Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 13

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 13

 

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 13

_BM_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE:12_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


     Fitowa su kayi daga cikin gidan bakunan su dauke da murmushi baki dayan su. 


Direba ya futa da sauri daga cikin mota ya dauki Ghana must go agaban Hamid ya shiga da ita cikin booth bayan ya kai katon akwatin ciki ya ajiye.


"Sannu da kokari."


"Sannun ku Hajiya. " Direban ya amsa su bayan ya rufe kofar booth din ya sake cewa,


"Ba wani abun ko?"


"Babu Falalu. " Cewar Hajiya jamila.


Suna tsaye ita da babbar yar su bayan sun fito daga cikin gida da suka kai mata ziyara tun safe itada Amaal kasancewar asabar ce. 


Can ne wata unguwa dake da tazara sosai da kandem estate. Sun dade basu hadu da yayar ta taba tun wata ziyara da yayar ta kai makka data biya ta madeena taje suka gaysa.


Su uku ne dama kawai wajen iyayen su wadanda Allah yayiwa rasuwa. Marigayi,  Malam (Abdulhamid) balarabe Na Bingini ance usulin sa balarabe na na Lebanon sai mahaifiyar su marigayiya malama Aminatu. Malam balarabe ne yafara rasuwa sakamakon ciwon daji daya kama shi lokaci daya. Sai bayan shekaru takwas da rasuwar sa malama Aminatu rasu bayan gajeriyar rashin lafiya itama. 


Su uku ne Allah ya azurci iyayen su da su, Hajiya Fauziyyah itace babbar yayar su. Daga ita sai Hajiya jamila sai kuma kanwar su da itama Allah ya mata rasuwa tun bayan data haifi dan ta dayaci sunan mahaifin su marigayi Abdulhamid. kwanakin sa uku da yayewa Allah ya dauki ran ta.


Rikon sa ya koma hannun Hajiya Aminatu mahaifiyar su. Shekarun sa takwas awajen ta Allah ya karbi ran hajiyan. Sai rikon sa ya koma hannun Hajiya Fauziyyah yayar mahaifiyar sa.


Nan ta hada ta rike su da sauran yaran ta. Daa Hajiya jamila ce zata rike shi saboda tsananin kaunar da take masa. Gashi kamar su daya tamkar ita haife shi daman ita da suaran yan uwan nata suna kama da juna. 


Don haka alokacin da zata karbe shi sai wani ciwo ya risketa sosai, lokafin tama futar da rai da haihuwa bayan shekara da shekaru. Har dai Fauziyya ta tausasheta tache tabari ta waarke 


Allah dai bayyi ta karbe shi sakamakon bayan ta samu lafiya daga baya wani gurmi ya taso aka hada sharri da gulma. Maigidan na su Amb junaid yache ba zata dakko masa dan kowa ba. Har ta cire rai.


Bayan shekaru Allah ya azurta da samun haihuwa ta haifi diya mace aka sanya mata sunan mahaifiyar Amb Junaid, wato Maryam suna mata laqabi da Amaal. Zaman su ya kasance tsakanin kasashe da dama kamar India, England, Saudi Arabia bangaren Riyadh sai kuma inda sukafi ko'ina dadewa wato madeenah (aba ad dud)


Har suka karachi wannan shekarun a akasashen suka waiwayo Nigeria hajia jamila bata futar da ran rikon Hamid ba. Idan tana ganin sa tamkar karamar kanwar su marigayiya take gani wato Rukayyah.


Tana ta addu'oin ta dai. Bayan dawowar su kuma rannan ta sake samun amb junaid da zancen, yace mata ya amince yana kuma matukar murna da hakan. 


Nan ta sake dagewa da adduoin da neman tsari daga sharrin masu sharri, sihiri da ma kambun baka da miyagu da suaran su. Don kallo daya zakai wa amb junaid kasan tabbas a shekarun baya da yaki amincewa bayin kansa bane....


Hamid suka rungume juna da hajia Fauziyya. Har da share kwallar ta,


"Shikenan Jamila kin rabani da auta na."


"Ni na isa Yaya? Zasu rika zuwa miki hutu in shaa Allah. Suma kuma su Yaya mujahid da Alwan da auta safwan Dan Allah su dinga zuwa mana hutu akai akai."


"In shaa Allah antyn su. Allah yasa ku koma a sa'a Allah ya tsone idon makiya.,


"Allahumma Aameen yaya."


Amaal ma ta rungume Hajiya Fauziyya suka mata sallama. Suka shiga mota suka tafi


Sai da suka kule sannan ta dena musu waiwaye da bye bye ta koma cikin gidah cike da kadaicin su musanmam ma Hamid fa da take jin sa tamkar dan data haifa acikin ta, Kawai tasan Alhamdulillah gidah ya koma can ma. Da nan da can din dik daya ne musanman acan din zaa fi rikon sa da gata tunda sunfi su kudi sosai ba ma za'a goga ba. 


Sai ita kadai sai yar aikin ta dake tayata aiki. Kasancewar yaran nata basa nan sunje kauyen mahaifin su gano godah dakuma ziyarar gonakin mahaifin na su...


  ××KANDEM ESTATE××


  Motar su ta shiga tankamemen gate din bayan masu gadi sun bude mu su.

Kai tsaye sukayi sashen Amb junaid. 


Bayan direba ya faka motar. Kai tsaye suka furfuto daga cikin motar. 


"Falalu kai kayan sa cikin gidah dan Allah ."


