayita yawo dasu daga sama zuwa qasa,can can qasan ranta tana tuna tsakin data sakar masa.


               Da wani irin hanzari ta nufi qofar da zummar fita,amma kuma kafin ta isa har ya maida qofar ya rufe,ya kuma sake sakata ta lula sama dasu. Wannan karon tsaiwa tayi daga bakin qofar yana lumshe idonta,ranta itama ya soma baci da rainin hankalinsa,ta yaya zayazo ya sameta a waje ya kuma dinga mata wasa hankali?,na meye?,zata tsaya gab da qofa,zataga gudun ruwansa,idan ta fita yasa qarin tuwo ya dawo da ita.


           Duk yadda taci buri kuwa suna isa sai gashi tsaye bakin qofar,abun yayi matuqar bata mamaki,batasan wanne irin zafin nama gareshi ba


"Excuse me mana,fita zanyi" ta fada da siririyar lallausar muryarta


"Wa kika yiwa tsaki?" Ya jefe mata tambayar kansa tsaye cikin izza da qasaitarsa kamar wani basarake,duk da yadda yayi mata matuqar kwarjini,amma motsawar tata izzar ta bata qwarin gwiwar amsashi


"Da wanda ya tsargu" ta amsa masa tana qoqarin kaucewa qwayar idanunsa,don har yanzu tana cike da takaicin abinda yayi mata dazu a kitchen.


"Ko?" Ya fadi wani miskilin murmushin gefen baki na subuce masa,duk da cewa ba murmushi bane na kyautatawa ko jin dadi,amma wani irin sirrin taccen kyau ya bayyana muraran kan fuskarsa,fuskarta yake duba,yanason gano daga inda ta samo wannan qwarin gwiwar tsaiwa ta gwada masa rashin kunya,yayi imanin batasan wane shi ba,amma a yadda ya lura akwai quruciya sosai tattare da ita,qaramin abu kawai zaiyi da zai bata zazzafan warning,ta yadda ba zata sake marmarin maida masa martanin magana ba.


            Bata taba kawowa ba ko kusa ko alama,kamar a mafarki taji an take dogayen yatsunta da qarfi,sosai zafi ya ziyarceta,ya kuma ratsata tun daga saman qafarta zuwa qwaqwalwarta


"Wayyo Allah na" ta fada a jigace


"Wa kika yiwa tsaki nace?" Ya sake maimaita mata tambayar wannan karon da wani irin zafin rai,har hakan na bayyana kan fuskarsa


"Sa'anki ne ni?" Ya kuma jefa mata tambayar,duk da bata samu damar amsa masa tambayar farko ba


"Ko don kinga Dr ya baki damarmaki da yawa kike tunanin kanmu daya dake?" Ya kuma fadi a mugun tsawace,sautin tsawar tasa tana ratsa mata kunne


"Bakizan tsaki zagi bane a gurin wanda ya girmeka?" Still dai ya tambayeta yana kallon fuskarta,wadda zufa ta fara wanke goshinta dake lullube da wasu irin gashi masu matuqar santsi


"Lemme warn you......daga yau,duk randa kika kuskura kika qara yimin tsaki ko......." Sai ya murza yatsunsa akan fuskarta


"Bazan koreki ba,bare kisa Dr yaga baqina,amma sai na ɓarka bakin tsakin,ki zama me d'a'a ga wanda yake sama dake" yana qarasa fada ya dage mata qafar,ya kuma kauce ya bata hanya yana jira ta fita. 


         A wahalce ta tashi daga tsugunnawar da tayi,hawaye sun jiqa mata fuska,wannan shine qarshen cin zarafi da tozarcin da zaiyi mata,ba tare data kalleshi ba ta juya ta fita daga elevator din tana jan qafarta da tayi mata nauyi.


