Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 7

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 7

Baƙon Munafiki (Ba na Mutum Daya ba ne) page 7

_*BAKON MUNAFIKI!!!*_
_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_
                _👺🏡👩‍👩‍👦‍👦_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


  _©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

       __AREWABOOKS:MSSXOXO_
     _WATTPAD:MISSXOXO00_

_PAID PAGE:07_

_________
     Sai sha biyu saura kwata na dare tukun sannan suka fara yiwa Hajiya sai da safe suka nufi sashen su.

Amb. Junaid ya gyara zaman sa sosai a gefen Hajiya daga kasa. Ya cigaba da matsa mata kafafun nata ... Tana ta shi masa albarka. 

"Allah yayi maka albarka.... Nagode nagode nagode. Ka je ka huta."

"Ai ban gaji ba hajjaju. Ko dai bacci kike ji?"

"Baccin ma ina jin sa.. Kun shisshhga wajen yan uwan kuwa?"

"Wallahi bamu zazzagaya ba Hajiya. Nan kawai muka yada zango..Da safe in shaa ALLAHU zamu jajje. Da ke sanda muka zo din nasan yawanci suna wajen aiki. Basu dawo ba da yawan su shi yasa."

"Toh Allah ya temaka... Idan Allah ya kai mu goben sai ku shisshhga."..

"Aameen hajjaju"

Dan gyangyadi ta fara yi. Charbin hannun ta da take ja har ya fadi kasa, da sauri amb junaid ya sanya nasa hannun ya gyara mata natan da kuma carbun daya fadi a kasa yadakko ya ajiye mata a gefen ta.

Ta farko da sauri tana sosa gefen idon ta na dama,

"Junaidu.."

"Naam Hajiya..."

"Ba dai bacci ka fara ba ko.?"

Dan murmushi kawai yayi ya girgiza kansa cike da girmamawa. 

"Kaje ka kwanta dare ya ja."

"Toh Hajiya in shaa ALLAHU..."

"Kunyi magana da yan uwan na ka kuwa?"

"Eh munyi a group chat."

"Na'am.. Guru me?"

"Afuwan... A kafar sadarwa ta yanar gizo dinnan da ake yanzu.."

"Ma shaa Allah! Allah ya kara hade kawunan ku Amin."

"Amin Hajiya... Kuna samun su baba kuwa a waya ko har yanzu?"

"Ana samun su mana... Dazu ma nan an kira sadiya ta kawo mun muka gaisa. Wani abun ya faru ne? Kar ka boye mun"

Yayi saurin girgiza Kansa. Don ba yaso ko kadan ya sanyata cikin damuwa.

"Babu abunda ya faru hajiyar mu...Allah ya dawo dasu lafiya Amin."

"Allahumma Aameen."

Ya sake gyara zaman sa cike da girmamawa ya ce,

"Hajiya bari naje.... Kema gwara ki kwanta. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana da imanin Allah."

"Allahumma Aameen... Junaidu. Tare da ku duka. Allah ya tashe mu lafiya."

"Allahumma Aameen.."

Mikewa tayi ahankali da ga kishingiden da take... Tashi yayi ya dakko sandarta da ke gefen tv..

"Hajiya muje ko?"

"Da ka bari sadiya ta mun rakiyar ai."

"A'a Hajiya ... Bari nima na yau samu ladan."

Dariya sukayi baki daya. Ta rike gefen sandar. Ahankali ya shiga temaka mata har suka karasa dakin nata  

Ya bude marikin ya tura suka shiga ciki. Ko'ina a tsaftace yake a dakin sai karatun Qur'ani ne ke tashi a jikin wata mp3. 

Da sallama a bakunan su. Ahankali ya karasar da ita bakin babban gadon nata me lallausar katifa da babban bargo me laushi shima. 

"Sannu Allah yayi albarka kaji?"

"Nagode Hajiya. Allah ya saka mkli da alkhairi."

"Allahumma Aamin"

"Ko zaki shiga makewayi?(bandaki)"

"Sadiya zata ..."

"Ai Hajiya yau so nake na kwashe duka ganimar ladan da sadiyar nan ke samu dai. A temaka dai."

Batai musu ba tayi murmushi kawai hadi da saka hannunta akan sandar ya temaka mata ta mike. Ya kaita har cikin bandakin bayan sunyi adduar shiga bandaki.

Kan wata kujera da take zama aciki saboda ciwon kafafun ta ya zaunar da ita akai. Ya janyo babbar buta duk kuwa da ruwa a famfo ya cika ta mata ya ajiye a gabanta.