"Tohm ranki ya dade yanzu kuwa..."


"Muje Hamid... "


Tana gaba suna biye da ita a baya shi da amaal.


"Ga computer school din can, can kuma islamiya ce, Ga kuma gym daga can duk dai zaka ga wajajen in shaa Allah."


"Tohm Hayateey..." Hamid ya fada yana murmushi,


Hajiya jamila ta juya ta kalle su tana murmushin itama,


"Amaal ta koya ta rokeka ka dinga fada ko?"


Girgiza kai yayi. Ta sake yin wani murmushin tana nuna amaal,


"Ba wani tare mata za kai, ai ta kosa kazo. Kullum zancen ta yaushe Yaya Hamid zai dawo? "


"Allah sarki..."Cewar Hamid.


"Hayateey.." Amaal ta fada tana murmushi.


Haka suka karasa shiga sashen na Amb junaid. Bakunan su dauke da sallama


Yana daga zaune a babban parlorn sa... Hannun sa dauke da wayar sa yana jujjuyawa. Sakonni masu tayar da hankali aka turo masa biyu ta kafafen sadarwa daya kuma ta direct text message.


"Assalamu alaikum" muryar su ta sake dokan dodon kunnen sa.


"Waalaykm Salam...." Ya dago a razane ya kalle su duka saboda yanayin yadda gaban sa ke faduwa yana Wani irin duka da harbawa fat fat fat.


Gefen sa ta nufa ta zauna ta gayshe shi ya amsa fuskar a sake. Amaal ma ta gayshe shi tare da Hamid dake daga gefe,


"Yau fa Allah yayi abbieyn su." Haj jameela ta fada wa amb Junaid tana mai nuna Hamid da yatsa tana murmushi,


Shi dai Hamid hannu ya saka a bayan keyar sa yana murzawa.


"Ma shaa Allah! Barka da zuwa Hamid."


"Barkan mu ranka ya dade."


"Ka saki ranka kysji? Nan gidah ne.. gidan ku ne. Ka dauka kai ma da ne acikin gidan mahaifan ka, Allah ya jikan Rukayyah ya mata gafara. Allah ya maka albarka ya raya mata kai Amin. Allah kuma ya bamu ikon kula da kai mu kyautata maka gwargwadon iko."


"Aamin ranka ya dade.",


"Ameen abbiey."


"Ameen abbiey sum"


"Ka rika kira na abbiey kaji ko? Kamar yadda kanwar ka Amaal ta fada."


"Tohm in shaa ALLAHU."


"Allah ya muku albatka Amin."


"Allahumma Ameen."


"Kuje ki kai shi parlor. Kayan kuma abule (me aiki) ta tayaki da shi ku shigar da ciki cikin dakin na sa."


"Toym Hayateey."


"Kuje Hamid kaci abinci ka huta kaji ko?"


"Tohm... A... Hayateey."


Fita sukai amaal na gaba yana biue da ita a baya. Tamkar ya da kanwar sa da suke ciki daya saboda har wani kama sike da juna. 


Su kai sashen Hajiya jamila. A Wani parlor da daki acikin sa amaal ta kai shi an jere abinci a tsakiyar parlorn komai an tanada.


"Yaya ka zauna. Ga dakin na ka nan bari mu shigar da kayan..."


"Da kun bashi dearest sissy.." Ya fada yana sakar mata kawataccen murmushin sa.


"A'ah Yaya... Ka huta."


Abule ta karasa duka shigar da akwatin nasa da Ghana must go cikin dakin da ke parlorn me dauke da kayan daki farare kal da ratsin bula. Komai yayi test din maza ya gama haduwa fiye da kalamai. 


Sai kamshi turaren wuta ne ke tashi a dakin da gidan baki daya samfarin khajingru na kamfanin turarrukan yerwa incense and more. 


Fuchewa sukai suka bashi guri. Hamid ya daddebe abincin da zai iya ci yaci ya kora da lemuka da ruwa yayi hamdala. Dakan sa ya shiga daukar kayan ya fara futa da su.


Dakyar me aikin data gansa ya fito da tray yana neman kirchen ta karba tana bashi hakuri. Shjma ya shiga bata kasancewar yana da girmamawa.


Daki ya koma ya duba bandaki ya shiga ya watsa ruwa hade da yo wanka da dauro alwala. Ya sauya kayan sa zuwa jallabiya fara ya feshe jikin sa ko'ina da turare


Har ya fara curo kayan zai jera a closet ya jiyo masallacin dake cikin gidan an fara kirayen kirayen sallah. Don haka ya ajiye ya futa daga dakin. 


Yana fita sukai kichibus da amaal dake sakkowa daga bene. Suka sakarwa juna murmushi. 


Yadda yasa jallabiyar ta mukatar masa kyau sai ta tuno da labarawan madeenah. Tunanin ta ya gangaro kan Hisham da dramar da suka ci. Ta murmusa kawai fuskarta na fadadawa,


Hamid na daga kansa daga kasan a tsaye ya tsaya yana kallon yadda fuskarta ke fadaada da murmishin ta mai kayatarwa.


Yar kanwar tasa na birge shi saboda yadda take da nutsuwa da girmamawa. 


"Dearest sissy.... Amaal." Ya fada a ararrabe yana sake kafeta da idanuwan sa,


Da sauri ta dago daga tunanin data tafi,


"Na'am ya Hisham..."


"Hisham?"


"Au... Ya Hamid... Fita za kai.......?
_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


 _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post