            Floor din qasa ya sanyata ta maidashi,yana tsaye yana kallon yadda take sauka qasa dashi,sai furzar da iska yake daga bakinsa,yana son ya fifita zuciyarsa daga zafin data dauka. A wajensa wannan din zallar raini ne,ba abinda ya tsana a duniya sama da tsaki,tsakinma a rasa daga gurin wanda zai fito sai mace?,macenma yarinya qarama wadda ya girmewa da shekaru masu dan dama,kuma ma ma'aikaciyarsu dake qarqashinsu,wanda kaf rayuwarsa ba yarinyar data taba masa irin hakan,kawai don ta samu dama daga gurin Dr,ko don tana ganin tana da kyau?, abinda ya gani dazu tsakaninta da hamza ya fado masa a rai,ya dunqule hannu ya kaiwa iska naushi,yana jin tsanar mata na nikuwa a ransa. Ya tsani mata totally, especially masu kyau irin haka,tabbas koda yaushe basu rabuwa da shaidan,babu wani alkhairi sam a tattare dasu sai tarin sharri,bazai bar mr hamza yaci gaba da barar musu da mutunci ba. Har ya saka dayan qafar zai fita yaji ya taka wani abu,sai ya dawo da baya yana duban qasa,wani abu me qyalli ne ruwan azurfa,ya duqa a hankali yasa hannu ya dauke,ya wulla a aljihunsa ya fice.


             A daddafe ta samu ta isa office dinta,tana budewa ta zube saman sofa ta saki wani nannauyan kuka me cin zuciya,tunda take apart from abinda adam ya aikata mata,ba'a taba tozartata irin wannan ba,saita koma ta kwanta sosai saman sofa din,tana jin zama yayi mata kadan,ta saki kukanta sosai tana share qwalla.


         A qalla ta kusan minti ashirin a haka sannan taji zuciyarta tayi sanyi,ta miqe ta zauna,dai dai lokacin kiran mahmud ya sake shigo mata,wanda wannan shine kira na biyar da yayi mata. Bata ko saurari wayar ba,ta miqe ta nufi toilet,ta wanke fuskarta da kyau,sannan ta dawo ta tsaya cikin office din ta dauki wasu qananun abubuwa nata ta zuba a jaka,da zummar har abada tabar aiki da kamfanin MT JARMA GROUP OF COMPANY,dama can sunci darajar yaa muhyi da bazata taba iya cewa a'ah ba.


            Tana shirin jefa wayar a jaka kiran nasa ya sake shigo mata,tuna tayi cewa a yanzun yanayin komai ne bisa iznin daya samu daga gurin mutumin da yafi kowa kima da martaba a wajenta,wanan ya sanya ta daga wayar,ta kuma mara a kunnenta ba tare da tace komai ba


"I hope kina lafiya ko?,ko zaki turomin full address na companyn,zan qaraso sai nayi dropping naki a gida idan an bani dama" bacin rai kan bacin rai,tadan cije lebanta tana jin sha'awar sakeyin wani kukan bayan wanda tayi,ita afifa zata yiwa haka?,haka sukayi da ita?,salon kawai ta zubda mata qima da mutunci zata kira wani mahmud wai yayi dropping nata


"Karka damu,ina hanyar gida,thanks" tayi maganar a gajarce,saboda batason tayi tsaho har bacin rai da fushin da bashi ya haddasashi ba ya shafeshi.


           Yau gaba daya sai takejin kamar ba ranar saarta bane,ranta a mugun jagule ta iso farfajiyar company din,kiran mechanic din ya shigo a dai dai,yace mata yana bakin gate din farko,sai tace ya qaraso ciki,ya sameta parking lot na company din.


            Tun daga nesa ta fahimci motocinsa da motarta ne kawai ya rage a gurin, zuciyarta na sake motsa mata da bacin ransa tana danneta har ta qarasa gurin. Ta matsa kusa da motarta tana amsa kiran wayar musa mechanic,ta gama ta jefa wayar a jakarta tana qunquni. Gaba daya guards dinsa sunyi carko carko a gurin kamar zasuci babu,kowannesu cikin shigar baqar suit ya qame,suna jiransa sanda yake tsaye yana sallama da baqin da ya gama ganawa dasu cikin garden din company din.


             A gaggauce ta yiwa musa bayani,don ta matsu taga ta fice daga companyn


"Idan ka gama ka kaimin ita gida,saika fadamin kudin gyaran"


"To idan ba damuwa,bari na fita na taro miki abun hawa mana" ya fada cikin girmamawa


"Meye ya samu abun hawan diyar tawa?" Dattijuwar muryarsa ta bayyana a gurin. Waiwayawa sãahar din tayi tana dubansa sanda ya tsaya daura dasu,masu tsaron lafiyarsa na tsaye daga bayansa,hannunsa dauke da mini laptop,yana dubanta cikin kulawa.