Sannan ya koma dakin yazauna zaman jiran ta. Data kammala ta dauro alwala ta saka sandar ta ta dogara har wajen kofar dakyar yana jiyo motsin ta ya tashi da sauri ya bude ya temaka mata suka koma cikin dakin.

"Allah yayi maka albarka..."

"Amin hajiyar mu."

Kwankwan Kwan...
"Salamu alaikum."

"Waalaykm Salam sadiya shigo."

Nan matashiyar budurwar ta shigo sanye cikin riga da zani . Da hijabi har gwiwa.

Tana shigowa ta dafe kirji tayi hamdala,

"Alhamdulillah.."

Hajiya tayi murmushi tana kallon ta,

"Kinata nema naa ko?"

"Eh saboda da kikace na bari su tafi sashen su tukun. Na fito naga ba kowa wallahi bakiji rai na na."

"Allah sraki sadiya. Bappan naku ne yace daren yau bari wai shima ya samu lada. Ya temaka mun na yo komai sai sallah da zanyi ta nafila sai na kwanta "

"Ma shaa ALLAHU... Barka da dare bappah."

"Barkan mu dai sadiya. Sannu da kokari da dawainiya da Hajiya Allah ya saka miki da alkhairi."

"Wallahi itace ke dawainiya da ni banida bakin godiya sai fatan Allah ya cika a mizani ya biya bukatu na alkhairi."

"Allahumma Aameen."

"Bari naje Hajiya zan dawo."

"To sadiya."

"Wallahi kaganta nan yarinya mai hankali da nutsuwa. Wannan yaron (Dan ta na fari) shine ya je har cikin shukaa na kandemi tahada jini da bappan ku Nata'ala (Dan uwan ta).. Ya auri kanwar mahaifiyar ta. Mai dakin sa ta uku. Gatanan komai ta dauke mun ga temako duk inda zani bata gajiyawa da rakiya."

"Allah sarki. Allah ya saka masa da alkhairi shima. Sadiya kema Allah ya saka da alkhairi. "

"Amin" suka hada baki wajen amsawa..

Ta fita daga dakin ta rufo musu kofar. Amb juanid ya mike shima bayan ya jira hajiyan ta yi nafila.

"Toh Hajiya bari na tafi. Allah ya tashemu lafiya"

"Aamin junaidu. Sannu da lokari kaji?"

Dan murmushi kawa yayi. Cike da girmamawa ya sake cewa,

"Allah ya kara miki lafiya da imanin Allah."

Ya sake dukawa yayi mata sai sa safe sai kma ya fiche ya nufi nasa sashen shi da iyalan sa.

Bayan ya shjga cikin bangaren na sa. Parlorn sa ya wuche ya zauna. Abubuwa masu tarin dama nata kwaranyo masa. Take kansa ya fara wani zugi da radadi kan barazanar fado masa saboda azabar ciwon da ya fara yi masa na kaife daya. 

Kansa ya daga sama yana tuno ko yau da safe ya kira lambar mahaifin na sa bata shiga kwata kwata. Haka sauran yan uwa da suke taren da mahaifin nasa kusan sati daya kenan a jere yana kira  ba sa daukar wayar ta sa. Har gwara Kawu Adamu shi yana ce masa baya kusa dasu ya fita...

Girgiza kai kawai yayi shi kadai. Ya saki murmushi mafi kuna a cikin zuciyar sa. 

Ahankali cikin sanyayyar muryar mai sauke da tarin damuwa marar misaltuwa can kasan makoshi yace,

"Toh Allah ka shiga lamuran mu... Ka yafe mana kurakuren mu Amin.."

Ya sake sauke wata ajiyar zuciyar a karo na uku kafin ya mike yana runtse idanun sa yayi cikin gidan.dake parlorn nasa shine a farko da bandaki sai kuma babban corridor dake dauke da flower vase da wani mudubi sai babbar kofar gidan mai kallon parlorn na sa. Dake daga wajen sa ana iya shiga sauran wajajen...

Dakin sa ya wuche kai tsaye. Bandaki ya fada ya tsaftace jikin sa hadi da daura alwala. Qur'ani ya dakko ya shiga karantawa.

Kafin bayan wani lokaci ya kai aya. Sai ya tashi yayi nafila. Ya bi lafiyar gado bayan yayi adduoin sa.

Abubuwa barkatai suka shiga masa yawo akai. Ya jima ainun yana tunane tunane kafin bacci barawo ya sache shi...


   _Afuwan..... Ma biya zafafa biyar..🙏_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*

_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276 
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k


  _MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post