           Har abada yana da wata kima da martaba a gurinta, saboda dattakonsa da kuma girmama dan adam da yake dashi,cikin mutuntawa irin ta uba da d'ansa tace


"Yadan baci ne abba,amma yanzun in sha Allah nasan zai gyara"


"Subhanallah,ashshsha,to yayi,ammm.....amma ame zaki koma gida?"


"Zan qarasa titi,zan samu abun hawa" kai ya girgiza,sannan ya yafito daya daga cikin guards dinsa ya masa magana qasa qasa,ya zabura da hanzari don cika umarnin ogansa yayi gaba.


             Rusunawa yayi daga bayan toufeeq daketa amsa waya,ba tare daya katse wayar ba ya waiwayo yana dubansa,tsaf har ya gama gaya masa saqon BOSS


"Okay" ya fada yana sauke wayar,ya taka a hankali don amsa kiran mahaifin nasa,masu tsaron lafiyarsa suka motsa da zummar binsa,ya tsaidasu ta hanyar umarni da hannu.


           Yana takawa zuwa inda suke tsayen ita da Dr ahmad jarma,idanunsa zube fes a kanta,can qasan ransa yana mamakin dalilin tsauwarsu haka shi da ita,dr din kuma na magana da ita cikin kulawa,tamkar yadda zaiyi magana da shi ko NADEEYA.


"Abba....akwai wani damuwa?" Toufeeq din ya fada a girmame yana duban fuskar mahaifinsa. Waiwayawa yayi ya dubi sãahar,wadda a sannan takejin kamar ta rufe ido ta bude ta ganta a gida,ta samu nasarar tsere musu sannan ya mayar da dubansa gareshi


"Ta yaya matsalar mota zata samu president dinka sannan ka tayar da dukka motocinka ku tafi ba tare da an kula da buqatarta ba?" Hannunsa ya murza kamar kadan,yana jifanta da wani irin bahagon kallo,dr din bai jira amsarsa ba yace


"Ka dauketa ku sauketa a gida,ka tabbatar kun ajeta har cikin gida kamar yadda muka karbo amanarta"


"In sha Allah " ya fada da lallausar muryarsa dake cike da bacin rai,shi yarinyar zata yankema schedules kawai saboda buqatar qashin kanta?.

    

              Dai dai lokacin sajjad ya qaraso gurin,akwai banbancin halaye masu yawa tsakaninsa da toufeeq,don shi din cikin sakin fuska yake tambayarta akwai matsala ne tayi late na komawa gida?.


"Dole haka wataran dama ta faru,tunda kunyi sakacin kula da buqatun ma'aikata,maza a sanyata a mota a kaita gida, motarta ce ta samu matsala"


"Yanzun nan abba" sajjad din ya fada gami da ce mata bismillah bayan yayi gaba,tabi bayansa. Tun isowar sajjad taoufeeq din ya wuce mota ya zauna abinsa,yasan tunda har ya iso wajen,abinda abban ma baice ayi ba sajjad din zai sake ruruta abun,ya fuskanci yana wani mugun bata girma na musamman,abinda ya kasa ganewa mene shi?.


            Kansa tsaye ya bude motar da toufeeq din kadai take dauka,saikumma shi idan tafiya ta hadosu tare


"Bismillah ko?" Ya sake fada cikin girmamawa fuskarsa a sake.a nutse ta fara sanya qugunta a motar,sannan ta dauke qafafunta a hankali saboda ciwon da 'yan yatsunta sukeyi mata. Tun bata waiwaya gefanta ba,qamshin turarensa shine abu na farko daya sanar mata da wanzuwarsa a gurin,sanann dukka jikinta ma ya bata. Ya hakimce a owners corner yana danna wayarsa hankali kwance,tamkar baiga shigowarta ba,amma can qasan ransa yana tsara yadda zai cimma sajjad ne,don ya qona masa rai matuqa. Muryar dr ta sake wanzuwa a gurin,ya tako da kansa ya qaraso bakin motar


"Akwai ciwo a qafarta fa .....taoufeeq,ka sauketa asibiti a dubata da kyau kafin ku wuce gida,kai kuma sajjad muje ka tayani ganin baqin can,Allah ya sawwaqe,ki miqamin gaisuwa gurin girema"


"Zaiji" ta fada softly,tana mamakin shin yasan abbanta ne dama?.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post